06/10/2022
Maudu'i: Gudunmawar da matasa zasu bada wajen kawo sauyi da cigaba a arewacin Nijeriya.
Tambayoyi
Amb: Zamusu muji takaitaccen tarihinka mallam musa?
Musa: Bayan gaisuwa mai yawa ta addinin musulunci Assalamu'alaikum. Da farko duk abun dazamu Fara mukan saka sunan Allah sannan mu tike dashi. Muna koma salati da salami ga Manzon tsira Sallallahu Alayhi Wassalam.
Da farko sunana musa sani aliyu, an haifeni talatin ga watan uni shekarar alif Dari tara da casa'in da hudu. An haifeni a unguwar kundila zoo road dake Kano municipal anan jihar Kano. Nayi makarantar firamare a standard international school dake unguwar kundila. Daganan Allah cikin ikonsa sai na tafe Kano capital a shekarar 2007 inda anan nayi aji daya da aji biyu inda kuma anan ne nasamu sauyin makaranta zuwa Government Secondary School Model dakenan hausawa kusada gidanmu domin mun tasu daha kundila mun dawo nan hausawa zoo road. Nayi aji daya da aji biyu na babbar sakandare a makarantar sabuwar kofa. Inda na kammala babbar sakondare a pragmatic college.
Na karanta computer science a mataki na diploma a Kano state polytechnic. Yanxu haka ina karatun digiri a fanin Information Communication Technology a Jami'are maitama sule dake jihar Kano.
Na Fara aikin jarida a pyramid FM daga nan kuma na tafe gidan radio amince a shekarar 2018. Nayi aiki da gidan rediyon guarantee a yanxu kuma ina aiki da gidan rediyo jalla.
Nayi aiki a matsayin coordinator na Arewa agenda.
Sannan ni mai aikin sakai (Volunteer). Nayi aikin sakai da kungiyoyi da dama.
Ra'ayina yafe karkata ga aikin jarida da kuma aikin sakai domin dorewar cigaban al'umma da kuma bangaran abun daya shafe kirkira (Creativity).
Amb: A matsayinka na matashi kuma Dan jarida wasu irin matsaloli kaki ganin Arewacin Nijeriya ki fuskanta a yanzu?
Musa: Da farko akwai rashen shugabanci Wanda ko jawu nakasu wajen hadin kai da magana da murya daya don kawu cigaba ga yankin.
Na biyu shine durkushewar masana'antu. A shekarun baya a Kano ko na a arewa akwai kamfanuni Wanda s**a durkushe sunkai Kimanin Dari biyar da tamanin da uku. Yau a arewacin nijeriya ko ashana ba'ayi ballantana tsinkin sakace. Wannan yajawu durkushewar tattalin arzikinmu da wutar lantarki.
Wanda masana'atun yajawo rashen aikinyi a tsakanin matasa. Yanxu a duniya 'Soft Skills' ake magana.
Abu na uku shine shayeshaye musamman a tsakanin matasa.
A matsayina na dan jarida dana sha zuwa rundunar yan sanda ta jahoyi da dama. Idan aka aikata muggan laifuka gudu goma ba shakka zanga guda takwas Ku tara daga cikinsu matasa ne Wanda basu wuce shekara sha biyar zuwa ashirin da uku ba s**a aikata. Wanda dalilin dayasa suke fadawa cikin kwazazzaben wannan laifin shaye shaye ne.
Abu na hudu shine rashen bada shawarware ga matasa Wanda a turanci ake kirada 'Mentorship'. babu wasu manya dasuke zama k**ar madubi ga matasa sannan su kuma manyan basa basu wani horu domin matasan su zama abun koyi gobe kuma ababen kwatance.
Amb: Wasu irin gudunmawa kaki ganin matasa zasubi wajen kawo karshen wannan matsalolin?
Musa: Na farko matashi ya tsaya ya fuskanci kushi waye sannan yasamu role model wanda zai rinka kalla yana kwaikwaiya domin komai a duniya sai kanada madubin dubawa.
Mutane su samarwa kansu wasu mutane wanda zasu r***a bibiya. Domin ance daga nagaba ake gane zurfin ruwa.
Sannan abu na biyu shine, yazama sun samu ingantaccen shugabanci saboda sune karfin. Kowace kasa a duniya tana alfahari da matasan ta saboda matasa sune kida jini ajika.
Don haka matasa su samar da wata murya wacce zai zama suna magana da ita.
Sannan matasa suyi ilmi. Domin shi ilmi haskene kuma karfine.
Abu na karshe shine matasa su daina tunanin rayuwar jindadi. Su rinka aiyukan sakai tun suna shekaru kanana domin a samu kwarewa da cigaba mai dorewa. Sannan su koyi abun da ake kira da 'Soft Skills'. Domin yanxu andaina amfani da kwalin karatu sai kwarewa. Kwarewa shine abunda kasani kuma abun da zaka.iya.
Amb: Mukalli bangaren siyasar matasa, wani hange kaki dashi idan har matasan mu s**a shiga siyasa domin kawo cigaba a nahiyarmu?
Musa: idan muka kalli bangaren siyasar matasa, matasa zasuyi tasiri sosai idan s**a shiga siyasa ta hanyar data dace saboda dasu ake cimma kowani gace a mataki irin na siyasa.
Matasa idan s**a samu ilmi da kuma ilmin dogaro dakai. Sabida akwai banbance tsakanin 'education' da kuma 'knowledge'. shiyasa majalisar dinkin duniya tace ayi 'Quality Education'.
Kwarewar da matasa s**a samu ta fannin ilmi zai taimakesu matuka wajen yanki hukunci saboda suna da kware ajiki dakuma kware a kwakwalwa.
Amb: A karshe, a matsayinka na matashi wacce gudunmawa kaki kokarinyi domin ganin an kawo warware matsalolin matasa?
Musa: Toh, a matsayina na matashi kokarin danake wajen ganin an warware matsaloli shine nakanyi shirye-shirye na wayar dakan matasa wanda ki zaburarwa da zakararwa na matashi ya fahimce baiwarsa ya kuma fahimce mai zai iya. Saboda akwai wadanda Allah yayisu a duniya ba lallai su iya karatu da rubutu ba amma Allah yayi musu wata baiwa.
Sannan abu na biyu shine nakanyi kokari na hada taro na wayar dakai da kuma bada horu akan wani Abu wanda matasa zasu samu su rikeshi a matsayin al'amari na dogaro da kai a harkar tunani da harkar sana'a.
Amb: Menene fatanka ga wannan zaure?
Musa: fatana ga wannan zaure shine; Ubangiji Allah ya sakawa wannan zaure da alkhairi da kuma wanda s**a assasashi. Babu shakka da ana samun irin wannan zauren tun abaya lokacin da su sardauna suke fadawa matasanmu mu tashi tsaye mufarga kuma karmuyi fargar jaji. Na tabbata yanxu da an wucce matakin da ake gurin matasa su fahimce kansu da kuma matukar gudunmawar dasuke bayarwa a kasa domin cigabanta.
Allah yasakawa wannan zaure da alkhairi kuma da fatan zai cigaba dayin wannan aiyuka na alkhairi.
Amb: Muna godiya sosai da bamu lokaci dakayi. Allah ubangiji ya Kara basira da tsawon rai. Ameen.