24/09/2021
Ciyo Wa 'Yan Nigeria Bashi Zalunci Ne, Tare Da Cutar Da Mutanen Baya, Cewar Shaikh Nuru Khalil
Daga Muhammad Kwairi Waziri
A makon daya gabata ne Gwamnatin Tarayya za ta kara ciwo wani sabon bashi domin gudanar da ayyyuka ga al'ummar kasar, labarin ya tayar da hankulan jama'a a kafafen sadarwa.
Sheikh Nuru Khalid ya soki cin bashi da shugabanni a matakan gwamnatoci uku suke yi da sunan yin ayyukan raya kasa ko tallafawa rayuwar al’umma, inda ya bayyana hakan a matsayin zalunci.
Sheikh Nuru Khalid yace, damuwoyin da suke sa a ciyo bashi a Musulunce sun hada da matsalar yunwa a tsakanin al’umma, annoba ko rashin nagartattun cibiyoyin kiwon lafiya da na ilimi da kuma samar da tsaro, kamar yadda ya shedawa wakilin Aminiya.
“Haka kuma za a iya ciyo bashi don yin aiki kamar na gyaran hanyoyi idan ana rasa rayuka a dalilin muninsu,” inji malamin.
Sai dai ya ce, Allah Ya wadata Najeriya da hanyoyin kudin shiga da za ta iya magance mataslolin gaba daya ba tare da ta ciyo bashi ba, kamar yadda ya ce masana a harkar kudi s**a yi ittifaki a kai.
Ya ce, matsalar kasar nan ita ce almubazzaranci daga bangaren wadanda suke rike da dukiyar kasar, inda suke sayen motoci da gidajen alfarma da yadda suke gudanar da bukukuwa a tsakaninsu.
Malamin ya ce Najeriya ba ta da matsalar talauci sai kawai matsalar kekashewar zukatan shugabanninta da ma’aikata da suke almubazzaranci da dukiyar al’umma da Allah Ya damka musu.
“Munin bashi ya sa har Manzon Allah (SAW) yana kin yin Sallah ga mamaci matukar ya mutu dauke da bashi a kansa.
“Sannan saboda nauyin bashi Musulunci ya yarda a dauki dukiyar zakka a biya wa mai bashin.
“Ba daidai ba ne mutum ya ciyo bashin da ba zai iya biya ba, sai dai ya ce ’ya’yansa ko jikokinsa ne za su biya, saboda yin hakan tamkar ya jinginar da su ne kuma zalunci ne kasancewar idan s**a gaza biya, za a bautar da su,” inji malamin.
Limamin ya bayyana irin bashin da gwamnatocin kasar nan suke ci a yanzu wanda yawanci wa’adin biyan na kai har bayan sun sauka