![An kaddamar da shuwagabannin kungiyar Ƴan Jarida ta NOMF masu amfani da kafafen sadarwa na zamani a KatsinaƘungiyar masu...](https://img3.medioq.com/626/059/630159306260592.jpg)
04/02/2025
An kaddamar da shuwagabannin kungiyar Ƴan Jarida ta NOMF masu amfani da kafafen sadarwa na zamani a Katsina
Ƙungiyar masu amfani da kafafen sadarwa na zamani mai suna National Online Media Forum (NOMF) reshen jihar Katsina ta gudanar da taronta na farko tare da zaɓar shugaban riƙon ƙwarya na ƙungiyar.
Taron wanda aka gudanar a wannan Lahadin a ofishin kafar sadarwar Reality New TV da ke Mangal Plaza Ƙofar Ƙaura a jihar ta Katsina.
A yayin jawabin manufar taron, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Umar Lawal Funtua, ya bayyana cewa, dalilin kafa ƙungiyar shi ne, inganta aikin jarida a tsakanin kafafen sadarwar zamani da kuma ceto aikin daga hannun ɓata garin mutane da ke tashi rana tsaka su k**a aikin ba tare da sanin mak**arsa ba.
Shi ma a yayin jawabinsa, jim kaɗan bayan karɓar takardarsa a matsayin shugaban riƙo na jihar, Abubakar Shafi'i Alolo, shugabn kamfanin kafar sadarwa ta Mobile Media Crew wanda Nasiru Umar ya amsa a madadinsa, ya bayyana cewa zai gudanar da aiki tare da ƴaƴan ƙungiyar cikin adalci da kuma kawo ci gaba mai ɗorewa.
Waɗanda s**a halarci taron sun haɗa da shugabannin kafafen yaɗa labaran da wakilansu Inda aka tattauna muhimman batutuwa tare da karɓar shawarwari daga mahalarta taron kan yadda tafiyar za ta kasance. Haka zalika s**a lashi takobin kawo gyara da kare martabar aikin jarida ta amfani da kafafen sadarwar na zamani.
Jerin kafafen sadarwar na zamani da s**a halarci taron, sun haɗa da;
Jadawali TV, Fitila, Online, Popular News, Reality News TV, Salwa RTV, Jakadiya Online Media, Xsound Media, Albishir Media, Verified Mews, Mobile Media Crew, FBC, Danmasani Online Radio, Katsina Post, Hikaya News Paper da Katsina Times.
A ƙarshen taron an ƙawata shi da miƙa takardar k**a aikin jagorancin ƙungiyar a matakin jiha ga Abubakar Shafi'i Alolo.