31/12/2023
Kaɗan daga Illoli dake tare da kallon fina-finai (Na series da mak**antansu)
1. Tozartar da lokaci ga barin ayyuka masu muhimmanci na ibada da na cigaban rayuwa.
2. Tozartar da dukiya, ta hanyar sayen data, subscription, chajin waya, biyan kuɗin turi da sauransu.
3. Tozartar da lafiya, ɗaukar lokaci mai tsayi ana kallon screen ɗin TV ko na waya akai-akai musamman acikin duhu yana iya cutarda lafiyar idanu.
4. Wahalar da tunani, ta yadda mai kallo zai yi ɓacin rai, kuka, farin ciki, fargaba, tausayi, alhini na babu gaira ba dalili. Halin da al'umma ke shiga na tsanani da tsaka mai wuya baya sanya mutum kuka da alhini sai shirin fina-finai na ƙarya, alama ce ta rafkana.
5. Daƙile karatu, ga 'yan makaranta manya da yara, yakan zaman silar faɗuwa jarabawa, resit, carryover, withdraw da mak**antansu. Ko ya hana ɗalibai samum kyakyawan sak**ako.
6. Saɓon Allah, cikin kaso 99% na fina-finan zamani ba'a rasa dokar Allah guda ko sama da haka da aka karya, don haka akwai laifi akan masu shiryarwa, dillanci da masu kallo. Wasu fina-finan ma saɓon Allah shine mafi rinjaye.
7. Makantar zuci, duk wanda ya musanya Ambaton Allah da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe da sannnu zuciyarsa zata makance har ya zamto bata sha'awar ayyukan ɗa'a, kuma bazai sami haƙiƙanin nutsuwar ruhi ba.
8. Shagala, ta yadda mutum zai rafkana ga barin tunanin mutuwa, hisabi, makomarsa ta lahira da ƙoƙarin yin guzurin gobe Alƙiyama.
9. Gurɓatar tarbiyya, cikin kaso 90 na fina-finan zamani ba'a rasa mummunar ɗabi'a guda ko sama da haka wacca mutum zai iya koya cikin sauƙi ko ya sake zurfi a cikinta.
10. Gurɓatar tunani, ta yadda mutum zai dinga gwada rayuwar labari, mafarki, ƙirƙire da ta gaske (ta zahiri). Galibi rayuwar da ake nunawa cikin fina-finai tayi nisan nesa da rayuwar zahiri, dazarar mutum ya tasirantu da irin wannan rayuwar hakan zai jefa shi cikin ɗimuwa, ƙunci da rashin wadatar zuci a rayuwarsa.
Allah ya bamu ikon gyarawa!
18 Jumada II 1445 AH.
31th December, 2023.
Umar Sa'ad Abdullahi ✍️
_