Muryar Safinatun Najat صوت سفينة النجاة

Muryar Safinatun Najat صوت سفينة النجاة وَإِنِّي تَارِكٌ فِيكُمْ الثَّقَلَيْنِ كِتَابَ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ وَعِتْرَتِي أَهْلُ بَيْتِي

Gayyata! Gayyata!! A madadin da'irar "SON FADIMA SAI MAI RABO" karkashin jagorancin Sayyida Hajara, suna farin cikin gay...
17/02/2024

Gayyata! Gayyata!!
A madadin da'irar "SON FADIMA SAI MAI RABO" karkashin jagorancin Sayyida Hajara, suna farin cikin gayyatar 'yan uwa masoya Manzon Allah (S) da Ahlul-Bayt (A.S) zuwa wajen Gagarumin Mauludin "AHLUL KISA'I" wanda s**a saba shiryawa duk shekara.

Taron zai gudana kamar haka:
Rana: Alhamis 22nd February 2024
Lokaci: 6:00pm zuwa abnda ya sawwaka.
Wuri: Kofar gidan Sayyida Hajara Opp. Makarantar Abu Zar Kandahar Street Kofar Idi Bauchi.

Allah ya bada ikon halarta Ameen!

Sanarwa daga:
Sajjad Adam Vijay
Media & Publicity
Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation
Bauchi State Chapter.

MECECE DARIQAR FADIMIYYA?Sannan Wanene Mujaddadin Ta Na Wannan ƙarni 15?ATAƘAICE:Darikar Fadimiyya ba irin Darikun da mu...
17/02/2024

MECECE DARIQAR FADIMIYYA?
Sannan Wanene Mujaddadin Ta Na Wannan ƙarni 15?

ATAƘAICE:
Darikar Fadimiyya ba irin Darikun da muka sani bane, misali Shaziliyya Nakashabandiyya, Qadiriyya da Tijjaniyya d.s tare da nuna ganin girmansu.

Ita wannan dariƙar wuridinta direct ne daga bakin Annabi Muhammad (S) zuwa kunnuwan Sayyida Fadima Azzahra (AS) Babu wani Sila ko tsani a tsakani.

Mujaddadin Darikar Fadimiyya kuma shine
Maulaya Sidi Sharif Al-Alawi Hafizahullah.

Dalibi, Khadimi Kuma Muridin wannan Darika wanda shine Sidi Sharif Al-Alawiy, Jikan Imam Hassan (AS) da Imam Hussaini (AS) shine yake tajdidinta.

Cikin Ikon Allah yau dan uwanmu dake garin Bauchi mai suna SIDI ABDUL HAUSAWA GAGARE ya waƙe wannan Darika tare da Mujadaddinta.

Don samun wannan Kasidar a tuntubi:
1. Sharif Jawad
+234 803 878 7051

2. Nasir Al-Alawi
0814 004 6780

3. Abdul Hausawa
+234 810 323 9291

Qs Naseer Al-muhammady
Media and Publicity II
Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation
Bauchi State Chapter.

Yayin gudanar da Karatun Silsilatu Ahadithul A'immatu AHLUL-BAITI
16/02/2024

Yayin gudanar da Karatun Silsilatu Ahadithul A'immatu AHLUL-BAITI

16/02/2024

Karatun Silsilatu Ahadithul A'imma Tare Da Al-Muballig Sheikh Tahir Umar Sulaiman.

Ina masoya annabi saww da iyalan gidansa tsarkaka ku ajiye salati Annabi  hadiyya ga babban Jagora kudubut tauhid maulay...
15/02/2024

Ina masoya annabi saww da iyalan gidansa tsarkaka ku ajiye salati Annabi hadiyya ga babban Jagora kudubut tauhid maulaya sidi shareef Al'alawiy (H)

13/02/2024

RAHMAR ALLAH, RUFIN ASIRI YALWAR ARZIƘIN DUNIYA DA LAHIRA YA TABBATA GA DUK WANDA YA RUBUTA "LABBAIKA YA HUSSAIN".🌹

10/02/2024
10/02/2024

Jawabin Sayyed Nuruddeen Gwallaga a wajen Taron Mauludin Imam Ali (A.S) mai taken "WANENE IMAM ALI A CIKIN QUR'ANI" wanda Shelelen Imam Ali ya saba shiryawa karkashin Da'irar Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation Bauchi State.

10/02/2024

Filin Taron Mauludin Imam Ali (A.S) kenan mai taken "WANENE IMAM ALI A CIKIN AL-QUR'AN MAI GIRMA" wanda dan uwanku Shelelen Imam Ali ya saba shiryawa duk shekara.

Gayyata! Gayyata!! A madadin da'irar Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation Bauchi State Chapter. Karkashin jagorancin Kud...
08/02/2024

Gayyata! Gayyata!!
A madadin da'irar Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation Bauchi State Chapter. Karkashin jagorancin KudbutTauhid Maulaya Sidi Shareef Al-Alawiy (H) muna farin cikin gayyatar 'yan uwa masoya Ahlul-Bayt (A.S) zuwa wajen Gagarumin Mauludin Imam Ali (A.S) hadi da Walima, wanda 'dan uwanmu Abubakar Shalelen Imam Ali AS ya saba shiryawa duk shekara.

Wanda za'a gudanar kamar haka:
Rana: Asabar, 10th February 2023.

Lokaci: 02:00pm zuwa 6:00pm

Wuri: Harabar Makarantar Abu Zarrul Giffar Kandahar Street Kofar Idi, Junction Ashabul Kahfi Mosque.

🎉🎉🎉🌹🌹🌹🎈🎈🎈
Sha'iran Yabon Imam Ali (A.S) zallah:
1) A M B. Na Fada
2) Imamun Shalele
3) Abdulrahman Khalifan Shalele
4) Badamasi Saqafa
5) Dausayi Rainon Fada
6) Mai Ado Da Salaty
7) Aliyu Ruwan Bege
8) Aliyu Mai Badagire
9) Sidi Mu'ab Abdullahi
10) Abdul Hausawa
11) Syyd Khabir Ambato
12) Shaukin Bege
13) Kawu Dalhat Mai Ma'asumiya
(14) Shehuwa Abdullahi

TAKEN MAULUD:
Wanene Imam Ali (A.S) a cikin Al-Qur'an Mai Girma? Daga bakunan malamanmu na cikin gari.
1) Sheikh Sani Haris Bauchi
2) Sheikh Sayyid Nurr Gwallaga Bauchi
3) Sheikh Taheer Umar Suleiman Bauchi
4) Sheikh Shu'aibu Wa'izi Bauchi.

Sanarwa daga:
Sajjad Adam Vijay
Media & Publicity
Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation
Bauchi State Chapter.

YAUMUL MAB-ATH, RANAR FARIN CIKI GA MUMINAI." Yau Alhamis wanda ya zama 27 ga watan Rajab a irin wannan rana ne Allah Ma...
08/02/2024

YAUMUL MAB-ATH, RANAR FARIN CIKI GA MUMINAI.

" Yau Alhamis wanda ya zama 27 ga watan Rajab a irin wannan rana ne Allah Mad'aukakin Sarki ya aiko da Annabinsa kuma Manzonsa na karshe daga cikin Annabawa da Manzonninsa (Amincin Allah ya tabbata a gare su).

Rana ce mai girma ga al’ummar wannan Annabi din ma’abocin girman daraja, kuma rana ce ta murna da farin ciki ga daukacin mabiya Mazhabar Iyalan Gidan Manzon Allah (S) a duk inda suke saboda kasancewarta ranar da hasken Shugabanninsu ta fara bayyana ga talikai baki daya.

Shi Annabi ba mutane bane suke haduwa su zabe shi ba a'a Allah ne yake dubawa a cikin halitta cewa wanenne ya cancanta a bashi wannan matsayi, Allah (T) shi ya san inane zai sanya manzoncinsa. A itikadin mu, mutane basu da ta cewa wanene zai zama Annabi da wasiyinsa ba A'a,

Allah ne yake za'ba ko magajin Annabi ko wasiyin Annabi. Haka khalifofin Annabi 12 ne na farkon su Imam Aliyu (As) na karshen su Imam Mahdi (As) wannan Allah ne ya kaddara haka.

Amincin Allah ya kara Tabbata gareka ya ma, aikin Allah 🌹🌹🌹

📝 Qs Naseer Al-muhammady
© media and publicity ii

Safinatun Najat Al'alawiy foundation bauchi state chapter.
08/February/2024.

AFUWAN AI MANA AIKIN GAFARAR KARATUN HADISI DA YASABA ZUWA DUK SATI Karatun hadisi da yake zuwa duk sati bazai samu Dama...
08/02/2024

AFUWAN AI MANA AIKIN GAFARAR KARATUN HADISI DA YASABA ZUWA DUK SATI

Karatun hadisi da yake zuwa duk sati bazai samu Daman zuwaba sakamako wasu dalilai, amma insha allahu dazo gobe juma'ah tareda addu'o'l daga shugaban comeeteen shura na Safinatun najat bauchi state.

Addu'o'ln damu yi shine sakamako abun Alkairin da yasa me mune a jihar bauchi kasatan akan malamin mu sheikh Tahir Umar Sulaiman bauchi.

Signed :
Qs Naseer Al-muhammady
Media and publicity ii

Safinatun Najat Al'alawiy foundation bauchi state chapter
08/February/2024.

MAULAYA SIDI SHARIF AL-ALAWIY YA GWANGWAJE AL-MUBALIGH MALLAM TAHIR DA MOTA TA ALFARMA.Babban Jagora Maulaya Sidi Sharee...
07/02/2024

MAULAYA SIDI SHARIF AL-ALAWIY YA GWANGWAJE AL-MUBALIGH MALLAM TAHIR DA MOTA TA ALFARMA.

Babban Jagora Maulaya Sidi Shareef Al-Alawiy (H) wanda shine Shugaban Da'irar Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation na duniya kuma Shugaban Darikar Fadimiyya karni na 15. Yayi kyautar mota ƙira Acura Ash color, wa Shehin Malaminmu Almuballig Sheikh Tahir Umar Sulaiman.

Amadadin ilahirin mabiya da masoyan Da'irar nan tamu mai albarka dake garuruwa daban-daban cikin Nigeria da kewaye, muna godiya wa Babban Jagora da fatan Alkhairi Allah yasa Sayyida FADIMA AZZAHRA (H) ta karba.

Signed:
Sajjad Adam Vijay
Media & Publicity
Safinatun Najat Al-Alawey Foundation
Bauchi State Chapter.

-Ammar Bn Yasir (R.T.A) Yana Cewa: "Wata Rana Ni da Imam Ali (AS) Muna Tafiya Sai Muka zo Wucewa ta Wurin Gidan Tururuwa...
07/02/2024

-Ammar Bn Yasir (R.T.A) Yana Cewa: "Wata Rana Ni da Imam Ali (AS) Muna Tafiya Sai Muka zo Wucewa ta Wurin Gidan Tururuwa Masu Yawan Gaske, Sai Nace Ya Amirul Mu‘mineen, Shin Ko ka San Wani Mutum da Yasan Adadin Waɗannan Tururuwan?

-Sai Imam Ali (AS) Yace: "Tabbas Na San Mutumin da Yasan Adadinsu Ya Kuma San Mace da na Mijinsu.

-Sai Ammar (R.T.A) Yace: "Waye Wannan Mutumin?" Sai Imam Ali (AS) Yace: "Shin Baka Karanta Bane A Suratu Yaseen, inda Allah (S.w.t) Yake Cewa:

ﻭﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﺃﺣﺼﻴﻨﺎﻩ ﻓﻲ ﺇﻣﺎﻡ ﻣﺒﻴﻦ .

-Ma'ana: "Duk Wani Abu da Yake da Kuma Wanda Zai Faru Nan Gaba Mun Bayyana Shi ga Imamim Mubeen.

-Sai Ammar Yace: "Tabbas Na Karanta Sai Imam Ali (AS) Yace: "To Wannan Imamim Mubeen ɗin Ni ne."

-Don Ƙarin Bayani Sai A Duba Suratu Yaseen, Aya ta 12 Tafsir Burhan: Juz'i Na 4, Shafi Na 7, Mujalladi Na 10, Ko Kuma: Madinatul Mu'ajiz: Juz'i Na 1, Shafi Na 301

© Qs Naseer Al-muhammady
Media and publicity ii

Safinatun Najat Al'alawiy foundation
Bauchi state chapter

06/02/2024

25 ga watan Rajab🌙
Ranar shahadar Imam Musa Alkazim(A. S. )
Salati📿 guda 1 hadiyya ga ruhin Imam.

Wane mutum maza suna magana👇👀👈👉👀👈👇 Imam Ali as محمد النبي أخي وصهري           وحمزة سيد الشهداء عميMuhammad Annabi Dan u...
05/02/2024

Wane mutum maza suna magana
👇👀👈👉👀👈👇 Imam Ali as

محمد النبي أخي وصهري
وحمزة سيد الشهداء عمي
Muhammad Annabi Dan uwana ne Kuma sirikina ne
وجعفر الذي يضحي ويمسي
يطير مع الملائكة ابن أمي
Jaafaru Wanda yake. Hantsinta yake maraituwa Yana tashi tareda mala'iku shikuma Dan baffana ne
وبنت محمد سكني وعرسي
مشوب لحمها بدمي ولحمي
Yar' Muhammad saw Abokiyarzamana ce Kuma Amaryata ce
Namanta yacakuda da jinina da nama na
وسبطا أحمد ولداي منها
فمن منكم له سهم كسهمي
Jikokin Ahmad Saw ya'ya' nane daga gareta
Waye 👈👉cikin ku yakeda rabo kamar rabo na ?
سبقتكم إلى الإسلام طرا
غلاما ما بلغت أوان حلمي
Na rigayeku zuwa muslinci dukkanku
Lokacin ha'lin kasancewata yaro ban Kai lokacin mafarki ba wato ban balagaba.

📝 Qs Naseer Al-muhammady
© media and publicity ii

Safinatun Najat Al'alawiy
foundation bauchi state chapter
15th February 2024.

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Yan uwa mabiya wannan page dinmu mai albarka ta Muryar Safinatun Najat ص...
03/02/2024

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Yan uwa mabiya wannan page dinmu mai albarka ta Muryar Safinatun Najat صوت سفينة النجاة , bamusan wani irin godiya da muyi mukuba, bisa nuna mana goyon baya da bibiyan wannan shafi namu mai albarka da kukeyi ba, sai dai godiya wa Allah madaukakin sarki.

Yan uwa muna bukatan shawar warinku gameda wannan page din mu ta bangaren gudanarwa da mukeyi ta ina muka gaza ku fadamana mugyara, memukeyi yafi burgeku mu kara himma akan hakan muna jiran ra'arinku a comment section

Writeen by : 📝 Qs Naseer Al-muhammady
Media and publicity II

Safinatun Najat Al'alawiy foundation bauchi state chapter
03/February/2024

03/02/2024

"Yawan Cin Abinci Yanasa Bushewar Zuciya"

__Imam Ja'afar As-sadeeq {AS}🌺❣️🌺

ALLAH DA IKONSA 🙏  MUN BUDE GARRUKA BIYAR (5)1.Gumel LGA Jigawa State.2.Dutse LGA Jigawa State.3.Zaranda, Toro LGA Bauch...
01/02/2024

ALLAH DA IKONSA 🙏 MUN BUDE GARRUKA BIYAR (5)
1.Gumel LGA Jigawa State.
2.Dutse LGA Jigawa State.
3.Zaranda, Toro LGA Bauchi.
4.Jakusko Yobe State.
5.Gashuwa Yobe State.

HAUSAWA SUNCE "INDA BA ƘASA NAN AKE GARDAMAR KOKOWA"
Babban jagora, KhudbutTauhid, Shugaban Dai'rar Safinatun Najat Al-Alawey Foundation na Duniya Sidi Sharif Al'alawiy (H) ya samu damar Kaddamar da Da'irar Safinatun Najat Al-Alawiy Foundation a Garruka biyar 5 acikin sati guda.

Gari na farko shine ƙaramar hukumar Gumel dake garin Jigawa. Kaddamar da wannan Da'ira ta kasane ranar Alhamis ne 25/01/2024.
Daga bisani Babban jagora ya shiga Garin Dutse anguwar Kudai domin mauludin Imam Aliyu tare da kaddamar da Da'irar da kuma naɗa sidi Sadisu a matsayin Wakilinsa. Hakan ta faru ne a ranar Jumma'a 26/01/2024.

Jim Kadan Bayan kwana ɗaya sai Maulaya ya shiga Garin Zaranda ƙaramar hukumar Toro na musamman don Mauludi tare da kaddamar da Da'ira a sa'ilin ne ya Wakililta Wakilinsa a wanna Gari Mai albarka.28/01/2024.

Ranar Monday ya shiga garin Jakusko Yobe state, inda aka yi mauludin da akayi gagarumin Mauludin da ba'a taba yi ba aka basu wuridin Sayyida tare da littafin Hadisin da Sharifi ya wallafa. Hakan ta faru ne 29/01/2024

Ranar Talata 30/01/2024 muka shiga garin Masoya wato garin Gashuwa Yobe state ya kuma ƙaddamar da tafiya tare da naɗa wakilai a garin.

A duk wannan Garruka Maulaya ya Basu litattafai na hadisan da ya wallafa mai suna " Salsalatul ahadisi A'immatul Ithna Ashra" don koyar da yara a makaranta tare da basu wuridin Nana Fadima (AS)

Safinatun Najat Al-Alawey Foundation Nigeria

Muryar Safinatun Najat صوت سفينة النجاةةالنجاة
Mujamma'u Ashabil Kahfi Warraqeem NigeriaaNigeriaEveryone
Everyone

🏵️💎 SHUGABAN SAFINATUN NAJAT NA DUNIYA A GARIN GASHUWA L.G.A YOBE STATE 💎🏵️‌Labari cikin hotuna dake nuna ziyara tare da...
30/01/2024

🏵️💎 SHUGABAN SAFINATUN NAJAT NA DUNIYA A GARIN GASHUWA L.G.A YOBE STATE 💎🏵️

‌Labari cikin hotuna dake nuna ziyara tare da kaddamar da Safinatun najat a garin gashuwa yobe state, a yau ne 30/01/2024 mujaddadin darikar fadimiyya na karni 15 maulaya sidi shareef Al'alawiy (H) yaje garin gashuwa gidan kadiriyya domin ziyara tare da kaddamar da wannan da'irar mai albarka.

‌A cikin jawabin maulana kudubut-tauhid yayi batu akan maulana sheikh Dr Abduljabbar kabara, da kuma mazlumiyuan da a keyimasa da sanadin abunda yasa a keyi masa wannan babban zalincin.

‌Maulana shareef Al'alawiy yakara dacewa irrin miyagun hadisai da malam Abduljabbar yake korewa wa janibin annabi (saww) shiya jawomasa wannan zalincin da ake masa na cewa yayi su'ul adab a janibin ma'aikin allah.

‌Daga karshe shareef yace maulana amirul wa'izina bezagi ma'aikin ba

📝_Qs Naseer Al-muhammady
© Media and publicity ii
Safinatun najat Al'alawiy foundation bauchi auchi state chapter
30/JANUARY/2024

Insha Allah nan ba da jimawa ba zamu kawo muku karatun Babban Jagora anan garin Jakusko Yobe state.
29/01/2024

Insha Allah nan ba da jimawa ba zamu kawo muku karatun Babban Jagora anan garin Jakusko Yobe state.

29/01/2024

Babban Jagora KhudbutTauhid Sidi Sharif Al'alawiy Garin Jakusko Yobe State

28/01/2024

Insha Allahu nan bada jimawaba damu kawo muku cikekken jawabin babban Jagora maulaya shareef Al'alawiy (H)

SAKON BAN GAJIYA DAGA DA'IRAR SAFINATUN NAJAT BAUCHI STATE Amadadin wannan Da'ira maisuna a sama tana mika Sakon ban gaj...
28/01/2024

SAKON BAN GAJIYA DAGA DA'IRAR SAFINATUN NAJAT BAUCHI STATE

Amadadin wannan Da'ira maisuna a sama tana mika Sakon ban gajiya ga dukkanin mahalarta taron mauludin sayyidatu nisa'il alamin fadimatuz-zahra'u da imam Ali (A.S)

Muna fatan kowa da kowa yakoma gida lapia allah yasaka da alkairi da wannan irrin soyayyar da kuka nuna gaskiya muna godiya sosai sosai

_Qs Naseer Al-muhammady
© media and publicity ii
Safinatun Najat Al'alawiy foundation bauchi state chapter

27/01/2024

Abba waziyada Safinatun Najat

Address

Kandahar
Bauchi

Telephone

+2347065191456

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Safinatun Najat صوت سفينة النجاة posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muryar Safinatun Najat صوت سفينة النجاة:

Videos

Share

Category

Nearby media companies


Other TV Channels in Bauchi

Show All

You may also like