Bahaushiya Online Media

Bahaushiya Online Media Domin kawo maku labarai wadanda aka tantance aka tace, a cikin harshen Hausa.

Malam Yusuf Aminu Jby ya wallafa a shafinsa:Kafar Sadarwar Facebook duniyata ce. Don haka ba zan wohintar da iyaye, yayy...
09/02/2024

Malam Yusuf Aminu Jby ya wallafa a shafinsa:

Kafar Sadarwar Facebook duniyata ce. Don haka ba zan wohintar da iyaye, yayyai da abokaina ba.
Gayyata ce gamammiya, da neman sanya albarka.

Na gode.

Kotu ta bai wa Abubakar Yahaya Kusada kujerar majalisar wakilai ta Kankiya/ Kusada/ Ingawa.
08/09/2023

Kotu ta bai wa Abubakar Yahaya Kusada kujerar majalisar wakilai ta Kankiya/ Kusada/ Ingawa.

Jibiya Ta Shiga Jerin Garuruwan Da S**a Gudanar Da Bikin Zagayowar Ranar Hausa Ta Duniya...Majalisar dinkin duniya ce da...
27/08/2023

Jibiya Ta Shiga Jerin Garuruwan Da S**a Gudanar Da Bikin Zagayowar Ranar Hausa Ta Duniya...

Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware ranar 26 ga watan Ogusta a matsayin ranar Hausa ta duniya. Hakan ya sa dalibai da malamai masu nazarin harshen Hausa na karamar hukumar Jibiya s**a shiga sahun wadanda s**a gudanar da bikin zagayowar ranar.

Kamar yadda jaridar Jibia Media News ta ruwaito ta ce bikin ya gudana ne a filin wasa na Firamaren Tudun Wada (Pilot) ya samu tagomashin samun mahalartan da ba a yi tsammani ba. Daga cikin mahalartan akwai shugaban sashen nazarin harshen Hausa na kwalejin kimiyya ta Katsina, (Dr. Isah Dahiru) wanda yana cikin masu gabatar da makala, Akwai sanannen malamin malamin nan da ya yi fice wajen koyar da harshen Hausa a karamar hukumar, (Malam Mansur Mamuda). Mai girma sarkin Arewa hakimin Jibiya ya shi ma ya amsa kiran taron ta hanyar wakilcin Yariman Jibiya, (Mubarak Rabe Rabi'u). Sarkin noma, da sarkin makera, da sarkin bakin Jibiya sun amsa katin gayyatar taron.

Malaman makaranta, da daliban makarantun gwamnati da masu zaman kansu, sun cika taro. Inda mafi yawancin abubuwan da s**a gudanar daliban makarantun ne s**a gudanar. Taron ba zai cika ba idan ba a ambaci masu kide-kiden gargajiya, da masu bushe-bushe.

Abubuwan da s**a gudana a wurin baya ga makaloli guda biyu masu taken, "Muhimmancin Rikon Al'adu Ga Hausa.", da "Yaduwar harshen Hausa a Duniya." Sannan akwai raye-rayen gargajiya, da wasan dambe, wasan 'Yar tsana, wasan tafa-tafa, wasan wargin fadawa, Al'adar bakar magana, Gasar Karin Magana, da sauran abubuwa masu kayatarwa.
Bayan kammala taron, al'ummar gari dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan taron, da kuma yin tsokaci. Yayin da wasu suke korafin yadda aka ci aka tsire ba tare da sun jiwo kashin taron ba.

Bahaushiya Online Media

26/08/2023

Ku karasa mana wannan karin maganganun akwai kyautar Katin waya ga wanda ya riga bayar da amsa daidai:

◇ Da sauran kuka,...
◇ Ala Suturu bukui,...
◇ Kowa ya raina tsayuwar wata,...
◇ Kashin turmi,...
◇ Maraba gasasshe,...

Allah ya ba mai rabo sa'a.

Gwamnan Katsina Ya Kar6i Bakuncin Kwamitin Majalisar Dattijai Ta Kasa Kan Ayyukan Jami'an Kwastan Musamman a Titin Katsi...
14/08/2023

Gwamnan Katsina Ya Kar6i Bakuncin Kwamitin Majalisar Dattijai Ta Kasa Kan Ayyukan Jami'an Kwastan Musamman a Titin Katsina-Jibia

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, a ranar Litinin 14th Agusta, 2023 ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dattawa kan ayyukan jami'an kwastam a gidan gwamnatin jihar.

Aikin da kwamitin ya zo yi a Katsina, shi ne na kyautata alaka tsakanin 'yan kasuwar da ke yankin Jibia da sauran yankunan da ke kan iyakar jihar Katsina da Jamhuriyar Nijar da kuma jami'an hukumar kwastam da ke aikin tabbatar da an bi dokar da kasa ta tanadar wajen shiga ko fitar da kaya.

Dama dai Gwamna jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD na bin duk wasu hanyoyin da s**a kamata domin ganin al'ummar jihar Katsina sun samu hanyoyin gudanar da kasuwancinsu na halal ta yadda tattalin arzikin jihar zai bunkasa.

A lokacin ziyarar, Malam Dikko Umaru Radda ya yaba wa majalisar dattijai ta kasa da ta kafa wannan kwamitin da zai tabbatar da an tsaftace alaka tsakanin jami'an hukumar kwastam da al'ummomin da ke makwabtaka da iyakokin Jamhuriyar Nijar a jihar Katsina.

Malam Dikko Umaru Radda ya bukaci wannan kwamiti da ya yi dubar tsanaki game da korafe-korafen da 'yan kasuwar wannan yakunan s**a bijiro da su domin samowa tare da lalubo hanyoyin da za a bi a warware su cikin sauki da kuma kara kimar aikin na hukumar kwastam.

Ya bayyana matsayarsa ta kin nuna goyon baya ga ayyukan 'sumogal' sannan ya ce zai ba jami'an kwastam duk hadin kai da goyon bayan da suke nema na ganin an dakile dabi'ar 'fasa-kwauri' a kasar nan.

Shugaban kwamitin Sanata Francis ya ce dalilin wannan ziyarar shi ne don su binciki ayyukan jami'an hukumar kwastam a titin Katsina-Jibia domin samar da kyakkyawar alaka tsakanin jami'an da al'ummar da ke yankunan.

A cikin kwamitin akwai Sanatan Katsina ta tsakiya Abdulaziz Musa Yar'adua da na shiyyar Funtua Muntari Dandutse da sauransu.

Madogara:
Apc Youth Mobilization Batagarawa Local Government.

Kungiyar tawaye da juyin mulki ta 6ulla a Nijar...
09/08/2023

Kungiyar tawaye da juyin mulki ta 6ulla a Nijar...

Danmajalisar Bichi Abba,Ya Biyawa Daliban BUK Yan Bichi Su 157 Kudin Registration Miliyan 16 Da Dubu 484 Da Dari 836.
04/08/2023

Danmajalisar Bichi Abba,Ya Biyawa Daliban BUK Yan Bichi Su 157 Kudin Registration Miliyan 16 Da Dubu 484 Da Dari 836.

'Yan Bindiga Sun Sace Boka A Anambara....Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani shahararren boka...
25/07/2023

'Yan Bindiga Sun Sace Boka A Anambara....

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani shahararren boka ɗan asalin jihar Anambra, mai suna Chinedu Nwangwu a ɗaya daga cikin otel ɗin sa a karamar hukumar Idemili ta Arewa.

Bokan da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki, na nufin ‘kwai mai karya kwaran manja’ a turance.

Kamar yadda BBC ta ruwaito cewa an kashe mataimakansa guda biyu a lokacin da aka yi garkuwa da shi a daren Lahadi.

Wata majiya ta ce mutumin wanda ake kyautata zaton yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi a jihar ta Anambra, an yi garkuwa da shi cikin sauki a otal ɗin sa mai suna Triple P Hotel, tare da bindige wasu mukarraban sa guda biyu har lahira.

Ana kuma kallon Akwa Okuko Tiwaraki a matsayin mai maganin gargajiya mafi kuɗi a jihar.

A 2022 ya gina tare da ƙaddamar da otal guda biyu, waɗanda aka ɗauka a matsayin mafi girma a Oba.

Majiyoyi, sun ce sace shi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi.

Hukumomin ƴan sanda a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda ma magana da yawunsu, DSP Toochukwu Ikenga ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare, sai dai daga bisani an sako bokan da aka sace.

15/07/2023

QAFILATUL MUHABBA, JIBIA LOCAL GOVERNMENT, KATSINA STATE.

Taron kara wa juna sani kan muhimmancin tsaftace muhalli da dashen itatuwa.

"Kiwon shanuna sai ya fi min sauki fiye da mulkin 'yan Najeriya" in ji - Shugaba Buhari
29/05/2023

"Kiwon shanuna sai ya fi min sauki fiye da mulkin 'yan Najeriya" in ji - Shugaba Buhari

"Ina shiga Maƙabarta in yi satar Allunan Kabari da ƙarfe 03:00 na dare"- inji wannan matashin 😢Kuma yace idan ya sayar y...
24/05/2023

"Ina shiga Maƙabarta in yi satar Allunan Kabari da ƙarfe 03:00 na dare"- inji wannan matashin 😢

Kuma yace idan ya sayar yana amfani da kuɗin wajen sayen abincin da zai ci da kuma Taba Sigari😔

Daga Isa Abdullahi Dankane

wannan yarinnyar mai kimanin Shekaru 13, an same ta ne kwance bakin hanya kan p**i Road,  Kaduna State, tana kuka tana j...
24/05/2023

wannan yarinnyar mai kimanin Shekaru 13, an same ta ne kwance bakin hanya kan p**i Road, Kaduna State, tana kuka tana jin yunwa sunanta Safiya, kuma ta fito daga Abuja ta zo neman kawar mamarta ba ta gane gidan ba.

Bisa bayaninta ta ce mahaifanta duk sun rasu,a Katsina, In Allah ya sa an gane 'yan uwanta a tuntubi mai unguwa Abdullahi dan London. 08036522799 ALLAH ya sa mu dace.

Don Allah a yada sanarwar don a samu 'yan uwanta.

Bayan bayyana sakamakon zaben jahar Kano, wasu fusatattun sun banka wa gidan mawaki Dauda kahutu rarara wuta.
20/03/2023

Bayan bayyana sakamakon zaben jahar Kano, wasu fusatattun sun banka wa gidan mawaki Dauda kahutu rarara wuta.

Ya rasu sakamakon murnar zabe a Kano.
20/03/2023

Ya rasu sakamakon murnar zabe a Kano.

Sun Kashe Sa Sun Ja Tunga A Kan Gawarsa:Biyo bayan kisan gillar da ɓarayin daji s**a yi wa wasu jami'an sa-kai a garin J...
27/01/2023

Sun Kashe Sa Sun Ja Tunga A Kan Gawarsa:

Biyo bayan kisan gillar da ɓarayin daji s**a yi wa wasu jami'an sa-kai a garin Jibiyar Jahar Katsina su biyu, sun tsare gawar ɗaya daga ciki. Malam Aminu Abubakar (Ladani ne a Masallacin Juma'a na Salmanul Farisi). Bayan sun harbe shi, sun ƙona gawarsa, sannan sun ja tunga a kan ba za su bayar da gawarsa ba.

A ɗayan ɓangaren kuwa, Maharazu (Barde) sun kashe shi ne ta hanyar yankan rago, amma an yi nasarar ɗauko gawarsa.

Tuni dai garin na Jibiya ya rincaɓe da alhinin rasa waɗannan jajirtattun matasa da s**a sadaukar da ransu a kan kare al'umma.

Muna fatan Allah ya jiƙan su da gafara, ya kawo mana zaman lafiya madawwami.

Wata Babbar Kotun Musulunci A Kano Ta Yanke Wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara Hukuncin Kisa A Yau.Shin Anya Wannan Huk...
15/12/2022

Wata Babbar Kotun Musulunci A Kano Ta Yanke Wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara Hukuncin Kisa A Yau.

Shin Anya Wannan Hukunci Bai Yi Tsauri Ba??

Allahu Akbar KabiranAllah ya jaddada rahama.
26/09/2022

Allahu Akbar Kabiran
Allah ya jaddada rahama.

Allah ya yiwa Babban Malami Sheikh Yusuf Al'qardawiy rasuwa

Shahararren malamin addinin Musulunci, Youssef al- Qaradawi wanda ke cikin kusoshin kungiyar Muslim Brotherhood ya rasu.

Tsohon shugaban kungiyar, kuma Limamin Musulunci na duniya ya rasu ne yana da shekaru 96.

An haife shi a Masar kafin ya koma Qatar da zama.

Youssef al- Qaradawi ya wallafa litattafan musulunci da dama.

Yana gabatar da shirin talabijin a tasha al-Jazeera kuma miliyoyin mutane ne ke bin wa'azinsa a fadin duniya.

Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa ya kyautata makwanci. Amin.

Madogara:
BBCHAUSA
Jibwis Nigeria

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬

Allah ya yiwa Babban Malami Sheikh Yusuf Al'qardawiy rasuwaShahararren malamin addinin Musulunci, Youssef al- Qaradawi w...
26/09/2022

Allah ya yiwa Babban Malami Sheikh Yusuf Al'qardawiy rasuwa

Shahararren malamin addinin Musulunci, Youssef al- Qaradawi wanda ke cikin kusoshin kungiyar Muslim Brotherhood ya rasu.

Tsohon shugaban kungiyar, kuma Limamin Musulunci na duniya ya rasu ne yana da shekaru 96.

An haife shi a Masar kafin ya koma Qatar da zama.

Youssef al- Qaradawi ya wallafa litattafan musulunci da dama.

Yana gabatar da shirin talabijin a tasha al-Jazeera kuma miliyoyin mutane ne ke bin wa'azinsa a fadin duniya.

Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa ya kyautata makwanci. Amin.

Madogara:
BBCHAUSA
Jibwis Nigeria

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬

Naziru Sarkin Waka Ya Watsa Wa Masoyansa Kasa A Ido:Wasu matasa kuma masoyan Naziru sarkin waka, sun dauri aniyar yin ta...
25/09/2022

Naziru Sarkin Waka Ya Watsa Wa Masoyansa Kasa A Ido:

Wasu matasa kuma masoyan Naziru sarkin waka, sun dauri aniyar yin tattaki tun daga jahar Bauchi har zuwa jahar Kano don nuna tsantsar soyayyarsu gare shi. Sai dai kashi! Nazirun ya aika sako zuwa gare su kamar haka, "A ce su koma, na gode. Ko babu komai ai akwai nisa, in ya so mu yi waya daga baya."

Anya kuwa hakan da ya yi daidai ne???

Ƴan bindiga sun harbe wani ɗan kasuwa Inyamiri a KanoƳan bindiga da ba a san ko su waye ba harbe wani Inyamiri ɗan kasuw...
25/09/2022

Ƴan bindiga sun harbe wani ɗan kasuwa Inyamiri a Kano

Ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba harbe wani Inyamiri ɗan kasuwa, mai suna Ifeanyi a unguwar Sabongari a Jihar Kano.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8:45 na dare a daidai ginin rukunin kantina na Azubros a kan Titin France da ke Sabongari a cikin birnin Kano.

Shaidun gani da ido sun ce ƴan bindigar sun iso wajen ne, sannan su ka harbe shi, inda ya mutu nan-take, su kuma su ka tsere.

"Dama, kana gani ka san shi su ka zo kashewa. Shahararren mai sayar da batira ne a Sabongari ," inji shaidun gani da ido.

DAILY NIGERIAN ba ta samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, Abdullahi Kiyawa ba a lokacin haɗa rahoton.

10/09/2022
08/09/2022

INA MASU SHA'AWAR YARANSU SU KWANKWADI MADARAR ILIMI DA TARBIYYA...???

CITADEL GROUP OF SCHOOLS JIBIA ITA CE TA YI DAIDAI DA KU.

Wannan shahararriyar makaranta take sanar da al'umma cewa tuni ta fara kar6ar sabbin dalibai a 6angarori daban-daban. Kamar Nazire,(Nursery), Firamare,(Primary), da kuma Sakandare,(Secondary).

Za ku iya neman form din shiga makarantar a:

√ Harabar makarantar dake bisa hanyar Magama.

√ Shagon Alhaji Salisu Ojan Bakin Kuka, Jibiya.

√ Shagon Sanusi Bakin Bene, Magama.

Ko a tuntu6i wadannan lambobi don neman karin bayani: 08132497647/08102675086.

Samar da nagartaccen ilimi da tarbiyya shi ne burinmu.

Muna maraba da kowa da kowa.

08/09/2022

Sarauniyar England Elizabeth (II) ta rasu a yau tana 'yar shekara 96.

Wasu iyalan masarautar ne s**a wallafa hakan a shafukansu na sada zumunta.

Address

Dando Street, Jibia
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bahaushiya Online Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bahaushiya Online Media:

Videos

Share


Other News & Media Websites in Katsina

Show All

You may also like