Flash News Hausa

Flash News Hausa Ya Allah dan girman zatinka ya Allah dan matsayin Manzon ka Annabi Muhammad S.A.W Allah kasa mucika da Imani, ya Allah kasa muna cikin bayinka yantantu.
(1)

Harin Kuje: Sheikh Zakzaky yace ba wata Kungiya an yine da Sunan A Kashe Mutane  "Ko lokacin da s**a kai hari gidan yari...
13/07/2022

Harin Kuje: Sheikh Zakzaky yace ba wata Kungiya an yine da Sunan A Kashe Mutane

"Ko lokacin da s**a kai hari gidan yarin Kuje sun yi amfani da bindigogi nau'i uku duk ba wanda ake siyar dasu a kasuwa, sun yi amfani da RPG wanda ake harbin Tanka dashi irin bindigan da akan goya a kafaɗa tana da baki biyu in harsashin ya fita wuta zata fito ta baya, dan haka ba a tsayawa ta bayan ta in ana harbawa, to da ita s**a harbi get ɗin. A yaki ake amfani dashi wajen harbin Tanki (tankan yaƙi) dan in RPG ya fita harsahin in ya kutsa cikin ƙarfe sai ya shiga cikin Tankan ƙarfe sannan yake fashewa, to amma waɗannan wai suna dashi."

"Sannan kuma akwai wata irin nau'in bindiga da ake ce mata AA wanda take harba manya-manyan harsasai, sannan kuma banda wannan da AK me jigida din nan wanda take sarrafa kanta tana ɗiban harsashi, to da irinsu s**a je su goya akan mota sai wurrr.... To dan Allah in zaka samu bindiga ka ɗan riƙe yar ƙarama ina kai ina faɗa da waɗannan? To amma dai baza su fi ƙarfin Allah ba, Allah mai iko ne kan komai. To muma kuma abin mamaki mu "problem" irin waɗannan ba k**awa suke aiki akanmu ba, da RPG s**a je har da ma tankan sun harba, sun sa tanka irin wanda ake harbi a yaƙi s**a dinga harbawa akan mutane, wanda sam ya saɓawa ƙa'ida. Tsakanin soja da soja ake amfani da waɗannan mak**an to akan farar hula s**a je s**a yi, to yanzu wannan ɓarnar da suke yi ba yanda za ayi me hankali ya yarda cewa wai wata ƙungiya ce wanda ba a san inda take ba sai kawai tazo tayi wannan aiki. Da mak**an da muka san cewa ba yanda za ayi ka iya sarrafa waɗannan mak**an sai an maka training (Training na Soja) dan mak**an sojoji ne, dashi suke zuwa su dira gari suyi biji-biji da garin, manufar shine kawai a hallaka mutane."

– Sheikh Ibraheem Zakzaky a cikin jawabinsa na ganawa da shugabanni da Limaman al'ummar garin Abuja a jiya Talata a gidansa dake Abuja.

Duk Kiristan Da Ya Zabi Jam’iyyar APC A Zaben 2023 Ya Juyawa Yesu Baya, Cewar Wani Fasto, Bishop Irabo Wisdom
13/07/2022

Duk Kiristan Da Ya Zabi Jam’iyyar APC A Zaben 2023 Ya Juyawa Yesu Baya, Cewar Wani Fasto, Bishop Irabo Wisdom

Ƴan Bindiga Sun Kashe Da Sace Ƴan Yawon Barka Da Sallah A Katsina’Yan bindiga sun kai hari kan wasu ’yan yawon Sallah s*...
13/07/2022

Ƴan Bindiga Sun Kashe Da Sace Ƴan Yawon Barka Da Sallah A Katsina

’Yan bindiga sun kai hari kan wasu ’yan yawon Sallah s**a kashe daya daga cikinsu tare da yin garkuwa da wasu biyu a Jihar Katsina.

’Yan bindigar sun kai wa ’yan yawon Sallan da ke hanyarsu ta dawowa daga Katsina hari ne a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.

’Yan yawon sallan sun yi mugun gamon ne a wani shingen tare ababen hawa da bata-garin s**a kafa a kan hanyar.

Matashin da ’yan bindigar s**a kashe, Anas Adamu, dalibin ajin karshe ne a Kwalejin Ilimi da ke Katsina.

Wani abokin mamacin, Muhammad Aliyu, ya ce bayan ’yan bindigar sun kafa shingen a cikin dare ne motocin matasan s**a kutsa cikinsu a bisa kuskure.

“Bayan bukukuwan Sallah s**a baro Katsina da misalin 8:30 na dare zuwa Jibiya.

“A hanya, sai motar da ke gaba ta ga shingen a kurkusa ta fada ciki, amma direban ya yi sa’a, ya sake dawo da motar kan t**i, s**a tsere.

“Mota ta biyu da ta uku kuma ’yan bindigar sun riga sun far musu, s**a harbi daya direban a kafa s**a yi kokarin sace sauran mutum biyu da ke cikin motar

“Shi kuma mamacin ya yi kokarin tserewa amma s**a k**a shi s**a rika saran shi, s**a karya mishi hannu da kafa sannan s**a cinna mishi wuta, a haka ya rasu.”

Mun tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, amma ya ce ba shi da labari.

HAPPY SALLAH: Tsohuwar Jarumar Fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu Tsamiya
13/07/2022

HAPPY SALLAH: Tsohuwar Jarumar Fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu Tsamiya

Buhari Ya Gaggauta Yin Murabus Idan Mulkin Ya Yi Masa Wahala__— HURIWAKungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, HURIW...
13/07/2022

Buhari Ya Gaggauta Yin Murabus Idan Mulkin Ya Yi Masa Wahala__— HURIWA

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, HURIWA, a ranar Talata ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus nan take idan aikin ya yi masa wahala.

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, HURIWA, a ranar Talata ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus nan take idan aikin ya yi masa wahala.

HURIWA ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar yayin da yake kira ga Buhari da ya yi murabus don rage barnar da “rashin iyawarsa” zai janyowa kasar idan ya tsaya har zuwa ranar 29 ga Mayu, 2023.

Jaridar Dimokuradiyya ta rahoto cewa Buhari a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana shekaru bakwai da yayi akan karagar mulki a matsayin masu tsauri.

Shugaban, wanda ya ce “ya kosa ya sauka daga mulki”, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC, ‘yan majalisar dokoki, da shugabannin siyasa a gidansa da ke Daura a Jihar Katsina, a lokacin bikin Sallah.

A wani bangare na sanarwar HURIWA k**ar haka: “Bayan amincewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi cewa fadar shugaban kasa na da tsauri kuma yana da muradin zuwa, kira ya je ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, daga kungiyar kare hakkin bil’adama ta Najeriya da ya yi gaskiya ya yi murabus a yanzu. don rage ɓacin ransa da rashin iya aikinsa da rashin aikin yi zai sa ƙasar ta halaka idan ya tsaya har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, 2023.”

Yan Najeriya Ne Masu Rura Wutar Ta’addanci Ta Hanyar Biyan Kudin Fansa – Garba ShehuGarba Shehu, babban mataimaki na mus...
13/07/2022

Yan Najeriya Ne Masu Rura Wutar Ta’addanci Ta Hanyar Biyan Kudin Fansa – Garba Shehu

Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce biyan kudin fansa da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ke yi na kara rura wutar ta’addanci a Najeriya.

Shehu wanda ya yi magana a gidan Talabijin na Channels TV a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce za a ci gaba da yin garkuwa da mutane har sai ‘yan Najeriya sun daina biyan kudin fansa sannan su kyale jami’an tsaro su yi aikinsu.

Ya ce, “Duk wadannan abubuwan da kuke fada game da masu garkuwa da mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma shugaban kasa ko a sakonsa na Sallah ya ambaci rokon da yake yi wa ’yan kasa da su tona asirin su (masu aikata miyagun laifuka), ya shaida wa jami’an tsaro inda a wasu lokuta kuma kuna iya tausayawa ƴan uwa a cikin wannan yanayi mai ban sha’awa.

“Babban abin da aka ba su na farko shi ne dawo da iyalansu kuma a shirye suke su biya, kuma sun biya kuma wadannan kudaden, ko wani ya so ko bai so ba, za su ci gaba da rura wutar ta’addanci, dole ne mu yi koyi da abubuwan da s**a faru sauran kasashen da idan kun biya ku ke rura wutar ta’addanci. “

“Kuna kara rura wutar sace-sacen jama’a kuma hakan zai ci gaba da tafiya har sai mutane kawai su kawar da kai a shirye su ba da damar jami’an tsaro.”

Shehu ya kuma yi magana kan harin da wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne s**a kai a gidan yarin Kuje.

Ya ce, “Ni dan Najeriya ne, ina da ’yan uwa da ke rayuwa a cikin al’umma, ba na zuwa daga wani waje, ina ji kuma ban taba ba da shawarar cewa babu wahala a kasar nan ba, ba a kowane wuri ko matsayi da ya nuna cewa babu laifi.”

Tonon silili: Anga agogon naira miliyan N455 a hannun gwamna Jihar Imo Uzodinma wacce zata iyawa dalibai gini mai ajujuw...
13/07/2022

Tonon silili:

Anga agogon naira miliyan N455 a hannun gwamna Jihar Imo Uzodinma wacce zata iyawa dalibai gini mai ajujuwa shida sau 75

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya saka agogon kasaita ta naira miliyan 455 a ziyarar daya kaiwa shugaba Buhari a Daura.

Gwamnan yana daya daga cikin gwamnonin da shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu ya jagoranta s**a kaiwa Buhari ziyara a Daura.

Wani ma’aikacin dake gina gidaje ne ya bayyana hakan cewa kudin agogon zai iya ginawa dalibai gini mai ajujuwa shida a cikinsa sau 74 amma banda kudin fili.

Kuma kudin zasu iya gina asibitoci kusan talatin kan naira miliyan 15 a kowane gini guda.

Dalibai da dama suna fama da matsalar ajujuwa da kuma karancin bencina makarantun su na jihar.

Ya Kamata Jaruman Fim Mu Rinƙa Auren Junan Mu, Cewar Zakiyya Ibrahim AbdullahiMe za ku ce?
13/07/2022

Ya Kamata Jaruman Fim Mu Rinƙa Auren Junan Mu, Cewar Zakiyya Ibrahim Abdullahi

Me za ku ce?

Jarumin Fina-finan Kannywood Kuma Mai Baiwa Gwamnan Jihar Kano Shawara Kan Farfaganda  Alhaji Mustapha Naburaska Tare Da...
13/07/2022

Jarumin Fina-finan Kannywood Kuma Mai Baiwa Gwamnan Jihar Kano Shawara Kan Farfaganda Alhaji Mustapha Naburaska Tare Da Iyalansa.

Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya, Bimbo Akinsanya, tace har a yanzu da take shekaru 52 bata ga nagartacce...
12/07/2022

Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya, Bimbo Akinsanya, tace har a yanzu da take shekaru 52 bata ga nagartaccen namijin da ya dace da ita ba.

A cewarta, matukar zata yi aure, tun a yayin soyayya zata lura da idon basira kan saurayin da kuma danginsa, don ba kowa bane ke da tarbiya tagari.

Namiji Nake So Amma Ba Ko Wanne Sakarai Ba, Wanda Bai Taba Taba Mace Ba Nakeso ~ Cewar Wannan BudurwarMe zaku ce Daga Ni...
12/07/2022

Namiji Nake So Amma Ba Ko Wanne Sakarai Ba, Wanda Bai Taba Taba Mace Ba Nakeso ~ Cewar Wannan Budurwar

Me zaku ce

Daga Nigerian News Hausa

Ango Honarabul Murtala NAK Da Amaryarsa Aisha KabirAllah Ya Ba Da Zaman Lafiya Da Zuri'a Dayyaba!
12/07/2022

Ango Honarabul Murtala NAK Da Amaryarsa Aisha Kabir

Allah Ya Ba Da Zaman Lafiya Da Zuri'a Dayyaba!

KE DUNIYA INA ZAKI DAMU: Babrisky Kenan Namijin Da Ya Rikidar Da Kansa Zuwa Jinsin Mata
12/07/2022

KE DUNIYA INA ZAKI DAMU: Babrisky Kenan Namijin Da Ya Rikidar Da Kansa Zuwa Jinsin Mata

12/07/2022

Babban Birnin Tarayya Abuja Da Jihar Nasarawa Nacigaba Da Kokawa Kan Tashin Kayan Abinci.

Jarumar Fina-finan Kannywood, Mansura Isah Tare Da Mahaifiyarta Da Kuma Ɗiyarta Iman Sani Danja
12/07/2022

Jarumar Fina-finan Kannywood, Mansura Isah Tare Da Mahaifiyarta Da Kuma Ɗiyarta Iman Sani Danja

Allah Sarki, Jiya Ba Yau Ba!Marigayi Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Muhammad Kabir Usman A Lokacin Da Ya Kaddamar Da...
12/07/2022

Allah Sarki, Jiya Ba Yau Ba!

Marigayi Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Muhammad Kabir Usman A Lokacin Da Ya Kaddamar Da Fara Digawa Yara Riga-kafi A Fadarsa Dake Kofar Soro A Ranar 9 Ga Watan Nuwamba, 2002

Idan Har Zan Fadi A Zaben 2023 To Kowa Ma Ya Fadi Amma Banda Tinubu, Cewar KwankwasoDaga Datti AssalafiyBisa alama Kwank...
12/07/2022

Idan Har Zan Fadi A Zaben 2023 To Kowa Ma Ya Fadi Amma Banda Tinubu, Cewar Kwankwaso

Daga Datti Assalafiy

Bisa alama Kwankwaso Bola Ahmad Tinubu yake yiwa kamfen ba kansa ba, mai neman fahimtar hakan ya nemi cikakken hiran da akayi da Kwankwaso a tashar Arise News TV.

Kwankwaso ya yabi Tinubu sosai duk da barnan da Tinubu ya yiwa 'yan Arewa a Lagos a wancan lokaci da su Marigayi Malam Ja'afar suke zazzafan khuduba a kansa, Kwankwaso yace yana tare da Tinubu tun daga shekarar 1992 har zuwa yau suna alaka.

Har Kwankwaso yana cewa wai idan ya rasa kujeran Shugaban Kasa to kowama ya rasa amma Tinubu ya samu bukata ta biya.

Magana ta gaskiya shi kansa Kwankwaso ya san cewa lokacinsa na neman takaran Shugaban Kasa baiyi ba, fitowarsa a yanzu daidai yake da yunkuri na tarwatsa kuri'un 'yan Arewa.

Abinda zai faru shine; Kiristocin sun duba sun lissafa sunga cewa suna da yawan da zasu iya kawo shugaban Kasa, shine sai s**a umarci Peter Obi ya fita daya PDP zuwa LP, sannan sai s**a tilastawa Kiristocin Nigeria yin rijistan katin zabe, s**a haramtawa duk kiristan da baiyi katin zabe ba shiga coci.

A lokacin da Musulmai zasu zabi Bola Tinubu, Musulmai zasu zabi Atiku Abubakar, Musulmai zasu zabi Kwankwaso, to an tarwatsa kuri'un Musulmin Nigeria kenan, an bawa Kiristocin Nigeria damar lashe kujeran shugaban Kasa.

Su kuma Kiristoci gaba dayansu Peter Obi zasu zaba, wannan shine ajandarsu tunda sunfi Musulmai katin zabe, don haka cikin sauki Peter Obi sai a wayi gari yayi nasara.

Babu shakka Kwankwaso mutum ne mai kirki wanda zuciyarsa take cike da tausayin talakawa, amma tsarinsa ba irin na 'dan siyasa da yake son zama shugaban Kasa a murdaddiyar Kasa irin Nigeria bane.

Dalili kuwa shine Kwankwaso bai yadda da tsarin uban gida siyasa ba, duk jam'iyyar da ya shigeta yana so ya zama shine yake da ta cewa a cikinta, dalili ne biyu shine, farin jinin Kwankwaso da tasirinsa a siyasa ya tsaya ne a Arewacin Nigeria, Arewan ma jihar Kano.

Kuma idan kishin Arewa ne babu dalil

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNTsohan Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Katsina Ya RasuAllah Ya Yi Wa Tsohan Ɗan Takarar Gwam...
12/07/2022

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Tsohan Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Katsina Ya Rasu

Allah Ya Yi Wa Tsohan Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Katsina A Karkashin Jam'iyyar PRP Alhaji Bashir Lawal Yar'adua Rasuwa.

Marigayi Alhaji Bashir Lawal Yar'adua Shi Ne Mai Hajara Farms Ya Rasu A Abuja A Daren Jiya Litinin Kuma Ya Tsaya Takarar Gwamna A Karkashin Jam'iyyar PRP.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Zamu fice daga tafiyar Tinubu tunda ya zabi Musulmi a matsayin Mataimakinsa__AbboTinubu ya ci amanar Kiristoci, ba zan c...
12/07/2022

Zamu fice daga tafiyar Tinubu tunda ya zabi Musulmi a matsayin Mataimakinsa__Abbo

Tinubu ya ci amanar Kiristoci, ba zan cigaba da mara masa baya ba tunda ya zabi musulmi mataimaki duk inji Sanata Abbbo.

" Za mu hakura da tafiyar Tinubu tunda ya zabi musulmi, mu kiristoci ba za mu yi tafiyar sa ba. Zan zabi abinda ya fi dacewa kasar mu ne ba siyasar zaben 'yan addini daya su yi takara ba.

*ALLAHU_AKBAR: Fitaccen MawakinAnnabi (S.A.W) Umar Adul'aziz Fadar Bege Kano Yau Yake cika Shekara 9 cif cif da Rasuwa."
12/07/2022

*ALLAHU_AKBAR: Fitaccen MawakinAnnabi (S.A.W) Umar Adul'aziz Fadar Bege Kano Yau Yake cika Shekara 9 cif cif da Rasuwa."

Masu Garkuwa da Fasinjojin Kaduna/Abuja sun bukaci kudin fansa N4.3 Billion a kan naira Milyan 100 kan duk mutum ɗayaYan...
12/07/2022

Masu Garkuwa da Fasinjojin Kaduna/Abuja sun bukaci kudin fansa N4.3 Billion a kan naira Milyan 100 kan duk mutum ɗaya
Yanzu haka dai akwai ragowar Fasinjojin 43, a wajen yan garkuwar

Yan ta’adda na neman a biya su N100m kudin fansa kan kowane fasinja, daga cikin fasinjoji 43 da aka sace a Kaduna, wadanda har yanzu suke hannunsu, inji rahoton jaridar The PUNCH.

An sanar da bukatar ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a makon jiya.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan da wasu da dama dauke da mak**ai s**a kubutar da wadanda ake zargin sun kitsa garkuwa da su daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Kungiyar IS da ke yammacin Afirka ta dauki alhakin kai harin a wani faifan bidiyo da ta fitar bayan sa’o’i 24.

A yayin harin, sama da mayakan Boko Haram 300, wadanda aka yanke wa hukunci da sauran fursunoni, ‘yan ta’addan ne s**a arce.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta sanya bayanan kwamandojin Boko Haram 64 a cikin ma’adanar bayanai ta Interpol da s**a tsere daga hannunsu a lokacin harin.

Mun ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, inda s**a kashe takwas tare da yin garkuwa da fasinjoji akalla 61.

A wani bangare na bukatunsu, sun bukaci a sako kwamandojin ‘yan ta’adda 15, da ‘ya’yansu da sojoji ke tsare da su da kuma wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba.

A ranar 12 ga watan Yuni ne ‘yan ta’addar s**a sako wasu mutane 11 da aka yi garkuwa da su bayan shafe kwanaki 75 a hannunsu, yayin da wasu bakwai s**a sake samun ‘yancinsu a ranar Asabar.

Rahotanni sun ce an sako wadanda lamarin ya rutsa da su ne ta hanyar taimakon mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna, Malam Tukur Mamu, wanda ke tattaunawa da mayakan.

Da yake karin haske kan lamarin a ranar Lahadi, wani dan uwan wadanda aka sace, wanda bai so a buga sunansa ba, ya shaida wa daya daga cikin wakilanmu cewa, ‘yan ta’addan na neman kowane iyali Naira miliyan 100 na kudin fansa domin a sako ‘yan uwansu.

Farashin abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi a AbujaFarashin kayan abinci na ci gaba da tashi  gwauron zabi a Abuja...
12/07/2022

Farashin abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi a Abuja

Farashin kayan abinci na ci gaba da tashi gwauron zabi a Abuja da jihar Nasarawa, inji rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN.

Wani bincike da NAN ta gudanar ya nuna cewa a Nasarawa da babban birnin tarayya, mazauna garin na cikin takaici saboda karin farashin kayan abinci.

Wani ɗan kasuwa a kasuwar Kubwa, Dini Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun wake kan Naira 27,000 amma yanzu a na sayar da shi kan Naira 49,000.

Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun shinkafar yar gida tsakanin N15,000 zuwa N20,000, inda ya ce a yanzu ana sayar da shi kan Naira 29,000, yayin da buhun shinkafar ƙasar waje da ake sayar da ita kan Naira 25,000 yanzu ta koma N34,000.

Buhun garri mai launin rawaya, wanda aka sayar akan N8,000, a halin yanzu ana sayar da ita kan N22,000 yayin da farar garri da aka sayar akan N6,000 a halin yanzu ana sayar da shi akan N17,000.

Suleiman ya ce buhun masara a baya ana sayar da shi kan N6,000 yanzu ya koma N20,000.

Ya alakanta hauhawar farashin kayan abinci da tsadar sufuri, wanda ya ce hakan ya shafi karfin saye, wanda hakan ya sa farashin kayan abinci ya tashi.

Yajin aikin ASUU ya isa haka nanShugaban ya yi kira ga ƙungiyar malaman jami’a ASUU da su janye yajin aikin da s**a shaf...
12/07/2022

Yajin aikin ASUU ya isa haka nan

Shugaban ya yi kira ga ƙungiyar malaman jami’a ASUU da su janye yajin aikin da s**a shafe watanni suna yi.

Buhari ya bayyana damuwa kan tasirin yajin aikin ga makomar ilimi da ci gaban Najeriya. Yana mai cewa “yajin aikin ya isa haka nan.”

Ya ce duk da ya fahimci buƙatunsu, amma za a ci gaba da tattaunawa yayin da ɗalibai ke ajin karatunsu.

Hotunan Ministan Sharia Na Najeriya Abubakar Malami(SAN) Da Amaryarsa Nana Khadija, Bayan An Daura Auren su Nana Khadija...
11/07/2022

Hotunan Ministan Sharia Na Najeriya Abubakar Malami(SAN) Da Amaryarsa Nana Khadija, Bayan An Daura Auren su

Nana Khadija Diya Ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Tana Da Shekaru 41

A Yanzu Ta Kasance Mata Ta Ukku(3) A Cikin Matan Ministan

Shin Gwamna Ganduje ya fifita siyasa a kan Hawan Nasarawa ne?A jihar Kano, wasu na zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar G...
11/07/2022

Shin Gwamna Ganduje ya fifita siyasa a kan Hawan Nasarawa ne?

A jihar Kano, wasu na zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da rashin nuna damuwa da al'adar Hawan Nasarawa da ke zama mafi muhimmanci a 'hawan' da Sarki ke yi a duk bikin Sallah. Bayanai na cewa a cikin shekaru 116 da aka fara wannan al'ada a Kano, kusan a kowacce shekara Sarkin Kano na kai wa gwamna gaisuwar Sallah a gidan gwamnati. Sai dai a wannan Litinin da aka yi Hawan Nasarawa, Gwamna Ganduje, bai karbi bakuncin Sarki ba, inda ya tafi Abuja domin halartar wasu muhimman tarurruka na kasa, a cewar majiyoyi na gwamnati, matakin da ya rage wa bikin armashi sannan ya haifar da cece-kuce. Duk da wannan bayani daga gwamnati, wasu mazauna Kano na zargin gwamnan da rashin mutunta gidan Sarauta, domin a ganinsu, babu wani abu mai muhimmanci da ke a Abuja, da ya kai girman Hawan Nasarawa a wurin mutanen Kano. Shin ya kuke kallon lamarin?

Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!Allah ya yiwa Babban Hakimin Kwami, Alh. Haruna Abdullahi (Ajiyan Gombe) rasuwa. Wan...
11/07/2022

Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!

Allah ya yiwa Babban Hakimin Kwami, Alh. Haruna Abdullahi (Ajiyan Gombe) rasuwa. Wannan Bawan Allah daya ne daga cikin Dattawan da Jihar Gombe ke tinkaho da su a doron kasa.

Muna addu'ar Allah ya jikansa da Rahama da sauran Magabatan mu Musulmai baki daya.

Zainab Bukar Kenan, Matashiyar Da Ta Lashe Wankar Sallah A Kafar Sada Zumunta Ta Twitter.Wane Fata Za Ku Yi Mata?
11/07/2022

Zainab Bukar Kenan, Matashiyar Da Ta Lashe Wankar Sallah A Kafar Sada Zumunta Ta Twitter.

Wane Fata Za Ku Yi Mata?

Ba Zan Iya Ci Gaba Da Shiga Tsakani Ba Wajen Neman A Sako Sauran Fasinjojin Da Aka Sace – Malam Tukur MamuBayanai sun yi...
11/07/2022

Ba Zan Iya Ci Gaba Da Shiga Tsakani Ba Wajen Neman A Sako Sauran Fasinjojin Da Aka Sace – Malam Tukur Mamu

Bayanai sun yi nuni da cewa har yanzu akwai sauran mutum 44 a hannun 'yan bindigar dajin.

Sa'o'i kadan da sakin karin mutane bakwai daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja Kaduna da 'yan-bindiga su ka sace, shugaban kamfanin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu wanda ya jagoranci sakin mutanen, ya ce ba zai kara shiga cikin maganar ba duk da ya ke ya tabbatar da cewa har yanzu akwai mutane 44 a hannun 'yan-bindigan.

A ranar Asabar ne dai labarin sakin mutane 7 cikin ragowar 51 dake hannun 'yan-bindigan da su ka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja Kaduna, ya bazu ko ina.

Malam Mamu ya ce ba zai kara tsoma baki game da maganar fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kadunan da ke hannun 'yan-bindigan ba saboda rayuwarsa ta na cikin hadari.

Sai dai duk da haka ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa sauran mutane 44 da ke hannun 'yan bindigan su nan a raye.

Wadanda aka saki a ranar dai su ne Sadiq Ango Abdullahi, wanda da ne ga shugaban kungiyar dattawan Arewachin Najeriya da Muhammad Dayyabu P**i, tsohon shugaban karamar hukumar Ikara kuma shugaban wata hukuma a jihar Kaduna, sai Bosede Olurotimi da Abubakar Zubairu da Alhassan Sule da Aliyu Usman da kuma Muhammad Abuzar Afzal, wanda dan asalin P**istan ne.

Malam Sani Lawal, daya ne daga cikin masu magana da yawun 'yan'uwan wadanda aka sacen kuma ya ce yanzu duk mutane bakwan da aka saki suna gida tare da iyalansu.

Malam Lawal ya ce mutane bakwan da aka sako duk sun rame kuma dun yi baki amma dai suna cikin hankalinsu don har sun kawo sakon gaisuwa daga sauran wadanda su ka rage a hannun 'yan bindigan.

Tun ranar 28 ga watan Maris na wannan shekara ne 'yan-bindiga su ka datse jirgin kasan Abuja-Kaduna inda su ka sace mutane sama da sittin (60) sannan su ka kashe wasu kuma su ka bar wasu da raunika amma daga bisa su saki mutane 11 naya sakin wani dattijon da su ka ce saboda bashi da lafiya ne.

Address

Lay Out
Katsina
K/S

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Flash News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Flash News Hausa:

Videos

Share