Katsina24 News

  • Home
  • Katsina24 News

Katsina24 News Shafin Katsina24News ya shahara wajan kawo labaran jihar katsina da kasa najeriya baki daya cikin harshen Hausa da Turanci.

Katsinawa naku ya samuƘungiyar sakatarorin ƙananan hukumomin Nijeriya za su karrama Dikko Radda a matsayin gwamnan da ya...
26/10/2025

Katsinawa naku ya samu

Ƙungiyar sakatarorin ƙananan hukumomin Nijeriya za su karrama Dikko Radda a matsayin gwamnan da ya fi kowane gwamna kwazo a Nijeriya yau Lahadi a Abuja

PUBLIC NOTICE & SPECIAL INVITATION 🟩

The National Association of Local Government Council Secretaries (NALGCS)
cordially invites the general public, especially the good people of Katsina State, to a

🏆 GRAND AWARD OF EXCELLENCE CEREMONY

In Honour of
His Excellency, Malam Dikko Umar Radda, Ph.D, CON
Executive Governor of Katsina State

As
Best Performing Governor in Nigeria on Local Government Administration

This prestigious recognition is in appreciation of His Excellency’s outstanding performance, visionary leadership, and unwavering commitment to grassroots and rural development across Katsina State and Nigeria at large.

📅 Date: Sunday, 26th October, 2025
🕑 Time: 2:00 PM
📍 Venue: NICON Luxury Hotel, Abuja

Join us as we celebrate a leader whose dedication to good governance continues to inspire excellence nationwide.

All are cordially invited!

Signed,
Hon. Bashir Umar Maigora Council Sec. Faskari LGC
Public Relations Officer (PRO)
For: National Association of Local Government Council Secretaries (NALGC.

‎KATSINA24NEWS — Rahoto‎‎Direban babur (Dan achaba) ya tarar da matarsa tare da shugaban makaranta,  suna abinda bai dac...
26/10/2025

‎KATSINA24NEWS — Rahoto

‎Direban babur (Dan achaba) ya tarar da matarsa tare da shugaban makaranta, suna abinda bai dace ba sannan ya yi musu rangadi a gaban al'ummar gari.

‎Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a garin Siaya (Kenya) inda wani direban babur ya k**a matarsa tare da shugaban wata makaranta cikin makaranta, abokan aikinsa ne s**a taimaka masa s**a cire musu tufafi sannan s**a yi rangadi dasu cikin gari a gaban mutane don suji kunya.

‎An ruwaito cewa abokan dan achaban ne s**a fara hango matar tana ziyartar shugaban makarantar, s**a shaida wa direban wanda daga bisani ya kai matakin basu kunya ta hanyar cire tufafi da kuma ketarawa dasu cikin gari. Sai dai hakan ya janyo cece-kuce daga jama'a da dama.

‎Wasu daga cikin mazauna sun soki matakin, suna cewa ya k**ata ya bi hanyar doka ko kuma ya saketa maimakon ya yiwa matar da shugaban makaranta irin wannan abun Jin kunya, musamman ma kasancewar dukansu manya ne. A gefe guda, wasu sun goyi bayan matakin.


‎KATSINA24NEWS tana ci gaba da bibiyar lamarin don kawo karin bayani daga wurin, da kuma ra'ayoyin shari'a da na zamantakewa game da irin wannan lamari.

26/10/2025

Gwamnatin Jihar katsina taci gaba da biyan dalibai scholarship dinsu.

12/10/2025

Matsalar Ruwa a Marabar Gurbi, Kankara: Mazauna Sun Nemi Taimakon Gaggawa

Marabar Gurbi, Kankara – Katsina24News

Mazauna ƙauyen Marabar Gurbi da ke cikin ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina sun koka kan matsalar rashin ruwa mai tsanani da suke fama da ita a halin yanzu, inda s**a nemi taimakon gaggawa daga hukumomi da masu hannu da shuni.

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa babbar rijiyar da jama’ar ƙauyen s**a gada tun daga kakanni ta rufe gaba ɗaya, kuma ta zama haɗari ga waɗanda ke ƙoƙarin kusantarta saboda lalacewar da ta yi.

A cewar Bishir Kabir, ɗaya daga cikin mazauna yankin wanda ya sanya hannu a madadin al’umma, ya bayyana cewa:

> “Rijiyarmu da muke amfani da ita tun iyaye da kakanni yanzu ta rufta. Mutane suna tsoron matsawa kusa da ita saboda fargabar kada su fada. Muna roƙon gwamnati da masu alhakin al’umma su taimaka su gyara mana ko kuma su samar mana wata hanyar samun ruwa.”

> “Wallahi muna bukatar taimakon gaggawa,” in ji Bishir Kabir.

📞 Tuntuɓa: 09079721624.

‎An Yi Zargin Son Rai a Cikin Jerin Sunayen Masu Nasara na Hukumar Kwastam‎‎Katsina24News ta samu rahoton cewa ana zargi...
12/10/2025

‎An Yi Zargin Son Rai a Cikin Jerin Sunayen Masu Nasara na Hukumar Kwastam

‎Katsina24News ta samu rahoton cewa ana zargin an yi son kai da rashin daidaito a cikin jerin sunayen wanda s**a tsallaka zuwa matakin gaba a shirin daukar sabbin ma'aikata da Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta fitar.

‎Bayanan da s**a bayyana sun nuna cewa daga cikin wadanda aka zaba, mutane 541 ne daga Arewacin Najeriya, yayin da mutane 1244 s**a fito daga Kudancin Najeriya. Wannan bambanci ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda jama’a da dama ke tambayar ko an yi adalci a tsarin aikin.

‎Wasu daga cikin ‘yan Najeriya na ganin wannan lamari na nuna bambancin siyasa da yankin ƙasa, wanda zai iya rage amincewar jama’a ga tsarin daukar aiki a hukumomin gwamnati.

‎Masu ruwa da tsaki sun bukaci Hukumar Kwastam da Gwamnatin Tarayya da su fito fili su bayyana ma’aunin da aka yi amfani da shi, domin tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin ‘yan kasa.

‎> “Ba a adalci idan bangare guda ke amfana fiye da kima. Ya k**ata a gyara irin wannan tsarin domin tabbatar da hadin kan kasa,” in ji wani mai sharhi a shafin sada zumunta.

‎Katsina24News ta ci gaba da bibiyar wannan batu, kuma za ta rika kawo muku cikakkun rahotanni yayin da lamarin ke kara daukar zafi.

Gaskiya Soja Boy Yana Tsula Tsiyarsa Da Yarinyar Nan IFTIHAL Yadda Yake so, Ko Matarsa ce ae sai haka.Soja boy Fa yasake...
10/10/2025

Gaskiya Soja Boy Yana Tsula Tsiyarsa Da Yarinyar Nan IFTIHAL Yadda Yake so, Ko Matarsa ce ae sai haka.

Soja boy Fa yasake jawo maganganu a social media a wajen daukan sabon wakan sa mai suna Kauna.

Wai Bayace ya tuba ya daina kalar wannan wakokin ba?.

Idan Wannan yar gidanku ce wani mataki zaka dauka akan ta?.

Allah yakara Shiryar Damu 🙏🙏

ZABEN 2027: Ko Kana Daga Cikin Kanawan Da Za Su Sake Zabar Gwamna Abba Kabir A Karo Na Biyu?
10/10/2025

ZABEN 2027: Ko Kana Daga Cikin Kanawan Da Za Su Sake Zabar Gwamna Abba Kabir A Karo Na Biyu?

10/10/2025

Yadda wasu mutane ke chin Neman kare

An Rufe Sakatariyar Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC a Jihar Katsina Saboda Rashin Biyan Harajin ƘasaLabarai daga: Katsina24newsR...
09/10/2025

An Rufe Sakatariyar Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC a Jihar Katsina Saboda Rashin Biyan Harajin Ƙasa

Labarai daga: Katsina24news

Rahotanni daga jihar Katsina na nuna cewa hukumomi sun rufe sakatariyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Katsina, sak**akon gazawar ƙungiyar wajen biyan kuɗin harajin ƙasa (land use charge) da aka ɗora musu.

Wannan mataki ya biyo bayan gargaɗin da aka sha yi wa ƙungiyar, inda hukumomin jihar s**a bayyana cewa duk wani gini ko fili da ke karkashin mallakar kowace kungiya ko mutum dole ne ya biya haƙƙin harajin ƙasa k**ar yadda doka ta tanada.

Wani jami’i daga hukumar kula da haraji ta jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an bayar da isasshen lokaci da sanarwa kafin daukar wannan mataki, amma kungiyar NLC ta ki biyan kuɗin duk da hakan.

Sai dai har zuwa yanzu, shugabannin kungiyar NLC a jihar ba su fitar da wata sanarwa ko martani kan lamarin ba.

Labari cikin hotuna: Hoton Makadi Mai K**a da Biri Ya Ƙayatar da Masu Kafofin Sada Zumunta.Hotunan wani makadi daga ƙasa...
09/10/2025

Labari cikin hotuna: Hoton Makadi Mai K**a da Biri Ya Ƙayatar da Masu Kafofin Sada Zumunta.

Hotunan wani makadi daga ƙasar K**aru sun janyo ce-ce-ku-ce da muhawara a dandalin sada zumunta, bayan da jama’a s**a fara bayyana matuƙar mamakinsu kan yadda siffar fuskar makadin ke k**a da ta dabbar biri.

Wasu masu amfani da dandalin sun bayyana cewa wannan bai k**ata ya zama abin dariya ba, domin halittar kowanne ɗan Adam daga Allah take. Sauran kuma sun ɗora hoton da barkwanci, suna ƙoƙarin kwatanta shi da fina-finai ko hotunan labaran da s**a saba gani.

Makadin wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, ana ganinsa cikin farin ciki yana bugun kayan kida, wanda hakan ke nuna cewa bai damu da yadda mutane ke kallonsa ba. Wasu sun yaba da ƙarfin gwiwarsa da yadda yake bin rayuwa cike da nishadi.

Katsina24News na ci gaba da bibiyar cikakken labarin domin kawo muku ƙarin bayani idan akwai.

Ina ya Garin Daura?An ɗauki wannan hoton a Daura cikin shekarar 1984 Shekaru Arba'in da ɗaya kenan da s**a Gabata. Ba wa...
06/10/2025

Ina ya Garin Daura?

An ɗauki wannan hoton a Daura cikin shekarar 1984 Shekaru Arba'in da ɗaya kenan da s**a Gabata. Ba wani karin bayani da da muka samu daga wannan hoton amma watakila a samu ƙarin bayani daga mabiya wannan shafi 'Yan Daura.

Katsina24news.

Najeriya ta fi ƙarfin PENGASSAN. Alhaji Aliko Dangote jagora ne a ɓangaren tattalin arziƙin ƙasar nan. Ya zama wajibi gw...
06/10/2025

Najeriya ta fi ƙarfin PENGASSAN. Alhaji Aliko Dangote jagora ne a ɓangaren tattalin arziƙin ƙasar nan. Ya zama wajibi gwamnati ta kare kamfanoninsa da kuma muradunsa, domin ci gaban ƙasa.

— Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima

Katsina24News.

Address


Telephone

+2349138321277

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina24 News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Katsina24 News:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share