22/06/2022
TIRKASHI ANKAMA WANI SABON DAN FARA
Ɗan damfara da yaudara a facebook, wanda ke nuna kansa a matsayin Zahra Mansur ya shiga hannu
Dubun wani matashi mai suna Musa Lurwanu Maje ta cika bayan da Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Kano ta cafke shi bisa yaudara da damfarar mutane ta kafar facebook.
Maje, wanda ya ke nuna kansa a matsayin Zahra Mansur a facebook, ya shiga hannun ƴan sanda ne bayan da Rundunar ta fara karɓar ƙorafi a kansa tun daga watan Afrilu zuwa Yunin da mu ke ciki.
A wata sanarwa da Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a yau Lahadi, Maje ya shiga hannu ne bayan da Kwamishinan Ƴan Sanda, Sama'ila Shu'aibu Dikko ya bada umarnin a kamo shi.
Kiyawa ya ƙara da cewa tuni jami'an ɓangaren binciken sirri na rundunar su ka fara aiki har sai da su ka gano da kuma cafko Maje, ɗan shekara 26, mazaunin ƙauyen Sitti a Ƙaramar Hukumar Sumaila.
Ya ce Maje ya amsa laifinsa na ƙirƙirar shafin Facebook na ƙarya, inda ya ke yaudarar maza da su aiko da bidiyon tsaraicin su, sai ya ce su aiko masa da kuɗi ko ya yaɗa su.
SP Kiyawa ya kuma bayyana cewa an samu wayar hannu ƙirar Redmi Note 11 Pro, mai kimanin darajar Naira dubu 200, da kuɗaɗe Naira dubu 70, da sauran abubuwa da ya samu wajen damfarar al'umma.
An kuma samu hotuna da bidiyo na tsaraicin mutane da dama a wayar ta Maje.
Kiyawa ya ce za a gurfanar da shi a gaban kuliya da zarar an kammala bincike a kansa.