![Yadda ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas ka iya raunata ƙungiyarFicewar ƙasashen Mali da Nijar da Burkina...](https://img4.medioq.com/835/217/578492288352171.jpg)
29/01/2025
Yadda ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas ka iya raunata ƙungiyar
Ficewar ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga ƙungiyar Ecowas a ranar Laraban nan bayan kwashen fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakanin ƙungiyar da ƙasashen guda uku, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga cigaba da kasancewar ƙungiyar ta Ecowas.
A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne ƙasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta s**a sanar da ƙungiyar Ecowas a hukumance dangane da buƙatar ficewar tasu.
To sai dai bisa dokokin Ecowas, ƙasashen na buƙatar sanar da ƙungiyar shekara guda kafin amincewa da ficewar.
Kuma a ranar Larabar nan ne wa'adin ke cika, bayan dukkan ƙasashen uku sun yi watsi da kiran ƙungiyar ta Ecowas na su ƙara tsawaita zamansu mambobinta na watanni shida domin samo mafita.
Yanzu dai ƙasashen na Burkina Faso da Mali da Nijar sun zama ƙawaye inda s**a cure wuri guda ƙarƙashin ƙungiyar da suke kira Haɗakar Ƙasashen Sahel (Allaiance of Sahel States (AES).
Shugabannin mulkin sojin ƙasashen dai sun zargi Ecowas da ƙaƙaba musu takunkumi na "rashin imani kuma haramtattu" bayan juyin mulkin da ya kawo su kan karaga.
Sun kuma yi amannar cewa ƙungiyar ta Afirka ta Yamma ba ta ba su cikakkiyar gudunmawa ba wajen yaƙar ƴan'adda. Sun kuma yi amannar cewa Ecowas ɗin ƴar kanzagin tsohuwar uwar gijiyarsu ce wato Faransa.
Faransa ta kasance abokiyar hamayyar wannan ƙasashen da sojoji ke jagoranci da a yanzu haka s**a ƙwammace yin hulɗa da ƙasashe irin su Rasha da Turkiyya da Iran.