Taskar Jaridu

Taskar Jaridu Taskar Jaridu Shafin Samar da labarai Na Cikin Gida Har Da Kasashen Ketare, Kana Da Kuma Isar Da Koken Talakawa Zuwaga Shugabanni Cikin Gaggawa...

Labarin da wasu ke yaďawa akan cewa Kasar Saudiyya ta ďauki Farfesa Maqary Limanci ba Gaskiya bane, Daga Sheikh Mustapha...
21/08/2022

Labarin da wasu ke yaďawa akan cewa Kasar Saudiyya ta ďauki Farfesa Maqary Limanci ba Gaskiya bane, Daga Sheikh Mustapha Adinga

In akwai wanda yafi fir,auna zalinci dashi ya kamata a kwatanta buhari saboda shi fir,auna baya cutar da masoyansa Amma ...
25/07/2022

In akwai wanda yafi fir,auna zalinci dashi ya kamata a kwatanta buhari saboda shi fir,auna baya cutar da masoyansa Amma buhari kashe su ma yakeyi 🤧

Parfesa Suleiman Sanadi

Allah ya jikan Nura Mustapha Waye..
03/07/2022

Allah ya jikan Nura Mustapha Waye..

Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya gargaɗi magoya bayansa da su rinƙa ha...
03/07/2022

Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya gargaɗi magoya bayansa da su rinƙa haƙuri da ra'ayoyi mabambanta na ƴan Najeriya don kada hakan ya hana yin maja da wasu jam'iyyu a nan gaba.

Mista Obi ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya gode wa magoya bayan nasa dangane da irin haɗin kan da suke ba shi.

Jan kunnen nasa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa yunurinsu na yin haɗaka da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, bai yi nasara ba saboda sun kasa daddalewa kan wanda za a mara wa baya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa duk da an san halin da ake ciki a Najeriya na fushi da takaici, "ya zama wajibi a yi amfani da kuzarin da ake da shi wurin samun goyon bayan wasu da kuma haɗin kai".

Obi ya yi kalaman ne bayan Rabiu Kwankwaso ya ce ba zai iya zama mataimakin wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓen 2023.

Waɗannan kalamai na Kwankwaso sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta, inda magoyan Obi s**a dinga s**arsa da kalamai marasa daɗin ji.

Gimbiya Online ✍

Dalibai yan asalin jihar Kano sun yi tur da tofin Allah tsine ga shugaban kungiyar daliban Comr Yahya Usman Kabo bisa si...
24/06/2022

Dalibai yan asalin jihar Kano sun yi tur da tofin Allah tsine ga shugaban kungiyar daliban Comr Yahya Usman Kabo bisa siyasantar da kungiyar daliban da yake yi da sunan neman kuɗi.

Daliban sun kara bayyana cewa shugaban nasu babu abinda yake yi sai son zuciya tare da nuna dalibai a matsayin kwadayayyu alhali miyarsa kawai yake wankewa da sunan dalibai.

Cikin fushi wani dalibi mai suna Muhammad Musa ya sake jaddada cewa duk abinda shugaban yake yi cin mutuncin dalibai yan asalin jihar Kano ne kuma suna Allah wadai da abinda yake yi.

Wannan duk yana biyowa ne bayan shirin da shugaban daliban yayi ma yin taron marawa APC baya a jihar Kano a ranar Lahadi mai zuwa.

Rahotan: Nigerian New's Hausa

"An gano wasu biliyoyin kudade a gidan buratai dake Abuja, kudaden da ake kaddara na makamaine da gwamnati ta bayar.
23/06/2022

"An gano wasu biliyoyin kudade a gidan buratai dake Abuja, kudaden da ake kaddara na makamaine da gwamnati ta bayar.

Musulmi Dan Shekara 30 Ya Auri Kirista Mai Shekaru 75 A Jamus Daga Barista Nuraddeen Isma'eel"Wani matashin balarabe Dan...
22/06/2022

Musulmi Dan Shekara 30 Ya Auri Kirista Mai Shekaru 75 A Jamus

Daga Barista Nuraddeen Isma'eel

"Wani matashin balarabe Dan asalin kasar Iraqi mai suna Muhammad, ya auri wata tsohuwa mai shekaru 75 ita kuma haifaffiyar kasar Jamus."

"Rahoton yacigaba da bayyana cewa! Ya hadu da baturiyarne mai suna Jessica a kasarsu ta jamus bayan sharfe shekaru 7 yana zaune a kasar."

"Majiyar bai boye Mana komaiba; inda Matashi Muhammad s**a kwashe wasu lokuta masu tsayin gaske suna soyayya da juna, bisani baturiya Jessica taji Kawai burinta ta auri wannan matashi, ba'ayi wata-wataba baturiyan ta fara bude masa ido da kudi, kanama hadda bashi mota ta miliyan "350" a domin ya fattama a gari."

Daga karshe dai Muhammad ya yarje an daura masa aure da Jessica."

2023 | Engr Abubakar Matazu  Yayi kira Ga kungiyoyi da Matasa cewa suyi structure tun daga mazaba {poling Unit} zuwa sam...
22/06/2022

2023 | Engr Abubakar Matazu Yayi kira Ga kungiyoyi da Matasa cewa suyi structure tun daga mazaba {poling Unit} zuwa sama, saboda kuri'a daga mazabu ake kirgata,

kuma yayi kira Ga Al'ummar Jihar Katsina kan Su Fito ƙwansu da Ƙwarkwata Suyi wa Dr Dikko Umar Raɗɗa Ruwan ƙuri'u a babban zaɓe Mai zuwa na 2023 Domin kawowa jihar Katsina Cigaba..

Kasan Cewar Gwagware Katsina Dr Dikko Umar Raɗɗa Kan kujerar Gwamnan Jihar Katsina Abun alfahari ne
Saboda zai tsaya a ko'ina a duniya ya kare martabar jahar shi ko a gaban waye ba zaaji kunya ba. Kuma zaka bugi gaba kace wannan Gwamna na ne.

Kuma in mukayi tawakkali ga Allah, to lallai Allah zai kawo mana Canje-canje Masu Yawa, Kamar Fannin Lafiya, Fannin Ilmi, Bunƙasa Tattalin arzikin Jiha, Fannin tsaro, da Raya Gari..

Injiniya Abubakar Matazu Ya ƙara Da Cewa" Tabbas a daidai Irin Wannan Lokacin Jihar Katsina tana Buƙatar Gwarzo, Jajirtacce Mai ilmin Islama da Boko wanda ya mika ma Allah tafiyar shi gabadaya kuma Allah ya shige mashi gaba kamar PhD Dr Dikko Raɗɗa.

Allah yayi mana jagora Duniya da lahira ameen

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN Babban Limamin Masallacin Juma'a Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna Ya RasuAllah Ya ...
22/06/2022

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN

Babban Limamin Masallacin Juma'a Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna Ya Rasu

Allah Ya Yi Wa Babban Limamin Masallacin Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna, Sheikh Dahiru Lawal Abubakar Rasuwa.

Ya Rasu A Asibitin Sojoji Ta 44 Bayan Yar Gajeruwar Rashin Lafiya.

Za'a Yi Jana'izarsa Da Misalin Karfe 1:00 Na Rana A Masallacin Juma'a Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Ƴan Najeriya Sun Gaji Da Jam’iyyun PDP Da APC, Cewar Gwamnan Jihar EdoGwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce ‘yan Nije...
22/06/2022

Ƴan Najeriya Sun Gaji Da Jam’iyyun PDP Da APC, Cewar Gwamnan Jihar Edo

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce ‘yan Nijeriya ba su da sha’awar manyan jam’iyyun siyasar kasar nan guda biyu – PDP da APC, kawai suna neman canji ne.

Obaseki yayin da yake hira da gidan Talabijin na AIT, bayan Kammala zaben gwamnan jihar Ekiti, ya bayyana cewa makomar siyasar kasar nan tana canzawa.

Gwamnan Edo ya ce, “Ta yaya PDP a tarihin ta na girma ace ba ta yi nasara Ba? Ba ta zo na biyu ba ma.

Don haka, za ku iya ganin cewa wani abu yana faruwa. Makomar siyasarmu a kasar nan tana sauyawa.

Dalilin Da Ya Sa INEC Ta Karɓi Sunan Sanata Ahmed Lawan Wanda Bai Shiga Takara Ba, Maimakon Na Shariff Machina Wanda Ya ...
21/06/2022

Dalilin Da Ya Sa INEC Ta Karɓi Sunan Sanata Ahmed Lawan Wanda Bai Shiga Takara Ba, Maimakon Na Shariff Machina Wanda Ya Lashe Zaɓe, Inji Kwamishinan Zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana dalilan da ya sa ta aikata abin da wasu su ka yi wa fahimtar cewa kamar ta yi son kai wajen karɓar sunayen wasu 'yan takara da ake ganin cewa ba su shiga zaɓen fidda gwani ba.

Sunan Sanata Ahmad Lawan, wanda shi ne Shugaban Majalisar Dattawa, ya bayyana a jerin sunayen 'yan takarar da APC ta damƙa wa INEC alhali ko takarar zaɓen fidda gwani bai shiga ba.

Sai dai kuma INEC ta ƙi karɓar sunan tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, wanda shi ma takarar shugaban ƙasa ya tafi kamar Lawan, sai daga baya ya garzaya neman takarar sanata a makare.

Lawan dai bai shiga takarar sanata ba, takarar shugaban ƙasa ya shiga, amma sai ga sunan sa APC ta bayar ga INEC a matsayin halastaccen ɗan takarar da ya ci zaɓen fidda gwani.

Yayin da Kwamishinan INEC na Tarayya da ke Jihar Akwa Ibom Mike Igini ya haramta wa Akpabio shiga jerin 'yan takara, shi kuwa Lawal ya samu shiga kai-tsaye, duk kuwa da ƙorafi da barazanar da wanda ya lashe zaɓen ya yi.

Wannan ne ya sa masu sharhi, lauyoyi da 'yan siyasa ke cewa INEC ta nuna son kai, ta ƙi yi wa Machina adalci, sannan ta fifita Lawan kan Akpabio.

A martanin da Mohammed Haruna na INEC ya yi wa marubuci Farooq Kperogi, ya bayyana cewa, "INEC ba ta da ikon ƙin karɓar ko ma sunan wanene jam'iyya ta kai mata.

"Jam'iyya ce ke da ikon gudanar da zaɓe, ita kuma INEC doka cewa kawai ta yi ta je ta sa ido ta ga yadda aka gudanar da zaɓe, ta kai rahoto a hedikwata, idan an bi ƙa'ida ko ba a bi ba.

"Ƙarfin INEC a nan shi ne duk wanda ya kai ƙara kotu cewa an yi masa rashin adalci a zaɓen, to da rahoton mu zai yi amfani ya kai ƙara, kotu ta ƙwatar masa takarar sa."

Kafafen yaɗa labarai sun ba da labarin yadda Akpabio ya shiga zaɓe a makare, da kuma yadda kotu ta haramta wa INEC ta haramta wa APC shiga zaɓen gwamna a Jihar Akwa Ibom.

Sannan kuma an buga labarin da Machina ya ce canja sunan sa da na Sanata Lawan rashin mutunci ne, zai garzaya kotu.

Bashir Machina, wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin APC na Sanatan Yobe ta Arewa, ya bayyana cewa ya yi mamakin ganin yadda APC ta maye sunan sa da na Lawan a jerin sunayen da ta miƙa wa INEC.

Ya ce ya yi mamaki, amma dai ya na fatan kuskure aka tafka, kuma shi ne halastaccen ɗan takarar, wanda ya shiga zaɓen fidda gwani, kuma ya samu ƙuri'u 280, alhalin Sanata Lawan ko takara bai shiga ba.

Machina, wanda tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Harkokin Jiragen Ruwa ta Ƙasa ne, ya ce maye sunan sa da sunan Lawan rashin mutunci ne kuma tantagaryar rashin imani ne.

Lawan dai ya yi watsi da shiga takarar sanata, ya shiga takarar shugaban ƙasa. Sai bayan da ya janye a ranar zaɓen fidda gwani ne, bayan nasarar Bola Tinubu, sai ya zabura neman kujerar sanata, ko ta halin ƙaƙa, bayan an yi zaɓe, har Machina ya yi nasara.

Sashe na 31 na Dokar Zaɓe ya ce za a iya canja sunan ɗan takara idan ya mutu ko kuma ya janye don kan sa, ta hanyar rubuta wa INEC wasiƙar sanarwar janyewar.

Machina, wanda ya taɓa yin ɗan Majalisar Tarayya a Jamhuriya ta Uku, ya yi gargaɗin idan ba a mai da sunan sa ba, zai yi ƙara.

Ahmed Lawan ya fafata zaben fidda gwani na Sanatan Yobe kuma shine yayi nasara ~ shugaban APC
21/06/2022

Ahmed Lawan ya fafata zaben fidda gwani na Sanatan Yobe kuma shine yayi nasara ~ shugaban APC

An gwangwanje iyayen wacce tayi batanci ga Manzon Allah a jihar Sokoto Deborah da katafaren gidan cin abinci da jari mai...
21/06/2022

An gwangwanje iyayen wacce tayi batanci ga Manzon Allah a jihar Sokoto Deborah da katafaren gidan cin abinci da jari mai nauyi.

Apostle chibuzer yace anyi hakan ne domin rage musu raɗadin kisan gillar da aka yiwa yar ta su Deborah wacce take daliba ce a jihar Sokoto.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Mu musulmi mun dauka Al-Qurani tare rantsuwa cewa za muyi adalci kuma wallahi Adalcinnanfa sai mun yi___El-rufai
20/06/2022

Mu musulmi mun dauka Al-Qurani tare rantsuwa cewa za muyi adalci kuma wallahi Adalcinnanfa sai mun yi___El-rufai

Ya kamata 'Yan Najeriya su waye na ganin suna zabo nagartattun shuwagabanni ba wai don jam'iyyar su ba. ~Inji Petter Obi
20/06/2022

Ya kamata 'Yan Najeriya su waye na ganin suna zabo nagartattun shuwagabanni ba wai don jam'iyyar su ba. ~Inji Petter Obi

RADDI  | Kaida akayi zaɓen Fitar da gwani a immediate Constituency ɗinka Musawa/Matazu aka kashe mutane s**a mutu har la...
19/06/2022

RADDI | Kaida akayi zaɓen Fitar da gwani a immediate Constituency ɗinka Musawa/Matazu aka kashe mutane s**a mutu har lahira, kuma sauran Yantakarar s**afice daga Jamiyyar kana mataimakin Shugaban Jam'iyya..

Sakon Sakataren Jam'iyyar APC na Jihar Katsina Ga mataimakin Shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina..

kaida yakamata kanemarma Jamiyyar APC Nasara da haɗe kan sauran yantakara domin kada su fice APC kuma kaine kake ikirarin Zaka Kori Mutane daga APC Kuma kana ikirarin gara Jamiyyar ta fadi zaɓe..

Yakamata wanan shugaban asamashi alamar Tambaya..

Shiga Wannan Link domin kallon cikakkiyar Firar da akayi da akayi da Sakataren Jam'iyyar APC na Jihar Katsina Malam Sh*tu S. Sh*tu..

👇👇👇
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10217507217152871&id=1849742066

Kudaina kashe sauro yayin da yake cizonku, sakon wani baturen faransa Mai fafutukar kare hakkin dabbobi...
19/06/2022

Kudaina kashe sauro yayin da yake cizonku, sakon wani baturen faransa Mai fafutukar kare hakkin dabbobi...

"Yan Nijeriya basa binmu bashin matsalar tsaro domin kuwa gwamnati na ta kawo karshen ta'addanci___"Inji Buhari
18/06/2022

"Yan Nijeriya basa binmu bashin matsalar tsaro domin kuwa gwamnati na ta kawo karshen ta'addanci___"Inji Buhari

Duk Arewa Babu Jagoran Talakawa Irin Kwankwaso ~ Professor Wole Soyinka Fitaccen Marubucin Nan Na Duniya Wanda Ya Shahar...
18/06/2022

Duk Arewa Babu Jagoran Talakawa Irin Kwankwaso ~ Professor Wole Soyinka

Fitaccen Marubucin Nan Na Duniya Wanda Ya Shahara A Nahiyar Africa Dama Duniya Baki Daya professor Wole Soyinka Ya Bayyana Kwankwaso A Matsayin Jogaran Da Yafi Kaunar Talakawa A Duk Fadin Arewa

*Soyinka Ya Bayyana Cewa -Duk Fadin Arewa Babu Mutumin Dake Son Ganin 'Ya'yan Talakawa Sunyi Karatu Kamar Eng. Rabi'u Musa Kwankwaso- Cewar wole soyinka

Sannan Ya Bayyana Kwankwaso A Matsayin Mutum Mai Mutukar Kishin Yankinsa Na Arewa Wanda Ya Kamata Ace Mutanen Arewa Sun Bawa Goyon Baya Fiye Da Sauran Yan Siyasa

Shin Kun Amince Da Wannan Magana Ta Professor Wole Soyinka Kuwa?

Matukar 'Yan Nijeriya s**a rasa ni a matsayin shugaban ƙasa ko sun Roƙeni na kuma fitowa takara a shekara na gaba ba Ko ...
17/06/2022

Matukar 'Yan Nijeriya s**a rasa ni a matsayin shugaban ƙasa ko sun Roƙeni na kuma fitowa takara a shekara na gaba ba Ko kallon su Bazan ba ~Inji Peter Obi

Wannan itace kasuwar Hausawan Delta ta Abaraka wadda Gwamnan Jihar Okowa ya Ruguza ta Kuma ya tashe su daga wurin...
16/06/2022

Wannan itace kasuwar Hausawan Delta ta Abaraka wadda Gwamnan Jihar Okowa ya Ruguza ta Kuma ya tashe su daga wurin...

ABIN A YABA | Wani Sanata A Jihar Kogi Ya Biyawa Wasu Daliget Musulmi su 5 kujerun Aikin Hajji Yayin da S**a dawo masa K...
16/06/2022

ABIN A YABA | Wani Sanata A Jihar Kogi Ya Biyawa Wasu Daliget Musulmi su 5 kujerun Aikin Hajji Yayin da S**a dawo masa Kuɗinsa bayan An hana su zaɓarsa...

Daga Falalu Lawal Katsina

Sanatan Mai Suna Smart Adeyemi ya ce abin da s**a yi yasa ya ƙara girmama musulunci don sun fada masa cewa haramun ne kuɗin a wurin tunda ba su zaɓe shi ba.

Ya kuma ce su rike kudin a matsayin kyauta saboda gaskiya da rikon amana da s**a nuna.

HOTUNA | Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Halarci Bikin Yaye Jami'an Ƴan Sanda Na Makarantar Horas Da Jami'an Ƴan Sanda...
16/06/2022

HOTUNA | Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Halarci Bikin Yaye Jami'an Ƴan Sanda Na Makarantar Horas Da Jami'an Ƴan Sanda Dake Wudil A Jihar Kano Yau ALHAMIS..

MATAIMAKIN ATIKU ? Ifeanyi Arthur Okowa, shekararsa 63. A yanzu gwamna ne mai ci a zango na biyu daga jam'iyyar PDPi na ...
16/06/2022

MATAIMAKIN ATIKU ?

Ifeanyi Arthur Okowa, shekararsa 63. A yanzu gwamna ne mai ci a zango na biyu daga jam'iyyar PDPi na jihar Delta, Dan siyasa ne gidi kuma kwararren likita. Ya taba zama sakataren karamar hukuma. Ya rike kwamishina a ma'aikatu biyar daga 1999-2011. Ya rike mukamin sakataren gwamnatin jihar Delta. Ya taba zama zababben Sanata. Yanzu kuma shi ne wanda Atiku Abubakar zai hada sunansa a mikawa INEC domin ya rufa masa baya a zaben 2023 a karkashin jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP tana da gwamnoni 13, biyar a arewa, takwas a kudu.

~ Bello Muhammad Sharada

Zaɓen 2023: Rarara Ya Waƙe Bola Tinubu, Ya Saka Gasar Bidiyon Waƙar Inda Zai Raba Motoci FITACCEN mawaƙin siyasa, Dauda ...
16/06/2022

Zaɓen 2023: Rarara Ya Waƙe Bola Tinubu, Ya Saka Gasar Bidiyon Waƙar Inda Zai Raba Motoci


FITACCEN mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya taya ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar lashe zaɓen fidda-gwani da ya yi a ranar Asabar ta makon jiya.

Haka kuma ya rera masa waƙa tare da bayyana gasar bidiyo inda zai ba gwaraza kyautar motoci da manyan wayoyi samfurin Iphone-13.

Rarara, wanda shi ne shugaban mawaƙan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC na Arewa, ya miƙa saƙon taya murnar ne kwana ɗaya da bayyana Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyya a babban zaɓen 2023 a wani bidiyo da mai taimaka masa a harkar soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya fitar a dukkan shafukan sada zumunci na mawaƙin.

Da farko dai Rarara ya ce, “Babu abin da za mu ce wa Allah sai godiya. Babbar nasara da aka samu an yi zaɓe lafiya, an gama lafiya. Wanda mutum ya tara mutane dubunnai ko miliyoyi a wuri ɗaya don a haɗu a yi wani abu da ya fuskanci ƙasa, a ce an samu dama Allah ya yi mana iko, Allah ya taimake mu an yi an gama lafiya, babu abin da ya fi wannan daɗi.”

Ya ƙara da cewa, “Sai kuma godiya da zan yi ga su daliget, waɗanda su ka yi namijin ƙoƙari wurin turzawa da zakuɗawa su zaƙulo mana nagartaccen mutum ɗan siyasa, wanda ya san darajar siyasa, ya san mutuncin ‘yan siyasa. Ka ga wannan ba ƙaramin jin daɗi za a yi ba.

“Ina godiya ga shugaban ƙasa, shugaban jam’iyya, shugabannin wannan gwamnati, waɗanda su ka gabatar da wannan zaɓe, dole a yi masu ban-gajiya. Mutane sun kwana a wuri don a tabbatar da zaɓe cikin adalci.”

Rarara ya ci gaba da cewa, “Ni kowa ai nawa ne. Ina kira ga su ‘yan takara, ai da ma abu ne jam’iyya da aka yin zaɓe wanda Allah ya ba shi ne. Allah ba ya sabon aiki, da ma Allah ya riga ya zaɓi Malam Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar APC da yardar Allah kuma shugaban ƙasar Nijeriya.

Karanta kuma Tinubu na cikin tsaka-mai-wuya
“Ni kira na ga ‘yan takara, mu zo mu haɗa kan mu jam’iyya mu dai jam’iyyar mu ce, duk inda za ka je babu inda ya fi gidan ka. Saboda haka mu zo mu yi ƙoƙari duk bakin ƙoƙarin da za mu yi, mu yi ƙoƙari mu ga mun haɗa kan jam’iyyar nan, yadda bakin gwargwado mu ga mun ɗora wannan ɗan tahaliki ya zama shugaban ƙasa, wanda kuma mu zo mu fuskanci Nijeriya da kuma abin da ya kamata mu taimaki ƙasar mu da ‘ya’yan mu.”

Dangane da waƙa da ake zaton kila zai fitar nan ba da daɗewa ba, Rarara ya ce, “Ai da ma na ce duk wanda ya ci zaɓe za a ji waƙar da zan yi masa. Ai da ma ɗan jam’iyya ta ne, duk ɗan jam’iyya ta idan ya ci da ma haka mu ke fata.

“Mu abin da mu ka so da mu ka yi magana, ai da ma cewa mu ka yi a yi dimokiraɗiyya, kuma ita da ma dimokiraɗiyyar nan ita ta kawo kowa. Saboda duk lokacin da aka ce wane, wani zai ce shi ba a kyauta masa ba, inda an bari an yi zaɓe, inda kaza, to yanzu zaɓen aka ce a yi.

“Inda shugaban ƙasa ya burge ni, inda ya ce a’a ai gaba ɗaya kowa ma ya dawo a yi zaɓe. Da an ce an sasanta an bar wa Kudu, sai aka ce a’a kowa ma ya na da damar ya shiga, ka ga yanzu an ba wa kowa ƙuri’a, wani ma ya cewa ai shi zai ci zaɓe, shi zai yi kaza, amma ana shiga zaɓen sai Allah ya nuna wanda ya riga ya tsara zai zama. Nan da zuwa gobe za ka ji abin da ni kuma zan faɗa.”
!
Ko yaya batun sauran jam’iyyu? Sai ya kada baki cikin dariya ya ce, “Duk wata jam’iyya da ta ke rara-gefen ta ko kuma tashen kumfar kilin, ai ana faɗa masu Bola Tinubu ne kowa hankalin sa ya tashi, duk wata jam’iyya yanzu – ba jam’iyyar PDP kawai ba, duk wata jam’iyya irin masu tashen kumfar kilin ɗin nan – yanzu hankali ya tashi, saboda an ce Asiwaju ne. Shi kuma Asiwaju an san ɗan siyasa ne gogagge, ‘grassroot’ ɗin siyasa, wanda duk inda ka je akwai tushen sa ko kuma akwai furen shi ko kuma akwai jijiyar shi. Saboda haka mutum ne wanda shi ɗan siyasa ne, ya san darajar ‘yan siyasa, ya kuma iya tafi da ‘yan siyasa. Saboda haka ba za a samu tasgaro ba a wannan tsarin, zaɓe ‘full’ na gaya maka, cin zaɓe da wuri ma in Allah ya yarda.

“Ni da ma ko a jiki na, duk wanda da ma ya ci zaɓe shi ne nawa.

“Ina yi mana fatan alkhairi gaba ɗaya. Ina ƙara yi wa daliget godiya na wannan ƙoƙari da su ka yi, dole a gode masu. Mun gode, mun gode!

“Kuma in Allah ya yarda za su ga amfanin wannan abu da su ka yi, za su ga amfanin zaɓen Asiwaju da su ka yi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

“Akwai abin da ya sa na ke cewa daliget sun mana ƙoƙari, saboda mun ɗan samu matsala. Akwai waɗanda aka ba muƙamai wanda in ka je wurin su sai su ce su ba ‘yan siyasa ba ne. Asiwaju ko shi ba zai yi maka haka ba. Idan za ka ce kai ba ɗan siyasa ba ne, ba ka isa ka shiga ‘system’ ɗin gwamnatin shi ba, saboda siyasa ne ta kawo ‘yan jam’iyya dukkan mu kan mu a haɗe ya ke. Ba za ku gane wannan ba sai an shiga akwatin zaɓe, duk wani ɗan takara da ya ke rawar ƙafa (dariya) zai gane da ruwa ake shayi! Na gode.”

A ranar Alhamis, Rabi’u Garba Gaya, mai taimaka wa mawaƙin a ɓangaren soshiyal midiya, ya fara gutsura wa duniya ‘yar guntuwar waƙar da ba ta wuce ta sakan goma ba. Nan da nan jama’a su ka fara tambayar cikakkiyar waƙar, inda a safiyar Juma’ar su ka sanar da lokacin da za su saki cikakkiyar waƙar.

Duk inda ka leƙa yanzu a shafukan sada zumunci za ka ji waƙar kawai ake ɗorawa.

A wannan karon ma dai mawaƙin ya yi abin da ya saba yi lokaci zuwa lokaci idan ya saki sabuwar waƙa na saka gasa.

Fitaccen furodusa Abubakar Bashir Maishadda da fitacciyar jaruma A’ishatul Humaira sun sanar da saka gasar waƙar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’ a jiya Asabar, 11 ga Yuni, 2022. Ga yadda gasar waƙar za ta kasance.

Waɗanda su ka lashe gasar daga na 1 zuwa na 3, za su samu kyautar mota kowannen su, daga na 4 kuma zuwa na 10 za a ba su kyautar wayar hannu ƙirar Iphone-13.

Su kuma ‘yan Instagram da Facebook bidiyon waƙar za su yi wanda bai wuce ƙasa da minti biyu ba ‘standard’, a gefe da gefe kuma za su saka hoton Tinubu da hoton APC. Su ma waɗanda su ka lashe gasar daga na 1 zuwa na 3 za su samu kyautar mota kowannen su, daga na 4 zuwa na 10 kuma kyautar waya ƙirar Iphone-13. Duk wanda ya yi bidiyon zai ɗora a shafin sa, sannan ya yi amfani da hashtag kamar haka .

Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden zai kai ziyara Saudiyya da Isra'ilaShugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Gabas ta Ts...
15/06/2022

Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden zai kai ziyara Saudiyya da Isra'ila

Shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Gabas ta Tsakiya a karon farko a matsayinsa na shugaban ƙasa.

Ana sa ran shugaban zai kai ziyara ƙasashen Saudiyya da Isra'ila da kuma wasu yankunan Palestine.

Shugaban zai yi tafiyar ne a watan Yuli mai zuwa inda zai shafe kwana huɗu yana rangadi.

Mista Biden dai zai kafa tarihi a matsayinsa na Shugaban Amurka idan ya je Saudiyya daga Isra'ila - hanya ce ta jirgi da Saudiyya ba ta cika bari ana bi ba sakamakon rashin jituwa irin ta diflomasiyya tsakanin Isra'ila da Saudiyya.

Ayarin Motocin Shugaban Karamar Hukumar Ungogo Dake Jihar Kano
15/06/2022

Ayarin Motocin Shugaban Karamar Hukumar Ungogo Dake Jihar Kano

Gwamnan Jihar Rivers, Nysom Wike Ya Samu Nasarar Lashe Zaɓen Kwamitin Fitar Da Mataimakin Shugaban Kasa Na Jam'iyyar PDP...
14/06/2022

Gwamnan Jihar Rivers, Nysom Wike Ya Samu Nasarar Lashe Zaɓen Kwamitin Fitar Da Mataimakin Shugaban Kasa Na Jam'iyyar PDP, Inda Ya Samu Kuri'u 16 Abokin Takararsa, Gwamnan Jihar Dalta, Okowa Ya Samu Kuri'u 3

Nikaɗaine zan iya fitar da Najeriya a Wannan Uƙuba da tsadar Rayuwa da APC ta jefata - Cewar Atiku
14/06/2022

Nikaɗaine zan iya fitar da Najeriya a Wannan Uƙuba da tsadar Rayuwa da APC ta jefata - Cewar Atiku

Address

No 25, Madatai Street
Kano
700151

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Jaridu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Taskar Jaridu:

Videos

Share

Nearby media companies



You may also like