Prime Time News Hausa

Prime Time News Hausa Hausa reliable online Newspapers
(2)

Hotuna: Gwamnan Kano Ya Bada Auren 'Yar Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi IIGwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ...
19/04/2024

Hotuna: Gwamnan Kano Ya Bada Auren 'Yar Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi II

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya zama waliyin Amarya, Yusrah Sanusi 'yar Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi na II inda Gwamman jihar Kwara, Abdulrazzak ya zama wakilin Ango a auren da aka daura a yau Juma'a a masallacin Juma'a na Al-Fur'qan.

Hotuna: Ibrahim Adam/Facebook

Daga karshe dai mawakin nan Rarara ya ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu
19/04/2024

Daga karshe dai mawakin nan Rarara ya ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu

Yanzu-Yanzu: Babbar Kotun jihar Kano ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga jam'iyyar APC
17/04/2024

Yanzu-Yanzu: Babbar Kotun jihar Kano ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga jam'iyyar APC

Shugaban kasa ya ce wannan kujera ta shugabancin jam'iyyar APC ina kai daramdam - GandujeGanduje ya bayyana hakan ne yay...
17/04/2024

Shugaban kasa ya ce wannan kujera ta shugabancin jam'iyyar APC ina kai daramdam - Ganduje

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin shugabannin jam'iyyar na jihar Kano.

Sallah: Abba Bichi Ya Buƙaci Al'ummar Musulmai Da Su Ci Gaba Da Yiwa Ƙasa Addu'aƊan Majalisar wakilai mai wakiltar ƙaram...
10/04/2024

Sallah: Abba Bichi Ya Buƙaci Al'ummar Musulmai Da Su Ci Gaba Da Yiwa Ƙasa Addu'a

Ɗan Majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Bichi a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Abubakar Kabir Abubakar yayi kira ga al'umma da su ci gaba da yiwa ƙasa addu'a.

Ɗan Majalisar ya bayyana hakan ne cikin sakon Barka Da Sallah da ya aikawa al'ummar Musulmai.

"Ni, Honorable Abubakar Kabir ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Bichi a majalisar wakilan Najeriya, ina taya al'ummar mazaɓata da na Masarautar Bichi dama al'ummar jihar Kano baki daya murnar bikin karamar Sallah wanda ake gudanarwa bayan kammala Azumin watan Ramadana.

"Haƙiƙa, muna godiya ga Allah maɗaukakin Sarki bisa tsawaita rayukanmu wajen ganin kammaluwar Ibadar Azumi. A don haka ina kira ga dukkan al'ummar Musulmi da su aiwatar da kyawawan halayen da s**a koya a watan Ramadana.

"Sannan ina kira a gare su da su yi amfani da wannan lokacin domin yin addu'ar ci gaban ƙasa. Haƙiƙa Najeriya na buƙatar addu'ar dukkaninmu a wannan yanayi."

Masarautar Kano ta Umarci Hakimai su shigo birni domin bikin Hawan Sallah KaramaA wata wasika da aka aikawa hakimai mai ...
03/04/2024

Masarautar Kano ta Umarci Hakimai su shigo birni domin bikin Hawan Sallah Karama

A wata wasika da aka aikawa hakimai mai dauke da kwananan watan 2 ga Afrilu, masarautar ta bukaci hakimai su shigo Kano a ranar Lahadi 28 ga watan Ramadan domin fara shirin hawan.

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu Ya Dakko Hanyar Inganta Karatun Tsangayu - Samarin TijjaniyyaAn bayyana nadin ...
28/03/2024

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu Ya Dakko Hanyar Inganta Karatun Tsangayu - Samarin Tijjaniyya

An bayyana nadin da Shugaban Kasar Najeriya yayi wa Ritaya Janar Lawal Jafaru Isa Kano da Dr. Sani Muhammad Idris Yobe da cewa abu ne da zai Kara inganta harkar ilimin addini Musulunci a Kasar nan.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Abubakar Balarabe Kofar Naisa, Sakataren yada labarai na kungiyar, Tijjaniyya Youth Enlightenment.

Sanarwar ta ce jawanin hakan ya biyo bayan wata sanarwar da kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa ta fitar mai dauke dasa hannun Babban Sakataren Kungiyar na Kasa Shehu Tasi'u Ishaq da Babban Jami'in yada Labaran Kungiyar na Kasa Abubakar Balarabe Kofar Naisa.

Sanarwar yace idan akayi la"akari da irin gudunmawar da wadannan mutane biyu s**a bayar wajan cigaban addinin Musulunci da inganta makarantun tsangayu Shugaba Tinibu yayi namijin kokari da hangen nesa wajan basu wadannan muk**ai.

Sai dai kuma Kungiyar Samarin Tijjaniyyar ta Kasa taja hankalin wadanda aka bawa wadannan muk**ai suyi aiki tsakaninsu da Allah bisa amana da gaskiya k**ar yadda aka sansu tareda nuna rashin banbanci ko bangaranci domin ciyar da Kasar nan gaba.

Sanarwar ta yabawa Shugaba Ahmed Bola Tinibu bisa yadda yake nada muk**ai ta hanyar zabo jajirtattu da kuma ajiye kowa a gurbinsa wanda ya kware a fannin da yake domin gudanar da aikin cigaban Kasa.

Daga nan Kungiyar Samarin Tijjaniyyar tayi kira ga yan Najeriya su cigaba da yiwa wannan Kasar aduu'ar samun zaman lafiya da karuwar arziki da dorewar tattalin arziki da kuma samun cikakken tsaro musamman a wasu jihohi da ake fama da tabarbarewar tsaro.

Yin Sahur A Lokacin Ibadar Azumi Yana Da Matukar Muhimmanci - Malama Sa'adatu IlyasuAn bayyana mahinmancin yin sahur yay...
27/03/2024

Yin Sahur A Lokacin Ibadar Azumi Yana Da Matukar Muhimmanci - Malama Sa'adatu Ilyasu

An bayyana mahinmancin yin sahur yayin Ibadar Azumi a watan Ramadana duba da wasu mutanenen ba su fiye yin sahur ba saboda wasu kalubale da suke fuskanta na rashin lafiya da dai sauran su.

Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin Malama Sa'adatu ILyasu Ali a wajen taron fadakarwa wanda Sakatariyar kungiyar mata 'yan jarida NAWOJ Hajiya Wasila Ladan ta hada a ofishin kungiyar 'yan jarida NUJ dake farm center a Kano.



Malama Sa'adatu ta kara da cewa akwai Lada mai tarin yawa wajen yin sahur ga Wanda ya san hakan, ta ce yana da kyau kungiyar mata 'yqn jarida su ci gaba da wanan taro na fadakarwa akan abunda ya shafi addinin musullunci Koda bayan Ramadan.

Shima ana sa bangaren shugaban Rediyon Kano Alhaji Abubakar Rano ya yabawa Sakatariyar kungiyar mata 'yan jarida bisa sabon tsari da tayi na taron fadakarwa da koyi da abunda Allah ya fada, Inda ya ce wanan shi ne karo na farko da kungiyar mata tayi duba akan abun da ya shafi bangaren addini, ya ce a shirye suke don bada na su gudunmawa a duk lokacin da ake bukatar Hakan,

Itama ana ta jawabin Secretary kungiyar mata yan jarida NAWOJ Hajiya Wasila Ladan ta nuna farin cikin ta inda ta ce makasudin wanan taro na fadakarwa da ta hada a watan Ramadan dan mata su karu akan bangaren addini islama da Kuma yanda zasu kauracewa abunda zai bata musu azumi.

Ta Kara da cewa wanan shi ne karo na farko da kungiyar 'yan jarida ta fara hadawa a kasa baki Daya,

A karshe taron ya samu halarta manya Baki da mallamai mata da sauran mata dake kungiyar NAWOJ.

Bukola Saraki Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗalibai 100 A Jami'aTsohon shugaban majalisar dattawa ta kasa, Dr. Abubakar Bukola...
20/03/2024

Bukola Saraki Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗalibai 100 A Jami'a

Tsohon shugaban majalisar dattawa ta kasa, Dr. Abubakar Bukola Saraki Saraki ya ɗauki nauyin dalibai 100 domin su yi karatu a jami'ar Muhammad Kamaldeen dake jihar Kwara.

A yayin ziyarar gani da ido, domin ganin yadda ake tantance ɗaliban da gidauniyarsa ta Abubakar Bukola Saraki Foundation ta ɗauki nauyi, Saraki ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da tallafawa matasa domin su cimma burinsa na karatu.

Sannan ya jinjinawa kwamitin tantancewar bisa sadaukar da kai da s**a yi da kuma yin aiki da gaskiya wajen tantance ɗaliban da kuma tabbatar da ganin kowanne a cikin su ya bi ƙa’idar da aka saka.

"Ilimi shi ne babban abin da na ɗauka da muhimmancin gaske saboda yana kawo ci gaba kai tsaye. Hakan ne ma yasa na mayar da hankali a kansa, kuma na kawo tsare-tsare a lokacin da nake cikin gwamnati da yanzu da yake ɗan ƙasa mai zaman kansa.” A cewar Saraki.

Kawo yanzu dai an kammala tantance ɗalibai 80 saura guda 20 inda tuni shirye-shirye s**a yi nisa wajen fara karatun ɗaliban.

Sannan Saraki ya shawarci ɗaliban da basu cike ba suje su shiga shafin na yanar gizo https://t.co/Sf4y68SFrt domin su cike don a kammala gurbin mutum 20 da ba a samu ba tunda mutum 100 da aka yi niyyar ɗaukar nauyin karatun nasu.

Daya daga cikin ma'aikatan gidan Gwamnatin jihar Kano ke yin Sujjadar Godiya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya basu talla...
17/03/2024

Daya daga cikin ma'aikatan gidan Gwamnatin jihar Kano ke yin Sujjadar Godiya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya basu tallafin kayan abinci da kudin cefane a yau Lahadi.

10/03/2024

Azumi: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bada Umarnin Kulle Gidajen Galar Dake Fadin Jahar Kano

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano na ganawa da Sheikh Aminu Daurawa
04/03/2024

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano na ganawa da Sheikh Aminu Daurawa

Gombe 2027: Kungiyar Matasa Na Kiran Farfesa Ali Pantami Da Ya Amsa Kiran su Ya Fito Takara Daga Abubakar Rabilu, Gombe ...
03/03/2024

Gombe 2027: Kungiyar Matasa Na Kiran Farfesa Ali Pantami Da Ya Amsa Kiran su Ya Fito Takara



Daga Abubakar Rabilu, Gombe



Gamayyar Kungiyar Matasa ta ci gaban arewa maso gabas a jihar Gombe mai suna North East Coalition of Youth for Progressive Governance and Sustainable Development’ ta kirayi tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin arziki Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da ya amsa kiran su a shekarar 2027 wajen fitowa takarar gwamana a jihar



Kungiyar tayi wannan kiran ne ta bakin Sakataren ta na jihar Gombe Gideon Musa, a lokacin wani taron manema labarai da ta kira a ranar Asabar.



Yace su amincewa tsohon Ministan ne sak**akon irin dinbin Nasarorin da ya samar a lokacin da ya zama Darakta a hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) da kuma lokacin da ya ke ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani.



A cewar kungiyar, Pantami ya bai wa al’ummar jihar Gombe damar yin amfani da fasahar zamani ta hanyar bude cibiyoyin fasahar sadarwa ta zamani (ICT) a makarantu da sassa daban-daban na jihar inda aka horar da mutane tare da ba su damar shiga yanar gizo kyauta.



“Farfesa Pantami ne ya jagoranci samar da ofisoshi a fadin kasar nan ciki har da jihar Gombe a arewa maso gabas,tsohon ministan ya samar da ci gaba da samun dama ga ayyukan fasaha a yankin”



Sun kuma kara da cewa wadannan ofisoshin ba kawai inganta haɗin guiwa ba ne amma sun ba wa ma'aikatan jihar ƙarin dama don haɗin guiwa da dandalin kirkiro da musayar bayanai.", in ji shi.



Daga nan sai kungiyar ta yi kira ga tsohon ministan da ya amince da kiran da s**a yi masa na ya fito ya tsaya takarar gwamnan jihar ta Gombe a zabe mai zuwa na shekarar 2027 sannan s**a nemi gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da ya mara masa baya a matsayin wanda zai gaje shi.

Farashin Bahaya Ya Koma Naira 200 A BauchiKungiyar masu gidajen wanka da bahaya ta jihar Bauchi ta sanar da karin kaso 1...
26/02/2024

Farashin Bahaya Ya Koma Naira 200 A Bauchi

Kungiyar masu gidajen wanka da bahaya ta jihar Bauchi ta sanar da karin kaso 100 na masu amfani da gidajen wankan.

Shugaban kungiyar, Ibrahim Kabo ne ya sanar da karin kudin yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na NAN.

Ya ce an kara farashin yin Bahaya zuwa Naira 200 daga Naira 100 da yake a da, yayin wanka da ruwan zafi ya koma Naira 200 maimakon 100.

Kabo ya ce karim kudin ya zama dole duba da karin kudin kayayyakin da ake amfani da su a gidajen wankan.

"Muna amfani da sabulu da Omo da maganin wankin ban daki da tsintsiya domin tsaftace gidajen Wanka.

" A gefe guda kuma mun kara kudin aiki ga ma'aikatunmu domin suna taka muhimmiyar rawa wajen kula da wuraren sana'armu", inji shi.

Kwastam Ta Dauki Matakan Ladabtarwa Kan Jami'inta Da Ake Zargi Da Karbar Kudi Ga Wani Mai Mota A Hanyar MokwaHukumar han...
26/02/2024

Kwastam Ta Dauki Matakan Ladabtarwa Kan Jami'inta Da Ake Zargi Da Karbar Kudi Ga Wani Mai Mota A Hanyar Mokwa

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa Kwastom ta dauki matakan ladabtarwa kan jami'inta da ake zargin ya karbi kudi har Naira dubu dari biyar daga wani wanda ya siyi mota mai suna Muhammad Dahiru Ahmad a hanyar Mokwa zuwa Jebba a jihar Niger.

Kwanturolan dake kula da shiyya ta 2 dake Kaduna, Kwanturola Dalha Chedi ne ya mika jami'in ga mataimakin shugaban sashin bincike na kwastam a shelkwatar sashin dake Kaduna a yau Juma'a 26 ga watan Fabarairu na 2024.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, Kwanturola Chedi ya tabbatar da cewa jami'in da ake zargin da aikata aikin na karbar rashawa jami'i ne na shiyyar da aka tura tawagar sintiri dake Mokwa a jihar Niger kuma lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis 22 ga watan Fabarairu k**ar yadda rahotan korafi ya nuna.

Ya ce "Jim kadan bayan samun labarin wannan abu na rashin jindadi. Na umarci sashin 'yan sanda na hukumar kwastom dake da alhakin yin ladabtarwa da su k**a jami'in kuma su kai shi Shelkawatar sashin dake Kaduna domin amsa tambayoyi. Haka kuma an gayyaci wanda ya shigar da korafin domin taimakawa wajen gudanar da bincike".

Acewarsa, kwanturola janar na hukumar hana fasa kwauri ta kasa, Bashir Adewale Adeniyi MFR da jami'an hukumar sun nuna bacin rai kan dabi'ar jami'in, " a don haka irin wannan abu, kwamitin ladabtarwa zasu yi aikinsu yadda yak**ata. Tabbas wannan hukumar tana tsayawa tsayin daka kan matakan ladabtarwa kuma wannan ma ba zai tafi a banza ba".

Ya mika jami'in da ake zargi ga mataimakin shugaban sashin 'yan sanda na hukumar domin fadada bincike.

"Anan nake mika jami'in nan ga mataimakin sashin 'yan sanda na hukumar Kwastom domin yin bincike kuma abinda bincike ya nuna za a mika shi ga shelkwatar hukumar hana fasa kwauri ta kasa domin daukar mataki, inda hukumar gudanarwar Kwastom wacce ke da alhakin dauka da kara matsayi ko hukunta jami'i zata dauki matakan da s**a dace".

Kwanturola Chedi yayi Alla-Wadai da abinda ake zargin jami'in yayi sannan yayi alkawarin cewa za a sanar da al'umma sak**akon binciken da aka samu ga al'umma.

"Wannan ya saba da ka'ida kuma baza a amince da shi ba. An fara bincike mai zurfi kan wannan batu. Za a sanar da al'umma kan abinda bincike ya nuna domin jan kunne ga masu hali irin nasa".

" Mun Damu Matuka, kuma muna tabbatarwa da al'umma cewa za a duba wannan lamari da gaskiya", inji shi.

Haka kuma ya bukaci al'umma kada su gajiya wajen baiwa hukumar goyan baya.

Makarantar Madarasatu Ta'alimul Qur'an Ma'adirasatul Islamiyya Wal-Arabiyya  Bakin Ruwa Ta Yaye Dalibai 43 Da S**a Sauke...
11/02/2024

Makarantar Madarasatu Ta'alimul Qur'an Ma'adirasatul Islamiyya Wal-Arabiyya Bakin Ruwa Ta Yaye Dalibai 43 Da S**a Sauke Al-Qur'ani

An gudanar da bikin saukar al-Qur'ani mai girma na Dalibai 43 na makarantar Madarasatu Ta'alimul Qur'an Ma'adirasatul Islamiyya Wal-Arabiyya dake unguwar Bakin Ruwa a karamar hukumar Dala anan cikin birnin Kano.

Taron bikin Saukar wanda ya kunshi Maza 6 da Mata 37 ya samu hala rtar masu unguwanni da Limamai na unguwar Bakin Ruwa da Ayagi da Dirimin Kaigama da 'Yar Kasuwa.

Da yake zantawa da gidan Rediyon Jami'ar Bayero, shugaban makarantar, Malam Hassan Sa'idu Sani wanda ya ce an kafa makarantar tun shekarar 2007 ya bayyana cewa kasancewar makarantar nada tarin dalibai suna neman karin muhallli wajen guidanar da karatunsu.

Haka kuma a jawabin da ya gabatar gaban iyaye da manyan baki da s**a halarci Saukar ya ce wasu dalibaan makarantar da aka yaye sun bude makarantu a jihohin Najeriya daban daban inda suke koyarwa.

A yayin taron bikin saukar dai, Liman Salisu Sani yayi jawabi kan Fasahohin Al'Qur'ani a yayin da Malama Ta Sallah Nabulisi tayi jawbi kan kula d tarbiyar matasa.

Suma wasu daga cikin daliban makarantar sun bayyana farin cikinsu kan kammala Saukar ta Al'Qur'ani mai girma.

A yayin bikin Saukar, Dr. Nura Salihu Adam wanda aka fi sani da Salihannur ya bada gudunmawar Naira dubu 50 ga Malam Makarantar sai daliban makarantar da aka rabawa Naira dubu 2 kowannensu, haka shima Alhaji Audu Ladiyo ya bada gudunmawar Naira dubu 100 ga makarantar .

An Buɗe Sabon Asibitin Da Ɗan Majalisar Jiha Na Tarauni Ya Gina A HotoroDaga Safiya UsmanAn shawarci masu ruwa da tsaki ...
09/02/2024

An Buɗe Sabon Asibitin Da Ɗan Majalisar Jiha Na Tarauni Ya Gina A Hotoro

Daga Safiya Usman

An shawarci masu ruwa da tsaki da ƴan siyasa da su haɗa hannu wajen ganin an inganta fanin lafiya a nan jahar Kano.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mataimakin Gwamna jahar Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya samu wakilcin kwamishina lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, a lokacin da aka buɗe sabon asibit na primary health care na Hotoro Dan marke Dake Karamar hukumar Tarauni.

A yayin buɗe asibitin wanda ɗan majalisa Tarauni, Hon Kabiru Dahiru ya samar kwamishinan ya kara da cewa tabbas wanan sabon asibit zai taimakawa mazauna yankin musamman a lokacin da ake buƙatar kulawa ta gagawa, sanan ya shawarci ɗan majalisa da ya ci gaba da bawa ɓangaren lafiya kulawa don samun lada Al'ummarsa.



Shima ana sa ɓangaren ɗan majalisar Tarauni Hon Kabiru Dahiru ya ce ƴana mai godiya ga maii grima gwamna jahar Kano bisa bashi goyon baya dan ganin ya kawo ci gaba a ɓangaren lafiya a Ƙaramar hukumar Tarauni, ya ce nan ba da jimmawa ba zasu kawo maguguna da za a rabawa marasa lafiya a sabon asibit.

Ɗan majalisar ya ce zai kawo ayyukan ci gaba, da Kuma inganta lafiyar alummar sa.


Mazauna yankin Hotoro Danmarke dake Ƙaramar hukumar Tarauni sun yabawa ɗan majalisar bisa sabunta musu wanan asibitin, tare da zuba sabin kayan aiki don inganta lafiyar Alummar yankin.

A karshe taron ya samu hartar manyan baki daga ciki da wajen jahar Kano.

Gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a yau yayin wani taro da 'yan kasuwar jihar domin lalubo hanyar magance tsadar rayuw...
05/02/2024

Gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a yau yayin wani taro da 'yan kasuwar jihar domin lalubo hanyar magance tsadar rayuwa da ake fama da shi.

Yanzu-Yanzu Masu Gurasa A Jakara Na Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Tsadar Kayayyakin Da S**a Hada da Fulawa Da S**ari
02/02/2024

Yanzu-Yanzu Masu Gurasa A Jakara Na Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Tsadar Kayayyakin Da S**a Hada da Fulawa Da S**ari

02/02/2024

Zanga-zangar lumana da masu Gurasa ke yi a Kano kan tsadar Fulawa.

Gwaman Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf  tare da Takwaransa na jihar Zamfara, Dauda Lawan Dare.
31/01/2024

Gwaman Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tare da Takwaransa na jihar Zamfara, Dauda Lawan Dare.

Rushe Masallatan Juma’a 2 Na Tumu Da Pindiga Ba Shi Ne Ribar Siyasa Ba ---Al’ummar Yankin Ga Sanata Danjuma Goje Masalla...
30/01/2024

Rushe Masallatan Juma’a 2 Na Tumu Da Pindiga Ba Shi Ne Ribar Siyasa Ba ---Al’ummar Yankin Ga Sanata Danjuma Goje



Masallatan Mu Sabbi Ne Bama Bukatar Rushe Su A Sake Wani Gini A Yanzu---- Masarautar Pindiga



Daga Abubakar Rabilu Gombe



Masarautar Pindiga da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe ta fitar da sanarwar cewa basu amince da aniyar Sanata Muhamamd Danjuma Goje, da ya nuna na rushe musu masallatan juma’ar garin Tumu da Pindiga dan sake gina su ba.



Sanarwar mai dauke da sanya hannun Sakataren Masarautar Mohammad Audi, a madadin masarautar, inda ta nuna cewa da yammacin ranar Litinin ne Masarautar da masu ruwa da tsaki na garuruwan Tumu da Pindiga tare da Hakiman su s**a yi taron gagggawa kan aniyar da Sanatan ya nuna na zai rushe musu masallatai ya sake gina su.



“Masallatan mu dukkan su suna da kyau basu da wata matsala tsarin su ma na zamani ne domin ba’a jima da sake gina su ba dan haka bama bukatar wani ya rushe su dan a sake gina su” inji Sanarwar.



Har ila yau sanarwar ta kara da cewa duk wani mai son ya yi wani abu a yankunan ba Masallatan zai rushe ba ya nemi wani aiki da ake da bukata ya yi musu amma abar musu masallatan su yadda suke.



A cewar su wata jita jita s**a ji tana yawo akan cewa Sanatan Gombe ta tsakiya Muhamamd Danjuma Goje, na cewa zai rushe masallatan ya sake gina wasu wanda suke ganin yin haka shisshigi ne wa gwamnati.



S**a ce da jin wannan jita-jitar ne s**a kira taron gaggawa na duk wani mai fada a ji a garin Tumu da Pindiga gami da Hakiman su s**a tattauna inda s**a zartar da matsaya na cewa ba za su yarda wani abu ya raba kan su ko ya kawo musu kowanne irin rudani ba.



“Bisa Ladabi da biyayya da kuma girmamawa mu al’ummar Tumu da Pindiga muna sanar da Sanata Danjuma Goje cewa bama bukatar wannan aiki a bar mana masalallatan mu yadda suke.




An Fara Hangen Hoton Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Da Shugaban Kasa Tinubu A Yayin Da Ake Yin Shirin Sulhu Tsakanin APC...
23/01/2024

An Fara Hangen Hoton Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Da Shugaban Kasa Tinubu A Yayin Da Ake Yin Shirin Sulhu Tsakanin APC Gandujiyya Da NNPP Kwankwasiyya

Shin kuna ganin Sulhu tsakanin jam'iyyun zai yi tasiri a jihar Kano?

18/01/2024
Za mu yi aiki tukuru don magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da kwacen waya a Kano - Gwamnatin KanoGwamnatin jihar Kano...
17/01/2024

Za mu yi aiki tukuru don magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da kwacen waya a Kano - Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta kafa kotun tafi da gidanka wadda za ta yi aiki tare da kwamatin kar ta kwana da gwamnatin jihar ta samar don magance matsalolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da kwacen waya a faɗin jihar wato (Kano State Government Committee on Illicit Drugs and Phone snatching).

Bakoji Jami'in hulda da Jama'a na kwamitin ya rawaito cewa shugaban kwamitin Birgediya Janaral mai ritaya Gambo Mai'adua ya sanar da hakan a wajen taron manema labarai da kwamitin ya gudanar a ranar Talata 12 ga watan Janairu, 2024. Inda ya ce kwamitin kar ta kwanan ya na da wakilci daga kowane sashen tsaro da ke jihar Kano.

"Za mu shiga kowanne lungu da sako Dan hukunta duk wani mai hada-hada ko ta'ammali da miyagun kwayoyi. Haka kuma za mu dinga kai masu shaye-shaye gidan gyaran tarbiyya domin su dawo cikin hayyacinsu."

Bakoji ya kara cewa Birgediya Mai'adua ya nemi gwamnatin Kano da ta kara ba su haɗin kai wajen samun nasarar aikin, domin kwamitin a shirye ya ke Kamar yadda Gwamnatin itama shirye take don ganin an kawo karshen matsalar shan miyagun kwayoyi da kwacen waya a faɗin jihar Kano.

Mene ra'ayinku da shawarwarinku akan kwamitin?

Tawagar Gwamna Abba Kabir Yusuf  kenan yayin da ta nufu jihar Kano bayan samun nasara a kotun kolin kasarnan.
14/01/2024

Tawagar Gwamna Abba Kabir Yusuf kenan yayin da ta nufu jihar Kano bayan samun nasara a kotun kolin kasarnan.

12/01/2024

Bidiyo: Yanzu-Yanzu: Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya isa kotun koli inda za ta yanke hukunci kan shari'ar zaben Kano a wannan rana.

Hotuna: Yadda Rundunar Kare Fararen Hula da Kadarorin Gwamnati ta Civil Defense ta gudanar da bikin kara girma ga jami'a...
09/01/2024

Hotuna: Yadda Rundunar Kare Fararen Hula da Kadarorin Gwamnati ta Civil Defense ta gudanar da bikin kara girma ga jami'anta 385 a Kano.

Taron ya samu halartar wakilai daga hukumomin tsaro da jami'an gwamnati da Sarakuna.

Yadda sabon Bidiyon Waƙar Tarko ke haskawa a masana'antar KannywoodDaga Ibrahim HamisuKamfanin Bee Safana production Pla...
02/01/2024

Yadda sabon Bidiyon Waƙar Tarko ke haskawa a masana'antar Kannywood

Daga Ibrahim Hamisu

Kamfanin Bee Safana production Place ya fito da wani sabon Bidiyon waƙa mai suna TARKO, wanda fitaccen Jarumi a masana'antar Kannywood Daddy Hikima (Abale) da fitacciyar Jaruma mai haskawa Bilkisu Bee Safana s**a fito a ciki,

Wakar wacce ta fito da sabon salo mai ban sha'awa ta samu karɓuwa kuma tana kan samu a daidai wannan lokaci. Bidiyon waƙar ya nuna yadda wani azzalumin shugaba ke k**a wata budurwa (Bee Safana) ya daddaureta da igiya yayin da shi kuma masoyinta (Abale) ya ke zuwa yana arangama da wadannan mutanen mutane don ganin ya kwato kwato masoyi yar ta, amma duk a cikin waƙe,

Bee Safana hakika ta taka rawar ban mamaki, ganin irin yadda aka daddaureta da igiya a wakar, wanda wannan ba kowace Jaruma ba ce za ta iya hakan,

Babban darakta a Masana'antar Kannywood wanda shi ne Furodusan waƙar Kamilu Ibrahim Dan Hausa ya bayyana cewa abubuwa uku ne s**a sanya waƙar farin jini inda ya ce:

"Abu na farko shi ne mun yi amfani da salo wanda ba'a saba gani ba a Kannywood wanda wasu ma da dama gudinsa suke, na biyu mun yi amfani da Jarumai da ake yayi wato Daddy Hikima wato (Abale)da kuma Jurumar wakar Bilkisu Bee Safana da take tashe a yanzu,

"Sai abu na uku shi ne mun samar da mutane 500 da s**a fito a wakar, sannan muka samu kwararru da s**a gina mana alkarya, inda za'a ga cewa wani Azzalumin shugaba ne ya ke k**a karya yake garkuwa da mutane da amfani da miyagun kwayoyi duka dai don masu kallo su Nishadantu to wannan ya sa wakar ta samu karɓuwa a cikin al'umma" a cewa Kamilu DanHausa,

Bidiyon waƙar wanda ya fito a yan kwanakin nan na sabuwar shekarar 2024 za'a iya kallonsa a kafar YouTube da kuma shafin Daddy Hikima Yu tube.

Address

Nasarawa GRA
Kano
23471

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Prime Time News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Prime Time News Hausa:

Videos

Share

Nearby media companies


Other News & Media Websites in Kano

Show All