Kadarko TV

Kadarko TV Gaskiya da Amana Shine Jarin Mu

Kadarko TV kafar yada labarai da aka kafa domin samar da ingattatu

Sojojin Najeriya sun kashe 'ƙasurgumin ɗan fashi' Junaidu FasagoraDakarun sojin Najeriya da aka tura jihar Zamfara domin...
28/03/2024

Sojojin Najeriya sun kashe 'ƙasurgumin ɗan fashi' Junaidu Fasagora

Dakarun sojin Najeriya da aka tura jihar Zamfara domin yaƙar ta'addanci sun kashe shahararren jagoran ƴan bindiga mai suna Junaidu Fasagora tare da wasu mayaƙansa, a cewar rundunar.

Wata sanarwa da ta wallafa a intanet ta ce sun yi nasarar ce bayan fafatawa da kuma musayar wuta mai zafi a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

"Junaidu Fasagora tare da sauran ƴan bindiga abokansa sun dade suna garkuwa da mutane tare da aikata wasu ayyukan ta'addanci ga al'ummar jihohi da dama na yankin arewa maso yammacin kasar," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa kawar da su "wata gagarumar nasara ce a yaƙin da ake yi da ta'addanci da kuma rashin tsaro".

Mutuwar Fasagora na zuwa ne yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin mutuwar shahararren ɗan fashin daji Dogo Gide, wanda har yanzu BBC ba ta kai ga tabbatar da mutuwarsa ba.

Tinubu ya kafa kwamitin farfaɗo da tattalin arzikin NajeriyaShugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kafa kwamitin karta-kwana ...
28/03/2024

Tinubu ya kafa kwamitin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kafa kwamitin karta-kwana da zai samar da hanyoyin daidaita tattalin arzikin ƙasar da ke ci gaba da fuskantar tasku.

Farashin kayan abinci da mai ya yi tashin gwauron zabi kuma mutane da dama na fama kasancewar albashinsu bai wadatar ba wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum ba.

Ƙalubalen tattalin arzikin ya janyo matsin rayuwa ga mutane da dama abin da kuma ke ƙara matsa lamba kan gwamnatin Tinubu.

Wasu na ganin janye tallafin mai da faɗuwar darajar naira ne s**a janyo matsalolin.

Sai dai hukumomi sun ce yi wa tattalin arzikin ƙasar garambawul ya zama dole saboda makomar ƙasar.

Shugaban ya umarci kwamitin ya gabatar da cikakken tsarin farfaɗo da tattalin arziki cikin mako biyu wanda za a aiwatar cikin wata shida.

Manyan jami'an gwamnati da kuma ƴan kasuwa ne mambobin kwamitin.

Shugaban ya kuma kafa kwamitin shugaban ƙasa da zai kula da harkokin tattalin arziki, wanda kuma zai jagoranci sa ido kan sauye-sauyen tattalin arziki.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayar da tabbacin cewa Naira za ta ci gaba da samun tagomashi akan kudaden k...
28/03/2024

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayar da tabbacin cewa Naira za ta ci gaba da samun tagomashi akan kudaden kasashen waje.

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Da...
28/03/2024

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura jihar Katsina a wannan rana ta Laraba 27 ga Maris 2024.

Baka Bukatar Sai Ka Sanni,  Ko Wani Daga Cikin Muƙarraban Gwamnati, Domin Samun Matsayi a Aikin Gwamnati, Inji Gwamna Ma...
28/03/2024

Baka Bukatar Sai Ka Sanni, Ko Wani Daga Cikin Muƙarraban Gwamnati, Domin Samun Matsayi a Aikin Gwamnati, Inji Gwamna Mal. Dikko Umaru Radda

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda Ph.D, ya fadi haka ne a yau, Laraba 27/03/2024, lokacin da ya Jagoranci rantsar da sabbin manya sakatarori a fadar gidan gwamnatin jihar katsina.

A lokacin da yake jawabi gwamnan ya taya wadanda da s**a samu nasarar zama manyan sakatarorin murna san nan kuma ya bayyana cewa dukkan su an zabe su ne a bisa chanchanta ba tare da sun zo neman alfarma wajen shi ba, ko kuma wane ya san wane ba.
Ya bayyana kowanen su sai da ya tsallake ƙa'idojin da aka tanadar kafin aka bashi matsayin.

“Dole sai anbi ƙa'ida wajen bada matsayi a aikin gwamnati matukar muna so aikin ya Inganta” Inji gwamnan.

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda yaja hankalin su da suyi amfani da damar da Allah ya basu wajen taimakon jihar Katsina musamman a wannan lokacin da jihar ke fama da rashin tsaro, matsin tattalin arziki, tsadar abinci da sauransu.

Manyan sakatarorin da aka rantsar sun fito ne daga kananan hukumomin Batagarawa, Bindawa, Jibia, Kankia, Mashi, da Safana, domin cike guraben kananan hukumomin da basu da manyan sakatarori.

Daga karshe yayi kira ga daukacin al'ummar jihar Katsina da su dage wajen saka jihar nan cikin addu'o'in su musamman a lokacin da suke buda baki cikin wannan wata mai alfarma da niyyar Allah SWT ya tsare jihar daga matsalolin da take fama da su musamman na rashin tsaro.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Jobe; Babban Jojin Jihar Katsina, Justice Musa Danladi Abubakar; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Nasir Yahya Daura; Sakataren Gwamnati, Barista Abdullahi Faskari; Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnati Jihar Katsina, Hon. Jabiru Tsauri; ƴan majalisar dokoki, yan majalisar zartarwa, Shugabanin kananan hukumomi da sauran al'umma ne s**a halarci taron.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
27/3/2024

Jam’iyyar APC ta Jihar Katsina ta Rusa Kwamitin Masu Ruwa da Tsaki a Matakin Jiha da Kananan HukumomiJam’iyyar APC reshe...
28/03/2024

Jam’iyyar APC ta Jihar Katsina ta Rusa Kwamitin Masu Ruwa da Tsaki a Matakin Jiha da Kananan Hukumomi

Jam’iyyar APC reshen jihar Katsina ta rusa dukkanin mambobin kwamitocin masu ruwa da tsaki a matakin jiha da kananan hukumomi. Mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha Alhaji Bala Abubakar Musawa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina.

Da yake jawabi a madadin shugaban jam’iyyar, Alhaji Sani Ali Daura, mataimakin shugaban na jiha ya jaddada cewa rusasu zai fara aiki nan take. Ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba jam’iyyar za ta fito da hanyoyin da za a bi wajen sake kafa mambobin kwamitocin masu ruwa da tsaki, k**ar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

Da yake yaba wa masu ruwa da tsaki masu barin gado bisa irin gudunmawar da s**a bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zabukan da s**a gabata, shugaban ya mika sakon taya murna bisa ga gudunmuwar da s**a bada kuma ya nemi fahimtarsu da gaske tare da yi musu fatan alheri a harkokin siyasarsu na gaba.

Bugu da kari, shugaban ya bada tabbacin cewa za’a gudanar da zaben sabon kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a matakin jiha da kananan hukumomi cikin adalci da adalci.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media; for APC Vice Chairman Katsina State.
27/3/2024

Gwamnatin Nijeriya ta yi alkawarin daukar nauyin karatun 'ya'yan sojoji da aka hallaka a jihar Delta.
27/03/2024

Gwamnatin Nijeriya ta yi alkawarin daukar nauyin karatun 'ya'yan sojoji da aka hallaka a jihar Delta.

Gwamna Radda Ya Amince da Naira 15,000 a Matsayin Tallafin Ramadan/Sallah Ga Ma’aikata A Jihar KatsinaGwamna Malam Dikko...
27/03/2024

Gwamna Radda Ya Amince da Naira 15,000 a Matsayin Tallafin Ramadan/Sallah Ga Ma’aikata A Jihar Katsina

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya amince da raba tallafin azumi da Sallah ga daukacin ma’aikata a fadin jihar.

A cikin wata wasika da shugaban ma’aikatan jihar ya rattaba ma hannu, gwamnan ya umarci ma’aikatar kudi da ta saki kudi naira 15,000 ga kowane ma’aikacin da aka lissafa a cikin albashin jihar. Bugu da kari, ya umurci ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu da ta samar da kudi naira 15,000 ga duk ma’aikatan kananan hukumomi na Jihar Katsina.

Bugu da kari, an umurci ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu da kuma hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa da su shirya biyan Naira 15,000 ga kowane ma’aikacin da aka rubuta a cikin jerin sunayen kananan hukumomin ilimi 34.

Matakin da Gwamnan ya dauka na bayar da tallafin Azumin Ramadan da Sallah ya nuna yadda ya jajirce wajen ganin an samu kwanciyar hankali da walwalar ma’aikata.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
27/3/2024

Sabbin malaman Makarantar da Malam Dikko Umaru Radda PhD ya dauka aiki sun fara samun albashinsuBiyo bayan tantancewa do...
27/03/2024

Sabbin malaman Makarantar da Malam Dikko Umaru Radda PhD ya dauka aiki sun fara samun albashinsu

Biyo bayan tantancewa don tsame tsaki daga tsakuwa a tsakanin sabbin malaman makarantar da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD ta dauka aiki su 7,325 ya zuwa yanzu dai wasu daga cikinsu sun fara samun albashinsu.

An dai dauki malaman makarantar ne domin su koyar a makarantun firamare da na sakandare da ke fadin jihar.

A baya dai an yi ta ce-ce-kuce a kafar sadarwar zamani ta soshiyal midiya, biyo bayan dan tsaikon da aka samu wajen biyan albashin. Sai dai wannan tsaikon ya samo asali ne bayan da aka gano yadda wasu ke son kutsa shafaffu da mai a cikin sabbin malaman makarantar da ba su ma cancanci a dauke su aikin malanta ba.

Ya zuwa yanzu malaman makaranatar dake aiki karkashin Hukumar Ilimin bai Daya ta Jihar Katsina (SUBEB) sun samu albashin watan Fabrairu kuma an bada umarnin a sakar da albashin watan Maris na shekarar 2024.
Shirye-shirye sun yi nisa na fara biyan malaman makarantar da ake aiki karkashin (Teachers Service Board) nan da dan wani lokaci.

Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD a kodayaushe na nanata kudirinsa na baje abu a faifai domin tsage gaskiya komai dacinta, da kokarin kwatanta adalci da shimfida shugabanci nagari a jihar Katsina.

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda PhD ta yi godiya ga wadannan sabbin malaman makaranta bisa nuna hakuri da fahimtarsu a lokacin da ake cikin wannan yanayi. Kazalika, gwamnatin ta nuna aniyarta ta ba su horo da su da daukacin ma'aikatan jihar Katsina domin su samu kwarewa a aikinsu.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
27/3/2024

Gwamna Radda Ya Nada Daraktoci Shida A Matsayin Manyan Sakatarori (Permanent Secretaries)Bayan gudanar da jarabawar gwaj...
26/03/2024

Gwamna Radda Ya Nada Daraktoci Shida A Matsayin Manyan Sakatarori (Permanent Secretaries)

Bayan gudanar da jarabawar gwaji karo na biyu da wasu Daraktoci domin cike gurbin muk**ai na Manyan Sakatarori, Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ya amince da nada mutum shidda (6) Daraktoci a matsayin Manyan Sakatarori daga Kananan Hukumomin da basu da manyan Sakatarori.

Wadanda aka nada sun hada da;

•Jamilu Yakubu Batagarawa- Batagarawa

•Sama’ila Yusuf Bindawa-Bindawa

•Lawal Suleiman Abdullahi- Jibia

•Hamza Mani Tafashiya-Kankia

•Ahmad Hassan Mashi- Mashi

•Ibrahim Mua’azu Safana-Safana

A ranar Laraba 27 ga Maris, 2024 ne za a rantsar da sabbin sakatarorin a fadar gidan Gwamnatin Jihar Katsina da karfe 11:00 na safe.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
26/3/2024

Gwaman Malam Dikko Radda Ya Rantsar da Sabon Shugaban Karamar Hukumar SafanaA yau ne, Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, M...
26/03/2024

Gwaman Malam Dikko Radda Ya Rantsar da Sabon Shugaban Karamar Hukumar Safana

A yau ne, Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, PhD, ya rantsar da Hon. Abdullahi Sani Safana, a matsayin sabon Shugaban Karamar Hukumar Safana a Babban Dakin Taron Fadar Gidan Gwamnatin Katsina.

Rantsuwar ta biyo bayan rasuwar tsohon shugaban Karamar Hukumar Safana, Marigayi Hon. Muhammad Kabir Umar wanda ya rasu a satin da ya gabata bayan rashin lafiya da yayi fama da ita.

A lokacin rantsuwar, Gwamnan ya yi ta’aziyya ga masu ruwa da tsaki na Karamar Hukumar Safana da kuma Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi (ALGON) bisa ga wannan babban rashi tare da adduar Allah ya gafarta ma mamacin ya karbi shahadar shi.

Gwamnan Radda yaja hankalin sabon Shugaban Karamar Hukumar Safana da yaji tsoron Allah ya gudanar da aikin shi ba tare da son kai ba ko kuma wariya ga al’ummar da yake jagoranta. Ya kuma yi kira gare shi da yayi kokari ya hada kan duk wasu mutane a jagorancin shi domin samun nasara a cikin mulkin shi.

Wadanda s**a halarci bikin rantsuwar sun hada da Babban Jojin Katsina, Justice Musa Danladi Abubakar; Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ma Jihar Katsina, Hon Abduljalal R***a; Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari; Sanatocin Shiyyar Katsina da Daura, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Tsauri; Kwamishinan Kananan Hukumomi Da Masarautun Gargajiya, Prof Badamasi Charanchi, da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha da sauran manyan mutane.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
26/3/2024

Mai girma Gwamna Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya halarci tafsirin watan Ramadan wanda ya gudana a ranar Talata,...
26/03/2024

Mai girma Gwamna Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya halarci tafsirin watan Ramadan wanda ya gudana a ranar Talata, 27 ga watan Maris 2023 a gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Wadanda s**a halarci taron sun hada da Babban Jojin Jihar Katsina, Justice Musa Danladi Abubakar; Kwamishinan Addinai, Hon. Isiya Shehu Dabai; Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Hon Hamza Sulaiman Faskari; da kuma Alh Usman Abba Jaye.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
26/3/2024

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina ya gana da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC dake Karamar Hukumar Safa...
26/03/2024

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina ya gana da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC dake Karamar Hukumar Safana a fadar Gidan Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Talata, 26 ga watan Maris 2024.

Ganawar dai anyi ta ne a asirce wadda ta samu halartar Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha da Mataimakin sa, Alh Sani Aliyu da Alh Bala Abu Musawa,Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Katsina, Rt. Abduljalal Haruna R***a; Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Tsauri; Tsohon Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Safana, Batsari da Danmusa, Hon. Ahmed Dayyabu Safana; Hon. Abdulkadir Zakka, Hon Abba Dayyabu Safana da sauran su.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
26/3/2024

An yanke wa ɗan Chinan da ya kashe Ummita hukuncin kisaWata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa ɗanƙasar China Frank Ge...
26/03/2024

An yanke wa ɗan Chinan da ya kashe Ummita hukuncin kisa

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa ɗanƙasar China Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe budurwarsa, Ummukhulsum Sani Buhari.

Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Haruna Dederi ne ya tabbatar wa BBC hukuncin kotun bayan zaman shari'ar da aka yi ranar Talata.

Ya ce "alƙali ya yi hukunci inda ya sami Frank da laifin kisan kai wanda hukuncinsa kisa ne kuma ya zartar da hukunci a kan haka." in ji kwamishinan.

Ya ƙara da cewa "ita shari'a tana da farko tana da ƙarshe, kuma abubuwan da aka iya bi sawu aka gano yayin tuhumar wanda ake tuhuma sune ake kafa hujja da su a kai ga hukunci,"

"Abubuwan da s**a gabata sune s**a wajabta wa kotu ta ɗauki irin wannan matsayi." k**ar yadda kwamishinan ya bayyana.

A ranar 16 ga Satumban 2022 ne ɗanChinan ya daɓa wa marigayiyar wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano.

Ƙarin kuɗin kujerar hajji bai shafi masu adashin gata ba – NahconHukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta bayyana cewa...
26/03/2024

Ƙarin kuɗin kujerar hajji bai shafi masu adashin gata ba – Nahcon

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta bayyana cewa ƙarin kuɗin kujerar hajj da ta yi a baya-bayan nan ba zai shafi maniyyatan da s**a biya ta tsarin adashin gata ba.

Hukumar ta Nahcon ta bayyana haka ne ƴan kwanaki bayan fitar da sabon farashin kujerar hajjin ga maniyyatan bana.

Nahcon ta ce ita ce za ta ɗauki nauyin biyan cikon kuɗaɗen maniyyatan da s**a biya ta tsarin adashin gata abin da ke nufin maniyyatan ba za su biya ƙarin ko sisi ba.

A ranar Lahadi ne hukumar ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin s**a koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya tare da bai wa maniyyatan wa'adin kwana huɗu su cika kuɗin.

Ta jingina matakin nata ga yadda farashin dala ke ci gaba da hauhawa wadda da ita ce ake yin ƙiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke buƙata.

Tun bayan sanar da ƙarin kuɗin ne al'umma suke ta bayyana ra'ayoyinsu inda wasu ke ganin matakin ya zo a ƙurarren lokaci ganin yadda ake fama da tsadar rayuwa a ƙasar.

Adashin gata tsari ne da Nahcon ya ɓullo da shi shekarun da s**a gabata domin saukakawa maniyyata wajen tara kudin gwargwadon halin da mutum yake da shi.

Hukumar alhazai ta dauko wannan tsari na adashin gata daga kasashe k**ar Malaysia da Indonesia, inda 'yan kasar ke irin wannan tarin kudi don sauke faralli.

Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa sau biyu a wata ɗayaBabban Bankin Najeriya ya yi ƙarin kuɗin ruwa da kashi 2% ...
26/03/2024

Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa sau biyu a wata ɗaya

Babban Bankin Najeriya ya yi ƙarin kuɗin ruwa da kashi 2% karo na biyu kenan cikin wata ɗaya, inda yanzu ya kai kashi 24.75, a cewar gwamnan bankin Olayemi Cardoso.

Shi ne karo na biyu da CBN ya yi ƙarin a cikin wata daya, bayan ƙara kashi 4% a watan Fabrairu.

Shawarar babban bankin wanda shi ne ƙari mafi yawa a cikin kusan shekara biyu, na da nufin taƙaita samun kuɗaɗen jari da rage hauhawar farashi.

Hauhawar farashi a Najeriya yanzu ta kai kashi 31.7%, sanadin tsadar farashin abinci da na mak**ashi, tashin kuɗin sufuri da kuma taɓarɓarewar tsaro a yankunan da ake samar da abinci.

Kayan abincin sun haɗar da burodi da shinkafa da nama da nono da kayan marmari duka sun ninka farashinsu.

Najeriya mafi girman tattalin arziƙi a Afirka na fuskantar tsattsauran yanayin tattalin arziƙi, lamarin da ya ingiza mutane da dama cikin talauci.

Hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta ce ta damƙa kuɗin mamata ga danginsu a BauchiHukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta jihar B...
26/03/2024

Hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta ce ta damƙa kuɗin mamata ga danginsu a Bauchi

Hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta jihar Bauchi ta ce ta damƙa wa dangin wasu mutane da hatsari ya ritsa da su a kan hanyar Bauchi zuwa Toro, kuɗi naira 1, 680,700, mallakar 'yan uwan nasu.

Rilwanu Sulaiman Birnin Kebbi, jami'in wayar da kai na hukumar ya ce kuɗin mallakar mutum uku ne, a cikinsu har da wanda yake da naira 1, 648, 500.

Ya ce hukumarsu ta damƙa kuɗin ne ga dangin waɗanda s**a mutu a ofishinta da ke yankin Toro, bayan kammala bincike a ranar Litinin.

Hatsarin dai ya yi muni, wanda Rilwanu Sulaimanu ya ce ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu, yayin da uku s**a jikkata kuma suna kwance suna jinya a asibiti.

Hatsarin mota kusan ruwan dare ne a Najeriya, inda ɗumbin mutane suke mutuwa a kan tituna sanadin karon ababen hawa da sauran dalilai.

Kotu ta sanya wa Murja Kunya takunkumin amfani da soshiyal midiyaWata babbar kotu da ke Kano ta ba da belin fitacciyar j...
25/03/2024

Kotu ta sanya wa Murja Kunya takunkumin amfani da soshiyal midiya

Wata babbar kotu da ke Kano ta ba da belin fitacciyar jarumar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya a kan kuɗi naira dubu 500 da kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata.

Baba Jibo Ibrahim, mai magana da yawun kotunan Kano ya tabbatar wa BBC wannan labarin, inda ya ce kotun ta ba da belin Murja ne bayan zaman kotun da aka yi a yau Litinin.

Alƙalin ya ce dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya mata ya zama ɗan'uwanta na jini, sannan ɗayan kuma dole ne ya zama yana da shaidar mallakar fili a Kano.

Alƙali Nasiru Saminu ya kuma ce ya bayar da belinta ne bisa hujjar cewa matashiyar 'yar Tiktok din ta wuce kwana 30 a garƙame.

Sai dai alƙalin ya haramta wa jarumar tiktok ɗin amfani da shafukan sada zumunta har zuwa lokacin kammala shari'ar.

Alƙalin ya kuma ce kwamishinan ƴansanda na da ikon sake k**a Murja matuƙar ta ƙi mutunta umarnin haramta mata amfani da shafukan sada zumuntar tare da gabatar da ita gaban kotu.

Mai shari'ar ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Mayu don ci gaba da zama.

Hukumar Hisba ta jihar Kano ce ta k**a Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami'an tsaro bisa zargin ta da laifukan da s**a shafi yada baɗala a shafukan sada zumunta.

Daga bisani kuma wata kotu a Kano ta tura ƴar tiktok ɗin zuwa asibitin kula da lafiyar masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta

Gwamnatin Nijeriya ta fara gyaran tsohuwar fadar shugaban kasa ta Dodan Barrack da ke Lagos
24/03/2024

Gwamnatin Nijeriya ta fara gyaran tsohuwar fadar shugaban kasa ta Dodan Barrack da ke Lagos

Gwamnatin jihar Katsina na cigaba da gyara makarantun firamare 150 a kananan hukumomi 34Gwamnatin jihar Katsina tare da ...
24/03/2024

Gwamnatin jihar Katsina na cigaba da gyara makarantun firamare 150 a kananan hukumomi 34

Gwamnatin jihar Katsina tare da hadin guiwar ma’aikatar kula da ilmin firamare da na sakandare da hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar, a halin yanzu suna yin wani gagarumin kokari na daukaka darajar ilimi a jihar Katsina. Wannan shiri ya kunshi gyaran makarantun firamare 150 da aka bazu a kananan hukumomin ilimi 34 na jihar.

Gwamna Malam Dikko Radda, a ranar 10 ga watan Fabrairu ya amince da ware sama da Naira bilyan hudu domin gyara wadannan makarantun firamare da s**a lalace cikin gaggawa. Yana da kyau a lura cewa an raba wadannan kudade ne ga makarantun da ke da bukatar gyara a jihar. Babban makasudin wannan yunƙurin shi ne don inganta wadannan makarantu don samar da ilmi mai inganci ga dalibai.

Kwamitin Gudanarwa na Makarantu wato SBMCs na waɗannan makarantu ne za su sa idanu don gudanar da ayyukan ta hanyar amfani da tsarin ci gaban al'umma CDD. Waɗannan ayyukan sun haɗa da gina ƙarin gine-gine masu azuzuwa uku, ofis, da wuraren ajiya. Haka kuma, za a yi tanadin samar da ruwa da tsaftar muhalli, k**ar rijiyoyin burtsatse da bandaki na ‘yan mata. Bugu da ƙari, za a gudanar da manya ko kananan gyaran azuzuwa.

A ranar Juma’a 22 ga watan Maris 2024 tawagar sa ido daga ma’aikatar kula da ilimin firamare da sakandare ta jihar Katsina ta ziyarci makarantun firamare na Kirkini da Kafin Soli da ke Kankia, da kuma makarantar firamare ta Shagumba da ke karamar hukumar Batagarawa. Wannan tawaga ta ƙunshi mambobi da yawa, ciki har da Kwamishinar kula da ilmin firamare da sakandare da Babbar Sakatariya, Hajia Mairo Muhammed ta wakilta. Shugaban hukumar SUBEB da mai kula da ayyuka na jiha Hajia Binta Abdulmumin kuma sun halarci taron, tare da ’yan tawagar aikin, daraktoci daga hukumomi daban-daban, wakilai daga ma’aikatar ilimi ta tarayya da UBEC, tawagar injiniyoyi, da ni kaina, da sauran su. .

Wannan muhimmin aiki kuma na tare da haɗin guiwar sauyin tsarin ilmi a matakin Jiha (TESS) da BESDA-AF.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
24/3/2024

Mai taimaka ma Gwamnan Jahar Katsina kan kafafen sadarwa na zamani Hon. Isa Miqdad AD Saude ya samu damar halartar mazab...
23/03/2024

Mai taimaka ma Gwamnan Jahar Katsina kan kafafen sadarwa na zamani Hon. Isa Miqdad AD Saude ya samu damar halartar mazabar Wakilin Kudu II a karamar hukumar Katsina domin gane ma ido na yadda rabon kayan masarufi da Gwamnatin Jihar Katsina ta karya farashin shi yake gudana.

Makasudin ziyarar tashi ita ce ganin irin namijin kokarin da Gwamna Malam Dikko Radda da gwamnatin sa suke yi na tallafawa marasa galihu a jihar Katsina.

Karkashin Jagorancin Gwamna Radda, Jihar Katsina ta ware buhunan hatsi iri-iri 72,200 da s**a hada da Masara, gero, da dawa. Ana siyar da wadannan hatsi a kan kudi Naira 500 kachal kan kowane mudu. Wannan shiri dai na da nufin rage wahalhalun tattalin arziki da tsadar hatsi a fadin kasar nan.

A matsayin shi na mai rike da mukamin gwamnati mai wakiltar gundumar, ya tabbatar da cewa tsarin rabon ya bi ka’idojin gaskiya da rikon amana. Yana da matukar muhimmanci a kiyaye wadannan ka'idoji domin sauke nauyin al’umma da ya rataya a kan mu.

Ya samu rakiyar zababben Kansilar mazabata, Hon. Zahraddini Mai Dubu-dubu; Supervisory Councilor, Hon. Khalid Mamman da kuma Liason Officer na Karamar Hukumar Katsina, Hon. Abba Abdulhafiz.

Gwamnan Kano bai ji dadin yadda ake raba abincin bude baki baGwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa kan...
23/03/2024

Gwamnan Kano bai ji dadin yadda ake raba abincin bude baki ba

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa kan yadda ake gudanar da aikin shirin raba abincin azumi da ake yi a jihar.

Yayin wata ziyarar bazata da ya kai ɗaya daga cibiyoyin da ake aikin raba abincin a Ƙaramar Hukumar Municipal, gwamnan ya nuna rashin jin dadi game da irin abincin da ya gani ana rabawa a cibiyar.

Alala ce da farar shinkafa da manja, inda ya rika tambayar yaran da aka rabawa cewa "manja suke samu ku ba miya ba?".

Gwamnan ya koka kan yawa da kuma ingancin abinci da ya ga ana rabawa, wanda a cewarsa ya sha banban da abin da gwamnainsa ta amince ta kuma sahale a rika rabawa.

"Wannan wane irin shirme ne," in ji gwamnan lokacin da yake zantawa da masu dafa abincin, yana tambayarsu wanene ya ba su damar dafa abincin a wannan tsari.

Abba ya ja kunnan masu dafawar tare da ba su sako su shaidawa waɗanda s**a ba su damar aikin, cewa kada ya sake dawowa ya tarar da irin wannan abincin da hankalinsa bai kwanta da shi ba.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun yi nasarar dakile wani yunkurin garkuwa da mutane a kan hanyar Bur...
23/03/2024

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun yi nasarar dakile wani yunkurin garkuwa da mutane a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna a makon nan.

Sojoji sun kubutar da daliban makarantar tsangaya da aka yi garkuwa da su a makon jiya jihar Sokoto.
23/03/2024

Sojoji sun kubutar da daliban makarantar tsangaya da aka yi garkuwa da su a makon jiya jihar Sokoto.

Gwamnatin jihar Bauchi ta yiwa fursunoni 96, dake daure a gidan gyaran hali afuwa.
22/03/2024

Gwamnatin jihar Bauchi ta yiwa fursunoni 96, dake daure a gidan gyaran hali afuwa.

Dole ne a hukunta waɗanɗa s**a kashe mana sojoji 17 - TinubuShugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce waɗanda s**a kashe sojo...
22/03/2024

Dole ne a hukunta waɗanɗa s**a kashe mana sojoji 17 - Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce waɗanda s**a kashe sojoji a jihar Delta za su fuskanci hukunci, yana mai gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kai hare-hare kan sojoji da ababen more rayuwa ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar dattawan kasar a yayin wani zaman cin abincin buɗe baki a fadar gwamnati a ranar Alhamis.

Tinubu ya ce sojoji za su ci gaba da samun goyon bayan gwamnatinsa wajen kawar da barazanar tsaro a faɗin kasar.

"Rundunar sojojinmu na aiki tukuru, kuma ba za mu bar maharan su lalata mutunci da ƙimar sojojinmu da kuma shugabancinta ba."

"Za mu ci gaba da karfafawa da gwagwarmayar neman ƴancinmu da haƙƙinmu na zama daya, kuma za mu yi nasarar kawar da talauci daga kasarmu,’’ in ji Tinubu. Shugaba.

Tinubu ya shaida wa shugabannin Majalisar Dattawan cewa, mutuncin Majalisar Dokoki dole ne ya ci gaba da wanzuwa, kuma a ko da yaushe gwamnatinsa za ta ƙarfafa hadin gwiwa don ci gaban kasa.

"A kan matsalar tattalin arziki da muke fuskanta yanzu, muna ƙoƙarin gaske don ganin mun magance wannan matsalar, kudaden shigarmu sun inganta."

"Abin da ya k**ata mu yi shi ne mu kula da yadda muke kashe kuɗaɗe da kuma yadda za mu sarrafa kanmu da kyau."

"Nan ba da jimawa ba za ku ga sauyi, murmushin 'yan Najeriya ya kusan dawowa," in ji shugaban.

A nasa jawabin, shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya godewa shugaba Tinubu bisa karbar bakuncin ‘yan majalisar, inda ya bayyana cewa yin mu’amala akai-akai zai ƙara fahimtar juna da gudanar da shugabanci mai inganci.

Dalibai biyu sun mutu a wurin turmutsutsun karbar tallafi a NassarawaAkalla dalibai mata biyu na jami'an jihar Nassarawa...
22/03/2024

Dalibai biyu sun mutu a wurin turmutsutsun karbar tallafi a Nassarawa

Akalla dalibai mata biyu na jami'an jihar Nassarawa da ke Keffi ne s**a mutu sak**akon wani turmutsutsu da aka yi a wajen karbar kayan tallafi na gwamnati a dandalin taro na jami'ar da safiyar Juma'a.

Gwamnatin jihar Nassarawa dai ta yi amfani da dandalin taron da ke jami'ar ne wajen raba kayan tallafin wahalar rayuwa ga daliban jami'ar.

Wani dan jarida da ya shaida yadda al'amarin ya faru ya fada wa BBC daliban matan da s**a rasu na daga cikin wadanda s**a je neman tallafin.

Mataimakain gwamnan jihar ta Nassarawa, Emmanuel Akadeh wanda ya je jami'ar domin jajantawa dangane da faruwar al'amarin ya ce faruwar al'amarin na da takaici kuma "za mu kafa kwamitin da zai binciko hakikanin abin da ya faru.

Gwamnati ta umarci dakaru 2,200 su hana haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida baGwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar kula da...
22/03/2024

Gwamnati ta umarci dakaru 2,200 su hana haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba

Gwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar kula da ma’adanai ta tabbatar da ayyukan dakarun tsaro 2,220 a karkashin sabon tsarin tsaro, inda ta kuma umarce su da su yi maganin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma ta buƙaci sabbin dakarun da su dakile sata da duk wasu munanan ayyuka da s**a shafi ma’adinan kasar domin bai wa al’umma damar cin gajiyar amfani da abubuwan da Allah ya h**e musu.

Ministan ma’adinai, Dele Alake, ne ya bayar da wannan umarni a lokacin taron karɓar jami'an da aka horar na musamman da kuma aka zayyana zu daga hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya mai suna “Mining Marshal Corps” a hedikwatar ma’aikatar a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja.

Wannan sabon al’amari ya zo ne watanni biyu bayan da Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin ma’aikatu karkashin jagorancin ministan ma’adinai na kasa don yin shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen cimma wa’adinsa na samar da wani tsari na tabbatar da albarkatun kasa da s**a hada da ma’adanai da dazuka da kuma tattalin arzikin ruwa.

A cewarsa, kafa dakarun a hukumance zai tabbatar da tsaro a wuraren da ake haƙar ma’adanai, da kawar da baragurbi, da tsaftace muhallin da ake haƙar ma’adanan a cikinsa da kuma safarar ma’adanai daga Najeriya.

Ya bayyana hakan a matsayin babban nasara a cikin ajandarsa guda bakwai.

Ministan ya kara da cewa jami’an hako ma’adinai da aka kirkira domin su zama jami’an tsaro a tsakanin hukumomin za su hada da jami’ai na musamman daga sauran hukumomin tsaro k**ar ‘yan sandan Najeriya da sojoji da sauransu.

Da yake jawabi a yayin taron, Alake ya ce, “Rashin tsaro ya durkusar da bangaren tattalin arziƙin ma’adinai tare da hadewa da sauran abubuwan da za su iya haifar da karancin kudaden shiga na ƙasar. Don haka, yaƙi da rashin tsaro a wannan fanni yana da matukar muhimmanci idan za mu sami nasarar cimma wata nasara."

"Muna fata kuma mun yi imanin cewa ma’adinan za su zama hanyar ceton tattalin arzikin Najeriya.”

A nasa jawabin, kwamandan hukumar rundunar farin kaya ta NSCDC, Abubakar Audi, ya bayyana cewa sabbin jami’an hako ma’adanai za su bai wa hukumar hadin kai wajen kare kadarori da ababen more rayuwa na kasa da ma’adanai.

Audi ya bayyana cewa jami’an tsaron za su yi hulda da hukumar kula da ma’adanai a jihohi domin samun bayanan sirri kuma za su kasance a karkashin jagorancin ministan ma’adanai kai tsaye domin gudanar da aiki yadda ya k**ata.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da rabon tallafin Kayan azumi da dan Majalisar Tarayya mai wa...
21/03/2024

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da rabon tallafin Kayan azumi da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Katsina, Hon Sani Aliyu Danlami ya gudanar a ranar Laraba, 20 ga watan Maris 2024.

A lokacin da yake jawabi, Gwamnan ya nuna Jin dadin sa da wannan kokari da Dan Majalisar yayi wajen ganin ya kawo ma al’ummar da yake wakilta sauki a cikin wannan yanayi. An raba akalla sama da buhu dubu biyu na shinkafa ga mabukata, gajiyayyu, kungiyoyi da kuma yayan Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Katsina.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
21/3/2024

Tinubu ya sanya wa jami'an gwamnati takunkumin fita waje na wata ukuShugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sa haramcin tafiye...
21/03/2024

Tinubu ya sanya wa jami'an gwamnati takunkumin fita waje na wata uku

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sa haramcin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje tsawon wata uku ga ministoci da shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Shugaban ma'aikata a fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da umarnin cikin wata takarda da aka aikewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

An bayyana ƙalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi da buƙatar alkinta kuɗin gwamnati da ake kashewa yayin irin waɗan nan tafiye-tafiye a matsayin dalilan da s**a sa aka ƙaƙaba haramcin kan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

Takardar ta ce jami'i na buƙatar amincewar shugaban ƙasa idan yana son a ɗage masa haramcin kuma dole a yi hakan mako biyu kafin lokacin tafiyar.

Matakin na zuwa ne bayan bulaguron baya-bayan nan da ofishin akanta janar na ƙasa ya yi da ta janyo cece-kuce.

Ofishin ya gudanar da wani taron ƙarawa juna sani a birnin Landan wanda ya samu halartar kwamishinonin kuɗi da jami'ai daga ofishin akanta janar.

Ƴan Najeriya dai sun yi ta tsokaci a kai, abin da s**a ce ya zo ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da kuma tashin dala da ke shafar darajar kuɗin naira.

Address

Katsina
KT

Telephone

+2348035562339

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kadarko TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kadarko TV:

Videos

Share

Nearby media companies