Oriya Reporters Hausa

Oriya Reporters Hausa Labaran Duniya....
Nishaɗi....
Wasanni...

Ra'ayi.......Bayyana mana gwaninka Tare da fadin Ayyukansa Muhimmai guda biyar...
27/01/2025

Ra'ayi.......

Bayyana mana gwaninka Tare da fadin Ayyukansa Muhimmai guda biyar...

Kwamishinan 'Yansanda a jihar Kano Salman Dogo Garba, ya ce rundunar ta cika hannu da mutumin ne bayan samun rahoto na y...
27/01/2025

Kwamishinan 'Yansanda a jihar Kano Salman Dogo Garba, ya ce rundunar ta cika hannu da mutumin ne bayan samun rahoto na yunkurin kai hari.

Har ila yau, Garba ya ce an samu nasarar kwace abubuwan fashewa daga hannun wanda ake zargi.

Da dumi'dumi: An kulle Sowore  har sai Baba ta gani hakan ya faru ne bayan da ya yi watsi da sharadin 'beli Wanda Yace A...
27/01/2025

Da dumi'dumi: An kulle Sowore har sai Baba ta gani hakan ya faru ne bayan da ya yi watsi da sharadin 'beli Wanda Yace An gindaya sharadin ne ba bisa ka'ida.

Tunda barko dai Rundunar Yan sandan ta gundayawa Sowore sharadin dole sai ya kawo Wanda zai karbe shi beli ma'aikacin Gwamnati Mai matakin 17 Wanda daga baya s**a rage sharadin zuwa 16.

Da dumi'dumi: Mun gano Bama-bamai da muggan mak**ai a Mauludin Tijjaniyya na Kano -- CP
27/01/2025

Da dumi'dumi: Mun gano Bama-bamai da muggan mak**ai a Mauludin Tijjaniyya na Kano -- CP

Budurwa ta mutu a rijiya a Kano Rahotanni sun bayyana cewa wata budurwa ta mutu bayan ta fada rijiya a Kano.Daily Trust ...
27/01/2025

Budurwa ta mutu a rijiya a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa wata budurwa ta mutu bayan ta fada rijiya a Kano.

Daily Trust ta rawaito cewa marigayiyar ta fada cikin rijiya da ke cikin wani gida a unguwar Danbare daura da gidan Amana a karamar hukumar Kumbotso.

A cewar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa daga wani Bashir Salisu, wanda ya shaida wa dakin sintiri da kai ɗauki.

Ya ce, “Tawagar agajin gaggawa daga hedikwatar jihar ta garzaya zuwa wurin da lamarin ya faru, bayan isowarta ne aka fito da ita daga rijiyar.

“Iyayenta sun tabbatar wa jami’an cetonmu cewa ba ta yi aure ba, kuma tana da damuwa daga ‘yar cutar tabin hankali.

"Nan da nan ne tawagarmu ta fito da ita a sume kuma daga baya aka tabbatar ta mutu."

Abdullahi ya kara da cewa an mika gawar ga Mai Unguwar Danbare Magaji Kasim, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.

Mutane da dama na zargin Ganduje da Hannu wajen Assasa Fitina a Jihar ko To wallahi Mafi Akasari Barau ne.______ JA'AFAR...
27/01/2025

Mutane da dama na zargin Ganduje da Hannu wajen Assasa Fitina a Jihar ko To wallahi Mafi Akasari Barau ne.

______ JA'AFAR JA'AFAR.

Ɓarawo ya mutu garin satar waya a taransifomaWani mutum da ba a kai ga gane sunan sa ba ya mutu sak**akon konewa da wuta...
26/01/2025

Ɓarawo ya mutu garin satar waya a taransifoma

Wani mutum da ba a kai ga gane sunan sa ba ya mutu sak**akon konewa da wutar lantarki yayin da ya ke kokarin sata a cikin taransifoma a yankin Akute, Jihar Ogun.

Jaridar PUNCH Online ta gano cewa al’ummar yankin suna fama da matsaloli na satar wayoyin lantarki da lalata injinan wutar su.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, ta ce mamacin ya hau gidan injin wutar kuma yayin da yake kokarin yanke waya, wutar ta kashe shi.

Ta bayyana cewa jagoran al’ummar Irewole ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yansanda.

26/01/2025

Waɗanda s**a shirya gasar wanda ya fi kowa daɗewa da iya jima'i sun shiga hannu a Jihar Sokoto

An Ce Wannan Kallon Soyayyar Da Aka Yi A Cikin Shirin Garwashi Ya Tashi Kan Masu Kallo
25/01/2025

An Ce Wannan Kallon Soyayyar Da Aka Yi A Cikin Shirin Garwashi Ya Tashi Kan Masu Kallo

Buhari ya bawa Mawaƙi Ɗan Soja kyautar zunzurutun kuɗi har Dala 100, kwatankwacin Naira 162,000 a kuɗi Nijeriya.
25/01/2025

Buhari ya bawa Mawaƙi Ɗan Soja kyautar zunzurutun kuɗi har Dala 100, kwatankwacin Naira 162,000 a kuɗi Nijeriya.

25/01/2025

YANZU-YANZU: Masu Bankin Opay kun saurari Radio kuwa?

Na fita daga Kwankwasiyya na kuma daina saka jarhula,Ina nan daram a Jam'iyyar NNPP mai kayan Gwari.Musa Nuhu Yankaba-
25/01/2025

Na fita daga Kwankwasiyya na kuma daina saka jarhula,Ina nan daram a Jam'iyyar NNPP mai kayan Gwari.

Musa Nuhu Yankaba-

Da Dumi-Dumi ‘Yan sandan sun k**a jagoran yaki da cin hanci na gwamnatin Kano Muhuyi Magaji kan karbe iko da wasu kadaro...
24/01/2025

Da Dumi-Dumi

‘Yan sandan sun k**a jagoran yaki da cin hanci na gwamnatin Kano Muhuyi Magaji kan karbe iko da wasu kadarori da aka alakanta da Dr Abdullahi Ganduje a cewar jaridar Solacebase da ake wallafawa a Kano ta bayyana

AN KUMA: An Daura Auren Jarumin TikTok G-Fresh Da Amaryarsa Maryam A Garin YolaWane fata za ku yi musu ?
24/01/2025

AN KUMA: An Daura Auren Jarumin TikTok G-Fresh Da Amaryarsa Maryam A Garin Yola

Wane fata za ku yi musu ?

24/01/2025

Luwadi:An Sauke wani Mai-Unguwa a Kabara ta Jihar Kano kan zargin Lalata Wani karamin Yaro ta baya

24/01/2025

Barazanar Hare-Hare a Kano

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta ce ta gano shirin hare-haren ta’addanci a jihar.

A saboda haka ne ma rundunar ke gargadi ga Al’ummar jihar da su kaucewa shiga cunkoso.

Rundunar tace tana kokarin murkushe barazanar hare-haren.

Da Dumi-DumiShugaban jam‘iyyar APC ta Nijeriya Dr Abdullahi Ganduje na cikin mutane 42 da fadar shugaban kasa ta aike wa...
24/01/2025

Da Dumi-Dumi

Shugaban jam‘iyyar APC ta Nijeriya Dr Abdullahi Ganduje na cikin mutane 42 da fadar shugaban kasa ta aike wa da kafofin yada labarai ciki har da Oriya Reporter's Hausa,inda sanarwar ta ce tsohon gwamnan na Kano zai rike mukamin shugaban hukumar gudanarwa wato Board Chairman. Sai dai sanarwar wacce Bayo Onanuga mai magana da yawun Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ta ce, wadannan sabbin muk**ai ba za su yi katsalandan ga ayyukan shugabannnin hukumomin da gwamnati ta sanar tun da farko ba

Da Dumi Dumi💥💥💥Wata wuta ta sake bayyana a birnin Los Angeles dake United States of America jiya Laraba. Wutar ta b***e ...
23/01/2025

Da Dumi Dumi💥💥💥

Wata wuta ta sake bayyana a birnin Los Angeles dake United States of America jiya Laraba. Wutar ta b***e da yamma ta kone filaye da abubuwan dake cikin su, k**ar gidaje, motoci, kamfanonin da shaguna, girman filin da ya kai kilomita dubu 3,800.

~ An kwashe mutane dubu 31,000 daga gidajen su domin gudun konewa ko samun raunuka.

Zuwa safiyar yau jiragen sama na kokarin shawo kan wutar mai karfin gaske.

Address

Kano

Telephone

+2348182936818

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Oriya Reporters Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Oriya Reporters Hausa:

Videos

Share