Alhamdulillah.
Ni'ima ta sauka a Kano. Allah ya bamu damuna mai albarka.
Sabuwar waƙar mawaƙi Rarara da ya kira Tangal-Tangal ta sake jawo masa zagi. Kuna ganin a siyasance ya dace ya saki wannan waƙa?
Kiciɓis da Jafaar Jafaar ya yi da Gwamna Ganduje a London.
Jafaar ya shaidawa gidan Freedom Radio cewa an yi raha, inda gwamnan ya tsokane shi da ya gudo, shi kuma ya ce ai shi ya koro shi.
Kuna ganin maganar faifan dala a binne ta?
Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga musulmi da su yi watsi da wasu ɓata gari da aka samu labari suna yaɗa saƙonni don ɓata Sheikh Usman Ɗan Fodiyo da jihadinsa.
Wannan yunƙuri ne na raba kan musulmai tare da ƙoƙarin kitsa fituna.
Allah Ɗaya Gari Bambam: Arziƙi Damfare a Dafin Kunama
Yayin da ake gudin kunama saboda illar dafinta, a wasu ƙasashen arziƙi ne babba.
Rahaton BBC Hausa ya nuna yadda ake sarrafa ruwan dafin Kunama zuwa kayan kwalliya da magunguna.
Kalli yadda magani yake a gonar yaro.
Wata matashiya mai kwaikwayon murya.
Gwarzuwar Duniya:
'Yar Najeriya Oluwatobiloba Amusan, cikin hawaye yayin taken Najeriya don taya ta murnar lashe kambun gwal a gudun mita 100 na gasar duniya ta Athletics Championships da ake gudanrwa a Eugene, Oregon, USA
Yara masu irin wannan baiwa na da yawa a wannan al'umma tamu. Saratu kenen daga ƙauyen Shagogo, wanda Allah ya yi wa baiwar lissafi ajin farko.
Godiya ga mai taimakawa shugaban ƙasa, Bashir Ahmad da gidauniyarsa ta ɗauki nauyin karatunta har matakin jami'a.
Wani Alhajin jihar Kano da bai samu jirgi ba don halartar aikin hajjin bana, ya fara gabatar da aikin hajjinsa a sansanin alhazai na jihar Kano, a yau Alhamis.
Wani magoyin bayan ƙungiyar kwallon ƙafa ta Real Madrid ke kuka bayan sun sha kashi a hannun ƙungiyar Barcelona da 4-0.
Hatsaniyar da ta sa matar Gwamna mai barin gado ta sha mari.
A wajen bikin rantsar da sabon gwamnan Anambra Farfesa Chalse Soludo ne hatsaniya ta kaure tsakanin matan manya, har ta kai ga mari.
Bidiyo ya nuna yadda matar gwamna mai barin gado, Ebele Obiano ta miƙe daga inda take zaune ta ƙarasa gurin matar Ojukwu, wato Bianca Ojukwu. Wanda hakan ya nuna akwai wata 'yar tsama a tsakaninsu.
Abin da aka iya gani shi ne yadda Bianca Ojukwu ta miƙe tare da ɗauke matar Obiano da mari.
Tuni dai rantsatsan Gwamnan Anambra Prof. Soludo ya nemi afuwar jama'a bisa wannan hargitsi.