One News Hausa

One News Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from One News Hausa, Media/News Company, Federal low cost housing Estate, Bauchi.
(2)

ONE NEWS HAUSA Jarida ce dake kawo muku labarai da ɗumi-ɗumi gami da rahotannin cikin gida da na waje a cikin harshen Hausa daga Kamfanin 5STARS MEDIA PRODUCTION.

-Aikin mu domin al'umma ne.
-Burinmu kasancewa ji da ganin marassa galihu a ko ina.

12/01/2025

Budurwarsa ta cinƴe masa kuɗi sama da million 3.5 Kuma taki auren sa😫

Vedio: Tubeless Media

Tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello tare da gwamnan jihar mai ci, Alhaji Ahmad Usman Ododo cikin yanayin raha.
12/01/2025

Tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello tare da gwamnan jihar mai ci, Alhaji Ahmad Usman Ododo cikin yanayin raha.

Na kwashe shekaru ashirin ina fim a Amurka amma har yanzu a talauce na ke - Djimon HounsouShahararren jarumin Hollywood ...
12/01/2025

Na kwashe shekaru ashirin ina fim a Amurka amma har yanzu a talauce na ke - Djimon Hounsou

Shahararren jarumin Hollywood din nan Djimon Hounsou ya bayyana cewa ya na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki duk da sana'ar fim da ya ke yi sama da shekaru ashirin.

A wata hira da CNN a wani shirin su na matasan Afirka, a yau Asabar, Hounsou ya bayyana cewa ya na ganin cewa ana yi masa ƙwange a albashi kuma har yanzu ya na fama da talauci.

"Har yanzu ina fama yanayi a rayuwa. Na kasance cikin harkar shirya fina-finai sama da shekaru ashirin, tare da lashe lambobin girma na Oscar guda biyu da fina-finai da yawa, amma duk da haka, har yanzu ina fama da rashin kuɗi. Babu shakka ƙwangen albashi ake yi min," inji shi.

Wannan tonon silili ya ba wa mutane da yawa mamaki, ganin irin nasarorin da ya samu, gami da lashe lambar yabo ta Academy sak**akon kwazon saba fim din 'Blood Diamond' da 'In America'.

Daily Nigerian Hausa

TSUFA MAI ALBARKA: Malama Hauwa'u Usman kenan, mai shekaru 76 tana ɗaya daga cikin ɗaliban da s**a sauke Ƙur'ani a makar...
12/01/2025

TSUFA MAI ALBARKA: Malama Hauwa'u Usman kenan, mai shekaru 76 tana ɗaya daga cikin ɗaliban da s**a sauke Ƙur'ani a makarantar Hidaya dake Kaura Namoda a jihar Zamfara

Wanne fata za ku yi mata?

Fasahar AI ba barazana ba ce ga aikin jarida, Injiniya Abbas Abdullahi Injiniya Abbas Abdullahi ya bayyana cewa fasahar ...
11/01/2025

Fasahar AI ba barazana ba ce ga aikin jarida, Injiniya Abbas Abdullahi

Injiniya Abbas Abdullahi ya bayyana cewa fasahar AI ba barazana ba ce ga ci gaban al'umma. Inda ya jaddada cewa fasahar AI za ta inganta ne da sauƙaƙawa al'umma wajen gudanar da ayyukan su ciki kuwa harda ƴan jarida.

Injiniya Abbas ya bayyana hakan ne a yayin taron da jaridar Almizan ta shirya na murnar cika shekaru 35 da kafa ta.

Bikin na bana na gudana ne a garin Kano wanda aka soma a daren ranar Juma'a 10 ga watan Janairun 2025 bayan isowar baƙi daga garuruwa daban-daban.

A taron na yau Asabar 11 ga watan Janairun 2025 wacce ta kasance a rana ta biyu da soma wannan taro, Injiniya Abbas Abdullahi ya gabatar da jawabi a kan maudu'i mai taken: Fasahar AI: amfani da matsalolinta.

Injiniya ya yi tilawar tarihi da asalin fasahar AI, inda ya yi kawo bayanai dangane da yadda za a ribaci fasahar ta AI da kuma illolinta. Sai dai ya jaddada cewa fasahar AI ci gaba ne k**ar ci gaban sauran fasahohi da aka samu.

Ya jaddada cewa ƴan jarida za su iya ribatar fasahar AI ta hanyoyi da dama wanda ya haɗa da rubutu, gyarawa, tantance bayanai da labarai, tantance hotuna da bidiyo, gyaran rubutu, bidiyo, da murya da sauran ayyukan da s**a shafi ƴan jarida.

Bayan ya kammala jawabinsa, mahalarta sun gudanar da tambayoyi, ƙarin bayani da nazari, daga ƙarshe aka tafi sallah da cin abinci.

YANZU-YANZU: An sami katsewar Wutar Lantarki karo na farko a Wannan shekarar ta 2025, yau Asabar.-Manuniya
11/01/2025

YANZU-YANZU: An sami katsewar Wutar Lantarki karo na farko a Wannan shekarar ta 2025, yau Asabar.

-Manuniya

Sojojin Najeriya Sun Kwace Birnin Owerri Babban Birnin Biyafara A Rana Mai Kamar Ta Yau 11 Ga Watan Junairu shekarar 197...
11/01/2025

Sojojin Najeriya Sun Kwace Birnin Owerri Babban Birnin Biyafara

A Rana Mai Kamar Ta Yau 11 Ga Watan Junairu shekarar 1970 ne sojojin Najeriya s**a kwace babban birnin lardin Owerri, daya daga cikin wuraren da ‘yan Biyafara s**a yi karfi a baya, inda aka tilastawa Ojukwu tsere zuwa kasar Ivory Coast. Bayan kwana hudu, Biafra ta mika wuya ga Najeriya.

Obasanjo ya karbe Owerri a watan Janairun 1970

Bayan yunkurin diflomasiyya da Najeriya ta yi ya kasa hada kan kasar, yaki ya barke tsakanin Najeriya da Biafra a watan Yulin 1967. Sojojin Ojukwu sun yi wani yunkuri na farko, amma karfin sojan Najeriya ya Rusa kasar Biafra sannu a hankali.

Biyafara ta yi asarar rijiyoyin mai babbar hanyar samun kudaden shiga - kuma ba tare da kudaden shigo da abinci ba, an kiyasta cewa fararen hula miliyan biyu ne s**a mutu sak**akon tsananin Yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Shafin Jarida New Nigeria Ta ranar 12 Ga Watan Janairu 1970. Ta buga cewa Yanzu an k**a Owerri, Ojukwu ya gudu daga yankinsa." Hotunan sojoji cikin jaridar. Obasanjo, Jallo, Bissala (Bissalla), Gowon.

Rundunar Sojan Najeriya ta dauki watanni 8 kafin ta k**a Owerri!! Yakin Owerri shi ne mafi muni a yakin baki daya.

Muhammad Cisse ✍️

IN DA RANKA: Wani ɓarawo da ba a san ko waye ba ya hana idon shi bacci inda ya bi dare ya sace tinkiyar da za a yanka wa...
11/01/2025

IN DA RANKA: Wani ɓarawo da ba a san ko waye ba ya hana idon shi bacci inda ya bi dare ya sace tinkiyar da za a yanka wa wata matashiya da zata yi saukar haddar Alƙur'ani a garin Kaduna.

Mallam Isma'il ya ce ƴan kuɗaɗen shi da ya jima yana tarawa kacokan ya ɗauka domin farantawa ɗiyar shi Hauwa'u Isma'il amma aka samu wani mara tausayi ya sace tinkiyar.

Da wannan iyayen yarinyar suke cikiya don Allah duk wanda aka kawo mishi wannan tinkiyar kada ya siya kuma ya kai ƙara caji ofis dake kusa da shi ko ya tuntuɓi Zinariya domin haɗa shi da mahaifin Hauwa'u.

Zinariya

10/01/2025

Kai Jama'a!!!!

HOTUNA: Masoyan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll sun ɓarke da murna bayan da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan dam...
10/01/2025

HOTUNA: Masoyan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll sun ɓarke da murna bayan da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan dambarwar masarauta a yau Juma'a a Abuja.

ADAP News

BIKIN ƳAN SHI'A A NAJERIYAƳan Shi'a sun yi alƙawari sai sun canza salon yadda biki ke gudana a tsakanin Musulmi ta hanya...
10/01/2025

BIKIN ƳAN SHI'A A NAJERIYA

Ƴan Shi'a sun yi alƙawari sai sun canza salon yadda biki ke gudana a tsakanin Musulmi ta hanyar maidashi kan turban addini a madadin yaɗa baɗala.

Nan wata amarya ce mai suna Nafisat Haruna a jiya Alhamis ta shirya ranar Qur'ani tare da ƙawayenta.

Ku yi mata fatan alkhairi.

HATTARA 'YAN MATA: Akwai Wani Sabon Salon Yaudara Da Wasu Mazan S**a Fito Da Shi Yanzu Na Karyar 'Genotype' Domin Su Fec...
09/01/2025

HATTARA 'YAN MATA: Akwai Wani Sabon Salon Yaudara Da Wasu Mazan S**a Fito Da Shi Yanzu Na Karyar 'Genotype' Domin Su Fece, Allah Ya Shirye Ku, Ya Toni Asirinku, Cewar Dalhat Zaynab

Me za ku ce?

Gararanɓa nake yi a kan t**i, na rasa wurin kwana kuma ina cikin tashin hankali - Zainab Ado Bayero
09/01/2025

Gararanɓa nake yi a kan t**i, na rasa wurin kwana kuma ina cikin tashin hankali - Zainab Ado Bayero

Babban Dalilin Shakuwa Ta Da Tinubu Shine Ya Gina Masallaci, Ya Gina Masaukin Malamai Da Makaranta Ga Kuma Tausayin Al'u...
09/01/2025

Babban Dalilin Shakuwa Ta Da Tinubu Shine Ya Gina Masallaci, Ya Gina Masaukin Malamai Da Makaranta Ga Kuma Tausayin Al'umma, Martanin Sheik Sani Yahaya Jingir Ga Gwamna Bala Mohammed

KBC Hausa

CIGIYA CIGIYA CIGIYA Muna cikiyar Wannan baiwar Allahn mai suna Basma Abubakar Chindo  ƴar kimanin shekaru 16 wacce ta ɓ...
09/01/2025

CIGIYA CIGIYA CIGIYA

Muna cikiyar Wannan baiwar Allahn mai suna Basma Abubakar Chindo ƴar kimanin shekaru 16 wacce ta ɓace kwanaki uku da s**a wuce.

Basma ta taso daga garin Magama dake Bauchi zuwa Jos ne inda har yanzu ba a samu labarin ta ba.

Muna roƙon wanda duk ya ganta ya taimaka ya tuntuɓi mahaifin ta Mallam Abubakar Chindo a waɗannan lambobin wayar

08064448145
07012222229

A taimaka a yi sharing.
Allah bayyana ta cikin aminci.

Zinariya

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIN RAJI'UN! Yanzu haka mun samu labarin rasuwar Jikan Bauri Kafin Hausa.Muna addu'ar Allah yasa...
08/01/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIN RAJI'UN!

Yanzu haka mun samu labarin rasuwar Jikan Bauri Kafin Hausa.

Muna addu'ar Allah yasa wannan jinyar da yayi ta zama masa kaffara a gareshi kasa ya huta.

08/01/2025

Tsakanin Gwamna Bala da Sheikh Yahaya Jingir

Shawarace fa, don na ga k**ar kana iya magana wa Mai girma Shugaban Ƙasa BOLA AHMAD TINUBU........

Da ace ni Namiji ne, ba zan ce ina son ƴar mutane ba, har sai na san wace ce Mahaifiyarta, don ba zan tsuguna a gaban Ub...
08/01/2025

Da ace ni Namiji ne, ba zan ce ina son ƴar mutane ba, har sai na san wace ce Mahaifiyarta, don ba zan tsuguna a gaban Uban yarinya domin yin complain ya ce sai dai nayi hakuri shi ma hakuri yake da ta gidan 😆

Sannan ko da wasa ba zan je neman aure a gidan da power mace ya rinjayi na namijin ba, domin ba lallai na ga dai-dai ba, saboda sawun da na gaba ya taka shi na baya zai taka. Kuma sanin kanmu ne mata a mafi yawan lokaci sun fi maza kwafsawa, sai yasa ma Allah yace maza ne a saman mata. Kuma kai Yallaboi kai daga jin ance maka gidan nan power mace ne yafi, kai kasan da damuwa, domin ba mijin ba ne ya karramata ya bata Award akan power ta yafi nasa. Wanda ko Allah bai ce haka ba, daga jin haka kasan ita ta samarwa kanta ta hanyar da bai da ce ba, domin idan dacewa ce, kai ai kasan ba ayi haka ba 😆

Zan bar musu kayansu. Don a shari'ance ma haramun ne ka auri uwa kuma ka auri ƴarta. Eh mana, kana aurar yarinya kana ginata akan tsari, daga waje ana rushe maka.

Ra'ayin ƴar jarida Aisha Kazimiyyah

Address

Federal Low Cost Housing Estate
Bauchi
740102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when One News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to One News Hausa:

Videos

Share