Danmasani online Tv and Radio

Danmasani online Tv and Radio Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Danmasani online Tv and Radio, Media/News Company, Katsina.

Sabon Comedy  Masana Episode 4Dukko Radda ba Gafiliba ne Shiyasa Allah yabashi TakaraAsha kallo lafiya๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป
10/10/2022

Sabon Comedy
Masana Episode 4
Dukko Radda ba Gafiliba ne Shiyasa Allah yabashi Takara
Asha kallo lafiya

๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป๐Ÿ‘Ž๐Ÿป

Dukko Radda ba Gafilibane shiyasa Allah ya Amshi Addu'ar sa

Sabon Comedy  Masana Episode 4Dukko Radda ba Gafiliba ne Shiyasa Allah yabashi TakaraZan sakeshi anjima da kare 10 na da...
10/10/2022

Sabon Comedy
Masana Episode 4
Dukko Radda ba Gafiliba ne Shiyasa Allah yabashi Takara

Zan sakeshi anjima da kare 10 na dare insha Allah a YouTube channel din Freedom media crew

IBRAGEEM KHALIL
05/10/2022

IBRAGEEM KHALIL

05/10/2022

Nigeria's leading provider of prepaid, postpaid mobile, & 4G services. Recharge your prepaid mobile & pay your postpaid bills online.

01/10/2022
Lokacin da Real Madrid ta sayi Eden Hazard, Darajarsa a kasuwa tana akan Yuro miliyan 150, a halin yanzu, an kiyasta dar...
29/09/2022

Lokacin da Real Madrid ta sayi Eden Hazard, Darajarsa a kasuwa tana akan Yuro miliyan 150, a halin yanzu, an kiyasta darajarsa akan Yuro miliyan 12 kacal, wadda ta ragu sosai. (Diarioas)

[Fagen Wasanni]

Na Shirya Don Neman Jagoranci Mai Kyau da kyakyawar makomar Kasaโ€“ "Inji Tinubu. Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-ma. A jiya ...
29/09/2022

Na Shirya Don Neman Jagoranci Mai Kyau da kyakyawar makomar Kasaโ€“ "Inji Tinubu.

Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-ma.

A jiya ne ne aka fara gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 a hukumance a fadin kasar Nan.

Tinubu ya bayyana cewa; yana gayyatar daukacin 'yan Najeriya da su Mara masu baya shi da maigirma Sanata Kashim Shettima kan wannan tafiya mai kayatarwa kuma mai matukar muhimmanci yayin da s**a tsara manufofinsu na Sabunta makomar al'ummar da kasa Najeriya a 2023.

A cikin makonni da watanni masu zuwa, za mu ci gaba da daukar burinmu na samarwa da Najeriya mai, aiki, lafiya, kwanciyar hankali da wadata a kowane bangare na Najeriya da kuma ci gaba da gabatar da shirinmu na jagorantar kasar nan zuwa kyakkyawar makoma.

Al'ummarmu tana tsaye a bakin kololuwar nuna goyon bayanmu don haka muna matukar godiyawa Al'ummar Nijeriya.

Dole ne mu nuna cewa; mun koyi da gyara kura-kurai, Dole ne mu zama masu hikima, dole ne mu zama masu hankali; dole ne mu zabi ci gaba. Dole ne mu fifita hankali fiye da tunani.

Mun shirya kuma a shirye muke, tare da mataimakina, don samar da shugabancin da zai zaburar da kasarmu ga daukaka da sabbin tunani, sabbin dabaru da hangen nesa.

Ina kira ga daukacin 'yan Najeriya da su taya mu.

Halin da ake ciki game da shirye shiryen fara Yakin Neman zaben kujerar Shugaban kasa a Nijeriya_____Alh Atiku Abubakar ...
29/09/2022

Halin da ake ciki game da shirye shiryen fara Yakin Neman zaben kujerar Shugaban kasa a Nijeriya
_____

Alh Atiku Abubakar na jami'iyyar PDP da โ€˜yan kwamitin yakin neman takaran sa sun hallara a babban dakin taro na ICC a garin Abuja domin bikin rantsarwar da komitin da fara Yakin Neman zaben 2023.

Alh Ahmad Bola tanibu na jami'iyyar APC mai mulki.
A lokacin da Atiku yake shirin kaddamar da kwamtin neman zabe โ€˜dan takaran jamโ€™iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya tafi kasar London

Komitin Yakin Neman zaben Jamโ€™iyyar APC ta dakatar da soma aikin kamfe, sannan tace za ta fadada kwamitin yakin zaben shugaban kasa wanda yake kunshe da mutum 422.

Peter Obi na jami'iyyar LP - :

Rahoton ya nuna shi ma Peter Obi mai neman mulkin Najeriya a zaben 2023 a karkashin LP bai fara yakin neman zaben shugaban kasa a iiyan ba.
Arabambi Abayomi wanda jigo ne a tafiyar Obi, bai fadi ranar da za su soma kamfe ba, amma yace a ranar da s**a fara yakin zabe, za su fitar da manufofinsu.

Santa Rabiu Musa kwankwaso na jami'iyyar NNPP - :

Sanata Rabiu Kwankwaso bai fito bai kaddamar da โ€˜yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba. Shima a halin yanzu.

Mark Zuckerberg ya yi asarar fiye da rabin dukiyarsaKamfanin Meta ya ba da rahoton raguwar kudin shigar da yake samu a k...
28/09/2022

Mark Zuckerberg ya yi asarar fiye da rabin dukiyarsa

Kamfanin Meta ya ba da rahoton raguwar kudin shigar da yake samu a karon farko cikin watan YuliImage caption: Kamfanin Meta ya ba da rahoton raguwar kudin shigar da yake samu a karon farko cikin watan Yuli

A karon farko tun cikin shekara ta 2015 mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya fita daga jerin mutum goma mafi arziki a Amurka.

Wani rahoton mujallar Forbes da ke tantance mutanen da s**a fi kudi a duniya, ta ce Zuckerberg ya yi asarar fiye da rabin dukiyarsa โ€“ kimanin dala biliyan 76.8 tun cikin watan Satumban 2021, inda ya fadi daga mataki na uku a jerin mutum 400 mafi arziki a Amurka zuwa mataki na 11.

Da dukiyar da ta kai dala biliyan 57.7 a jerin masu kudin Amurka na bana, Zuckerberg na bin bayan Jim Walton da tsohon magajin birnin New York Michael Bloomberg.

Rahoton ya ce a duk fadin Amurka babu mutumin da ya kai Mark Zuckerberg tafka asara a shekarar da ta wuce. Forbes ta alakanta raguwar dukiyar tasa da faduwar darajar hannayen jarin kamfaninsa na Meta wanda ya ragu da kashi 57% tun bara.

BBC

SHA'ABAN YA GANA DA WASU MANYAN MUTANEN YANKIN KASASHEN LARABAWA A KOKARINSA NA KAWOWA KANO CIGABA.Bayanin Dan Takarar G...
28/09/2022

SHA'ABAN YA GANA DA WASU MANYAN MUTANEN YANKIN KASASHEN LARABAWA A KOKARINSA NA KAWOWA KANO CIGABA.

Bayanin Dan Takarar Gwamnan Jahar Kano a Tutar Jam'iyyar ADP Mallam Shaaban Ibrahim Sharada Kenan Lokacin Da Yake Ganawa Da Wasu Manyan Mutanen Yankin Larabawa,

Mutanen Sun Hada Da Manajan Shiyya Na Bankin Riyadh Dr. Mamdud Abdu, Sannan Akwai Babban Wakilin Kasar Indonesia Dr. Nasrullah Sannan Kuma Akwai Babban Wakilin India Wanda Yazo Da Wakilcin Kasashe Kamar Haka
Kasar Iriteria, Masarautar Saudi Arabia Da Kuma Kasar Thailand.

Anyi Taron Ne a Riyadh Babban Birnin Kasar Saudi Arabia.

Allah Ka Bawa Sha'aban Gwamnan Jahar Kano.

Rabi'u Garba Gaya
Media Aide To Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara.

Tsohon gwamnan jihar Katsina Barr Ibrahim Shema, dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam'iyyar PDP Sen Lado, Majigiri d...
28/09/2022

Tsohon gwamnan jihar Katsina Barr Ibrahim Shema, dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam'iyyar PDP Sen Lado, Majigiri da sauran wasu jigajigan jam'iyyar PDP daga nan jihar Katsina sun halarci bikin kaddamar da yan kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar yau a birnin tarayya Abuja

Tsohon dan wasan Kamaru, Alexandre Song ya kammala aikin gina otal dinsa a Kamaru.  A halin yanzu yana taka leda a AS Ar...
28/09/2022

Tsohon dan wasan Kamaru, Alexandre Song ya kammala aikin gina otal dinsa a Kamaru. A halin yanzu yana taka leda a AS Arta Solar7 a Djibouti. [Fagen Wasanni]

'Yan ta'adda 90,000 ne s**a mika wuya a cikin shekara daya- ZulumGwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce sama da 'yan...
28/09/2022

'Yan ta'adda 90,000 ne s**a mika wuya a cikin shekara daya- Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce sama da 'yan Boko Haram 90,000 ne s**a mika wuya a cikin shekara guda da ta gabata a tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da kungiyar IS a yammacin Afirka.

Gwamnan, a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron da aka shirya a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 a birnin New York, ya ce โ€˜yan taโ€™addan da radin kansu sun mika wuya ga rundunar soji domin kwance damara, da kawar da tsattsauran raโ€™ayi da sake hadewa.

Zulum ya ce wannan bai taba faruwa a koโ€™ina a duniya ba, kuma yanzu an kawo karshen taโ€™addanci.

โ€œIna so in sanar da wannan taron cewa a cikin shekara daya da ta gabata, gwamnatin jihar Borno, da kuma gwamnatin tarayya ya zuwa yanzu ta karbi tubabbun โ€˜yan Boko Haram da ISWAP sama da 90,000,โ€ inji shi.

Cikin hotuna: Yadda aka yi zana'idar marigayi Umar Malumfashi, Ka-fi-Gwamna na shirin Kwana Casa'in da Allah Ya yi wa ra...
28/09/2022

Cikin hotuna: Yadda aka yi zana'idar marigayi Umar Malumfashi, Ka-fi-Gwamna na shirin Kwana Casa'in da Allah Ya yi wa rasuwa a kiya Talata a garin Kano

Allah Ya gafarta masa Ya sa ya huta

Jamie Carragher: "Idan da gaske kun kall wasannin Arsenal wannan kakar, suna k**a da za su iya zama masu fafutukar lashe...
28/09/2022

Jamie Carragher: "Idan da gaske kun kall wasannin Arsenal wannan kakar, suna k**a da za su iya zama masu fafutukar lashe Premier League.
Na kasance babban masoyin Mikel Arteta koyaushe. Ina tsammanin za su iya kusancin da yawa na lashewa fiye da abin da mutane ke ba su yabo. "

[Fagen Wasanni]

Rade Radin Rashin Lafiyar Tinubu Ban sani ba ko Tinubu yana Najeriya - Oshiomhole Mataimakin daraktan kwamitin yakin nem...
28/09/2022

Rade Radin Rashin Lafiyar Tinubu Ban sani ba ko Tinubu yana Najeriya - Oshiomhole

Mataimakin daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamโ€™iyyar "All Progressives Congress" (APC) Adams Oshiomhole a ranar Laraba ya ce, bai da masaniya ko dan takarar shugaban kasa na jamโ€™iyyarsu Bola Ahmed Tinubu yana Najeriya.

Ba na kai masa rahoto kullum, ban da tabbacin ko yana nan ko a'a," in ji Mista Oshiomhole a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television's Politics Today.

Mista Oshiomhole, tsohon shugaban jamโ€™iyyar APC na kasa, ya ce har yanzu ba a kaddamar da taron yakin neman zaben shugaban kasa na jamโ€™iyyar ba saboda shugaban kasar baya nan a birnin New York.

Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ya bar kasar ne zuwa kasar Birtaniya gabanin yakin neman zabe amma tawagarsa ba ta tabbatar da tafiyar a hukumance ba.

Da Duminsa: Dikko Radda ya fito ฦ™arara ya fadi dalilin da ya sa ya zabi Faruk Jobe a matsayin wanda zai masa mataimakiDa...
28/09/2022

Da Duminsa: Dikko Radda ya fito ฦ™arara ya fadi dalilin da ya sa ya zabi Faruk Jobe a matsayin wanda zai masa mataimaki

Dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam'iyyar APC Dr Dikko Umar Radda ya bayyana dalilan da s**a sa ya zabi Hon Faruk Lawal Jobe a matsayin wanda yake so ya yi masa takarar mataimakin gwamnan jihar Katsina na jam'iyyar APC.

Daga cikin dalilan da ya bayyana, ya ce Faruk Lawal Jobe ya fito daga shiyar da gwamna Masari ya fito ta Funtua, kuma shi ne wanda ya yi takarar gwamna sannan a 2019 ya fito takarar Sanata bai samu ba.

Dr yadda ya fadi hakan ne a yau, lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishin kamfen dinsa dake cikin birnin Katsina.

Daga karshen amsa tambayar Dikko Radda ya ce yana da tabbaci game da gogewar Hon Jobe, ta yadda duk inda zai wakilci al'ummar jihar Katsina kowane dan jihar zai bugi kirji ya ce lallai wannan ya cancanci zama gwamna ko mataimakin gwamna

KWANKWASO /BISHOP ISSAC 2023Yau 28/09/2022.An kaddamar da Yakin Neman zabeA Nijeriya.Wasu jihohi ne kuke Ganin. Kwankwas...
28/09/2022

KWANKWASO /BISHOP ISSAC 2023
Yau 28/09/2022.

An kaddamar da Yakin Neman zabe
A Nijeriya.

Wasu jihohi ne kuke Ganin. Kwankwaso/bishop Issac 2023
Zasu iya lashewa?

Address

Katsina

Telephone

+2348167406963

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Danmasani online Tv and Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Danmasani online Tv and Radio:

Videos

Share