Hon Badama Waziri

Hon Badama Waziri I LOVE YOU MUHAMMADU RASULILLAH (S A W)

Muslim
Islamic Research
Journalist Media
Writer✍🏼

Rayuwar sabon shugaban kasar Senegal kenan tare da matar shi a jiya da yau.Akwai darasi mai ɗumbin yawa a cike da waɗann...
03/04/2024

Rayuwar sabon shugaban kasar Senegal kenan tare da matar shi a jiya da yau.

Akwai darasi mai ɗumbin yawa a cike da waɗannan hotuna guda biyu, musamman ga waɗanda suke fifita sashin Talaka akan mai Arziƙi....

Hausawa s**a ce Dare ɗaya Allah kan yi Bature!

YANZU YANZU 💥 Motar siminti ta Dangote tayi haɗari mutane sun daka wawa.
06/02/2024

YANZU YANZU 💥 Motar siminti ta Dangote tayi haɗari mutane sun daka wawa.

17/11/2023

Har yanzu ban fahici waye boko haram ba. Kungiyar salafiyya ce ko kuma gwamnati ne.

Sun shigo har FADA da gajeren wando sun taka carpet da takalmi sun hada kafada da me martaba Wadannan mutane anyi marasa...
16/11/2023

Sun shigo har FADA da gajeren wando sun taka carpet da takalmi sun hada kafada da me martaba

Wadannan mutane anyi marasa daraja

Yanzu- Yanzu: Dan takarar gwamnan jihar Kogi, Dino Melaye ya nemi a mayar da masa da kud'insa sama da N105m daga manyan ...
16/11/2023

Yanzu- Yanzu: Dan takarar gwamnan jihar Kogi, Dino Melaye ya nemi a mayar da masa da kud'insa sama da N105m daga manyan PDP bayan raba N250,000 a kowace rumfar zabe don sayen kuri'a, a.

Sau shida ake sallah kullun a Gàzà, Sallar Asuba, Azahar, La'asar, Magriba, Isha sai Sallar Jana'izaYaa Allah Ka karbi s...
16/11/2023

Sau shida ake sallah kullun a Gàzà, Sallar Asuba, Azahar, La'asar, Magriba, Isha sai Sallar Jana'iza

Yaa Allah Ka karbi shahadarsu, Ka basu ikon cinye wannan jarrabawa

- Datti Assalafiy

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUNWaɗannan wasu daga cikin amfanin gonakin Al'umma ne da barayin daji s**a kona a karamar...
16/11/2023

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN

Waɗannan wasu daga cikin amfanin gonakin Al'umma ne da barayin daji s**a kona a karamar hukumar Kontagora dake jihar Neja.

Allah ka kawo mana ƙarshen wannan bala'i badon halin mu ba.

Hoto:- Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora

GWANIN BIRGEWA: Yadda wasu kananun yara s**a gina Masallaci suke yin Sallah cikin shi, a birnin Dutse, jihar Jigawa.
15/11/2023

GWANIN BIRGEWA: Yadda wasu kananun yara s**a gina Masallaci suke yin Sallah cikin shi, a birnin Dutse, jihar Jigawa.

ALHAMDULILLAHYau Allah Madaukakin Sarki ya saukar da ruwan sama k**ar da bakin kwarya a zirin Gàzà na FaIa$dinu bayan kw...
15/11/2023

ALHAMDULILLAH

Yau Allah Madaukakin Sarki ya saukar da ruwan sama k**ar da bakin kwarya a zirin Gàzà na FaIa$dinu bayan kwanaki 39 da ¥ah0dàwàn l$ràíIa s**a kàt$e ruwan fànfan0 a yankin na zirin Gàzà

AlhamdulilLah bayin Allah sun samu ruwa kyauta daga Allah sun adana ba don l$ràiIa taso hakan ba

Yaa Allah Ka taimaki bayinKa, Ka tabbatar musu da nasara akan taron dangin kàf0ràí

Daga Datti Assalafiy

MAHAIFI..........Kalma ɗaya bazata iya fassara shiba, rubutu bazai taɓa nuna matsayinsa ba, kwatance bazai Nuna ainahin ...
15/11/2023

MAHAIFI..........

Kalma ɗaya bazata iya fassara shiba, rubutu bazai taɓa nuna matsayinsa ba, kwatance bazai Nuna ainahin suffar saba.

Zamu iya cewa Jarumi ne, sadauki, Jajirtacce, Mai tausayi, kuma Sarkin sadaukar wa, Wanda yake sadaukar da farin cikinsa domin na iyalinsa, Yakuma damu da damuwarsu fiyeda tasa, mai tunanin nasarar iyalinsa Alokacin da suke bacci, mai yimusu addu'a Alokacin dasuke yawo, mai kawo musu abinci Alokacin da s**a tashi, mai yabonsu abayan idanunsu, mai ɓoye laifinsu a idanun duniya, mai roƙar musu yafiya, addu'a ta kyakkyawar rayuwa, wannan kaɗan daga cikin aikin mahaifi kenan.

Babu jarumi k**ar mahaifi, yafi kowa iya tare duka, yafi kowa boye damuwa, yana cikin matsala Hamsin (50) zaka zo masa da taka guda ɗaya yayi maka maganinta, fuskarsa cikeda murmushi, batare daka gane tasa damuwar ba.

Allah kasa Mugama da Iyayenmu Lafiya, wanda nasu suke raye Allah yabasu damar kyautata musu, wanda nasu s**a rasu Allah yaji qansu.

Abubakar Shehu Dokoki✍️

15/11/2023
13/11/2023

YADDA AKA SALLAMI YARINYAR NAN YAR 13 DAGA ASSIBITI BAYAN AN YANKE MATA HANNU SABODA TALAUCIN DA IYAYENTA SU KE FAMA DA SHI HANA SU KAITA ASSIBITI....

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.Wani Ɗan Arewa Ya Rasu A Yankin Kudu, Amma Kafin Rasuwarsá Ya Ce Shi Ɗan Jihar Borno...
12/11/2023

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.

Wani Ɗan Arewa Ya Rasu A Yankin Kudu, Amma Kafin Rasuwarsá Ya Ce Shi Ɗan Jihar Borno Ne

Jama'a ku taya mu binciken ƴan uwan wannan bawan Allah. Allah ya yi masa rasuwa a jihar Inugu ranar Juma'a, amma kafin ya rasu ya shaida mana cewa shi ɗan Maiduguri ne daga ƙaramar hukumar Shani a gundumar Bargu.

A taimaka a tayamu yaɗawa ko za'a dace.

Allah ya jikansa Allah kuma ya sa a sami 'yan uwansa.

YANZU YANZU: Wata gobara ta k**a shahararriyar Kasuwar Gamboru da ke Maidugiri a safiyar Lahadi. Har yanzu dai ba a san ...
12/11/2023

YANZU YANZU: Wata gobara ta k**a shahararriyar Kasuwar Gamboru da ke Maidugiri a safiyar Lahadi. Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba, sai dai an ga ’yan banga da s**a hada da CJTF da mazauna wurin suna kokarin kashe wutar.

Gobarar dai na zuwa ne kasa da watanni 9 bayan da gobarar ta tashi a babbar kasuwar Monday Market a Maiduguri, inda ta lalata shaguna da kayayyaki na biliyoyin naira....

Allah sarki Sunanta Fatima shu'aibu Yar Garin kofa ce a ƙaramar Hukumar Bebeji dake nan jihar Kano.🥲Ciwo ne ya sameta fu...
12/11/2023

Allah sarki Sunanta Fatima shu'aibu Yar Garin kofa ce a ƙaramar Hukumar Bebeji dake nan jihar Kano.🥲

Ciwo ne ya sameta fuskarta take nema ta ruɓe cikin ikon Allah da s**aje Asibiti aka samu aka yanke iya inda ya ruɓe ɗin shine aka sanya mata itace saboda kada wajen ya haɗe da haƙoranta.

Yanzu aiki akeso ayi mata domin a yanko wata fatar a dasa mata saboda kada wajen ya cigaba da ruɓewa gashi sha'anin yau da kullum ya kayar da iyayanta da sun gaza basu da damar ɗaukar nauyin ta dole tasa aka Buƙaci na ɗora a page ɗina domin jan hankalin masu ƙarfi su taimaka su ceto rayuwar ta k**ar yadda aka saba.

Ubangiji Allah yabada ikon taimaka Mata yabata lafiya.🤲

Daga M Abba Gidan Shanu. Dan Allah ku follow Page nan Hon Badama Wazirii

Gwanayen aiki....Samu ire iren su zayi matukar wahala a arewacin Nageriya, gwamnan jihar Nasarawa da gwamnan jihar Maidu...
12/11/2023

Gwanayen aiki....

Samu ire iren su zayi matukar wahala a arewacin Nageriya, gwamnan jihar Nasarawa da gwamnan jihar Maiduguri.

GOVERNOR SULE vs OMBUGADU: COURT OF APPEAL FIXES WEDNESDAY 15th FOR HEARING The Court of Appeal has fixed Wednesday, 15t...
12/11/2023

GOVERNOR SULE vs OMBUGADU: COURT OF APPEAL FIXES WEDNESDAY 15th FOR HEARING

The Court of Appeal has fixed Wednesday, 15th November for the hearing in the appeal instituted by Governor Abdullahi Sule of Nasarawa State, who is seeking to upturn the split decision of the Governorship Election Petition Tribunal in favour of the candidate of the Peoples Democratic Party (PDP), David Ombugadu.

This was contained in the notice of hearing issued to the parties in the case by Nasiru Alhassan, Electronic Desk Officer of the court on Saturday.

According to the notice, hearing in the case will commence by 9 am at the Court of Appeal, Abuja Division.

Gov. Abdullahi A. Sule Mandate

12/11/2023

COURT OF APPEAL tasa ranar saurare kara Governor ranar 15 ga wata ranar laraba.

Still we are waiting. All the best Engr. A Sule

Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Jihar Kano ta ce mutum dari da arba'in ne ke jiran a zartar musu da hukunci...
12/11/2023

Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Jihar Kano ta ce mutum dari da arba'in ne ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa bayan kotuna sun same su da laifuka.

11/11/2023

Kaji wani hauka koh

Sheikh Daurawa ya ce zargin da wasu ke musu cewar suna k**a masu gudanar da sana'o'i ba wai sun hana kasuwanci bane, sun...
07/11/2023

Sheikh Daurawa ya ce zargin da wasu ke musu cewar suna k**a masu gudanar da sana'o'i ba wai sun hana kasuwanci bane, suna kokarin tsaftace wurin kasuwancin ne.

Sheikh Aminu Daurawa ya ƙara da cewa kura-kuran da jami'ansu na Hizbah sukeyi yayin k**a mutane da ma ɗalibai suna yiwa jami'ansu faɗa domin su gyara wannan kuskure.

Ya ci gaba da cewa ba so suke a aikata laifi ba, kuma suna ƙara sauya salon tunkarar waɗanda suke zargi da aikata laifuka, inda suke kiransu domin yi musu nasiha.

Yanzu haka an wayi gari da rushe gadar da mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa Sanata Barau Jibrin yake yi a ga...
07/11/2023

Yanzu haka an wayi gari da rushe gadar da mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa Sanata Barau Jibrin yake yi a garin Kwakwaci dake k**ar hukumar Gwarzo, garin mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam.

A kwanakin baya dai ansamu hatsaniya kan aikin wannan gadar da ake zargin mataimakin Gwamnan da yunkurin hanawa wanda har takai ga Al'umma sun fito sun nuna rashin amincewarsu kan wannan yunkuri.

Abun tambaya shine me yakawo rushe wannan gada??? Kuma me hakan yake nufi???

Amurka ta nuna rashin jin daɗinta game da furucin wani minista a is'''raa''ila da ya ce a jefawa Falastine makamin Nukil...
07/11/2023

Amurka ta nuna rashin jin daɗinta game da furucin wani minista a is'''raa''ila da ya ce a jefawa Falastine makamin Nukiliya.

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin Kayan Abinci na ci gaba da karyewa a wasu Kasuwannin jihar Katsina, k**ar yadda Katsina Post ta r...
07/11/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin Kayan Abinci na ci gaba da karyewa a wasu Kasuwannin jihar Katsina, k**ar yadda Katsina Post ta ruwaito. Shin ya abin yake a yankinku?

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 20 A Wani Yankin Kamaru Mai Iyaka Da Najeriya.Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan wasu muta...
07/11/2023

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 20 A Wani Yankin Kamaru Mai Iyaka Da Najeriya.

Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan wasu mutane a lokacin da suke barci a wani gari da ke yammacin kasar Kamaru k**ar yadda wani jami'in karamar hukumar ya sanar a safiyar ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum akalla 20.

Garin na Mamfe da ke yankin Kudu maso Yamma na Kamaru bai wuce kilomita 50 daga kan iyaka da Najeriya ba.

Jami’in hukumar Viang Mekala ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa mutane bakwai na kwance a asibiti kuma
jami’an tsaro na gudanar da bincike a yankin.

"An shawo kan lamarin kuma bai k**ata jama'a su firgita ba," in ji shi.

Gwamnatin tarayya ta yi asarar makudan kudin da ya k**ata a ce an samu daga saida danyen mai a kasuwannin DuniyaA sak**a...
07/11/2023

Gwamnatin tarayya ta yi asarar makudan kudin da ya k**ata a ce an samu daga saida danyen mai a kasuwannin Duniya

A sak**akon masu fasa bututunmai da su ka addabi Najeriya, an sace danyen man fiye da Naira Tiriliyan 4.3 a shekaru biyar

Daga shekarar 2017 zuwa 2021, barayi sun fasa bututu sun sace ganguna fiye da miliyan 200 na arzikin danyen man Najeriya.

Wasu da s**ace Sai sun halakani Sunyi kokarin Kasheni jiya da yammaci Amma Allah  ya Tsirataddani.. Daga Zulkiflu Maqabu...
07/11/2023

Wasu da s**ace Sai sun halakani Sunyi kokarin Kasheni jiya da yammaci Amma Allah ya Tsirataddani..

Daga Zulkiflu Maqabuliyaa

Abin mamaki bayan na sanar da jamian Tsaro sun Umurceni da Natafi Hospital Sun kuma bini a Hospital don su Cika aikinsu Amma Allah yakwace ni..

Ina magana ne Akan Family Na Ibrahim Baba anga... Don Sunce zasu kasheni

Ina Neman dauki ga Allah da Jami'an Tsaro dama Al-umma Baki daya.. Pls

Allah ya kiyaye na gaba

Da ƴan Hizba sun rungumi Mace su sakacikin Hilux, da a bar su suna fasikanciwane yafi girma? Don haka ƴan Hizba karku da...
07/11/2023

Da ƴan Hizba sun rungumi Mace su saka
cikin Hilux, da a bar su suna fasikanci
wane yafi girma? Don haka ƴan Hizba kar
ku damu da surutan mutanen banza, ku ci
gaba da rungumarsu kuna saka wa cikin
Hilux - Cewar Sheikh Bello Yabo Sokoto

ABIN AL'AJABIN DA YA FARU DA WANI BATIJJANE A GADON ASIBITTI.Daga Sayyadi Dr. Rilwan Holma.Yace: Wani bawan Allah ne aka...
06/11/2023

ABIN AL'AJABIN DA YA FARU DA WANI BATIJJANE A GADON ASIBITTI.

Daga Sayyadi Dr. Rilwan Holma.

Yace: Wani bawan Allah ne aka kawo karfe 12 na dare jiya bayi da lafiya sai yake ta ihu kar ku kashe ni bana son in mutu ran lahadi Annabi Muhammad S. A. W ba ran lahdi yayi wafati ba ban son in mutu ran ladi.

Can sai ya fara ce yauwa ga Annabi S. A. W ya RASULALLAHI ka gaya musu kar su kashe ni ban son mutuwa ran lahdi, sai aka masa alluran bacci. Likitan, da nurses din da sauran Ma'aik kap lokacin ma musulmai bane.

Da safe sai naje nine da aikin safe, sai na shiga office na zauna sai aka gudu aka kira ni cewa patient din ya farka ya fara maganganu kuma, to ni ban ma san me ya faru da dare ba sai naje kan shi da gudu ni da nurses din,

Sai naji yana ce yauwa na gode da ban mutu ran lahdi ba, na gode, sai na tsaya ina ganin abun mamaki

Sai yace ga Annabi yazo na gode maka da ka hana su kashe ni ran lahdi ya RASULALLAHI na gode. Yana nuna saman ceiling haka yana ga Annabi yazo na gode maka ya RASULALLAHI da hana su kashe ni ran lahdi yanzu kam zan mutu na gode ya RASULALLAHI.

Suna jira inyi rubutu me za ayi wa patient din ina ta ganin abun mamaki. Nayi gudu na dauko waya na a office inje inyi video din sa ina dawowa na samu ya rasu. Ya rasu yana na gode ya RASULALLAHI na gode ya RASULALLAHI.

Da carbin darikar sa kewaye da hannunsa ya cika.

Shine s**a bani labarin abunda ya faru da dare din. Nayi hira da nurse da take nan abun ya faru akwai audio na hiran muna dashi saboda yan kanzagi

Kuma daga relative na mamaci din zamu samo daya mu tattauna kwaji karin bayani game da dabiun sa da halayen sa na kirki insha Allahu

Allah masa rahama ya sadashi da Shugaba da shehu da shehu.

Allah ka barmu a darikar shehu Tijjani.

Mai neman karin bayani zamu iya tura shi har Asibitin yaje ua sameta insha Allahu

ALLAH KA KARBE MU MUNA CIKAKKUN MASOYA MANZON ALLAH (S.A.W) YAN DARIKA NA GASKIYA.

Address

Lafia
Lafia Beriberi
0011

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hon Badama Waziri posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hon Badama Waziri:

Videos

Share

Nearby media companies