Boncy Channel's Tv

Boncy Channel's Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Boncy Channel's Tv, TV Channel, Bauchi.

REMARK BY THE LEADER SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H), AT THE INTERNATIONAL CONFERENCE ON TABLIGH (MASHHAD, IRAN) 18/05/2022B...
19/05/2022

REMARK BY THE LEADER SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H), AT THE INTERNATIONAL CONFERENCE ON TABLIGH (MASHHAD, IRAN) 18/05/2022

By Office of Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Bismillahir rahmanir rahim,

Wa sallallahu ala sayyidina wa nabiyina wa habibi qulubina wa shafi’i zunubina, Abul Qaseem Mustapha Muhammad (S); wa ala Alihid Daiyibinad Dahirinal Ma’asumin, siyama Baqiyatullahi fil ard Sahibul asr waz zaman (arwahuna lahu fida).

Assalamu alaikum wa rahmatullah ta’ala wa barakatuhu:

I will like to share with you, during this your blessed conference about ‘Tabligh’ which comes together different people from different parts of the world in order to participate in this very important conference.

Tabligh we might say is very much needed at this material time when the world, once again, is filled with oppression and darkness and ignorance. The solution is in the hands of the Muslims, for they have the right path with them, and they also have the right guided Imam (AF) living among them except that he is not known and he is not understood.

It is the duty of the ‘Muballighen’ at this material time to take the responsibility of enlightening the general public- the whole world is in need of the enlightenment- and this would be in the preparation for the appearance of the long awaited Imam (AF).

Tabligh should be in different levels. First of all, every ‘Muballigh’ must try to understand his place where he would carry out the message, it is better if he would take this message in his own area where he grown up (where he was born), or we might say at least in his own country or even his locality. He has to understand the need of the community first, and he has to understand the language of the community, and what the community can understand. And that ‘Tabligh’ should be at different levels.

The first level is that there should be a class- an adult school. This is very important. We sometimes assume that people from different walks of life know a lot, but when you come in direct contact with them you would find out that there are a lot of things they do not understand. You have to have classes for adults, and (those adults) should also be categorized: those who can be able to read and write- who have attended schools, who can understand the language when spoken to in a higher level; and those who can not (read, write, or understand the language when spoken to). Very important it has to be in the class- in a school- not in the open air. And that school for the adults should include both men and women.

The second category should be school for children, and this is the most important because the adults have already grown up and they knew very little in their childhood and now you have to use the language they can understand at their age. But if there is school for children they will grow up with it Inshaa Allah, and they will be the future generation that will teach the next generation. They will grow up in it. (Starting with) primary school, and then later secondary school, and even prepare them for higher education. This is very important.

The third category should be for the general public openly for everyone, for example in mosques during Friday prayers or in other locations even in the open air where you can speak to different people at different levels. As I have said earlier, you have to understand the people you are going to speak to. Are they people who can understand what you are saying? If they can not, you have to use the language they can understand. The language here doesn’t mean the dialect, what I mean is what you can speak to them at their level (of knowledge) and they can understand you. That is very important.

And also of course if there is the possibility to have the use of other media like radio, television, newspaper and what is very common in these days: the social media, all should be used in making ‘Tabligh’.

The ‘Muballighen’ you have to understand that you are the helpers of the awaited Imam (AF), you are doing the work of the awaited Imam (AF).

May Allah (SWT) bless you all, may He enable all of you carry out the duty bestowed upon you, Inshaa Allah!

Wa sallallahu ala Muhammad wa alihid dahirin.

Wassalam alaikum wa rahmatullah..

- Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H)
(Wednesday, May 18th 2022)

Hausa:

JAWABIN JAGORA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H) A TARON KASA DA KASA AKAN TABLIGH (BIRNIN MASHHAD, IRAN) 18/05/2022

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Bismillahir rahmanir rahim,

Wa sallalahu ala sayyidina wa nabiyina wa habibi qulubina wa shafi’i zunubina, Abul Qaseem Mustapha Muhammad (S); wa ala alihid daiyibinad dahirinal ma’asumin, siyama baqiyatullahi fil ard Sahibul asr waz zaman (arwahuna lahu fida).

Assalamu alaikum wa rahmatullah ta’ala wa barakatuhu:

Zan so na dan yi tsokaci kadan a wannan taro na ku mai albarka da dimbin muhimmanci akan “Tabligh” wanda mutane daga bangarori daban-daban na duniya su ka samu halarta.

Mu na iya cewa al’umma na tsananin bukatar ‘tabligh’ musamman a wannan lokaci da duniya ta sake cika da zalunci, duhu, da kuma rashin sani (jahilci). Mafitar kuma na hannun Musulmi ne, don su ke da tafarkin gaskiya, sannan su na rayuwa tare da limamin shiriya (AF) a cikin su, kawai dai ba a san shi ba ne kuma ba a fahimce shi ba.

Haqqi ne akan duk wani ‘muballighi’ a wannan lokacin ya daukar ma kan shi ‘takalifin’ wayar da kan al’umma- duniya ma baki daya na bukatar wayar da kai- wanda hakan zai zama tamkar shiri ne na bayyanar jagoran shiriya da ake jira (AF).

Ya kamata ‘tabligh’ ya zama a mataki daban-daban. Da farko, ya zama wajibi akan kowane ‘muballighi’ ya fahimci al’ummar da zai isar da sakon gare ta, ya fi kyautuwa idan zai isar da sakon ne ga al’ummar da ya tashi a cikin ta (inda aka haife shi); ko mu ce aqalla ya zama a kasar da ya ke, ko kuma yankin shi. Ya zama wajibi da farko ya fahimci bukatar al’ummar da zai isar ma da sakon, ya fahimci yaren al’ummar, da kuma abun da su za su iya fahimta. Sannan kuma wannan ‘tabligh’ din ya zama an yi shi mataki-mataki ne.

Matakin farko shi ne ya kamata a samar da ajin manya- ko makarantar manyan mutane. Wannan na da matukar muhimmanci. Wani lokacin mu kan yi tsammanin cewa mabanbantan mutane sun san abubuwa sosai, amma idan mu’amala ya hada ka da su, sai ka ga ba su san abubuwa da dama ba. Ya kamata ya zama akwai ajin manyan mutane, kuma shi ma ajin (na manya) ya kamata a raba shi ne: wadanda su ka iya rubutu da karatu- wadanda su ka halarci makaranta, wadanda za su fahimci karatu an yi musu; da kuma bangaren wadanda ba su iya (karatu ko rubutu ba). Kuma ya na da muhimmanci ya zama a cikin aji ne (makaranta) za a koyar da su- ba wai a bayyanannen fili ba. Kuma harwalayau, wannan makarantar ya kamata ya hada maza ne da mata.

Kaso na biyu shi ne samar da makarantar yara kanana, wannan ya ma fi kowanne muhimmanci saboda su manya tuni sun girma kuma sun san abu qalilan ne a yarintar su saboda haka yanzu sai dai a yi amfani da yaren da za su iya fahimta a shekarun su (na tsufa). Amma idan makarantar yara, to zai zama sun tashi da shi ne Inshaa Allah, kuma za su kasance al’ummar da za su koyar (da Ilimin) ga wadanda za su zo nan gaba. Za su girma cikin (Ilimin). Ya zama an fara daga matakin Firamare, zuwa Sakandare, har ma zuwa matakin gaba da Sakandare. Wannan na da matuqar muhimmanci.

Kaso na uku shi ne (Ilmantar) da sauran al’umma baki daya, wanda kowa zai iya kasancewa daga ciki. Misali, a Masallatai a lokacin sallar Juma’a ko a sauran gurare, hatta ma a bayyanannen muhalli inda za a iya magana da mutane daban-daban a mataki daban-daban (na Ilimi). Kamar yanda na fada tun farko, akwai bukatar a fahimci mutanen da za a isar da sakon gare su. Mutane ne da za su fahimci abun da a ke fada? Idan ba za su iya ba, to sai a yi amfani da yaren da za su iya fahimta daidai da kwakwalen su. Kuma yare a nan ba ina nufin harshen da ake magana da shi ba (dialect) ne, a’a ina nufin sakon da za a isar mu su kuma ya zama sun fahimta daidai da matakin Ilimi da fahimta da su ke da shi. Wannan na da muhimmanci sosan gaske.

Sannan kuma idan akwai hali za a iya amfani da kafafen isar da sako kamar radiyo, talabishan, jaridu da kuma abun da ya fi shahara yanzu- kafafen sadarwa na zamani; duk za a iya amfani da su wajen yin ‘tabligh’.

Ma su yin ‘tabligh’ ya na da kyau ku fahimci cewa ku mataimaka limamin shiriya da ake jiran bayyanar shi (AF) ne, ku na yin aikin Imamin da ake jira (AF) ne.

Allah Ya yi mu ku albarka, Ya ba ku ikon sauke nauyin haqqin da ya rataya a wuyan ku, Inshaa Allah.

Wa sallalahu ala Muhammad wa alihid dahirin.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah..

- Sayyid Ibraheem Ya’qoub Zakzaky (H).
(Laraba, 18 ga watan Mayu 2022).

“Prophet Muhammad (S) is the pinnacle of God's creation, he was sent to mankind with a message to be emulated so that ma...
18/05/2022

“Prophet Muhammad (S) is the pinnacle of God's creation, he was sent to mankind with a message to be emulated so that man can gain salvation in the hereafter. He is a man, unlike ordinary men...”

–Leader Sayyid Ibraheem Zakzaky (February, 2014)

Hausa:

"Annabi Muhammad (S) shi ne mafi ɗaukaka cikin halittun Allah, an aiko shi zuwa ga ‘yan Adam da saƙon da za a yi koyi da shi domin samun tsira a lahira. Mutum ne, ba kamar kowa ba....”

–Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (February, 2014).


GANAWAR JAGORA (H) DA DALIBAN HAUZADaga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)A yayin ganawar Jagoran Harkar Musulunci Shai...
14/05/2022

GANAWAR JAGORA (H) DA DALIBAN HAUZA

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

A yayin ganawar Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da wasu daga daliban Hauzar Ilimi wadanda s**a zo hutu tare da Tablig daga kasashen Iran, Iraq da Lebanon, a ranar Talata 11 ga watan Shawwal, 1443 (11/5/2022) a gidansa da ke Abuja, ya yi kira kan matakan da ya dace a bi wajen isar da sako da yada ilimi ga al’ummar wannan nahiya.

Jagoran ya kirayi daliban da cewa: “In mutum ya je muhallin da zai yi Da’awa (Tabligi) zai yi la’akari ne da bukatun mutanen wajen ne ya ga inda shi zai taimaka musu ya d**o su zuwa wani mataki da za su iya kaiwa fiye da wanda suke a kai. Ba zai zo da duk abin da ya karanto ne ya rika zuba musu ba, (in ya yi hakan) za su iya kasa fahimta su yi masa garau (suna kallonsa), kila ma su ce kansa da motsi, saboda ba za su gane abin da yake cewa ba, b***e su fahimci me yake koyar da su.”

Ya ba da misali da yadda wani Malaminsa na Usul da Mandiq a Jamhuriyar Musulunci ta Iran yake karfafa shi a kan muhimmancin koyar da karatun da yake yi a lokacin. Amma sai ya zama ba a samu wanda suke da ahaliyar da zai karantar da su wannan ilimin a nan ba (a lokacin). Har da ya fadawa Malamin haka, sai yake cewa: “Gaskiya ne, in ka je ka ga mutane ya zama su matsalarsu yanzu Alwala ne suke so su iya, kaga ba batun ka musu Usul ne ba, su abin da ya dame su kawai z aka koya musu.”

Ya bayyana yadda ya kamata a rika magana da mutane daidai da hankalinsu. Inda ya ba da misali da yadda bayan zuwansa Iran a 1980 ya ga taron mutane masu goyon bayan juyin Musulunci, da ya dawo ya yi kokarin sanar da mutane komai da komai, amma s**a kasa fahimta. Har wani ya shaida masa cewa wannan abin ba zai yiwu ka fadawa mutane su gane ba, sai dai in ka aikata su gani a tare da kai (ta haka za su iya fahimta su yi).

Yace “Na’am ba zai yiwu kowa da kowa ya gane ba, domin an ga Annabawa ai, amma sai aka ce musu basu da hankali. Me aka cewa shugaban Manzonni (S)? Aka ce masa boka, aka ce masa mawaki, har ‘Majnuni’ ma an ce masa. Ba abin da ba su fada ba. Don haka ba yana nufin kowa zai (gane har ya) karba bane.”

Shaikh Zakzaky yace: “Su mutane su fahimci tsari ya koma na addini shine (ya gagaresu), kowa ya rikice, ba wanda yake ganewa. Saboda ba yadda za a yi ka nunawa mutum nizami. Wasu sai su ce wai ana nema a hambare musu gwamnati. Nake cewa ai ba Gwamnati ake nufi ba. Gwamnatoci nawa aka yi? Ni daga wayau na zuwa yanzu na ga Gwamnati ya kai 13.”

Nan ya lissafa gwamnatocin da ya shaida tun daga na mulkin Bature, har zuwa na Soja da ta fararen hula har 13, Yace: “Ka ga in canjin gwamnati ne, to na ga wajen 13 ne. To ba canjin Gwamnati muke nufi ba, canjin nizami (muke nufi).”

Ya cigaba da cewa: “Shi kuma juyi yana da wahalar ganewa. Su mutane da an fara magana sai su ce wai za a kwace musu gwamnatinsu. Nace wa ke maganar gwamnati? Ana maganar mutane su koma nizamin addini, ku kuna ce za a kwace gwamnati. Gwamnatocinku duk da kuke yi gaba daya tun daga na mulkin mallaka har izuwa yanzu duk a kan nizami daya ne -Tun da turawan mulkin mallaka s**a zo s**a kafa nizaminsu har izuwa yau (iri daya ne).”

A nan ne ya kara haske kana bin da yake kiran al’umma a kansa ta hanyar ba da misali da yadda Shehu Usman ya samu al’ummar kasar nan bisa nizamin Gargajiya ya canza su zuwa addini, daga baya Bature ya zo ya canza su zuwa ga nizamin da ke iko yanzu, inda ya jaddada cewa mu kuma a yanzu muna kira ga komawa wannan addini din ne.

Yace: “Shehu Usman ya zo ya samu al’ummar nan ne tana nizamin Gwargajiya, akwai Sarakuna, amma al’ada suke bi. Ko da yake da yawansu Musulmi ne, amma dai nizamin da ke iko al’ada ne. To shi (Shehu) sai ya dora al’umma a kan nizamin addini.”

Ya cigaba da cewa: “Shi kuma da Bature ya zo shi kuma nizamin addinin ya kawar. Har na sha yin magana nace shi Bature fa bai boye mana ba, sosai maganar da Lugard ya yi a Sokoto, yace da can Fulani sun ci kasar nan da yaki, suna da ‘yancin su mallaki kasar nan, to mu kuma yanzu Ingilishi mun ci ku da yaki mu ke da ikon mu mulke ku, saboda haka muma akwai dokokinmu za mu so ku bi kamar yadda mu ma za mu dan yi bitan naku, amma ku bi namu, yanzu kuna bisa nizamin Ingila ne.”

Ya kara da cewa: “Shi kuma (Bature) ba Babarodo ya yi ba ma, sai da ya tara Sarakuna a Lokoja, ya dauko Alkur’ani ya nuna musu yace kun ga wannan da shi ke iko da ku, amma yanzu ba shi bane, bari ku ga makomarsa. Aka samu wani Bature ya yi wa Alkur’ani fitsari suna kallo. Yace kun ga makomarsa kenan. Aka dauko tutar Danfodiye mai rubutun ‘La’ilaha illahu Muhammadur Rasulullah’ aka ce da kuna karkashin wannan tutar, to bari ku gani, aka kona. Aka dauko tutar nan mai ‘Cross’ aka daga aka ce to yanzu kuna karkashin wannan. To me ya rage?”

Shaikh Zakzaky yace: “To yanzu mu abin da muke cewa shine za mu komawa addini ne. Amma sai mutane su rika cewa o’o’o’o! In dan boko ne yace maka ‘impossible’! In kuma bai yi boko ba sai yace ai ba zai yiwu ba, an yi nisa, ba zai yiwu ba. Me zai hana shi yiwuwa? Sai su ce ai kasar ba Musulmi ne duk ba. Sai mu ce ai Allah bai lizimta mana yin kasa ba, abin da ya lizimta mana yi shine yin addini.”

Ya kara da tambaya: “Ko Allah Ta’ala ya lizimta mana yin kasa ne? Ko akwai wata Aya da tace ya ku mutane in kuka samu kanku a wata kasa kuka ga akwai wasu mutane da ba Musulmi ba a cikinku ku ku ajiye addinin Musuluncinku?” Yace: “Da can ma da ake Musuluncin an ce dole kowa Musulmi ne? Ko da Bature ya zo kasar nan ya samu kowa Musulmi ne? Ya samu mutane da yawa suna addinai daban-daban, amma Musulunci ke iko ba Al’ada ba. Abin da ya zo ya samu kenan, shi kuma ya zo ya kawar.”

Jagora (H) yace: “Har yanzu sun kasa gane cewa juyin juya hali da ake yi ba juyin mulki bane, sauyin tunanin mutane ne. Su mutane ne suke canzawa, in sun canza dole ita gwamnatin da za a yi za ta zama irinsu ce. Amma in aka canza Gwamnati kuma nizamin (da ke iko) yana nan, to duk abu daya ne ai. Yanzu duk canje-canjen da ake na gwamnatocin nan kun ga bambanci ne?”

Yace: “Duk mutane yanzu sun zaku cewa badi a zo a yi zabe su samu sauyi… Tunanin da s**a rika yi kenan a da can ko? Sai kuma abin da s**a zaba ya zama musu abin da ya zama musu. To kuma mai yiwuwa in sun yi zaben kuma a sake ganin abu ya sake zama yadda zai zama. Amma abin da ake ce musu shine, shi nizamin yana nan (don haka ba wani canji don an canza mai tafi da shi).”

Ya kawo misali da motar da injinta ya buga, a maimakon a yi kokarin duba injin a canza, sai ya zama kullum ana kokarin canja matukinta ne da tunanin kowa bai iya tukin bane. “Na san duk wadannan misalan tun 1970s nake badawa, nake cewa kun ga abin da mutane suke ce mana mu gyara abin da ba zai gyaru bane, mun ki gane shi nizamin za mu canza ba kamar yadda kullum kuke tunanin wai sai a zabo shugabane wanda zai ja abin ba.” Yace.

Ya jaddada cewa: “Shi nizamin za a canza, domin in aka ce shugaba ne, sai aka canza shi, in shi shugaban mutumin kirki ne to ba sai kuma nizamin ya zama na gari ba. Ba sai komai ya zama daidai ba, saboda shima zai yi amfani ne da ma’aikatansa wadanda suke cikin nizamin, su kuma ga abin da suke a kai, shine za a cigaba a kai din, yana ji yana gani ba zai iya sauya abin ba, komai gyaruwansa, komai walittakansa wadannan mutane za su lalata masa komai. Za ma su yi abin da mutane shi za su zarga.”

Jagora yace: “Yanzu abin da yake kanmu shine a yi ta ilmantar da mutane, don wadansu kalaman nake ganin kila mutum in ya yi ilimi ne zai iya ganewa.” Ya kara da cewa: “To kuma ka san ilmantar da mutane daga mustawan da suke ka daga su shima ba karamin aiki bane, saboda haka in an je karatu misali a kauye, ya kamata a yi ajin manya, wadanda bukatunsu za a yi la’akari da shi. Sai an fara musu da tsarki da wanka, don ta yiwu wasu basu sani ba, haka nan suke rayuwa.”

Ya kawo misalsalan yadda jahilcin wasu ke bayyana bayan sun girma alhali ana dauka su sun san abubuwa in ba don hakan ya bayyana daga gare su ba. Yace: “Kar ku sha mamaki da yawan mutane sunansu Musulmi ne, amma in aka koma ana maganar (hatta) wankan janaba da yawa basu iya ba.”

Ya kawo misali da yadda wani limamin kauye ya ba da fatawar cewa in mutum ya sadu da mace in dai matarsa ce to ba sai ya yi wanka ba. Yace: “Liman ne a kauye yake ba da wannan fatawar. To ka ga irin wadannan jidali maka-Malam ka je irin wannan kauyen kana musu maganar Wulaya ma ai kana bata lokaci ne, ba shine ‘asasi’ ba. hawa-hawa za ka bi su, mataki-mataki.”

A karshe ya jaddada muhimmancin samar da ajin manya maza da mata, sannan ya ba da shawarar shirya Daurori ga musamman yara baya ga karantar da su na dindindin da ake yi, wanda hakan zai taimake su sosai wajen tasowa cikin turbar nagarta.


12/05/2022

TSOKACIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) KAN HALIN DA KASA KE CIKI"Wannan irin ƙasa, mutane suna ta ɓaganniya, ana ya...
08/05/2022

TSOKACIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) KAN HALIN DA KASA KE CIKI

"Wannan irin ƙasa, mutane suna ta ɓaganniya, ana yaƙarku amma ba ku gane ba. (Ana kaɗa ku) kamar shanu. Ka san saniya ina ruwanta in ma ƙwata za a kai ta (a yanka)? Ana tafiya tana cin ciyawarta.... Amma mutum wanda yake da hankali, kuna gani ana neman a ƙarisa ku, a gurgunta ku da ƙarfin tsiya.

"Har ma an riga an gama gurguntawar, ana ta ta yi ne, kudinku baya sayan komai. A 1980 Dala 1 ne Naira 2, Yanzu Naira 570+ ne Dala 1, amma da kuwa Naira 2 ne Dala 1. To kuma amma wai mu ke da 'Golden Zone', amma kudinmu bai da daraja.

"Mu nan irin diban 'Gold' din da suke a kewayen Zamfara din nan, Helicopters suke zuwa da shi su yi ta diba, har mutane sai su ce sun ji karar jirgin sama, wasu Helicoptoci ne, kuma 'Gold' ake diba a yi waje da su, ba tare da biyan ko kwabo ba. Kuma su wadanda ake cewa shugabannin sun sani. Su abin da ya dame su kawai a basu nasu kason.

"Kuma ni na lura magana ma in ka yi ma (kamar) ba amfani, saboda su mutanen kasar nan ma in ka yi maganar ma suna cewa kai mahaukaci ne. Wata rana da nake magana din nan, su wadanda nake maganar don su lura amma ba su damu ba, amma sai aka ce har wani General ya daki tebur, yace wannan mutumin 'is dangerous!' ka ga yana magana da talakawa ne. Lokacin da nake cewa ku gane ba wata Boko Haram, mai suke diba, yanzu haka akwai rijiyar mai 25 a Borno, mai ake diba. Shine ya bugi Tebur yana cewa akwai hadari don ana fadawa talakawa ne. To su kuma talakawar ba su damu ba ma....

"Wato muna wata irin kasa ce da komai ya faru, in musiba ta samu wani mutum, sai ka ga kamar ma har murna suke yi. Sai su yi ta murna. Ka san da ban mamaki ko? Idan musiba ta samu wani sai ka ga wani yana murna. Shima sai tasa ta zo, sai ya yi bakin ciki, sai wani kuma shima ya masa murna. Sai ta je ga wancan, ka ga ba wanda ya san yaushe za ta kare kenan.

"Yanzu wa ya san ya al'amari zai kasance nan da baɗi, ko kuma bayan shekara biyu zuwa uku? Tunda abubuwan suna gudu

07/05/2022

Ganawar sheikh zakzaky (H) da wasu ba'adin 'yan uwa daga bangarorin harka daban daban.
Ayi sauraro lafiya

Address

Bauchi

Telephone

+2349065997747

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Boncy Channel's Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Boncy Channel's Tv:

Videos

Share

Category


Other TV Channels in Bauchi

Show All