Wahda News

Wahda News Mun buɗe wannan group ɗin ne domin amfanar da junanmu dangane da Abubuwan Harka na yau da kullin.

Dag Ƙasar Makka.Daga cikin manyan abubuwan da s**a ɗauki hankalin al'umma a duniya a wurin Hawan Arfah yau a Ƙasar Makka...
15/06/2024

Dag Ƙasar Makka.

Daga cikin manyan abubuwan da s**a ɗauki hankalin al'umma a duniya a wurin Hawan Arfah yau a Ƙasar Makka shi ne, yadda al'umma ƙasar Iran suna Ɗaga Tutar Falastinawa, da kuma hotuna masu ɗauke da rubutun tsinuwa da la'ana ga Amerika da Israal.

Mahajjatan ƙasar Iran su sama da dubu 80 sun riƙa fadin mutuwa ga Amerika, mutuwa ga Izraal a cikin sauti mai karfin gaske a wurin hawan Arfah.

Ga wasu daga cikin hotunansu nan a ƙasa.

Abinda Alhazan Iran su s**ayi su aƙalla dubu 80 a filin Arfah yau a Saudiya abin a yaba ne, sunyi ta ɗaga murya a filin ...
15/06/2024

Abinda Alhazan Iran su s**ayi su aƙalla dubu 80 a filin Arfah yau a Saudiya abin a yaba ne, sunyi ta ɗaga murya a filin Arfa suna faɗin 'Mutuw@ ga Amurka, Mutuw@ ga Izra'ila. Suna faɗin “daga Gwagwarmayar har Nasara” suna faɗin Ƴancin Falsɗin, ƴancin Falasɗin.

Suna ɗaga hotunan zaluncin da akayi tare da Tutan Falasɗin, gaban TV a duniya baki ɗaya. Harma wasu musulmai daga wasu ƙasashen duniya s**ayi koyi da su yayin da aka haska kaitsaye ga duniya.

Imams week: HARISAWAN AZZAHRA ZONE, KATSINA UNIT SUN SHIRYA TARON TUNAWA DA IMAM KHOMAINI (QS). A yau Lahadi 9/June/2024...
09/06/2024

Imams week: HARISAWAN AZZAHRA ZONE, KATSINA UNIT SUN SHIRYA TARON TUNAWA DA IMAM KHOMAINI (QS).

A yau Lahadi 9/June/2024, harisawan azzahra zone, katsina unit karkashin jagorancin Shaikh Zakzaky (H) sun shirya taron tunawa da Imam Khumaini (Qs) kamar yadda s**a saba duk shekara.

Kamar ko wacce shekara a wannan shekarar ma an shirya program din a Markaz dake cikin garin katsina.

Da farko an gabatar da addu'a, karatun al'Qur'an, sai wake, daga nan kuma sai makasu din shi wannan program din.

Bayan nan kuma Malam Yaqoub Idris katsina ya gabatar da jawabi akan Wanene Imam Khumaini da irin gwagwarmayar da yayi a lokaci guda kuma da irin kalu-balen da ya fuskanta a wajen Yahudawa.

Lallai ya kawo irin hanyoyin da Imam ya rika amfani dasu wajen gina mutane su zama 'yan gwagwarmaya musamman matasa da yanda sauyi ya fara shiga a kwakwalen mutane har ta kai ga nasara ta samu.

Sannan ya cigaba da bayani akan irin gwagwarmayar Imam Khumaini da ta Maulana Shaikh Zakzaky (H) iri daya ce, sai dai canjin yanayi da kuma al'umma. Irin nasanar da Imam ya samu a kasar Iran irin ta Malam Zakzaky (H) zai samu a nahiyar Africa da yardar Allah.

Sannan ya karfafa yan'uwa musamman Haris ya tsayu kham akan turbar da su Malam (H) s**a doru akai, sannan ya kara neman kusanci da Allah domin shine babban makamin yin nasara a ko wacce tafiya. Kuma a shirya fuskantar kalu-bale, domin duk mai addini sai ya fuskanci jarabawa a nemi taimakon Allah.

Daga karshe anyi addu'a Allah ya inganta lafiyar su Malam (H) da mai dakinsa, ya cikasa masu abinda suke son gani na tabbatar addini a wannan nahiya tamu.


Gayyata zuwa ga dukkan yan uwa almajiran Allama syd zakzaky H, Maza da mata. Zuwa gagarumin taro dan tunawa da waki,ar f...
28/05/2024

Gayyata zuwa ga dukkan yan uwa almajiran Allama syd zakzaky H, Maza da mata.
Zuwa gagarumin taro dan tunawa da waki,ar fitina tawayiyya shekaru 30 da faruwarta.

Rana: Lahadi me zuwa 2/6/2024.

Guri : sabuwar markaz ta da,irar yan uwa na katsina.

Lokaci : 10:00am safe.

Babban bako mai jawabi na musamman: Malam Ibrahim Aqil.

A iso lafiya.

Gayyata : Ittihadushshu,ara harkatil islamiyya tahata sayyid ibraheem Yaqub Al, zakzak H. Amm.

Hotunan wasu daga cikin Shuwagabannin kasashen Duniya kenan, A lokacin da suke isar da sakon ta'aziyyar Shuwagaban Kasar...
22/05/2024

Hotunan wasu daga cikin Shuwagabannin kasashen Duniya kenan, A lokacin da suke isar da sakon ta'aziyyar Shuwagaban Kasar Iran Shahid Ibrahim Ra'esi Da Allah yayima Rasuwa.

Wasunsu suna mika ta'aziyyar ne ta hanyar zuwa kasar ta Iran daga kasashensu,inda kuma wasunsu ke isar da tasu ta'aziyyar ta hanyar offishin Jakadancin Iran dake a kasarsu.

22/05/2024
Wasu daga cikin hotunan yadda dandazon al'umma, s**a halarci jana'izar Ayatullah Shahed Sayyid Ibrahim Ra'isi, tare da s...
22/05/2024

Wasu daga cikin hotunan yadda dandazon al'umma, s**a halarci jana'izar Ayatullah Shahed Sayyid Ibrahim Ra'isi, tare da sauran waɗanda s**a yi shahada tare da shi, wadda jagoran juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i ya jagoranta.

Muna miƙa ta’aziyya ga jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da kuma al’ummar ƙasar Iran baki ɗaya, da sauran musulman duniya, akan wanann babban rashi da muka yi.

Allah ya karɓi shahadarsu, ya ɗaukaka matsayinsu, ya cike mana gurbinsu da waɗanda s**a fisu.


22/05/2024

Cikin Hotuna:-Shaikh Yakub Yahya Katsina, ya jagoranci zaman makokin Shahadar, shugaban ƙasar Iran Ibrahim Ra’isi, da Mi...
21/05/2024

Cikin Hotuna:-

Shaikh Yakub Yahya Katsina, ya jagoranci zaman makokin Shahadar, shugaban ƙasar Iran Ibrahim Ra’isi,
da Ministan harkokin wajen kasar, Hossein Amir Abdollahian, da Gwamnan Lardin Gabashin Azerbaijan, Malik Rahmati, da Limamin Juma’a na Tabriz, Muhammad Ali AlHashem, da sauran abokan tafiyarsa, waɗanda s**a yi hatsari sakamakon canjin yanayi na hazo, akan jirgi mai saukar ungulu.

Shaikh Yakub Yahya Katsina ya yi takaitaccen jawabi akan abinda ya faru, da kuma yadda kowane daga cikin su ya bayar da gudunmawarsa, wajen ganin an kare juyin juya halin na kasar. da sauran wasu muhimman abubuwan waɗanda s**a shafi tarihinsu.

Daga karshe an gabatar da Du’a’u Tawasul hadiya zuwa ga ruhikansu.

Allah ya bamu haƙurin rashinsu, ya mayar mamu da waɗanda s**a fi su. Allah ya ƙarbi Shahadarsu.

.
20/05/2024.

Al'ummar ƙasar Iran na ci gaba da juyayin Shahadar Shugaban ƙasar Ayatullahi Syed Ibraheem Ra'isi.
21/05/2024

Al'ummar ƙasar Iran na ci gaba da juyayin Shahadar Shugaban ƙasar Ayatullahi Syed Ibraheem Ra'isi.

Ga wasu sabbin fotuna na Program na dalibai mahaddata agarin Kano
18/05/2024

Ga wasu sabbin fotuna na Program na dalibai mahaddata agarin Kano

Alhamdulillah taro yayi taro anyi an gama Lafiya, Allah ya maida kowa gidansa lafiya.
18/05/2024

Alhamdulillah taro yayi taro anyi an gama Lafiya, Allah ya maida kowa gidansa lafiya.

Karin wasu Fotunan a wajen Taron Yaye dalibai mahaddata Alqur'ani mai girma a garin Kano.
18/05/2024

Karin wasu Fotunan a wajen Taron Yaye dalibai mahaddata Alqur'ani mai girma a garin Kano.

Taron Yaye Ɗalibai Mahaddata Alƙur'ani a garin Kano, Karo na (13)A yau Asabar ne 18/05/2024 aka gudanar da Taron Yaye Ɗa...
18/05/2024

Taron Yaye Ɗalibai Mahaddata Alƙur'ani a garin Kano, Karo na (13)

A yau Asabar ne 18/05/2024 aka gudanar da Taron Yaye Ɗalibai Mahaddata Alƙur'ani mai girma a garin Kano, karo na (13) kamar yadda aka saba gudanarwa lokaci bayan Lokaci na Daliban Makarantar Fodiyya Tahafizulƙur'an Ƙalƙashin Jagorancin Sayyeed Ibrahim Zakzaky (H)

Taron Mahaddata Alƙur'ani na gudana a Masallacin gidan Sarki a garin Kano yayin da Mahaddata Maza da Mata tare da Dubban ƴan'uwa Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky na garuruwa da dama tare Wakilan Sayyeed a filin Taron.

Bayan bude taro da addu'a, masu raira wakoki sun raira wakoki ga Annabi da Iyalan gidansa, sai Hafiza Fatima Salisu Zayiya ta gudanar da Karatun Alqur'a a yanzu haka a filin taro

Katsina Media Update 18/05/2024.
Isma'il Abubakar Idris K.t

Wajen Zaman Sayyeed ( H) da Wakilansa a filin Taron Mahaddata Alqur'ani a garin Kano
18/05/2024

Wajen Zaman Sayyeed ( H) da Wakilansa a filin Taron Mahaddata Alqur'ani a garin Kano

Rehoto na Farko daga Garin Kano wajen Taron Mahaddata Alqur'ani karo na 13, ki kasance tare da Katsina Media Update domi...
18/05/2024

Rehoto na Farko daga Garin Kano wajen Taron Mahaddata Alqur'ani karo na 13, ki kasance tare da Katsina Media Update domin samun Rohoto na kai tsaye.

Katsina Media Update 18/05/2024.
Isma'il Abubakar Idris K.t

“Imam Khumaini (QS) yace: “Idan ka ji Mutum yana rigimar Shi'a da Sunna, to shi ba ɗayan biyun bane, shi ba Shi'a bane, ...
15/05/2024

“Imam Khumaini (QS) yace: “Idan ka ji Mutum yana rigimar Shi'a da Sunna, to shi ba ɗayan biyun bane, shi ba Shi'a bane, shi ba Sunna bane.”

— Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin a jawabin ganawarsa da Ƴan Academic Forum a ranar tunawa da Wafatin Imam Khumaini (QS) a shekarar 2023 a gidansa da ke Abuja.

Kashe 'Yan shia: Kotu Ta Sake Cin Tarar ‘Yansandan Nijeriya Diyyar Naira Miliyan 200 Bisa Kashe ‘Yanshi’ar A Soba*Ta ce ...
15/05/2024

Kashe 'Yan shia: Kotu Ta Sake Cin Tarar ‘Yansandan Nijeriya Diyyar Naira Miliyan 200 Bisa Kashe ‘Yanshi’ar A Soba

*Ta ce matakin da ƴansanda s**a ɗauka haramtacce ne a kundin tsarin mulkin ƙasa.*

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta umurci hukumomin ƴan sanda da su biya zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 200 ga iyayen ‘yan Shi’a guda biyu da jami’anta s**a kashe a lokacin da suke gudanar da muzaharar Ashura a ranar 28 ga watan Agustan 2022 a garin Soba da ke ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna.

Mai shari’a Hawa Buhari, a cikin hukuncin da ta yanke, ta tabbatar da take haƙƙin waɗanda aka kashe kamar yadda aka tanadar a cikin sashe na 33, 38, 39, 40, 42 da 46 na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima); Ɓangare na 4,8,10, 11 da 12 na Dokar Yarjejeniyar Afrika (African Charter) kan ƴancin ɗan Adam da Jama'a (wacce aka sanya wa hannu aka ɗabbaƙa) ta shekarar 2004 da kuma Doka 1,2,3,4 da Oda ta 11,12, na Ƙa'idojin Aiwatar da Haƙƙin Bil-Adama na shekarar 2009”.

Alƙalin kotun ta ce dole ne a biya adadin kuɗi har Naira miliyan 100 ga kowanne iyayen waɗanda aka kashe, inda za a biya jimillar naira miliyan 200 ke nan a matsayin diyya da kuma ɓarnar da aka aikata, sannan kuma har wala yau za a biya ribar kashi 10 cikin 100 a duk shekara har sai an biya kuɗin baki ɗaya.

Mai shari’a Buhari, a hukuncin da ta yanke a ranar 13 ga watan Mayun, 2024, - kamar yadda ɗaya daga cikin lauyoyin masu ƙara ya bayyanawa manema labarai jim kaɗan bayan fitowa kotun- ta haɗa ƙararraki biyu (consolidation) dake gabanta waɗanda makusantan waɗanda aka kashe s**a shigar daban daban a kotun.

“Bayan da lauyoyi s**a tabbatar da ƙarar ta su tare da gabatar da shaidu kuma Kotu ta yi nazari hujjojin masu ƙara da kuma waɗanda ake ƙaran, sai ta yanke hukunci ta kuma bada umurni kamar haka:

“An haɗa ƙara mai lamba: FHC/KD/CS/142/2022, da mai lamba: FHC/KD/CS/144/2022.

“Dole waɗanda ake ƙara su biya kuɗi Naira miliyan 100,000,000.00 (Naira Miliyan Ɗari) ga kowann

14/05/2024

Kotu Ta Sake Cin Hukumar 'Yansandan Nijeriya Tarar Naira Miliyan 200 Kan Kashe Wasu 'Yanshi'a 2 A Garin Soba A Shekarar 2022.

Motar KTSTA Ta Yi Hatsari A Zariya.Wata Motar Sufurin jihar Katsina, KTSTA, wadda ta taso daga jihar Kaduna zuwa jihar K...
13/05/2024

Motar KTSTA Ta Yi Hatsari A Zariya.

Wata Motar Sufurin jihar Katsina, KTSTA, wadda ta taso daga jihar Kaduna zuwa jihar Katsina a ranar Lahadin nan, ta samu mummunan hatsari a kan hanyar dawowarta zuwa Katsina.

Shaidun gani ra ido sun bayyana mana cewar, motar ta yi hatsarin ne a daidai gadar Nihu Bamalli a Zariya, inda ta jujjuya da mutanen da ke a cikinta ta wurgo su waje, a nan kuma wasu s**a rasu, a yayin da aka garzaya da wasunsu Asibit Mutu-kwakwai-rai-kwakwai.

Daga cikin wadanda s**a rasu akwai Yakubu Musa wanda aka fi sani da Babagida Gemu mai sana'ar gyaran wayoyi a Kasuwar saida wayoyi da ake kira tsaitsaye a cikin birnin Katsina.

Tuni dai an yi jana'izartasa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin karfe 5:00 nanYammacin nan a gidansu da ke Unguwar Yammawa, inda aka rufe shi a Makabartar Dantakum Katsina.

Allah ya jikan wadanda s**a rasu, mu kuma ya kyauta namu tafiyar. Ameen.

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci Ayatollah Sheikh Mohammad Yaqoobi (H) a gidansa da ke Najaf.    03/Zulqada...
12/05/2024

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci Ayatollah Sheikh Mohammad Yaqoobi (H) a gidansa
da ke Najaf.




03/Zulqada/1445
11/05/2024

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taron ƙasa da ƙasa kashi na 2 don nuna goyon baya ga Al'ummar Falastinu ma...
08/05/2024

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taron ƙasa da ƙasa kashi na 2 don nuna goyon baya ga Al'ummar Falastinu mai taken "Ɗufanul Aqsa" da kungiyar samar da kusanci tsakanin mazhabobin musulunci da ake kira (Majma'a Taqrib bainal mazahib) ta shirya yau laraba a birnin Bagadaza, ƙasar Iraki.

Manyan malamai daga mazhabobi daban daban na musulunci s**a halarci taron.




29/Shawwal/1445
09/05/2024

ISMA Medical Care Initiative, _Sashen Kula da Lafiya Na Harkar Musulunchi,_ 🌹Sakamakon matsanancin yanayin ZAFI da dumam...
08/05/2024

ISMA Medical Care Initiative, _Sashen Kula da Lafiya Na Harkar Musulunchi,_

🌹

Sakamakon matsanancin yanayin ZAFI da dumamar yanayi da ake fama da shi a yankin Arewacin Nigeriya da yankunan Jamhuriyar Nijer, akwai tabbacin Bullar Annobar Cutar Sankarau mai kisa a jihohin Arewa da dama,

ISMA Sashen Kula da Lafiya na Harkar Musulunchi, almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

Na Farin Cikin Gayyatarku Gangamin Wayar da kai akan *CUTAR SANKARAU* Wanda aka tsara gabatarwa kamar haka:

🪻🪻🪻

Rana:

Lahadi, 12th May, 2024

Wuri:

Fudiyyah Sabuwar Kofa, Katsina,

Lokaci: 03 pm,

_Taken Taro:_

*KARIYA DA RIGA-KAFIN CUTUKA MASU YADUWA* ; _Alamomin Bayyanar Cutar Sankarau!_

*Kasidun da za'a gabatar:*

1) Annobar Cutar Sankarau,

2) Hadarin Cunkoso a Bullar Annobar Cutar Sankarau,

3) Matakan Kariya da Riga-Kafin Cutar Sankarau,

*Mahalarta* :
💉 International and Local Medical NGOs,

💊 Al'umma Maza da Mata,

✍🏼iSMA _Media_ 🎤

Jiya Talata Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci  Haramin AlKazimain, wanda ya haɗa haramin Imam Musa Khazim da...
08/05/2024

Jiya Talata Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci Haramin AlKazimain, wanda ya haɗa haramin Imam Musa Khazim da Imam Muhammad Jawad (S) a birnin Bagadaza dake ƙasar Iraki.





07/05/2024
28/Shawal/1445

JAN HANKALI.DAGA HARISAWAN HARKAR MUSLUNCI KALKASHIN JAGORANCIN SAYYEED IBRAHIM ZAKZAKY (H)
03/05/2024

JAN HANKALI.

DAGA HARISAWAN HARKAR MUSLUNCI KALKASHIN JAGORANCIN SAYYEED IBRAHIM ZAKZAKY (H)

01/05/2024

Magana Akan Iyayen Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam

21/04/2024

Shi'a tafi Sunna Gaskiya awajan alwala 💪🏾

Prof. Maqari

Yadda sojin saman Iran su kakkabo makami mai linzami 7 na Isra'ila a dajin Isfahan na kasar Iran
19/04/2024

Yadda sojin saman Iran su kakkabo makami mai linzami 7 na Isra'ila a dajin Isfahan na kasar Iran

TARON TUNAWA DA WAKI'AR 19/APRIL 1991 A KATSINA.A yau Juma'a 19/ April/2024ne  Ƴan'uwa Musulmai Almajiran Sayyeed Ibrahi...
19/04/2024

TARON TUNAWA DA WAKI'AR 19/APRIL 1991 A KATSINA.

A yau Juma'a 19/ April/2024ne Ƴan'uwa Musulmai Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky na da'irar garin Katsina na cigaba da gudanar da Taron tunawa da waƙi'ar 19 Aprl 1991 lokacin da John madawaki ke mulki a matsayin gwamnan Jahar katsina inada yayi alƙawalin kawar da Wakilin ƴan'uwa na Da'irar garin katsina Sheik Yaƙub yahya, gwamna John Madawaki yace zai kai Malam Yaƙub Yahya filin Folo a halbeshi sabida Sheik ya Jagoranci zanga-zangar Allah wadai da gidan Jaridar ( Daily Times, a magazine ɗinta mai suna Phone times) da tayi ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.a.w.w.), tare da kona Jaridar.

Taron tunawa Waƙi'ar na gudana a Markaz Kofar Marusa Katsina bayan Addu'a da Karatun Alƙur'ani mai girma tare da Raira waƙoƙin tinawa da waƙi'ar, sai aka gudanar da ƙwarya-ƙwaryar Jawabi akan waƙi'ar sai masu Tamsiliyya s**a fara gudanarwa kafin mai Jawabi ya fara gudanar da cikakken Jawabi a muhallin.

Ga kaɗan daga Fotunanda muka ɗauko maku a muhallin taron Markaz Kofar Marusa Katsina.

Katsina Media Update 19/April/2024.
Isma'il Abubakar Idris K.t

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gudanar da bukukuwan ranar sojojin ƙasar tare da dakaru daga dukkan sassan rundunoni, su...
17/04/2024

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gudanar da bukukuwan ranar sojojin ƙasar tare da dakaru daga dukkan sassan rundunoni, sun gudanar da fareti a manyan biranen kasar ciki har da Tehran babban birnin kasar.

Address

Gobarau
Katsina

Telephone

+2348166936199

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Wahda News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Wahda News:

Videos

Share

Nearby media companies


Other News & Media Websites in Katsina

Show All

You may also like