24/04/2024
ALBISHIRIN KU MUTANEN GARIN MIYA...
GAYYATAR BUDE SABON MASALLACIN JUMA'A
(MASJIDU I'ILANI SUNNATIN NABAWIYYAH MIYA)
Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah reshen garin Miya Malam Halliru Muhammad, shugaban majalisar malamai Imam Sulaiman Yakub, shugaban agaji Alaramma Sabo Muhammad Danfulani, a madadin dukkan shugabannin kungiyar, suna farin cikin gayyatar al'ummar Musulmi zuwa wajen bude sabon Masallacin Juma'a wanda zai gudana kamar haka:
✓ Rana: Juma'a 17/10/1445AH (26/4/2024)
✓ Lokaci: 12:30 na rana
✓ Wuri: Masjidu I'ilani Sunnatin Nabawiyya
dake unguwar sabuwar Abuja kusa da ruwan bara Miya.
✓ Alkali Musa Abbas, shugaban kungiyar Izala na karamar hukumar Ganjuwa shine zai jagoranci sallah yayin bude Masallacin.
Malam Safiyanu Ahmad shine zai cigaba da jagorancin sallar Juma'a da sallolin kamsu salawat.
Za'a fara nasiha tun karfe sha biyu saura.
Allah ya bada ikon halarta, Ameen.
Jibwis Social Media
Ganjuwa LG Bauchi State