Bauchi Daily Post

Bauchi Daily Post Domin samun ingantattun labarai a jihar Bauchi da Najeriya baki-daya
(1)

Nayi Alƙawarín Aúren Hafsat 'Yar TikTok, Idan Har Ta Amínce, A Cewar Matashi Prince Bilal Basheer. "Ni dan asalin jahar ...
22/09/2024

Nayi Alƙawarín Aúren Hafsat 'Yar TikTok, Idan Har Ta Amínce, A Cewar Matashi Prince Bilal Basheer.

"Ni dan asalin jahar Zamfara ne, na kuma na shirya tsaf tare da tsarkake niya, domin mu rufawa juna asiri akan auran Hafsat, tare da biyan sadaki k**ar yadda addinin musulunci ya tanada, inji matashin k**ar yadda ya bayyana a shafinshi na Facebook.

Wace shawara zaku bashi?

Yanzu-yanzu: Babban Mai Taimakawa Gwamnan Kano Kan Harkokin Rediyo Abdullahi Tanka Galadanchi ya sauka daga mukaminsa a ...
11/09/2024

Yanzu-yanzu: Babban Mai Taimakawa Gwamnan Kano Kan Harkokin Rediyo Abdullahi Tanka Galadanchi ya sauka daga mukaminsa a Gwamnatin Abba saboda zargin rashin iya aiki da makauniyar biyayya ga Kwankwaso.

TINUBU 2027: An Fara Dasa Allunan Tallar Neman Sake Zaɓar Shugaba Bola Ahmad Tinubu Akaro na biyu  Zaɓen dubu biyu da as...
11/09/2024

TINUBU 2027: An Fara Dasa Allunan Tallar Neman Sake Zaɓar Shugaba Bola Ahmad Tinubu Akaro na biyu Zaɓen dubu biyu da ashirun da bakwai (2027)A Birnin Abuja.

Wane fata zaku yi masa?

11/09/2024

Hisbah ta k**a wani Daraktan Fim na bogi da Budurwa mai neman zama Jarumar Kannywood daga jihar Nassarawa a wani Otal da ke Kano.

Shugaban kamfanin, Tim Cook ya ce saka AI a wayoyin Iphone zai ƙara faɗaɗa yawan abubuwan da wayar za ta iya yi. Dama da...
11/09/2024

Shugaban kamfanin, Tim Cook ya ce saka AI a wayoyin Iphone zai ƙara faɗaɗa yawan abubuwan da wayar za ta iya yi.

Dama dai Apple na shan s**a a kwanakin nan daga mutane masu ganin cewa kamfanin na fuskantar koma baya a ratar da ta bayar a fagen AI.

Kalli irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi a Maiduguri. Ambaliyar ta malale gidaje da dama wanda ya tilasta wa mutane tse...
11/09/2024

Kalli irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi a Maiduguri.

Ambaliyar ta malale gidaje da dama wanda ya tilasta wa mutane tserewa don neman mafaka a wasu unguwannin na daban.

Lamarin ya kuma shafi wani gidan ajiye namun daji, inda dabbobi da dama s**a fito cikin jama’a.

Fitacciyar jarumar fina-finan hausa Saratu Gidado ta rasu.Jarumar ta Rasu ne a yau Talata k**ar yadda wani makusancinta ...
09/04/2024

Fitacciyar jarumar fina-finan hausa Saratu Gidado ta rasu.

Jarumar ta Rasu ne a yau Talata k**ar yadda wani makusancinta ya bayyanawa Nasara Radio.

Mun tambayeshi ko Jarumar tana fama da wata lalurar amma yace lafiyarta kalau.

Muna Addu'ar Allah ya gafarta mata.

Gwamnan Bauchi ya cika wa maniyyata rabin kuɗin da aka ƙara musu.
30/03/2024

Gwamnan Bauchi ya cika wa maniyyata rabin kuɗin da aka ƙara musu.

27/03/2024

Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa sau biyu a wata ɗaya

An yi sammacin Sheikh Gumi saboda kalamansa kan ƴan bindigaƘarin bayani
27/03/2024

An yi sammacin Sheikh Gumi saboda kalamansa kan ƴan bindiga

Ƙarin bayani

Mai girma Gwamnan jihar Kano zai nada Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso mukamin Komishina a jihar Kano. Mustapha Rabiu Kwank...
27/03/2024

Mai girma Gwamnan jihar Kano zai nada Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso mukamin Komishina a jihar Kano.

Mustapha Rabiu Kwankwaso na daya daga cikin mutane 4, da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike da sunayensu majalisar dokoki, don nada su kwamishinoni. A jihar.

Akwai yiwuwar wannan watan mai kwanaki 30 ne, inji masana.
27/03/2024

Akwai yiwuwar wannan watan mai kwanaki 30 ne, inji masana.

27/03/2024

Tinubu ya karbo bashin ¥15bn daga kasar Japan, Najeriya za ta shafe shekaru 30 tana biyan bashin, inji Ministan kudi Wale Edun.

Kudurorin Majalisar Zartaswa Ta Jihar Jigawa A taron Majalisar Zartaswa ta jihar Jigawa na ranar Litinin (25/3/2024) an ...
27/03/2024

Kudurorin Majalisar Zartaswa Ta Jihar Jigawa

A taron Majalisar Zartaswa ta jihar Jigawa na ranar Litinin (25/3/2024) an amince da ƙudurori k**ar haka:

1. Majalisar Zartaswa ta duba Rahoton Kwamitin Tantance Rahoton Kwamitin Bincike akan Manyan Makarantun Koyar da Ayyukan Kiwon Lafiya na jiha, inda ta umarci Ofishin Babban Akanta na jiha da ya aiwatar da shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar tare da ɗaukar waɗannan matakai:

I. Sauke shugabannin Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Birnin Kudu da s**a haɗa da Provost, Bursar da Registrar tare da umarnin su kai kansu Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.

II. An sauke daraktocin Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Babura daga muƙamansu kuma za su kai kansu Ma’aikatar Lafiya.

III. Daraktocin Birnin Kudu, Hadejia da Babura za su biya kuɗaɗen da s**a bayar da ba’asi akansu.

IV. An sauke Provost, Bursar da Registrar na Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun daga muƙamansu sannan kuma za su kai kansu Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.

V. Provost na Kwalejin Kiwon Lafiya zai bayar da dalilai kan ɓacewar kuɗaɗen shiga na kwalejin da waɗanda aka samu daga gwamnati waɗanda ba a bayar da ba’asinsu ba.

VI. Dukkan jami’an da suke karɓar albashin da bai k**ata su karɓa ba sannan kuma ba a makarantun suke aiki ba amma sunayensu s**a kan jadawalin albashi na makarantun, za su mayar da kuɗin da s**a karɓa wanda ba haƙƙinsu ba ne.

VII. Ma’aikatar Lafiya za ta sabunta gine-gine da kayan aiki a Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.

VIII. Ma’aikatar Lafiya za ta ɗauki ƙarin ma’aikata domin cike giɓin ƙarancin malamai a waɗannan makarantu biyu.

IX. Gwamnati za ta kafa Hukumomin Gudanarwa na waɗannan makarantu biyu.

X. Ma’aikatar Lafiya za ta ƙara kuɗin abinci na ɗaliban Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.

2. Samar da ƙarin rancen kuɗi ga JASCO domin sayen buhunan takin zamani 90,000

(motoci 150) na NPK don kakar noma ta shekarar 2024 wanda za a sayar ga al’ummar jihar Jigawa. Za a sayo takin naira Biliyan Biyu (N2,000,000,000.00).

3. Gina gidajen kwana na ma’aikatan Ungozoma guda 7 tare da zagaye su a ƙananan cibiyoyin kiwon lafiya na: Abaya PHC a Dutse, Koya PHC a Miga, Kanzan PHC a K/Hausa, Madachi PHC a Kirikasamma, Yar’ Sara PHC a Roni, Chakwaikaiwa PHC a Taura da kuma Amanga PHC a Sule Tankarkar. Za a yi wannan aiki ne akan kuɗi naira N305,674,439.11.

4. Sabunta kwangilar samar da lantarki mai aiki da hasken rana (solar) a Babban Asibitin birnin Dutse daga naira N172,754,158.00 zuwa naira N252,849,395.50.

27/03/2024

Sauran kiris bashin da ake bin Najeriya ya cika Tiriliyan 100, inji hukumar NBS.

27/03/2024

Gwamnatin tarayya ta ayyana 29 ga watan mayu zuwa 1 ga watan afrilun 2024 a matsayin ranar hutu.

BAUCHI GARIN KAWAICIAdaidai Lokacinda Tsananin Rayuwa ke tilastawa Al'umma Daka Warwaso akan Manyan Motoci masu dauke ka...
25/03/2024

BAUCHI GARIN KAWAICI

Adaidai Lokacinda Tsananin Rayuwa ke tilastawa Al'umma Daka Warwaso akan Manyan Motoci masu dauke kaya, Alokacinne Motar BUA tayi Hatsari a Garin Daben Kasuwa Dake Karamar Hukumar Ganjuwan Jihar Bauchi:

Abin Sha'awa Kuma Abin burgewa shine: Babu Wani Mutum dayaje Kan motan da Sunan daka Diban Ganima saidai da Sunan Taimako, Saboda Imaninda suke dashi na cewe Kayan ba Halaliyarsu bane.

Dafatan Allah yaqara Mana Wadatar Zuciya

Sojoji sun ce sun ceto ɗalibai 137 ƴan makarantar Kuriga da aka SaceShalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta kuɓutar da ɗalib...
24/03/2024

Sojoji sun ce sun ceto ɗalibai 137 ƴan makarantar Kuriga da aka Sace

Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta kuɓutar da ɗalibai 137 na makarantar gwamnati ta Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Darektan da ke kula da harkokin yaɗa labarai na tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba a cikin wata sanarwa, ya ce sun ceto ɗaliban su 137 a dajin Zamfara.

A cewar sanarwar, sojojin sun ceto ɗalibai mata 76 da kuma maza su 61.

Tun a ranar 7 ga watan Maris ne aka sace ɗaliban firamare da na sakandare a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Kaduna kuma wani malamin makarantar da ya sha da ƙyar ya ce ɗalibai kusan 287 aka sace.

Malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi ya ce an sace ɗalibai na ɓangaren sakandare 187, sai kuma bangaren firamare ɗalibai 100.

"Sojoji tare da jami'an ƙaramar hukuma da na cibiyoyin gwamnati sun haɗa hannu wajen ceto ɗaliban da aka sace a makarantarsu da ke Kuriga," in ji Edward Buba.

Sai dai mai magana da yawun shugaban Najeriya, Abdulazeez Abdulazeez ya shaidawa BBC Hausa cewa "ɗaya daga cikin malaman da aka sace tare da ɗaliban ya rasu".

Tun da farko ƴanbindigar sun buƙaci a basu naira biliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa kafin ranar 27 ga watan Maris domin su saki ɗaliban. Kuma babu tabbas ko an biya kuɗin fansa kafin kuɓutar da ɗaliban.

Galibin ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

A ranar Lahadi da asuba ne gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar da wata sanarwar inda ya ce "an sako duka ɗaliban kuma suna cikin ƙoshin lafiya".

Sanarwar ba tayi ƙarin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban.

"Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kuɓutar da ɗaliban, kafin mu samu nasara," in ji Uba Sani.

Address

Nom 13, Yan-Doka Street Bauchi State, Mai Goro Plaza
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bauchi Daily Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Bauchi

Show All