Kasata ayau

Kasata ayau Manufar wannan shafi shine bayyana dukkan wani abinda ya shafi kasata najeriya dama sauran kasashen

Zanga-Zanga: Kasar Poland Ta Roki Najeriya Ta Saki Wasu 'Yan Kasarta Bakwai Da ta K**a Suna Daga Tutocin RashaDaga Abbas...
10/08/2024

Zanga-Zanga: Kasar Poland Ta Roki Najeriya Ta Saki Wasu 'Yan Kasarta Bakwai Da ta K**a Suna Daga Tutocin Rasha

Daga Abbas Yakubu Yaura

A ranar Juma’a ne gwamnatin kasar Poland ta roki Najeriya da ta saki wasu ‘yan kasar bakwai da aka k**a a Kano bisa zargin su da daga tutar kasar Rasha yayin zanga-zangar yunwa da aka yi a birnin.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Jakub Wisniewski ya gana da jami’an diflomasiyyar Najeriya a Warsaw inda ya gabatar da shari’ar sakin mutanen da aka k**a – malami da kuma ɗalibai shida.

Masu Zanga-zanga Dauke Da Hotunan Wandanda Aka Kashe A Zanga-zangar Yunwa  Sun Bukaci A Kori Sufeton 'Yan Sandan Najeriy...
10/08/2024

Masu Zanga-zanga Dauke Da Hotunan Wandanda Aka Kashe A Zanga-zangar Yunwa Sun Bukaci A Kori Sufeton 'Yan Sandan Najeriya

A yau Asabar da ake cika kwanaki 10 na zangazangar yunwa, tabarbarewar tattalin arziki da tsaro da shugabanci, wasu masu zangazangar a Legas da ke tattaki a Ikeja babban birnin jihar dauke da hotunan matasan da aka kashe a lokacin zangazangar, sun bukaci a kori sufeto janar na 'yan sandan Najeriya.

Yayin da masu zanga-zangar ke daga kwalaye rubuce da bukatunsu suna kewaye birnin Legas, jami'an 'yan sanda sun yi masu rakiya domin tabbatar da tsaro da oda.

Masu Zangazangar sun kuduri aniyar mamaye birnin Legas cikin tattakinsu hakan ne ya sa mahukunta s**a kara yawan jami'an tsaro da aka jibgesu a sassan birnin na Legas.

Wahala ta yi yawa: Ya k**ata Gwamnatin Tinubu ta amince ta yi kurakurai, ta gaggauta sake nazarin manufofinta da tsare-t...
10/08/2024

Wahala ta yi yawa: Ya k**ata Gwamnatin Tinubu ta amince ta yi kurakurai, ta gaggauta sake nazarin manufofinta da tsare-tsaren ta – Malam Ibrahim Shekarau ya shawarci Tinubu

Me zaku ce?

10/08/2024
Tsadar Rayuwa: Tinubu bai zo Ofis don ya haifar da matsaloli ba - Gwamnatin NajeriyaGwamnatin Tarayya ta dage cewa Shuga...
07/08/2024

Tsadar Rayuwa: Tinubu bai zo Ofis don ya haifar da matsaloli ba - Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta dage cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu bai zo Ofis ba domin ya wahalar da ƴan Najeriya.

Da yake jawabi ga mambobin kungiyar diflomasiyya, Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na ƙasa Mohammed Idris, ya ce Shugaban ya zo Ofis da kyakkyawar manufa tare da zummar warware matsalolin da s**a daɗe suna addabar ƙasar nan.

Ya ce Shugaban ƙasar ya kuduri aniyar gyara da yawa daga cikin manufofin da ba su da kyau waɗanda s**a yi sanadiyyar dakushe al’ummar ƙasar shekaru da dama.

Shugaban ya hau karagar mulki ne a lokaci mafi kalubalen da Najeriya ta fuskanta a tarihinta, inda ƙasar ke kashe kashi 97 cikin 100 na dukkan kudaden shigarta wajen biyan basuss**a, tare kuma da fuskantar yawaitar talauci da rashin aikin yi, da lalacewar ababen more rayuwa da rashin tsaro.

Idan aka fuskanci waɗannan abubuwa masu ban tsoro, Gwamnati ta ɗauki kwararan matakai tare da aiwatar da gyare-gyaren da aka dade ba a yi ba don ceto tattalin arzikin ƙasar daga durkushewa.

Tsawon shekarun da s**a gabata, tsarin ba da tallafin Man Fetur (Subsidy) ya hana Najeriya damar saka kuɗaɗe a muhimman ababen more rayuwa da jin dadin jama'a.

Don haka Shugaban ƙasar ya ɗauki mataki mai raɗaɗi don soke tallafin Man Fetur tare da karkatar da kuɗin zuwa sassa masu mahimmanci k**ar samar da ilimi, da kiwon lafiya, da tsaro wanda ke tasiri kai tsaye ga lafiyar 'yan ƙasa da ci gaban ƙasa," in ji shi.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa

Tafiyar El-Zakzaky tana burgeni, saboda shi kowa nasane, Musulmi da Kirista - Ƴar Jarida"Ita kanta amfani da kalmar kish...
07/08/2024

Tafiyar El-Zakzaky tana burgeni, saboda shi kowa nasane, Musulmi da Kirista - Ƴar Jarida

"Ita kanta amfani da kalmar kishin Arewan kuskure ne, Yiwa kishi iyaka da muhalli ko mutane yana daga cikin abubuwan da s**aiwa tarishin ɗan Adam ta'adi. Yin kishin Arewa, Kudu ko ƙasa duk shirme ne, Falsaface ta turawa wajen amfani da ita a matsayin makamin nesa da juna, Irin wannan kishin ƙasancin ne ya raba Sudan Uku, Ya Gididdiba 'Republic of Congo', Ya haɗa Algeria da Egypt faɗa, Ya datse Nigeria biyu, Duk wani 'Civil War' a Duniya shine dalili, Kenan kishin Arewa ko ƙasanci bashi da wani amfani".

"Ba a kishin Muhalli ko ɓangare, Idan kace kana kishin Arewa Kenan Idan abu ya samu ɗan Kudu babu ruwanka? Ka fahimci yanda tasirin wannan tunanin zai zagwanye maka ganin wanda yake cikin bala'i ba damuwarka bane tunda ba ɗan yankika bane, Wannan abun yana daga manyan abubuwan da s**a jefa duniya cikin masifa. Kalmomi Irinsu, Nationalism, Tribe, Liberalism, Colonialism, Imperialism, Negros, kai wani lokacin har Irinsu Humanity, Aikin turawa ne b***e wasu kungiyoyin Duniya".

"Inda tafiyar Al-zakzaky ke burgeni shi kowa nasa ne Musulmi ɗan Arewa da ɗan Kudu, Kai harma da kirista jiya cikin bincike-bincikena na Gano Wani pastor Almajirinsa, Kuma mabiyi da ma'anar mabiyi ance haddashi ma aka dunga fafutukar sakinsa a shekarun Baya. Malam Cirista ma yabi wane Kai da wani tsaurin ra'ayinka na kin gaskiya kace bazaka bi ba....?"

Wadanda Ke Cin Gajiyar Shigo Da Man Fetur Najeriya Suna Takaici Da Matatar Dangote - ObasanjoDaga: Abbas Yakubu YauraTso...
07/08/2024

Wadanda Ke Cin Gajiyar Shigo Da Man Fetur Najeriya Suna Takaici Da Matatar Dangote - Obasanjo

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce wadanda ke cin gajiyar sana’ar shigo da man Fetur za su yi kokarin dakile matatar man Dangote.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a sak**akon zargin da Shugaban Rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi na cewa wasu ‘Yan Mafiya na kokarin kawo cikas ga Matatar Dala biliyan 20.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar Financial Times.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar matatar man ta Dangote.

Ku tuna cewa a makon da ya gabata ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci kamfanin man fetur na Najeriya Limited da ya sayar da danyen mai ga matatar Dangote da sauran matatun man kasar a Naira.

A halin da ake ciki kuma, yayin da yake magana kan halin da Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote ke ciki, Obasanjo ya ce idan matatar ta yi kyau, ‘yan Najeriya da wadanda bama ‘yan Najeriya ba za su samu kwarin gwiwa su zuba jari a kasar.

Ya lura cewa masu "sayar da kayan da aka tace ga Najeriya" suna jin cewa za su rasa damar da za su samu.

“Sa hannun jarin Aliko a matatar mai, idan ya yi kyau, ya k**ata ‘yan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba su sa hannun jari a Najeriya.

“Idan wadanda ke siyar da kayayyaki da aka tace ga Najeriya suna ganin za su yi hasarar damar da za su samu, kuma za su yi iya kokarinsu don ganin ya bata masa rai,” in ji Obasanjo.

Devakumar Edwin, mataimakin shugaban masana’antun Dangote, ya yi tsokaci kan yadda kamfanonin mai na kasa da kasa ke damun matatar Dangote ta hanyar sayar da danyen mai a farashi mai tsada.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, Farouk Ahmed, ya zargi Dangote da nuna son kai.

Duk da haka, Dangote ya soki zargin na Ahmed.

Shugaba Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe a ƙarƙashin ma'aikatar Jin ƙai da kyautata rayuwar al'umma A ƙoƙarinsa na ganin sh...
07/08/2024

Shugaba Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe a ƙarƙashin ma'aikatar Jin ƙai da kyautata rayuwar al'umma

A ƙoƙarinsa na ganin shirin tallafawa al'umma ya gudana yadda ya k**ata, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabannin ma'aikatar jinƙai, agaji da kyautata rayuwar al'umma ta ƙasa. "Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development".

Mutanen da shugaba Tinubu ya naɗa sun haɗa da:

1. Dakta Badamasi Lawal, a matsayin shugaban shirin samarwa al'umma jari "National Social Investment Programme Agency (NSIPA)". Dakta Lawal yana da digirin digirgir a fannin ilimi, kuma tsohon kwamishinan ilimi ne a Jihar Katsina.

2. Funmilola Olotu, a matsayin shugabar shirin kula da al'umma. Tana da digirin digirgir a fannin kasuwanci, sannan kuma, babbar mataimakiya ce ta musamman ga gwamnan Jihar Legas.

Sauran sun haɗa da:

3. Aishat Alubankuɗi, mai kula da shirin tallafawa masu buƙata ta musamman.

4. Princess Aderemi Adebowale, mai kula da shirin ciyar da ɗalibai.

5. Malam Abdullahi Alhassan Imam, mai kula da shirin ba da tallafin rage raɗaɗi.

6. Misata Ayuba Gufwan, babban sakatare na ma'aikatar kula da sha'anin masu buƙata ta musamman.

7. Lami Binta Adamu Bello, daraktar hukumar yaƙi da safarar ɗan'adam.

Shugaba Tinubu ya buƙaci su gudanar da ayyukansu cikin nagarta da ƙwarewa su tabbatar ƴan Najeriya musamman masu ƙaramin ƙarfi sun amfana.

Rundunar Ƴan Sanda Ta K**a Wani Dan Fashi Tare Da Ƙwato Miliyan 5 A KanoDaga Shamsudeen M Sani Yakaji Rundunar ƴan sanda...
07/08/2024

Rundunar Ƴan Sanda Ta K**a Wani Dan Fashi Tare Da Ƙwato Miliyan 5 A Kano

Daga Shamsudeen M Sani Yakaji

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta ce ta cafke wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a karamar hukumar Kunchi, inda a tare da shi aka kwato sama da Naira miliyan 4 da bindiga kirar AK-47 guda biyu da harsashi guda 47.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, shi ne ya bayyana cewa an k**a Hassan Iliya dan asalin jihar Katsina ne bayan sun kai wani hari a kauyen Yandadi inda s**a yi fashin naira miliyan goma sha biyar.

A cewarsa, an k**a wanda ake zargin ne a lokacin da yake kokarin tserewa akan babur, inda ya kara da cewa an samu buhu a hannunsa dauke da kudi N4,986,000 da kuma bindigar AK-47 guda biyu tare da harsashi guda 47.

“A ranar 05/08/2024 da misalin karfe 02:00 na safe, wani mazaunin ƙauyen Yandadi dake karamar hukumar Kunchi ta jihar Kano ya kawo rahoton cewa wasu ‘yan fashi da makami sun dira gidan sa,inda s**a yi masa fashin naira miliyan goma sha biyar (N15,000,000.00).

“Haka kuma duk a rana ɗaya da misalin karfe 06:00 na safe rundunar ta k**a babban wanda ake zargi mai suna Hassan Iliya mai shekaru 35 a kauyen Alhazawa da ke karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina a lokacin da yake kokarin tserewa a kan babur.

“A wani bincike da aka gudanar an gano wanda ake zargi ɗauke da buhua ciki akwai bindigu kirar AK-47 guda biyu dauke da harsashi guda 47 da kudi, wanda adadin ya kai naira miliyan hudu, da dari tara, da naira dubu tamanin da shida (N4,986,000.00)”, in ji Kiyawa.

A cigaba da jawabi Kakakin ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da yake kira ga jama’a da su guji aikata wani abu da zai iya haddasa tashin hankali, su kuma yi taka tsantsan

KIRANYE: Zamu shirya tsarin kiranye ga wakilai marasa kishin al'umarsu... Wannan ma wata dama ce inji SharfdeenKu lissaf...
07/08/2024

KIRANYE: Zamu shirya tsarin kiranye ga wakilai marasa kishin al'umarsu... Wannan ma wata dama ce inji Sharfdeen

Ku lissafo mana waɗanda ya k**ata a fara yiwa shirin kiranye.....

Tallafin Mai Na Nan Dawowa a Najeriya – ObasanjoYanzu Haka Dai Tsohon shugaban kasar tarayyar Najeriya, Cif Olusegun Oba...
07/08/2024

Tallafin Mai Na Nan Dawowa a Najeriya – Obasanjo

Yanzu Haka Dai Tsohon shugaban kasar tarayyar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta cire a watan Yunin Shekarar 2023 ya dawo saboda hauhawar farashin kayayyakin abinci dana masarufi.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Financial Times.

Tsohon shugaban kasar ya zargi yadda gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafin man fetur.

A cewarsa, k**ata ya yi gwamnati ta sanya matakai kafin cire tallafin na man fetur.

“Akwai ayyuka da yawa da ya k**ata a yi. Ba wai kawai ka tashi da safe ka ce ka cire tallafin man Fetur ba.

“Saboda hauhawar farashin kayayyaki, tallafin da muka cire bai tafi ba. Ya dawo,”inji tsohon shugaban ya jaddada.

Sannan ya ce dole ne a samu amincewar masu zuba jari a Najeriya.

"Dole ne ku fita daga tattalin arzikin ciniki zuwa tattalin arzikin canji", in ji shi.

Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar yunwa a Najeriya

Zanga-zangar wacce aka fara tun ranar Alhamis ta shiga rana ta 5 a ranar Litinin da ta gabata da babbar murya ta mayar da tsarin tallafin man fetur.

Duk da haka, Shugaba Tinubu a cikin jawabinsa na ranar Lahadi ya yin da yake kira ga masu zanga-zangar da su dakatar da zanga-zangar, ya ce matakin da gwamnatinsa ta dauka na cire tallafin man fetur yana da zafi amma ya zama dole saboda ya zama wani rikici a kan tattalin arzikin "jugular na Al'ummarmu ya hana ci gaban tattalin arzikinmu da ci gabanmu."

JARIDAR ALKIBLAH ta bayar da rahoton cewa, ainihin hauhawar farashin kayayyaki ya karu zuwa wani lokaci mai tsawo na kashi 34.19 da kashi 40.87 cikin dari a watan Yunin 2024, a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Hukumar Yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna, ta k**a mutane 39 ciki har da wadanda suke ikirarin kwace motar Yansanda ...
05/08/2024

Hukumar Yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna, ta k**a mutane 39 ciki har da wadanda suke ikirarin kwace motar Yansanda kirar APC da masu barnatar da dukiyoyin mutane da sata da telolin dake dinka tutar kasar Rasha da sauran su.

Ƴan Sanda sun fara cika hannu da masu ɗinka Tutocin kasar Rasha a KanoRundunar ƴan Sandan Najeriya a ranar Litinin ta sa...
05/08/2024

Ƴan Sanda sun fara cika hannu da masu ɗinka Tutocin kasar Rasha a Kano

Rundunar ƴan Sandan Najeriya a ranar Litinin ta sanar da k**a wani Ahmed Taylor da yake buga tutocin kasar Rasha da wasu masu zanga-zanga ke amfani da shi a Kano da wasu Jihohin Arewa.

An kuma ce an k**a masu zanga-zangar kusan mutum 30 da ke ɗauke da tutoci tare da tsare su a Ofishin ƴan Sanda.

Kakakin Rundunar ƴan Sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar hukumar ta farin kaya (DSS) a wani taron manema labarai da ofishin mai baiwa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ONSA ya shirya.

Dimokuradiyya TV ta ruwaito yadda wasu mutane ɗauke da tutocin ƙasar Rasha su ke fitowa a kan titunan manyan biranen Najeriya ciki har da Kano, da Kaduna da dai sauransu yayin da zanga-zangar adawa da Mulkin rashin adalci ta shiga rana ta 5.

An ga masu zanga-zangar ɗauke da tutocin kasar Rasha suna tafiya kan tituna suna rera take daban-daban tare da wasu ɗauke da alluna masu rubutu.

Sai dai da yake magana a wajen taron Adejobi ya ce kafa tutocin wasu kasashe a Najeriya da ke matsayin ƙasa mai cin gashin kanta laifi ne, inda ya ƙara da cewa waɗanda aka k**a da wadanda s**a ɗauki nauyinsu za a gurfanar da su tare da hukunta su daidai da dokar kasar kan laifukan da s**a aikata.

Rike tutocin wata ƙasa a wata ƙasa babban laifi ne, Mun k**a su a safiyar yau mun k**a wani ‘Ahmed Taylor’ daga karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano bisa laifin samar da tutocin kasar Rasha masu yawa da aka baiwa matasan Najeriya don ɗagawa a wajen zañga-zañgã.

A bisa wasu dalilai nashi da bamu sani ba, amma dai mun nuna shi ga al'umma. muna ƙoƙarin nemo masu tallafa musu da ɗaukar nauyin su. K**ar yadda nake magana da ku haka abin ya faru a Jihar Kaduna. Don haka, a yanzu da nake wannan bayanin, mun samu nasarar k**a mutune 30 ɗauke da tutocin Rasha”. Babban jami'in ƴan Sandan ya ce.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa

An ɗauki wannan hoton yau da safe lokacin da Shaikh Hasina Firaministan Bangaladash ta biyo ta bayan gida ta hau jirgi t...
05/08/2024

An ɗauki wannan hoton yau da safe lokacin da Shaikh Hasina Firaministan Bangaladash ta biyo ta bayan gida ta hau jirgi ta tsere Indiya bayan matasa sun kwashe sati 3 suna zanga-zanga.

Kasar Bangaladash tanada mutane Miliyan 166 kaɗan Najeriya ta fisu yawa, ita wannan Matar shekarun ta 15 tana mulki a ƙasar, Matasa da ɗalibai suna cin wahala sun gaji sosai.

Yunwa tayi yunwa, babu aikin yi, ga cin hanci ga raba ayyukanyi tsakanin wasu ƴan kaɗan da watsar da wasu.

Ƙarshe s**a fara zanga-zangar rashin yadda sun sadaukar da mutane a ƙalla 400 aka kashe amma yanzu sunyi nasarar da s**a nema. Yanzu haka shugaban Sojojin ƙasar yana ganawa da Jami'yun ƙasar domin sake fasalin abubuwa.

A gaggauce Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya kirawo taron gaggawa da jagororin hukumomin tsaro, a fadar sa dake babban...
05/08/2024

A gaggauce

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya kirawo taron gaggawa da jagororin hukumomin tsaro, a fadar sa dake babban Birnin tarayya Abuja Villa.

Muna zuwa.

Kasata ayau

DSS Sun Cafke Jagoran Zanga-Zanga A AbujaDaga; Abbas Yakubu YauraJami’an hukumar tsaro ta DSS sun cafke daya daga cikin ...
05/08/2024

DSS Sun Cafke Jagoran Zanga-Zanga A Abuja

Daga; Abbas Yakubu Yaura

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun cafke daya daga cikin jagororin zanga-zangar kuncin rayuwa da ake yi a babban birnin tarayya Abuja, Mai suna Micheal Lenin.

Hukumar DSS ta k**a Lenin da misalin karfe biyu na safiyar ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Apo a babban birnin tarayya Abuja.

Da yake magana da jaridar Punch, Daraktan tafiyar ‘Take It Back Movement’, Damilare Adenola, ya ce jami’an DSS sun kai farmaki gidan Lenin.

Ya kuma yi zargin cewa, DSS ta kuma ci zarafinsa a lokacin da s**a k**a shi.

Ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun hukumar DSS ba, Peter Afunanya, har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

Lenin, wanda shi ne Babban Ko-odinetan na Kasa, na Yakin Kare Hakkokin Matasa, na daya daga cikin wadanda s**a shirya taron da s**a yi magana a taron manema labarai inda s**a nuna rashin jin dadinsu da jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan kasa kan zanga-zangar da ake gudanarwa a fadin kasar a ranar Lahadi.

A jawabin da ya yi, ya ce, jawabin da shugaban kasar ya yi, ya nuna cewa, bai san ma me ke faruwa ba a kasar.

LABARI: Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya daga zuwa London saboda zanga-zangar da ake yi a cen ta soma ƙazanta S...
05/08/2024

LABARI: Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya daga zuwa London saboda zanga-zangar da ake yi a cen ta soma ƙazanta

Sannan ta nemi yan Najeriya dake zaune a Ingila din su ƙauracewa shiga cikin cinkoso

Wajibi ne a bi wa yarinyar nan hakkinta!IDAN YAYAR KA CE KO KANWAR KA AKA YI MATA HAKA YA ZA KA JI?Wato a cikin wannan a...
05/08/2024

Wajibi ne a bi wa yarinyar nan hakkinta!

IDAN YAYAR KA CE KO KANWAR KA AKA YI MATA HAKA YA ZA KA JI?

Wato a cikin wannan al'ummar da muke ciki idan ba kai aka zalunta ba, to ba damuwar ka ba ce.

Wannan yarinyar Husainah tana gaban sana'ar ta ta suyan awara, wani yaro ya zo ya ja ta da cacar baki, har ya kai ga zagin Mahaifiyar ta. Ita kuma da ta ji zafi saibta rama.

Ramarwa ta ke da wuya, shi kuma ya sa kafa ya hantsala mata tafasasshen man awaran nan shi ne ya kona mata fuska da sauran sassan jikin ta.

Wannan mummunan lamari ya faru ne gaban sana'ar ta a layin Tanimu Kaya da ke Hayin Dogo, Samaru, Zariya a ranar Alhamis da ta gabata.

Har yanzu tana gida ba a kai ta asibiti ba saboda babu halin kai ta.

Don Allah al'umma a taimake ta.

Majiyar labarinmu ta ce an damke yaron da ya yi wannan ta'annuti.

Hoton farko Husainah ce kafin a watsa mata tafasasshen man gyada
Hoto na biyu kuma bayan wani yaro ya watsa mata man gyada

Address

Abuja
KASATAAYAU

Telephone

+81615886885

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kasata ayau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kasata ayau:

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Abuja

Show All