02/12/2023
Mai martaba Sarkin Katsina ya kira taron gaugawa da masu ruwa da tsaki, akan wani faifan bidiyo da Sheikh Bin. Usman ya fitar na s**ar sabon shirin nan na tallafa ma Ilmi watau (AGILE).
A ranar alhamis 30/11/2023, Mai Martaba Sarkin Dr. Abdulmuminu Kabir Usman ya kira wannan taro na gaugawa da masu ruwa da tsakin domin a tattauna akan wannan domin samun mafita.
Sheikh Bin. Usman a cikin faifan bidiyon da ya fitar ya soki shirin na AGILE, inda yace shirin yana da alamar tambaya, Malamin yana zargin shirin k**ar akwai makircin yahudawa a cikin shi.
Masu ruwa da tsakin da mai Martaba Sarkin ya kira sun hada ma'aikatar ilmi ta Jihar Katsina, ma'aikatar kula da harkokin addini ta Jiha, Malaman addini na bangarorin kungiyar Darika da Izalah, wakilai daga shirin na (AGILE). Da dai sauransu.
A jawabin da Mai martaba ya gabatar yayin gudanar da taron, ya bayyana cewa" tun daga lokacin da ya saurari wannan faifan bidiyo da Shehin Malamin ya fitar ya shiga cikin damuwa da tashin hankali.
Wannan dalilin na rashin natsuwa yasa ya yi tunanin kiran wannan taro domin a tattauna, a bada shawarwari, akan wannan abun da ake ganin zaya iya zama barazana ga tarbiyar yaranmu masu tasowa musamman 'Yaya mata kadai da shirin ya zaba.
Kwamishinan ma'aikatar kula da harkokin addini ta Jiha Hon. Ishaq Shehu Dabai, babban sakataren ma'aikatar Dr. Surajo Abukur, babbar sakatare ta ma'aikatar ilmi ta Jihar Katsina.
Sai Wakili daga sabon shirin na AGILE na Jihar Katsina, Manyan Malamai daga bangarorin addini daban-daban su ka tofa albarkacin bakinsu, kuma sun gabatar jawabai masu ma'ana.
Daga karshe Mai martaba Sarkin ya bada umurnin kafa kwamiti na musamman karka shin Jagorancin kwamishinan ma'aikatar kula da harkokin addini ta Jiha, domin ya binciki shirin ya kuma bada shawarwari akan binciken domin samar da mafita.
30 November, 2023.
Mobile Media Crew