Hajji Kiran Allah

Hajji Kiran Allah Hajji Mabrur!!!
(2)

12/06/2024

Wanne Shugaban Hukumar Alhazai ne yafi nuna jajurcewar aiki a wannan karon?

Kuyi Comment Da Sunansa ko Jiharsa.

HAJJ2024/1445:An sanya sababbin na'urorin sanyaya iska guda 45,600 a cikin hemomi dake Mina don ƙara ƙarfin yanayin sany...
12/06/2024

HAJJ2024/1445:

An sanya sababbin na'urorin sanyaya iska guda 45,600 a cikin hemomi dake Mina don ƙara ƙarfin yanayin sanyi.

Baƙin Allah a mikatin zul-khulaifa kafin su dau hanya zuwa birnin Makkah.
11/06/2024

Baƙin Allah a mikatin zul-khulaifa kafin su dau hanya zuwa birnin Makkah.

Wasu Alhazai ƴan asalin jihar Jigawa, a hanyarsu ta zuwa Birnin Makkah daga Madina.
11/06/2024

Wasu Alhazai ƴan asalin jihar Jigawa, a hanyarsu ta zuwa Birnin Makkah daga Madina.

HAJJI tafiyar da ba'a mantawa da ita.
11/06/2024

HAJJI tafiyar da ba'a mantawa da ita.

11/06/2024

HAJJ2024:

Cikin ikon Allah, wata Hajiya ƴar Najeriya ta samu damar haihuwa a can ƙasa me tsarki.

Rukunin farko na maniyyatan jihar Katsina yayin da s**a ɗauki hanyar barin Madinah, zuwa Makkah.Hajji Mabrur!!
10/06/2024

Rukunin farko na maniyyatan jihar Katsina yayin da s**a ɗauki hanyar barin Madinah, zuwa Makkah.

Hajji Mabrur!!

10/06/2024

Waccan shekarar da ta gabata Jiharmu ta Kano tazo mataki na 2 da Alhazai 6000+.

Amma wannan karon tazo mataki na 5 da Alhazai 3100+.

HAJJ2024/1445:Bayan kammala jigilar dukkan Maniyyata zuwa Kasa Mai tsarki, alkaluma daga Hukumar Alhazai ta kasa sun nun...
10/06/2024

HAJJ2024/1445:

Bayan kammala jigilar dukkan Maniyyata zuwa Kasa Mai tsarki, alkaluma daga Hukumar Alhazai ta kasa sun nuna Jihar Kaduna ta fi kowace jiha yawan mahajjata inda take da 4,785.

Jihar Sokoto ce take a mataki na biyu inda take da maniyyata 3738, yayin da Jihar kebbi tazo mataki na uku da maniyyata 3607.

Jihar Bayelsa ita keda maniyyata da s**a fi rashin yawa, inda take da maniyyata guda 13 kacal..

Allah yasa ayi karɓaɓɓiya ya dawo da kowa gida Lafiya. HAJJ MABRUR!!!

10/06/2024

ALHAMDULILLAH!!!

Hukumar Alhazai ta ƙasa Najeriya ta kammala jigilar maniyyatanta kaf zuwa ƙasa me tsarki.

Kuma ana sa ran Alhazai zasu fara dawowa gida Najeriya daga ranar 22, ga yuni.

HAJJ2024:Asibitin wucin gadi da Gwamnatin Jihar Kano ta samawa Maniyyatanta a ƙasa me tsarki.📸 Ibrahim Adam
09/06/2024

HAJJ2024:

Asibitin wucin gadi da Gwamnatin Jihar Kano ta samawa Maniyyatanta a ƙasa me tsarki.

📸 Ibrahim Adam

09/06/2024

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!

Wasu Alhazai guda 2 Ƴan asalin jihar Kwara sun tafi zuwa ga wanda ya fimu kaunarsu.

Allah ya jikansu ya saka musu da gidan Aljannah.

09/06/2024

Fiye da alhazai miliyan 1.3 ne s**a isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajji!

HAJJ2024:Jirgin kasa na Masha'er ya shirya tsaf don jigilar alhazai. Ya ƙunshi tashoshi 9 kuma jirgin yana gudun kilomit...
09/06/2024

HAJJ2024:

Jirgin kasa na Masha'er ya shirya tsaf don jigilar alhazai. Ya ƙunshi tashoshi 9 kuma jirgin yana gudun kilomita 80 a cikin awa guda.

Jirgin Max Air ɗauke da Maniyyatan Jihar Katsina guda 550, ya tashi zuwa ƙasa me tsarki yanzu da misalin karfe 7:00 na s...
09/06/2024

Jirgin Max Air ɗauke da Maniyyatan Jihar Katsina guda 550, ya tashi zuwa ƙasa me tsarki yanzu da misalin karfe 7:00 na safiyar yau Lahadi.

Allah ya saukesu Lafiya yasa ayi karɓaɓɓiya.

HAJJ2024: Yayin da amirul Hajji na Kano, kuma Mataimakin Gwamna Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo, tare da Darakta Janar da ...
08/06/2024

HAJJ2024: Yayin da amirul Hajji na Kano, kuma Mataimakin Gwamna Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo, tare da Darakta Janar da Shugaban Hukumar Alhazai ta kano suke kan hanyarsu ta tafiya zuwa Madinah a daren jiya Jumu'a......
..Sun sauka cikin koshin lafiya, kuma sune zasu jagoranci Alhazan Jihar Kano a hajjin bana, tare da wasu manyan jami'an gwamnatin ta jihar Kano.

Hajji Mabrur

Jirgin Max Air ɗauke da Maniyyatan Jihar Katsina guda 550, ya tashi zuwa ƙasa me tsarki yanzu da misalin karfe 4:15 na y...
08/06/2024

Jirgin Max Air ɗauke da Maniyyatan Jihar Katsina guda 550, ya tashi zuwa ƙasa me tsarki yanzu da misalin karfe 4:15 na yamma.

Allah ya saukesu Lafiya yasa ayi karɓaɓɓiya.

08/06/2024

Wato inda zaka tabbatar HAJJI/UMRAH kiran Allah ne; koda kudinka seda rabonka....

Wata Baiwar Allah ɗanta ya biya mata zata Umrah, tsohuwa da zumunci kawai ta dauki kafa ta tafi unguwa wai zata yiwa kawarta albishir, ƘADDARA..........😞😞😞😞

Wallahi Mai adaidaita sahu ne ya bigeta. Bayan jinya na ƴan watanni Allah ya karɓi abarsa...

HAJJ:20241) Sheikh Maher Shine Wanda Zeyi Huɗuba Ranar Arfah A Masallacin Namirah.2) Sheikh Sudais Shine Me Huɗubar Rana...
08/06/2024

HAJJ:2024

1) Sheikh Maher Shine Wanda Zeyi Huɗuba Ranar Arfah A Masallacin Namirah.

2) Sheikh Sudais Shine Me Huɗubar Ranar Idi A Masallacin Harami.

3) Sheikh Khalid Al Muhanna Shine Me Hudubar Ranar Idi A Masallacin Manzon Allah S.A.W.

08/06/2024

HAJJ2024:

Dukkan Alhazan jihar Kano su 3100+ sun Isa Birnin Makkah.

Yayin da wasu Alhazan jihar Kaduna suke kan hanyarsu ta zuwa miqati domin ɗaukar harama, daga bisani kuma su wuce birnin...
08/06/2024

Yayin da wasu Alhazan jihar Kaduna suke kan hanyarsu ta zuwa miqati domin ɗaukar harama, daga bisani kuma su wuce birnin Makkah domin fara ibada.

Hajji Mabrur💖💖

Yadda jami'an tsaro suke aiki tuƙuru don ganin an rage cinkoso a masallacin Manzon Allah (S.A.W).
07/06/2024

Yadda jami'an tsaro suke aiki tuƙuru don ganin an rage cinkoso a masallacin Manzon Allah (S.A.W).

07/06/2024

Jama'a....

Ya shirye shiryen Babbar Sallah?

Rukunin karshe na maniyyatan Jihar Kaduna da ke Madinah yau sun samu izinin shiga Raudah (Wani bangare da Manzo Sallalla...
07/06/2024

Rukunin karshe na maniyyatan Jihar Kaduna da ke Madinah yau sun samu izinin shiga Raudah (Wani bangare da Manzo Sallallahu Alaihi wasalam ya bayyana da cewa wani bangare ne na Aljannah).

📸 Kaduna Pilgrims

Allah kayi salati ga Annabinmu Muhammad. (S.A.W)🥰🥰🥰🥰
07/06/2024

Allah kayi salati ga Annabinmu Muhammad. (S.A.W)

🥰🥰🥰🥰

An ga jinjirin watan Dhul Hijjah 1445 a yau.Gobe Juma'a shine ze k**a 1 ga watan.Ranar Hajji (Arafat): Asabar, 15 Yuni 2...
06/06/2024

An ga jinjirin watan Dhul Hijjah 1445 a yau.

Gobe Juma'a shine ze k**a 1 ga watan.

Ranar Hajji (Arafat): Asabar, 15 Yuni 2024
Ranar Eidi: Lahadi, 16 ga Yuni, 2024.

Yayin da wasu Jami'an Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna s**a kai ziyara Makabartar Uhud, da Masallacin Quba da sauran wura...
06/06/2024

Yayin da wasu Jami'an Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna s**a kai ziyara Makabartar Uhud, da Masallacin Quba da sauran wuraren ibadah.

📸Kaduna State Pilgrims Agency

Abincin dare da Gwamnatin Kano take bawa Alhazan Jahar a Kasar Saudia.
06/06/2024

Abincin dare da Gwamnatin Kano take bawa Alhazan Jahar a Kasar Saudia.

06/06/2024

Saboda tsananin zafi a Makkah da Madina, Sheikh Sudais ya umurci Limaman jumua da su takaita Khutbah da Sallah gobe.

06/06/2024

HAJJIN BANA:
Ƙimanin Bas-bas guda 27,000, da kuma motocin haya 5,000 aka ware domin hidimtawa alhazai da s**a isa ƙasar saudi arabiya.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hajji Kiran Allah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Nearby media companies


Other News & Media Websites in Kano

Show All

You may also like