12/03/2024
Gwamna Malam Dikko Radda ya kaddamar da bude ofishin din-dindin na Gidauniyar Gwagware (Gwagware Foundation) tare da Kaddamar da bada tallafin abinci da dinkin sallah na marayu
A ranar Litinin, 11 ga watan Maris 2024, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya Kaddamar da bada tallafin kamar yadda aka saba duk shekara tare da bude ofishin gidauniyar na din-dindin dake akan hanyar zuwa Daura kusa da rukunin gidaje na makera.
Kayyakin da aka bayar sun hada da tirela 1 ta shinkafa da tirela 1 ta Gero tare da Masara, sai Kayyakin Sallah na yara marayu guda 4,000 da kayyakin makarantar na yara marayu su 3,000.
Da yake gabatar da jawabin shi Malam Dikko Radda ya yi godiya ga Allah wanda da ikon sa ne yasa shi ganin wannan rana domin sake gudanar da irin wannan tallafi mai mahimmanci.
Gwamnan ya bu'kaci masu hannu da shuni dasu taimakama wanda basu da shi watau mabukata da abinda Allah ya h**e masu wanda haka zai taimaka wajen kara rage rad'ad'in hali da al'umma suke ciki.
Daga karshe Malam Dikko Radda ya bu'kaci al'umma dasu yawaita addu'a a lokacin bud'e Baki domin neman afuwar Allah tare da neman gafara.
Har Ila yau, An karrama muhimman mutane da su ka assasa Gidauniyar tare da bada gudunmuwa domin habbaka ita gidauniyar.
Wadanda s**a tofa albarkacin bakin su sun hada da Shugaban Gidauniyar, Alh. Yusuf Ali Musawa, Minista ta al’adu da tattalin arziki na fasaha, Haj Hannatu Musa Musawa, Alh. Bilya Sanda, Mal Abu Ammar, Shugaban Hisba ta Jihar Kano, Mal Daurawa da sauran su.
Notifying.ng Hausa
12/3/2024