14/09/2022
*YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA*
*SAURANSU*
Daga: Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
[Rahimahullah].
(Malam ya yi wannan bayanin ne a Tafsirin
Maiduguri na shekarar 2006M a cikin Suratut-
Taubah aya ta 100)
“Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai
‘siffatul ijza’ (ta wadatar), kuma wacce ake kira
‘siffatu kamal’ (ta kamala).
*Wankan Janaba a siffar sa ta kamala* shi ne:
Idan ka zo za ka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a
gabanka. Farkon abin da za ka fara yi shi ne:
Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke
hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a
cikin ruwan sai ka debo ka wanke gabanka, a
dai-dai lokacin da za ka wanke gabanka a lokacin
za ka kulla niyya ta wankan Janaba (Ko
waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke
gabanka ma’ana ka yi tsarki kenan, to daga nan
kuma sai ka yi alwala irin yanda kake alwala ta
sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah za
kayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan
za ka kyale shi ba za kayi shi ba, to daga nan sai
ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba
tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka
saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da
maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma
yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude
musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa
a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani
abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin
tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka
tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake
kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko ina a
kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko ina a
kanka.
To idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game
dukkanin jikinka da shi kana mai farawa da
bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan
na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko ina. To idan
ka yi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi
ne sai ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka
ta hagu shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro.
Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan Janaba.
In wankan Janaba ne haka za ka yi, in na Haila
ne haka za a yi in ma wanka ne na Biki haka
mace za ta yi, idan wankan Jumu’a ne ma haka
za a yi, wankan Idi ma haka za ka yi, banbanci
kawai shi ne NIYYA.
*Idan mutum zai yi siffa ta ‘Al ijza’* wadda ta
wadatar ba sai ka yi alawa a cikin ta ba, kana
zuwa ka yi niyyar yin wanka din kawai sai ka
dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko’ina,
in ma wani kududdufi ne ko rami ko “swimming
pool” sai ka yi tsalle ka fada a ciki, dama ka kulla
niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da za
ka yi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki da
kuma shaka ruwa a hanci da fyacewa. Shi kenan,
kuma ya halatta ka yi sallah da wannan wankan,
Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.
Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fi ka
kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fi ka
cikar kamala, ya fi ka lada.
Kasancewar ba a yi alwala ba ciki, wannan ka’ida
ce ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL
ASGAR) idan sun hadu da babban kari
(HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da babban
kari, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai bane
idan ka kawar da karamin a ce babban ma ya
tafi.”