19/11/2024
Da sunan Allah mai rahama, Mai jin kai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) da Alayensa da Sahabbansa da dukkan mabiyansa da kyautatawa har izuwa ranar karshe.
Bayan haka, Sakamakon wasu matsaloli da muke fuskanta cikin jam'iyyar PDP nima na yanke shawara kamar yadda jagoran mu a jam'iyyar PDP kuma shugaban qungiyar LADON ALKHAIRI Alhj. Musa Gafai Ya yanke
na aje dukkanin wani mukami da nike dashi a cikin jam'iyyar PDP tun daga matakin kungiya har zuwa mazaba
Daga karshe ina bukatar addu'ar fatan alkhairi da zaben abinda yafi Zama alkhairi 🙏