27/12/2025
KOWA YA SHIRYA BIYA: Ba gudu, ba ja da baya za mu fara aiwatar da Dokar Haraji daga watan Janairu 2026 — inji Gwamnatin Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa babu ja da baya ko sassauci wajen fara aiwatar da Dokar Haraji daga ranar 1 ga Janairu, 2026, duk da cece-kuce da ake yi kan zargin an yi sauye-sauye da cushe a cikin dokokin da aka wallafa.
Ayau News ta ruwaito Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Sauye-sauyen Haraji, Mista Taiwo Oyedele, ya faɗi hakan bayan ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Legas.
Me zaku ce?