06/12/2023
MUHIMMAN AIYUKAN DA SEN SHEHU BUBA YAYI A WATAN NOVEMBER KAWAI NA SHEKARAR 2023 A KANANAN HUKUMOMI BAKWAI.
Sanata Shehu Buba Umar, mutumi ne, da kuma shugaba ne tamkar hanun dama, ka raba ka ba kowa. Wanda kuma baisamu ba, sai su danyi hakuri da saura gaba.
Acigaba da shirin Sai Godiya, ayyukan alkhairin Sanata mai wakiltan Bauchi ta kudu sai dai muce godiya Hamdullilah, musanman cikin watan Nawanba nan da s**a wuce, ayyukan nasa ya cancanci ace gaskiya, Bauchi ta kudu sunyi dace. Ku biyoni...
1. Biyan kudi naira Miliyan Hudu da Dubu-Dari Shida (4, 600,000) a matsayin kudaden jinyar wasu mara lafiya su uku (3) a asibitin koyarwa wato TH na garin Bauchi.
2. Biyan kudi naira Dubu Dari Hudu da Ashirin da Biyu (422, 000) ma wani mutum daga Bauchi a matsayin kudin sallama asibitin Nurudden Clinic and Maternity Nigeria Limited dake Adebayo na garin Jos.
3. Shimfidar Kafeti wato salaya iron ta zamani a Massalacin Gyar- Gokaru na karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi.
4. Taimakon wasu mata Biyu da kayan abinci da kuma kudade a garin Tilden Fulani.
5. Taimakon kudi naira Dubu Talatin ma Dokta Imam Tilden Fulani domin sayan magunguna akowace wata.
6. Ziyartan mai martaba, Sarkin Bauchi- Dokta Rilwan Suleiman Adamu (Masarautun Bauchi) da kuma Sarkin Dass- Dokta Bilyaminu Othman.
7. Taziyyan iyalan marigayi Hon. Chindo Abdu (Turakin Zungur).
8. Taimakon kudi ma Mallam Dauda na Sabon Garin Narabi.
9. Ziyara Masallacin Ajiyan Bauchi
10. Kyautan naira Dubu Goma-Goma (10, 000) ma yara sabain da hudu (74) wanda s**a hadace Al-Qur'an mai girma da kuma kyautan naira Miliyan Daya da Dubu Dari Hudu (1, 400 ,000) wa makarantar wato Madarasattul Hanifatuldemmil Islam) a garin Bauchi wanda suke zaman wucin gadi a makarantar jeka ka dawo na Gwamnati dake Khandahar Bauchi.
11. Gyaran wutan lantarkin Sabon Garin Nabordo, tona bohol na ruwansha, samowa makarantar kujerun zama, gyaran gina-ginan azuzuka da kuma kara albashin Mallamai makarantar garin Nabordo.
12. Shimfidar Kafeti wato salaya, wutan lantarkin mai amfani da hasken rana, wato solar, da kuma kayan sauti na zamani a Masallacin Ajiyan Bauchi.
13. Gudumowar naira Miliyan Daya (1, 000,000) makarantar Lajnattul Madarasattul Tahfeezul Qur'an na garin Bauchi.
14. Taimakon kudi domin jinyar wata yarinya a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano dake birnin Kano.
15. Tallafin kudi naira Dubu Dari (100, 000) ma Bala Baddiko
16. Biyan kudin makarantar wani yarobta hanun uban nashi.
17. Biya ma wani yaro daga garin Toro kudin makaranta naira Dubu Dari da Goma sha Shida (116, 000).
18. Tallafin kudi ma wasu mutane agarin Bauchi ta hanun Kabiru Dan-Hajiya.
19. Naira Miliyan Daya (1, 000,000) ma Kungiyar Da'awah rashen karamar hukumar Toro
20. Naira Miliyan Daya (1, 000,000) wasu mahadattan Qur"an a Masallacin Kaura dake garin Bauchi.
21. Tallafin kudi naira Dubu Goma-Goma wa wasu mutane Goma ta hanun Ibrahim Mato.
22. Naira Dubu Dari Hudu (400,000) domin gyaran wutan lantarkin Solar mai amfani da hasken rana a garin Toro.
23. Sakon taziyya da kuma tallafin kayan abinci zuwa gidan Alhaji Dan'Asabe mai Awo.
24. Daukan nauyin jinyar wasu mara lafiya Goma a rana guda a Asibitocin Abnira (Dokta Shugaba), Hope Hill, Lamingo Medical Center, da kuma JUTH, duk acikin garin Jos.
25. Sakon taziyya da gudumawar kayan abinci zuwa gidan tsohon Shugaban karamar hukumar Alkaleri- Alhaji Sule Leko dangane da rasuwar mahaifinsa.
26. Daukan nauyin jinyar Mallam Umar Direba Inkil na karamar hukumar Bauchi dangane da ciwon spinal cord da yake fama da shower.
27. Daukan nauyin jinyar Mallam Lawal dake fama da ciwon kansa a garin Bauchi.
28. Biyan kudi naira Miliyan Biyu (2,000,000) domin jinyar wata mata mai suna Iklimah Baraza daga karamar hukumar Dass.
29. Tallafin kudi karatu, wato Scholarship ma wasu dalibai Dubu Biyu (2000) na makarantar Ahlul Qur'an Foundation, musanman mahadattan Al-Qur'an a garin Bauchi.
30. Karin kudi naira Dubu Dari Biyu (200, 000) domin cigaba da jinyar Aminu Musa wanda ke fama da ciwon iddo 👀, biyo bayan bada naira dubu dari biyar (500, 000) can baya.
31. Taimakon kudin makaranta ma dalibi Ibrahim Saleh na jamiyyar ilmi na grain Pankshin jihar Filato ta hanun Shagari Us to.
32. Daukan nauyin jinyar wasu mutane udu (4) sake fama da ciwon iddo 👀 a asibitin Makkah dake garin Bauchi.
33. Tona bohol domin samun ruwan sha ma mazaunin unguwar Dokta Rilwan kwatas ta bayan NITEL a garin Bauchi.
34. Daukan nauyin jinyar Aisha Saidu daga garin Magama Gumau a asibitin TH a garin Bauchi.
35. Naira dubu dari bakwai (700, 000) na kudin jinyar Hon. Mohammed Bala wanda akafisani da Hon. Sallahu na kafin kaura Madaki garin Bauchi a Asibitin Mallam Aminu Kano.
36. Naira miliyan goma (10, 000,000) ma wasu kungiya.
37. Rabon forms na tallafi fiye da dubu biyu a mazabar Bauchi ta kudu.
38. Daukan nauyin jinyar wani yaro mai suna Aliyu Mohammed Tilde a babban asibitin Toro dake Miya Barakete.
39. Sakon taziyya da kayan abinci ma iyalan marigayi Mallam Babangida Liman Katagun.
40. Daukar nauyin jinyar Mallam Usman Abubakar Magama Gumau ta hanun Shuaibu Abdullahi a Asibitin Hope Hill dake Jos.
41. Tallafin naira dubu amsin (50, 000) ma Aisha Abdullahi dake Sabon Garin Narabi domin gyaran gidanta.
42. Samo da wutan lantarki mai amfani da hasken rana (solar) a hanyoyin Gwallaga dake garin Bauchi.
43. Daukar nauyin jinyar Adamu Pawan Gudu karamar hukumar Toro a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi.
44. Tona bohol wa masu hakan madinai agarin Rimin Zayam.
45. Tonar bohol a unguwar Dowar Dillalai dake garin Bauchi.
46. Daukan nauyin jinyar Naibin Limamin Masallacin Ajiya dake Bauchi, wato Mallam Ali Muhammad Inuwa a wani Asibitin mai suna H & B Memorial Hospital, Bauchi.
47. Naira dubu dari bakwai (700, 000) domin gyaran makabartan garin Tilden Fulani.
48. Da hadin gwiwan NITDA, samowa da kuma kafawa kumfutoci da wutan lantarki mai amfani da hasken rana (solar) a karamar hukumar Dads da Kirfi.
49. Gudumawar naira miliyan goma (10, 000,000) ma kungiyar Musulmai na Dalibai rashen jihar Bauchi domin horarswa Islamic Vocation Course (IVC 2023) wato Bauchi 2023.
50. Samo da kujerun zama da kuma gyaran hazuzukan makarantar Gwamnatin jeka ka dawo na garin Magama Gumau, akan kudi naira miliyan daya da dubu dari biyar (1, 500,000).
51. Taimakon kudin naira dubu dari biyu da amsin (250, 000) ma wani Mallamin Adini.
52. Taimakon kudin naira dubu dari (100, 000) ma wani maralafiya daga garin Tafawa Balewa.
53. Tonan bohol domin samun ruwan sha a unguwar Tashan Saleh (Magama).
54. Rabon taburmai da ababen zama ma makaratun tsangaya a yankin Bauchi.
55. Gina dakin karatu na makarantar tsangaya a garin Legga, yankin Toro.
56. Taimakon kudin jinyar Hats at Haruna Jajuwal a asibitin Toro dake Miya Barakete.
57. Sayan gida mai dakuna uku (3) ma wata baiwar Allah maisuna Hajiya Talatu da hakafisani da Hajiya Ba'ayi a unguwar zago wanda ke fama da nakasa agarin Tilden Fulani.
58. Taimakon kudi ma Mallamai masu kula da wadanda s**a Musulunta.
59. Taimakon kudi naira dubu dari ma Mallama Hajara Bashir a unguwar Dawaki dake Bauchi.
60. Samowar hasken wutan lantarki mai amfani da hasken rana ma garuruwan Anguwan Lowcost/Juwad, Rinjin Gani, Rinjin Bukur, Sabon Garin Nabordo, da kuma Konan Maje.
61. Naira dubu amsin ma wata maisuna Madam Mary Ali dake makarantar ATAP a garin Bauchi.
62. Rabon Al-Qur'an mai Girma da wasu litatafen adini da kuma kayyekin rubutu ma wasu Mallamai takwas (8) a rugan Ardo Altine dake yankin Jammah.
63. Shimfidar kafeti, wato salaya na zamani a Masallacin a Masallacin Hon. Tukur Ibrahim dake Jangini, Toro.
64. Rabon kayan makaratun ma Dalibai a yankin Bauchi ta kudu, musanman, firamari na kangere da Liman Katagun.
65. Naira dubu dari biyu (200, 000) domin jinyar Mallama Rukaiya Ibrahim Bauchi a asibitin Assalam dake gida dubu, agarin Bauchi.
66. Naira miliyan daya da dubu dari tara (1, 900,000) domin jinyar Adamu Suleiman Zalau a asibitin koyarwa na ATBUTH, Bauchi.
67. Cigaba da ayyukan gine-ginen azzuzuwa karatu a garin Tafawa Balewa.
68. Daukar nauyin jinyar yaron marigayi Professor Ladan Shehu dake fama da ciwon kafa.
69. Tona bohol agarin Zalau dake yankin karamar hukumar Toro.
70. Daukar nauyin jinyar wata matan Fasto maisuna Theresa dake garin Rijiyan Mallam, jihar Bauchi a asibitin Hope Hill, Jos.
71. Gudumawar naira miliyan daya (1, 000,000) ma makarantamakaranta maisuna Madarasatul Tarbiyatil Mahfizhul Qur'an Kareem karkashin FOMWAN na jihar Bauchi.
72. Naira dubu dari biyu da amsin (250, 000) da kuma shimfidar tabarmai ma makarantar Sheikh Jafar Adam dake Bauchi.
73. Tallafin naira dubu goma-goma (10, 000) ma mata dari biyu (200).
74. Daukar nauyin jinyar limamin Masallacin Ajiya dake Bauchi a asibitin kashi, wato orthopedics ta Kano.
74. Naira dubu dari da goma (110, 000) domin jinyar Mallama Amina Bala dake unguwar Gwallaga Bauchi.
75. Daukar nauyin jinyar Hon. Musa Bayero Raja, tsohon chairman na karamar hukumar Dass.
76. Daukar nauyin jinyar wata baiwar Allah daga karamar hukumar Dass.
77. Sayan kayan aikin watsa labarai irinsu Wayar Redmi, Laptop, Tripod stands, wireless microphones, video camera, external hard disks da dai sauransu ma Mujjadadiya Tv.
78. Daukan nauyin jinyar wasu maralafiya guda bakwai (7) a rana guda a asibitocin Hope Hill da Potters da suke garin Jos.
79 Da dai sauran ayyukan alheri da bamu sani ba kuma baki 👄 bazata iya fadi ba da s**a wakana tsakani siri.
Allah ya ja kwanan Sanata Shehu Buba Umar da muma gaba daya.
Alhamdullilah
Ismaila Abdulrahaman
Mai wallafa SAI GODIYA
November, 2023