06/03/2024
HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI (5)
Daidai da Fatawowin Ayatullah Sayyid Khamene’i (H)
ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI
Mas’ala ta 667:
“Abubuwan da suke karya Azumi guda goma (10) ne;
1&2- Ci da Sha, ta hanyar da aka saba ko ta wata hanyar daban.
3- Yin Jima’i da Halal ko da Haram, an yi ‘inzali’ ko ba a yi ba.
4- Fitar da Maniyi ta hanyar ‘Istimna’i’, ko kuma ta kowace hanya ta daban.
5- Yin karya ga Allah da ManzonSa da A’imma Ma’asumai (AS) a bisa Ihtiyadi na Wajibi.
6- Hadiye qura mai kauri, ko shan taba a bisa Ihtiyadi na Wajibi.
7- Nitsar da dukkan Kai a cikin ruwa a bisa Ihtiyadi na Wajibi.
8- Yin Allurar ruwa ko da kuwa saboda rashin lafiya ne, amma babu laifi da busasshe (kamar wanda ake turawa a dubura ko a gaba)
9- Yin Amai da gangan, ko da saboda lalura ne, amma yin Amai ba bisa rafkanuwa, ko kuma ba tare da zabin mutum ba, baya bata Azumi.
10- Ganganta zama cikin Janaba ko Haila ko Nifasi har Alfijir ya keto.”
MAS’ALOLI DANGANE DA ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI
Mas’ala ta 668:
“Abubuwan da suke bata azumi, wadanda aka lissafo su a Mas’alar ta da gabata, suna bata azumi ne kawai idan aka yi su da gangan, amma idan bisa mantuwa ne, ko bisa rafkanuwa, to ba su bata azumi, in banda Janaba. Da mutum zai Ci wani abu, ko ya Sha wani abu saboda ya manta cewa yana Azumi, to Azuminsa bai baci ba, duk daya ne kuma, azumin ya kasance na Wajibi ne ko kuma na Mustahabi.”
Wato in dai bisa mantuwa mutum ya aikata daya daga abubuwa goma din can da aka ambata, to azuminsa bai karye ba. In banda Jima’i, shi ko bisa mantuwa ko rafkanuwa aka yi shi yana iya bata azumi, kamar yadda bayanin hakan zai zo a rarrabe a nan gaba. Amma don mutum ya ci abinci ya koshi da rana, bisa mantuwar cewa yana azumi, to azuminsa bai baci ba, zai cigaba da abinsa, kuma ba sai ya sake azumin ba. Sai dai wajibi ne ya tofar da abin da ke bakinsa da zaran ya tuna a sadda yake kan ci.
Mas’ala ta 669:
“Idan mai Azumi ya aikata daya daga abubuwan da suke karya azumi bisa rafkanuwa, sannan ya sake aikata (abin da ke karya azumin) a karo na biyu (da gangan) bisa tunanin cewa ai dama Azuminsa ya riga ya baci tun farko, to (yanzu) Azuminsa ya baci.”
Ma’ana, na farko ya yi da mantuwa, bai san cewa hakan bai bata azuminsa ba, sai ya dauka cewa ai azuminsa ya riga ya baci tunda ya ci abu bisa mantuwa, don haka sai ya kara cin wani abu kawai a zimmar tunda azuminsa ya riga ya baci, to yanzu cigaba da aikata abin a karo na gaba ne ya bata azuminsa ba wai yin aikin a karo na farko bisa mantuwa ba.
Mas’ala ta 670:
“Idan mai Azumi ya fara kokonto (shakka) a kan shin ya aikata wani abu da ke bata azumi, ko bai aikata ba? Kamar da zai yi shakka akan shin ya hadiye wani abu daga ruwan da ya saka a bakinsa, ko bai hadiye ba? To a nan Azuminsa na nan Ingantacce (tunda shakka yake yi, bashi da tabbaci).”
Mas’ala ta 671:
“Bai halatta a sha ruwa (ko a aikata wani abu daga abubuwan da suke karya azumi ba) kafin a samu tabbacin shigowar dare, da mutum zai sha ruwa a wannan halin, to ramako da Kaffara sun wajjaba a kansa, ko da bai samu yakinin wanzuwar rana ba.”
Wato in har mutum bai da yakinin cewa rana ta fada, dare ya fara, to bai halatta ya sha ruwa ba. In har ba tare da samun tabbaci ba ya sha ruwa a yayin da yake shakku (kokono) kan dare ya shiga ko har yanzu da sauran rana, to wajibi ne a kansa ya rama azumin ranar, ya kuma yi Kaffara. Wajibi ne mutum ya sha ruwa ne a lokacin da yake da yakinin faduwar rana da farawan dare.
Mas’ala ta 672:
“Idan Mukallafi yana shakka a kan ketowar Alfijir (wato yana kokonto akan Alfijir ya fito, ko bai fito ba), to ba wajibi ba ne a kansa ya bincika don ya tabbatar kafin ya ci ko ya yi abin da ke karya azumi ba, sai dai kuma idan ya Ci din ba tare da binciken ba, sai daga baya ta bayyana masa ashe lokacin (da ya cin) Alfijir ya riga ya keto, to ya zama wajibi a kansa ya kame bakinsa a tsawon wannan yinin, sannan kuma ya rama Azumin daga baya, amma babu Kaffara a kansa.”
Saboda dama yana kokonto ne, tunda kokonto ne, to ba wajibi ne sai ya tashi ya bincika ba, amma idan ya bincika din ya fi masa, saboda zai samu tabbaci sai ya yi aiki da tabbacin. Saboda haka idan da zai zama yana da tabbacin Alfijir ya keto sai ya aikata abin da ke bata azumi, to wannan wajibi ne ya kame bakinsa a take, sannan ya rama azumin ranar, ya kuma yi kaffara. Amma idan yana shakka ne, wanda Malaman Fiqihu sun ce, shakka shi ne rabin tunanin mutum eh ne, rabi kuma a’a ne. To sai bai bincika ba, sai ya ci abinci, in daga baya ya gano lokacin Alfijir bai riga ya keto ba, shikenan azuminsa ya inganta, idan kuwa daga baya ya gane cewa ashe lokacin Alfijir ya fito, to ba shi da azumin ranar, sai ya rama shi amma ba tare da Kaffara ba, kuma wajibi ne ya kame daga aikata duk wani abu da ke bata azumi a tsawon wannan yinin.
Mas’ala ta 673:
“Idan (Mukallafi) ya zama yana shakka a kan Alfijir ya fito ko bai fito ba, sai ya bincika, sai ya tabbatar da cewa bai riga ya fito ba, sai ya ci abinci, sai kuma daga baya sabanin haka ya bayyana masa (wato ya bayyana masa ashe Alfijir din ya keto a lokacin), to Azuminsa ya inganta. Amma wannan a Azumin watan Ramadan ne kawai, amma a sauran Azumomin da ba na watan Ramadan ba, to azumi ya baci idan aka ci (ko aka aikata wani abu da ke bata azumi) a kowane hali.”
Wato in dai a cikin watan Ramadan, mutum ya fara shakka a kan Alfijir ya keto ko bai keto ba, sai ya bincika, sai ya tabbatar bai keto ba, sai ya ci abincinsa, sai daga baya kuma ta bayyana masa ashe a lokacin da ya bincika din nan ya keto fa, binciken ne bai bashi daidai ba. To tunda dai ya bincika shikenan, azuminsa na ranar ya inganta, ba sai ya rama ba. Sabanin da ace bai bincika ba, wanda aka yi bayanin hukuncinsa a sama.
To amma idan ba a azumin watan Ramadan ba ne, to ko a wane hali in ta tabbata wa mutum cewa ya ci abinci bayan ketowar Alfijir, ko ya bincika, ko bai bincika ba, ko ya samu yakini ko bai samu ba, to wannan azumin nashi babu shi, ya baci, ya sha ruwansa kawai.
Mas’ala ta 674:
“Ya halatta ga mata su yi amfani da magungunan da za su hana su, ko su jinkirta musu zuwan Al’adarsu (menstrual cycle) a cikin watan Ramadan, domin su Azumci watan bakidayansa ba tare da yankewa ba, matukar hakan bai lizimta musu cutarwa abin dogaro.”
Wato, in har an aminta da cewa, shan wani magani, ko amfani da shi don ya jinkirta zuwan jinin Al’ada, ko ma don ya hana shi zuwa gabadaya, ba zai cutar da mace irin cutarwar da za a lissafa shi a matsayin cutuwa mai illa ba, to babu matsala a shari’a ta yi amfani da wannan maganin, don ya dakatar mata da zuwan jini a watan Ramadan don ta yi azuminta lafiya ba tare da ta sha ko daya ba, in tana bukatar hakan. Amma in aka san cewa zai haifar da wani lalura ko illa abin dogaro, to bai halatta ba, saboda duk wani abu da zai jawowa mutum cutuwa a kan kansa, shari’a na kokarin kiyaye shi daga fadawa cikinsa.
Mas’ala ta 675:
“Idan mai azumi ya nitsar da dukkan Kansa a cikin ruwa da gangan, to bisa Ihtiyadi na Wajibi Azuminsa ya baci, ya zama wajibi a kansa ya rama Azumin wannan ranar. Idan kuma ya yi shakka a kan shin dukkan Kaina ya nitse a cikin ruwan ko bai nitse ba? To a nan (tunda kokonto yake yi, bai da tabbaci), Azuminsa ya inganta.”
Mas’ala ta 676:
“Idan mai azumi ya fada cikin ruwa ba tare da zabinsa ba (kamar idan wani ya tura shi a ciki, ko ya zame ya fada), sai kansa ya nitse a cikin ruwan, to azuminsa bai baci ba, sai dai kuma ya zama wajibi a gare shi ya gaggauta fitar da Kan. Irin wannan hukuncin ne ma yake a cikin cewa, da ace mutum zai manta yana Azumi, sai ya nitse a cikin ruwan (wato shima Azuminsa bai baci ba, tunda bisa mantuwa ne).”
Mas’ala ta 677:
“Ya zama wajibi a kan mai Azumi, a bisa Ihtiyadi na Wajibi, ya bar zukan Taba da dukkan nau’o’insa mabambanta, haka nan ma (ya bar) amfani da amfani da magunguna (Narcotics) wadanda ake amfani da su ta hanyar saka su a hanci ko wadanda ake saka su a karkashin harshe.”
Mas’ala ta 678:
“Idan mutum (mai azumi) ya yi gyatsa, sai abincin (da ke cikinsa) ya komo bakinsa, to bai halatta ya hadiye shi ba. Haka nan ma bai halatta (mai azumi) ya hadiye raguwan abincin da ke cikin bakinsa ba (kamar wanda ke jikin hakora), idan da zai hadiye shi ba tare da nufi ba, ba kuma tare da zabinsa ba, to Azuminsa bai baci ba, amma idan ya hadiye shi da gangan Azuminsa ya baci.”
Mas’ala ta 679:
“Idan mutum yana cikin cin abinci ya gano cewa Alfijir ya keto, ya zama masa wajibi ya fitar da ragowan abincin da ke cikin bakinsa, idan ya cigaba da ci, to Azuminsa ya baci.”
Wato in ya tofar da gaggawa, shikenan, sai ya kuskure baki ya cigaba da Azuminsa, kuma ya inganta. Amma idan yace tunda yana bakina, bari na karisa shi, to ya karya Azuminsa, kuma tunda da gangan ne ma ya yi hakan, to baya ga kame baki da zai yi na yinin, da ramako, sai ya kuma yi Kaffaran karya Azumin Ramadan da gangan.
* Akwai sauran Mas'aloli da suke bayani dangane da hukunce-hukuncen sauran abubuwan da ke karya azumi, wanda za mu cigaba a kansu insha Allah.
— Saifullahi M Kabir
25 Sha'aban 1445 (6/3/2024)
Whatsapp: 08062911212