Popular News Hausa

Popular News Hausa we are giving consultancy services on media activities and other matters arise

13/06/2024
25/05/2024

MAIMUNATU Ɗan'auta, tsohuwar matar shahararren mawaƙi kuma jarumin barkwanci a Kannywood, Ado Isah Gwanja, ta yi aure a karo na uku jiya Juma'a. Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta tabbatar wa da mujallar Fim labarin auren, wanda aka ɗaura a asirce a Kano a daidai lokacin da hankalin jama'a ya raja'a ka...

An Gudanar Da Zaɓukan Fidda Gwani Na APC A Bakori, Faskari Da Dandume Da Ke Katsina.An gudanar da zaɓukan fidda gwani na...
19/05/2024

An Gudanar Da Zaɓukan Fidda Gwani Na APC A Bakori, Faskari Da Dandume Da Ke Katsina.

An gudanar da zaɓukan fidda gwani na jam'iyar APC domin cike guraben yan takarar ƙananan hukumomi da na kamsiloli a shiyar Funtua.

Jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Katsina ne s**a duba zaɓukan a shiyar.

A Danja, an gudanar da zaɓukan cikin kwanciyar hankali.

Alhaji Nura Rabi'u Dabai shi ne aka naɗa a matsayin shugaban kwamitin kula da zaɓen na jam'iyar ta APC, yayinda aka naɗa Habibu Sa'i a matsayin sakataren kwamitin.

Dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyar Funtua, Sanata Muntari Dandutse, mataimakin shugaban jam'iyar APC na shiyar Funtua Ibrahim Danjuma da kuma kwamishinan kula da harkokin addinai Isyaku Dabai sun duba yadda zaɓen ya gudana a ƙaramar hukumar Danja.

A jawabinsu jin kadan da kammala zaɓen, Muntari Dandutse, Isyaku Dabai da kuma Ibrahim Danjuma sun yaba ma wakilan masu zaɓe wanda s**a gudanar da zaɓen tare da nuna halin dattaku.

A nashi ɓangaren, ɗan takarar jam'iyar na ƙaramar hukumar Danja Rabo Tambaya ya bayyana jin daɗi bisa samun nasarar gudanar da zaɓukan fidda gwanin cikin nasara.

Rabo Tambaya Danja ya bayyana hanyar da jam'iyar ta yi amfani da ita wajen gudanar da zaɓen ƴan takarar a matsayin wadda tafi dacewa don tabbatar da zaman lafiya a cikin jam'iyar.

Rabo Tambaya ya ce jam'iyar APC a ƙarƙashin shugabancin Dr. Dikko Umaru Radda ta yi abinda ya k**ata don ciyar da jihar ta Katsina gaba.

Ya yaba ma gwamnan bisa ɗaukar ma matsalar tsaro a yankin matakai.

A tsokacinshi, shugaban Kwamitin kula da zaɓen Nura Rabi'u Dabai ya ce zaɓen nasara ce sosai.

A gudanar da zaɓukan a Bakori, Dandume da Faskari cikin nasara.

An zaɓi yan takarar na ƙananan hukumomi da kamsilolin ne ba tare da hamayya ba.

An bayyana Aminu Dan Hamida a matsayin wanda ya samu nasara zama ɗan takarar ƙaramar hukumar Bakori, Surajo Daudawa wanda ya samu nasara a Faskari, sai Bishir Gyazama wanda ya samu nasara a Dandume.

Shugaban Ƙungiyar Nagarta Rice Sellers and Processors Association Bakori Ya Yi Kira Ga Gwamnatoci Su Riƙa Samar Da Talla...
17/05/2024

Shugaban Ƙungiyar Nagarta Rice Sellers and Processors Association Bakori Ya Yi Kira Ga Gwamnatoci Su Riƙa Samar Da Tallafi Ga Manoma.

Shugaban ƙungiyar masu saida shinkafa ta Nagarta Rice Sellers and Processors Association Bakori Alhaji Auwal Ibrahim ya yi kira ga gwamnatin tarayya data jaha da su riƙa samar da tallafin noma ga manoma a cikin lokaci tun kafin faɗuwar damina.

Kamar yadda Auwal Ibrahim ya bayyana, hakan zai tallafa wa manoman sosai wajen noma kayan abinci a wadace damin cigaban ƙasa.

Shugaban ƙungiyar masu saida shinkafa na Nagarta Bakori ya ce akwai buƙatar gwamnatin jihar Katsina ta rinƙa damka tallafin noma ga ƙungiyoyin manoma domin tabbatar da cewa manoma na gaskiya ne kawai s**a amfana da shi.

Ya koka akan cewa, mafi yawan tallafin noman da aka samarwa a yankin, waɗanda aka ba alhakin rabon na bada shi ne ga yaransu na siyasa waɗanda ba manoma ba ne.

Ya bukaci gwamnatin Dikko Umaru Radda da ta lura da hakan ta, ɗauki mataki.

Ya kuma shawarci manoma da su rinƙa sayen kayan feshin gona daga diloli da aka sani, maimakon saye daga bara gurbi.

Auwal Ibrahim ya kuma yaba ma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tunubu akan karfafa noma a cikin gida, maimakon bari a shigo da abinci.

Ya ce matakin zai taimaka wajen zaburar da manoman cikin gida su noma abinci.

Gwamnan Jihar Katsina Ya Ƙaddamar Da Gidan Talabijin Da Radiyo Na Masusska A Dutsinma.Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru ...
14/04/2024

Gwamnan Jihar Katsina Ya Ƙaddamar Da Gidan Talabijin Da Radiyo Na Masusska A Dutsinma.

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da gidan talabijin da radiyo na intanet mai suna Masuss**a a Hayin Gada cikin garin Dutsinma.

Gwamnan ya samu wakilcin shugaban riko na ƙaramar hukumar Dutsinma Kabir Abdulsalam Shema.

Ya ce zasu kawo cigaba ga ilimin addinin Muslunci da karatun Alkur'ani a jihar nan.

Da yake magana, dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar Dutsinma Mohammed Khamis ya bayyana gamsuwa da matakan da gwamnatin jihar Katsina ta ɗauka domin shawo kan matsalar tsaro, ya yi kira da a ƙara samun haɗin gwiwa da taimako na mutane domin samun nasara.

Daraktan cibiyar nazarin Alkur'ani da bincike na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma wato FUDMA, Farfesa Jabir Musa Suleiman ya hakikance cewa, waɗanda s**a samu ilimi Alkur'ani na samun sauki yin kowane karatu.

Da yake tsokaci, shugaban hukumar kula da daraktoci, na makarantar ƙasa da ƙasa ta Masuss**a Sheikh Yahaya Ibrahim Masuss**a ya ce an kafa gidan talabijin da radiyon na yanar gizo ne domin a wayar da kan mutane akan ilimin addinin Muslunci, sanin muhimmancin neman ilimin addinin Muslunci da na zamani, koyon sana'o'i da kuma son zaman lafiya.

Hukumar Zaɓe A Jihar Katsina Ta Tunatar Da Jam'iyyun Siyasa Su Bi Tsare-Tsarenta Gabanin Zaɓen Ƙananan Hukumomin.Hukumar...
04/04/2024

Hukumar Zaɓe A Jihar Katsina Ta Tunatar Da Jam'iyyun Siyasa Su Bi Tsare-Tsarenta Gabanin Zaɓen Ƙananan Hukumomin.

Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Katsina ta tunatar da dukkan jam'iyyun siyasa a jihar da s**a nuna sha'awar shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi na ranar 15 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa da su tabbatar da ganin sun bi dukkan tsare-tsaren da hukumar ta basu.

Bayanin hakan ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Shehu Sarki Idris ya fitar.

Kamar yadda sanarwar ta ce a cikin tsare-tsaren da aka basu, an bada kwanaki 60 ga dukkan jam'iyyun siyasa su gudanar da zaɓen fidda don fito da yan takardarsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa an bayyana wa'adin da za a fara daga ranar 20 ga watan Maris zuwa 20 ga watan Mayun shekarar 2024.

Sanarwar ta ce gudanar da zaɓen fidda gwanin na jam'iyun siyasar ya yi daidai da sashe na 84 ƙaramin sashe na 1 na dokar zaɓe ta shekarar 2022 da aka yima gyaran fuska.

Haka kuma sanarwar ta ce ya zama wajibi kowace jam'iyar siyasa ta bada wa'adin kwanaki 21 ga hukumar kafin gudanar da aikace-aikacenta, kuma ya k**ata a gudanar da zaɓen fidda gwanin daidai da tanade-tanaden jami'yar.

Gwamnan Jihar Katsina Ya Bayyana Buƙatar Ganin An Ƙara Maida Hankali Ga Yin Addu'o'i.Gwamnan jihar Katsina ya bayyana bu...
12/02/2024

Gwamnan Jihar Katsina Ya Bayyana Buƙatar Ganin An Ƙara Maida Hankali Ga Yin Addu'o'i.

Gwamnan jihar Katsina ya bayyana buƙatar ganin an ƙara maida hankali ga yin addu'o'i a wuraren taron addinai domin samun zaman lafiya a jihar dama ƙasa baki ɗaya.

Dikko Umaru Radda ya sanar da hakan ne a lokacin walimar yaye ɗaliban makarantar Madarasatul Ahbab Tudun Matawalle da ke cikin birnin Katsina.

Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren ma'aikatar kula da harkokin addinai Dr. Surajo Abukur, ya yaba ma gudunmawar da shugabannin addinai ke badawa domin samun zaman lafiya a cikin al'umma.

Dikko Umaru Radda ya sake bayyana taimakon gwamnatinshi ga dukkan abubuwan da s**a shafi addinin Muslunci, tare da bada gudunmawar Naira 500,000 ga makarantar.

Shima da yake magana, babban jojin jihar Katsina Musa Danladi Abubakar ya buƙaci iyaye su tabbatar da ganin ƴaƴansu sun koyi Alkur'ani mai girma domin cigaban al'umma baki ɗaya.

Musa Danladi Abubakar ya yi kira ga majalisar dokokin jihar Katsina tayi bitar dokokin da s**a kafa hukumar kula da ilimin addinin Muslunci domin samar mata da ƙarin kariya ta yadda zata yi harkokinta yadda s**a dace.

Wanda ya assasa makarantar Malam Ibrahim Idris Gora ya ce an kafa makarantar ne domin koyar da ilimin addinin Muslunci, ya alaƙanta nasarorin da aka samu ga gwamnatin jiha da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya yi kira ga iyaye su bada ƙarin gudunmawa domin ba makarantar damar koyar da ilimi.

Sauran da s**a yi magana a wajen walimar sun haɗa da dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Katsina Aliyu Abubakar Albaba, ma'assasiyar gidauniyar Almuassatul Khairiya Hauwa Umaru Radda da kuma shuagaban ƙaramar hukumar Katsina.

Kwamishinan wasanni da cigaban matasa na jihar Katsina ya gana da zauren masu ruwa da tsaki akan sha'anin wasanni domin ...
12/02/2024

Kwamishinan wasanni da cigaban matasa na jihar Katsina ya gana da zauren masu ruwa da tsaki akan sha'anin wasanni domin samun hanyoyin da zasu kawo gyaran inganta sha'anin wasanni a jihar.

Daga Mustapha Rabi'u Garkuwa Media Assistan to the Governor, Ministry Of Youth and Sport Development.

Kwamishinan wasanni da cigaban matasa na jihar Katsina Hon. Aliyu Lawal Shargalle ya yi ganawa ta musamman da zauren masu ruwa da tsaki akan sha'anin wasanni na Jihar Katsina domin samun hanyoyin da zasu kawo gyara dazai inganta sha'anin wasanni a Jihar Katsina.

Yayin Jawabinshi ƙwamishinan wasanni da cigaba matasa ya bayyana cewa an kira taron na masu ruwa da tsaki karon farko domin tattaunawa akan matsalolin da sha'anin wasanni yake fuskanta musamman a Jihar Katsina domin samun shawarwari daga masana al'amuran wasanni akan hanyoyin da Gwamnatin Jihar Katsina zata bi da zasu inganta sha'anin wasanni a Jihar

Masu ruwa tsaki akan sha'anin wasanni da masana al'amura wasanni da shugabannin ƙungiyoyin daga ɓangarori daban daban da s**a samu halartar taron sun bada shawarwari da dama akan hanyoyin da Gwamnatin zata yi amfani dasu domin dawo da martabar wasanni musamman wanda ake gudanarwa a ƙasashen duniya, wanda yanzu ba'a bugawa a Jihar Katsina

Ƙwamishinan wasanni Hon. Aliyu Lawal Shargalle ya ƙara jaddada kudirin Gwamnatin Mal. Dikko Umaru Raɗɗa na ƙoƙarin ɗauko matasa ƴan Jihar Katsina da suke da fasaha akan wasanni daban daban domin basu dama zama cikakkun ƴan wasa a ƙungiyoyin wasanni na Gwamnatin Jiha, Hon Aliyu Lawal Shargalle ya ƙara alƙawari kawo wasu sabbin tsare tsare na shigowa da sauran wasanni da aka bari baya wanda ake a faɗin duniya.

Hakazalika ƙwamishinan ya bayyana cewa ma'aikatar wasanni zatayi kirkiri wani sabon tsari zai ɗaga darajar filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium zuwa wani mataki dazai baiwa filin damar zama wani sashe na musamman da sauran ƙasashen duniya zasu riƙa zuwa a kallon wasanni da yawon shaƙatawa, sai gina hotel tare da jawo manyan kamfanunuwa na duniya su zuba hannu jarinsu dazai ƙara taimkawa wasannin.

Taron ya samu halartar babban sakataren ma'aikatar matasa da wasanni Alh. Sirajo Mika'ilu, Alh. Kabir Rimi Kadmashi shugaban ƙungiyar Katsina United, Amb. Habibu Yusuf, Alh. Abubakar Rimi, Alh Muhammad Daha Faruk Umar, Alh. Aliyu Sarkin Magina shugabannin ƙungiyoyin wasanni daban daban, daraktocin ma'aikatar tare da sauran masu ruwa da tsaki a sha'anin wasanni a Jihar Katsina.

Rohotonni daga ƙaramar hukumar Kankara na cewa an gudanar da zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓe 16 da ke mazaɓar Garagi.An...
03/02/2024

Rohotonni daga ƙaramar hukumar Kankara na cewa an gudanar da zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓe 16 da ke mazaɓar Garagi.

An bada rohoton cewa, an samu fitowar masu kaɗa kuri'a sosai masamman ma mata.

Hakazalika, tawagar jami'an tsaro daban-daban sun taimaka wajen samar da tsaro a lokacin zaɓen.

Wakilin namu ya bayyana cewa, akwatin kada kuri'a sun fara isa cibiyar tattara sak**akon zaɓe da misalin ƙarfe 03:15:pm.

Mai ba gwaman jihar Katsina shawara akan kafafen yaɗa labarai Munneerat Gwanda wanda ta jagoranci tawagar yan jarida zuwa rumfar zaɓen Tsamiyar Jino ta 1, ta 2 data 3, ta bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da zaɓen masamman ma yadda mata s**a fito da yawa.

Tunda farko saida jami'in zaɓen ƙaramar hukumar Yunusa Abdu ya ce an raba kayan zaɓen tunda misalin ƙarfe 4 na asuba a yau Asabar gaban masu ruwa da tsaki da wakilin jam'iyyu.

Yunusa ya ce an buga zaɓen ne tsakanin Shehu Dalhatu Tafoki na jam'iyar APC da takwaranshi na jam'iyar PDP Moh Jamilu.

Assalamu alaikum,Suna na Aliyu Rufa'i. Ina mika godiya ta gare ku bisa yadda kuka sadaukar da lokacinku da dukiyar akan ...
29/01/2024

Assalamu alaikum,

Suna na Aliyu Rufa'i. Ina mika godiya ta gare ku bisa yadda kuka sadaukar da lokacinku da dukiyar akan hidima ta na gode. Allah ya bar zumunci.

Matasan Arewa Sun Buƙaci Da A Kori keyamo, Da Gwamnan Babban Bank Sak**akon Sauyawa Hukumomi Wurare.Gungun kungiyoyin ha...
26/01/2024

Matasan Arewa Sun Buƙaci Da A Kori keyamo, Da Gwamnan Babban Bank Sak**akon Sauyawa Hukumomi Wurare.

Gungun kungiyoyin hadakar arewa sunyi kira kan sauke ministan zarga-zirgar jiragen sama Festus Keyamo da Kuma gwamnan babban bankin Nigeria Yemi Cadoso bisa ga yunkurin su na sauyawa ma'aikatun su wurare, k**ar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.

Kungiyar kula da walwala da jin dadin masu hakar ma' adanai ta kasa reshen jihar katsina  ta rushe shuwagabanninta.Mukad...
22/01/2024

Kungiyar kula da walwala da jin dadin masu hakar ma' adanai ta kasa reshen jihar katsina ta rushe shuwagabanninta.

Mukaddashin shugaban kwamitin amintattu na kungiyar mustapha Abdulmumini Danbaiwa, ya bayyana haka a cikin wata sanarwar bayan taro da ya karanta bayan kammala taro da shuwagabani da mambobin kwamitin zartaswa a anan katsina.

Ya bayyana cewa rushe shuwagabannin ya biyo bayan karewar wa'adin shuwagabannin na shekaru 4 k**ar yadda kudin tsarin mulkin kungiyar ya tanadar.

mustapha Abdulmumini Danbaiwa, yayi nuni da cewa kwamitin amintattu zai kafa kwamitin rikon kwarya don tafiyar da harkokin kungiyar.

Haka nan kuma ya ce za'a kafa kwamitin da zai shirya tare da gudanar da zaben shuwagabannin kungiyar.

Asibitoci Huɗu da Makarantun Biyu Za su Amfana Da sabbin Motoci daga Sanata Ahmed Babba Kaita Daga Shafin Sanata Ahmed B...
19/01/2024

Asibitoci Huɗu da Makarantun Biyu Za su Amfana Da sabbin Motoci daga Sanata Ahmed Babba Kaita

Daga Shafin Sanata Ahmed Babba Kaita

Sanata Ahmad Babba Kaita ya bayyana a shafin sa na kafar sadarwa ta Facebook cewa wasu cibiyoyin kiwon lafiya da ilimi da wasu kayayyaki.

Kamar yadda ya bayyana waɗanda da za su amfana harda hukumar kwashe gobara za su samu sabbin motoci domin inganta ayyukan su na Yau da kullum.

A cewar sa, gobe asabar ne za a yi wani ɗan kwarya kwaryar bikin ƙaddamar da waɗannan motoci domin fara aiki da su

Ga jerin cibiyoyin kiwon lafiya da da Makarantun da za su amfana da wannan gudunmawa k**ar yadda ya bayyana;

1. Akwai baban asibitin Katsina (Katsina General Hospital)

2. Akwai kwalejin gwamantin tarayya da ke Daura (Federal Polytechnic Daura)

3. Akwai makarantar gwamnatin tarayya ta Horas da masu aikin kashe Gobara ta Kankia (Federal Fire Training School, Kankia)

4. Akwai asibitin kula da marasa lafiya da ke Sandamu (Comprehensive Heath Center, Sandamu)

5. Akwai asibitin kula da marasa lafiya da ke ƙaramar hukumar Mai'adua (Comprehensive Health Center Mai'adua)

6. Akwai kuma Baban asibitin Kankia (General hospital Kankia)

13/01/2024

Dambe ke nan da Shagon Dan Zuru da kuma Luck Lolon Dan Ƙasar Ingila

Ku bayyana mana ra'ayin ku a comment

EMBLEM:Gwamnan Jihar Katsina Ya Ƙaddamar Da Asusun Taimaka Ma Tsaffin Sojoji.Gwamnan jihar Katsina ya ƙaddamar da asusun...
12/01/2024

EMBLEM:
Gwamnan Jihar Katsina Ya Ƙaddamar Da Asusun Taimaka Ma Tsaffin Sojoji.

Gwamnan jihar Katsina ya ƙaddamar da asusun taimaka ma tsaffin sojoji don bunƙasa rayuwarsu.

Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da asusun ne a dakin taron sakatariyar jihar Katsina wanda ke zama shagulgulan bikin tunawa da yan zaman jiya na shekara-shekara.

Gwamnan da ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Katsina Abdullahi Garba Faskari, ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan ɗaya cikin asusun.

Tunda farko, shugaban ƙungiyar tsaffin sojojin Najeriya reshen jihar Katsina ya yi bayani akan mahimmancin makon tunawa da yan mazan jiya.

Ahmad Hussaini ya yi kira ga gwamnati ta gyara masu sakatariyarsu, ta saka ƴaƴansu makarantar koyar da sana'o'i, tare magance ma ƙungiyar matsalar mota hawa.

Bikin ƙaddamarwar da asusun ya samu halartar manyan mutane da s**a haɗa da sarkin Katsina wanda ya samu wakilcin Madawakin Katsina, kwamishinan wasanni da bunƙasa rayuwar matasa, kwamishinan bunƙasa karkara da cigaban al'umma, masu ba gwamna shawara, kwamishinan yan sandan jihar Katsina, kwamandan birget ta 17, kwamandan sojin sama, membobin ƙungiyar tsaffin sojojin, da sauransu.

12/01/2024

Kotun Kolin ta tabbatar da nasarar Abba Gida-Gida

An Shawarci Al'ummar Jihar Katsina Da Suyi Koyi Da Sauran Jahohi Wajen Gudanar Da Ayyukan Hakar Ma'adanai Bisa Doka Da O...
07/01/2024

An Shawarci Al'ummar Jihar Katsina Da Suyi Koyi Da Sauran Jahohi Wajen Gudanar Da Ayyukan Hakar Ma'adanai Bisa Doka Da Oda.

An shawarci al'ummar jihar Katsina da suyi koyi da sauran jahohi wajen gudanar da ayyukan hakar ma'adanai bisa doka da oda domin cin ribar Albarkatun kasar da Allah ya huwace ma jihar.

Wani masani akan hakar ma'adanai dan Asalin jihar Shehu Muhammad Saani ya bada shawarar acikin wata zantawa da manema labarai a katsina.

Ya kokan akan yanda al'ummar jihar suke watsin da dumbin albarkatun kasar da jihar keda su wanda ya k**ata ace anyi amfani dasu yanda ya dace domin bunkasar tattalin arziki al'umma.

Shehu muhammad Sani yayi bayani akan ayyukan hanyoyin gudanar da ayyukan da s**a shafi hakar ma'adanai.

Sai dai ya alakanta rashin bin hanyoyin da doka ta tanadar wajen amfani da albarkatun kasa akan karancin wayarma da al'umma kai akan hanyoyin gudanar da ayyukan hakar ma'adanai daga kungiyar kula da harkokin ma'adanai wanda keda alhakin sanya ido akan ayyukan ma'adanai.

Masanin ya jaddada bukatar da ake da ita ga kungiyar da ta rika fadakar da al'umma akan harkar ma'adanai kan ka'ida don cin moriyar albarkatun kasa daga gwammati da kuma su kansu al'umma.

Yana mai ra'ayin cewa hakar ma'adanae kan ka'ida zae taimaka wajen magance kalubalen tsaro, samar da ayyukan yi hadi da bunkasa tattalin arzikin al'umma.

Haka zalika zai taimakawa jahar wajen rage dogaro da kudaden shigar daga man fetur.

Daga nan kuma Shehu muhammad Sani ya yabama gwamnatin jiha mai ci yanzu bisa damuwarta don tabbatar da ana gudanar da ayyukan hakar ma'adanai kan ka'ida don ribantar albarkatun kasar da jihar keda su.

Tinubu Ya Amince Da N28.78tn A Matsayin Kasafin Kuɗin 2024.Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kasa...
01/01/2024

Tinubu Ya Amince Da N28.78tn A Matsayin Kasafin Kuɗin 2024.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira Tiriliyan 28.78.

Waɗanda s**a halarci hannun, akwai shugaban majalisar dattawa, Goodswill Akpabio; Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudden; Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun; da kuma ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, Abubakar Bagudu, k**ar yadda majiyar Popular Hausa ta jaridar Premiumtimes ta bayyana.

Gwamnatin Katsina Zata Yi Haɗin Gwiwa Don Magance Shan Miyagun Ƙwayoyi.Gwamnatin jihar Katsina ta sha alwashin yin haɗin...
01/01/2024

Gwamnatin Katsina Zata Yi Haɗin Gwiwa Don Magance Shan Miyagun Ƙwayoyi.

Gwamnatin jihar Katsina ta sha alwashin yin haɗin gwiwa da ƙungiyar tuntuɓa ta Katsina don shawo kan shan miyagun ƙwayoyi da aikata sauran laifuka tsakanin matasa.

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ne ya bayyana hakan a wajen taron farko da ƙungiyar ta shirya kuma ya gudana a ɗakin taron shugaban ƙasa da ke nan Katsina.

Taron tattaunawar nada nufin tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki akan illar da ke tattare da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, da kuma gano mafita akan matsalar.

Dikko Umaru Radda da ya samu wakilcin mataimakinshi Faruq Lawal ya bayyana cewa shan miyagun kwayoyi shi ne matsalar da ke addabar lafiya, ilimi, tattalin arziki, da kuma ƙwaƙwalwar mutane.

Ya ƙara da cewa tana taimakawa wajen aikata laifuka a cikin al'umma.

Faruq Lawal ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya da ta jiha suna ƙoƙari wajen yaƙi da matsalar.

Mataimakin gwamnan ya yi nuni da cewa bada jimawa ne gwamantin jihar Katsina ta kafa jami'an tsaron al'umma da hukumar HISBA tare da sanya masarautun gargajiya da shugabannin addinai a ciki don yaƙi d matsalar.

Daga nan sai ya yaba ma ƙoƙarin ƙungiyar tuntubar ta Katsina bisa ƙoƙarin yaƙi da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.

Shirin BESDA Haɗin Gwiwa Da Ma'aikatar Ilimin Jihar Katsina Sun Buɗe Taron Ƙara Ma Juna Sani.Shirin nan na ilimi mai sam...
01/01/2024

Shirin BESDA Haɗin Gwiwa Da Ma'aikatar Ilimin Jihar Katsina Sun Buɗe Taron Ƙara Ma Juna Sani.

Shirin nan na ilimi mai samun taimakon banki duniya wato BESDA haɗin gwiwa da ma'aikatar kula ilimin bai ɗaya dana sikandire ta jihar Katsina sun buɗe taron ƙara ma juna sani na kwana 3 a ranar 31 ga watan Disambar 2023.

Shirin nan na ilimi mai samun taimakon banki duniya wato BESDA haɗin gwiwa da ma'aikatar kula ilimin bai ɗaya dana sikandire ta jihar Katsina sun buɗe taron ƙara ma juna sani na kwana 3.

Mahalarta 6 ne s**a je taron da s**a fito daga ƙananan hukumomi 7 na jihar nan.

Da yake jawabi, shugaban hukumar bayar da ilimin bai ɗaya ta jihar Katsina Dr. Kabir Magaji ya ce mahalarta taro zasu horas da malamai 1,500.

Shugaban hukumar ya ce ana tsare-tsaren ganin kowane malami ya samu horon da ake buƙata domin cimma abinda aka sanya gaba.

Da take jawabi a lokacin, babbar sakatariyar ma'aikatar Ilimi Mairo Usman Muhammad ta ce ma'aikatar zata duba yadda hukumar SUBEB ke gudanar da ayyukanta.

A saƙonshi na godiya, sakataren hukumar bayar da ilmin bai ɗaya ta jihar Katsina Dr. Isah Zakari ya bayyana jin daɗi ga gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda, ma'aikatar ilimi da kuma hukumar bayar da ilimin bai ɗaya.

Kamar yadda s**a bayyana, bada horon zai bunƙasa ƙwazon malami a cikin aji.

Kungiyar Katsina United Ta Bada Haƙuri Ga Masoyanta Sak**akon Wasan Da Aka Fafata Da Bayelsa United.Shuwagabannin kungiy...
28/11/2023

Kungiyar Katsina United Ta Bada Haƙuri Ga Masoyanta Sak**akon Wasan Da Aka Fafata Da Bayelsa United.

Shuwagabannin kungiyar kwallon kafar Katsina United sun bada haƙuri ga dubban masoyan ƙungiyar sak**akon wasan da aka fafata da Bayelsa United

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in yada labarai na ƙungiyar Nasir Sani Gide ya sanyama hannu.

Ban haƙurin ya zo ne daga shugaban riƙo na ƙungiyar Alhaji Kabir Danlami Rimi bayan kunnan doki da ƙungiyar tayi a gida da Bayelsa United

Alhaji Kabir Danlami Rimi da yake jawabi akan sak**akon da basu yi tsammani ba, ya sha alwashin yin iya ƙokari bisa jagorancinshi na ganin anyi abinda ya k**ata musamman a lokuttan wasannin ƙungiyar na gida

Kabir Danlamin ya kara da godiya ga ɗinbin magoya bayan da suke halartar filin wasan na Muhammad Dikko don gane ma idanunsu wasannin kungiyar da kuma ƙoƙarin su da soyayyar da suke nunawa, Kwamitin rikon ya sha alwashin cigaba da magance duk wata matsalar da zata iya kawo naƙasu a lokuttan wasannin ƙungiyar na gida

Shugaban ya kara da tabbatar da ganawa da Masu Horarwa Kungiyar don tattauna hanyar da za,a bullo wajen fidda jerin Yan wasan ta da kuma tabbatar da bada dama ga Yan wasan da sauka chanchanta don samun mafita da cigaban Kungiyar

Danlamin ya ce a karo na biyu zasu cigaba da bin hanyoyin nema ma ƙungiyar mafita da zata ciyar da ita matakin gaba ta kowane ɓangare.

An sake zaɓar Umar Jibril Bindawa a matsayin shugaban kungiyar masu lalalurar ji ta Jihar Katsina.An gudanar da zaɓen ci...
25/11/2023

An sake zaɓar Umar Jibril Bindawa a matsayin shugaban kungiyar masu lalalurar ji ta Jihar Katsina.

An gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, kuma ba tare da hamayya ba a ofishin shiya na bunƙasa rayuwar matasa da ke bayan babbar asibitin Katsina.

Sauran jami'an da aka zaba sun haɗa da Mustapha Awwalu a matsayin mataimakin shugaban kungiyar, Mamuda Muhammad babban sakataren kungiyar, Muhammad Hadi a matsayin mataimakin babban sakataren kungiyar, Murtala Aliyu a matsayin ma'ajin kungiyar, Muhammd Bello a matsayin mai tsawatarwa da kuma Awwalu Isa Malumfashi a matsayin mai magana da yawun ƙungiyar.

Sauran su ne Maryama Yahaya a matsayin sakatariyar kuɗin ƙungiyar, Kabir Sambo a matsayin jami'in ƙungiyar na shiyyar Katsina, Ahmad Usman a matsayin jami'in ƙungiyar na shiyyar Funtua, Abubakar Aminu Jifatu a matsayin mai binciken kudi na ƙungiyar, Nafisa Sule a matsayin shugabar mata ta ƙungiyar, Zahara'u Salisu a matsayin mataimakiyar shugabar mata ta ƙungiyar, Lawal Isah Kambarawa a matsayin shuagaban matasa na ƙungiyar da kuma Aminu Usman as sakatare mai kula da walwala na kungiyar.

An bada rohoton cewa, zaɓen ya gudana gaban jami'an tsaron yan sanda, jami'an Civil Defence, Jami'an DSS, iyayen kungiyar, da dai sauransu.

Kungiyar Kwallon Kafar Katsina United Ta Sake Samo Maki A Wasanin Waje.Kungiyar dai ta raba maki ne da ta kwarar ta  Enu...
20/11/2023

Kungiyar Kwallon Kafar Katsina United Ta Sake Samo Maki A Wasanin Waje.

Kungiyar dai ta raba maki ne da ta kwarar ta Enugu Rangers bayan sun tashi wasa babu ci a filin wasa na Akwa city a cigaba da wasannin karshen mako na gasar kwararru ta premier.

Wannan dae shine karo na farko da kungiyar keyin cancaras a gida tun bayan fara kakar wasa ta wannan shekarar.
Da yake zantawa da manema labarai mai horar da kungiyar katsina United Bishir Sadauki ya bayyana gamsuwar shi bisa rawar da yan'wasan s**a taka.

Ya kuma alakanta nasarar bisa gudumuwa da kuma goyan bayan da shuwagabannin kungiyar suke baiwa kumgiyar.

Bishir sadauki wanda ya tabbatar da cigaba da jajircewa don cigaba da kasancewa a mataki na sama, ya kuma godema al'ummar jihar bisa goyan bayansu da addu'oi da suke yima kungiyar.

Da wannan nasarar dai kungiyar tana a mataki na 9 da maki 12.

Rundunar Sojin Sama Sun Yi Magana Akan Rikicin Jami’ansu Dana EFCC.Rundunar sojin saman Najeriya ta mayar da martani kan...
18/11/2023

Rundunar Sojin Sama Sun Yi Magana Akan Rikicin Jami’ansu Dana EFCC.

Rundunar sojin saman Najeriya ta mayar da martani kan rikicin da ya barke tsakanin jami'anta dana hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a jihar Kaduna, a ranar Juma'a.

Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta ruwaito yadda jami’an sojin sama s**a mamaye hukumar EFCC ta Kaduna domin a sako wasu jami’anta da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta k**a.

Da yake amsa ma wakilin jaridar Dailytrust tambaya, mai magana da yawun rundunar sojin saman, Edward Gabkwet, Air Commodore, ya ce rundunar sojin na ci gaba da nazarin lamarin.

“A yanzu ina nazarin lamarin,” abinda Gabkwet ya shaida wa shaida wa jaridar Dailytrust ta saƙon wayar salula.

KATSINA WOMEN JOURNALISTS CONDEMNS ALLEGED SEXUAL ASSAULT ON FEMALE JOURNALISTS BY GM KATSINA STATE RADIO AND CALL FOR A...
16/11/2023

KATSINA WOMEN JOURNALISTS CONDEMNS ALLEGED SEXUAL ASSAULT ON FEMALE JOURNALISTS BY GM KATSINA STATE RADIO AND CALL FOR ACTION.

The attention of the Nigeria Association of Women journalists, katsina state Chapter ( NAWOJ), has been drawn to Alleged sexual assault on Female journalists at katsina state Radio.

This Alarming Trend represents a gross violation of human rights and an attack on Female journalists at their workplace.

We sincerely appreciate the Effort of the state Governor Malam Umaru Dikko Radda on immediate action in setting up a committee to investigate the matter, and we hope the committee will do their work without being bias .

And we want the State government to investigate the previous workplaces the said person in question how he has been sexually assaulting other female workers there and take profer action against him. Because people like him are not expected to be working under any official positions.

The query given to 18 Persons at the Katsina state Radio on 8th November,2023 was also part of his usual intimidation process for female journalists among the 18 Persons.

For the avoidance of any doubt katsina state NAWOj will exploit all legitimate windows to continue to frown at gender bias in the workplace as well as ensure that the perpetrators for this obvious victimization of Fauziya face the full wrath of the law

We will not allow the victimization of Journalists especially Women journalists to continue in our society by few individuals who have no respect for gender equality.

Signed
Hannatu Mohammed
Chairperson

Faith Awa Maji
Secretary

Korar Ma'aikaciyar Kajuwal Da Hukumar Gidan Radiyon Jihar Katsina Ta Yi.Hankalin kungiyar yan jarida mata ta Najeriya re...
15/11/2023

Korar Ma'aikaciyar Kajuwal Da Hukumar Gidan Radiyon Jihar Katsina Ta Yi.

Hankalin kungiyar yan jarida mata ta Najeriya reshen jihar Katsina ya karkata ga korar da aka yi ma ɗaya daga cikin ƴaƴanta mai suna Fauziyya Lawal Mamman Dawai ma'aikaciyar kajuwal ba bisa ka'ida ba.

Ba zamu ci gaba da amince ma wasu mutane da basu san darajar mata ba suna cin zarafin yan jarida masamman ma mata.

Shugaban gidan radiyon jihar Katsina ne ya kori Fauziyya daga aiki saboda rashin halartar taro a ranar da abun ya faru. Mun fahimci cewa tana aikin fassara labarai a lokacin da aka sanya ta yi wanda za'a karanta da misalin 12:pm na rana a dakin shirya labarai.

A irin wannan hali, ana buƙatar ma'aikatan da ke aiki a dakin shirya labarai su sanar da shugabanni ko mataimakan shugabanninsu cewa suna aiki domin a sahale masu zuwa taron. Kuma Fauziyya ta bi wannan matakai, amma aka yi watsi da hakan.

Daga hujjar da kungiyar yan jarida mata ta Najeriya NAWOJ ta tattara, Fauziyya ta cika dukkan sharuɗɗan da s**a wajaba kanta, kuma ta yi aikinta a dakin shirya labarai ba tare da barin wurin ba domin zuwa halartar taron. Ba zamu ƙi amincewa da yiyuwar samun matsalar fahimta ba, amma za'a ɗora alhaki akan Fauziyya bisa samun matsalar isar da saƙo, abinda cikin rishin sa'a ya yi sanadiyar hukumar gidan radiyon ta kore ta daga aiki ba tare da yi mata adalci ba.

Abokan Fauziyya daban-daban sun tabbatar da cewa, ta kasance mai matuƙar amfani ga gidan radiyon jihar Katsina shekaru da dama da s**a gabata, kuma mutum ce mai ƙwarewa, maida hankali ga aiki, da dai sauransu. Bayan jawo mata mutumtawa da ƙauna da irin wannan gudunmawar ta yi ga abokan aikinta ƴan jarida a jihar Katsina, an bada rohoton cewa hakan ya jawo ma gidan radiyon ƙima.

Korar da aka yi mata kwatsam bisa dalilin wani abu ɗaya da ya faru ba abun amincewa ba ce, kuma ya k**ata a maida ta bakin aiki bada ɓata lokaci ba, k**ar yadda majiyar Popular News Hausa ta bayyana.

Domin kauce ma dukkan wani shakku, kungiyar yan jarida mata ta ƙasa reshen jihar Katsina zata yi amfani da dukkan hanyoyi domin yin fatali cin zarafin mata a wuraren aiki, tare da tabbatar da cewa waɗanda s**a ci zarafin Fauziyya sun fuskanci hukunci.

Sa hannu
Hannatu Mohammed
Shugaba

Faith Awa Maji
Sakatariya

Maitaimak**a Gwamnan Katsina Akan Alummomi Mazauna Jihar Ya Jaddada Kudirin Gwamnati Wajen Magance Matsalolinsu.Maitaima...
14/11/2023

Maitaimak**a Gwamnan Katsina Akan Alummomi Mazauna Jihar Ya Jaddada Kudirin Gwamnati Wajen Magance Matsalolinsu.

Maitaimakawa gwamnan jihar katsina na musamman akan alummomi mazauna katsina ya jaddada kudirin gwamnati mai ci yanzu wajen magance matsalolin al'ummomin da ba yan'jihar ba.

Chukwuka Okoye ya fadi haka ne alokacin da ya halarci bikin ranar al'adu ta kungiyar yan'Barno mazauna jihar da ya gudana a dakin taro na tsohon gidan gwamnati.

A jawabin Mai baiwa gwamnan shawara ya jaddada muhimmancin cigaba da zaman lafiya da juna a jihar dama kasa baki daya.

Ya kuma roki goyan baya da hadin kai yan'asalin barno mazauna jihar wajen aiwatar da ayyukan cigaba da bullo da tsare-tsare da zasu amfani mazauna jihar ba tare da banbancin kabila ba.

Chukwuka Okoye yayi amfani da bikin wajen bayyana godiya ga gwamnan bisa yadda ya baiwa alummomin da ba yanjihar ba dama acikin gwamnatin shi.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Popular News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Popular News Hausa:

Videos

Share