21/12/2025
Gwamna Yusuf Ya Bukaci Sababbin Shugabannin NNPP Na Kasa Su kasance Masu Kishin Jam’iyya Da Hadin Kai
Disamba 20, 2025
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga sabbin shugabannin kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da aka zaba da su zamo masu jajircewa, aiki tukuru da kuma rungumar kowa da kowa domin ƙara wa jam'iyyar karsashi da kwarin guiwa domin cimma manufofinta.
Wakilin mu Hussain Kabir minjibir ya ruwaito mana, cewa Gwamna Yusuf ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar a bikin rantsar da sababbin shugabannin kasa na NNPP, wanda aka gudanar a birnin Abuja.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada kudirin jam’iyyar na tabbatar da nagartaccen shugabanci, walwalar al’umma da kuma kare ka’idojin dimokiradiyya a fadin Najeriya.
Ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar da su rungumi hadin kai, biyayya da sadaukarwa wajen matsayar da muhimman ginshikai na cimma burin al’ummar kasa baki daya.
Taron ya samu halartar manyan shugabannin jam’iyyar da wakilai daga jihohi 36 na kasar nan, inda aka tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi alkiblar siyasa da makomar jam’iyyar NNPP.