Arewa Media News

Arewa Media News Labaran kasarmu Najeriya danake kasashen ketare

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano da ga rushe gine-gine a kan titin BUKWata babbar kotu ta hana gwamnatin jihar Kano ci ...
15/07/2023

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano da ga rushe gine-gine a kan titin BUK

Wata babbar kotu ta hana gwamnatin jihar Kano ci gaba da rushe gidajen da ke kan titin BUK a karamar hukumar Gwale ta jihar.

Kotun ta bada umarnin ne ta gaggawa bayan ƙorafin da aka shigar mai kwanan wata 4 ga watan Yuli, wanda Ibrahim Adamu, Lauyan masu kara a madadin Bashir Abdullahi da wasu 19 su ka gabatar.

Wadanda ake karar sun hada da Gwamna Abba Kabir Yusuf da babban lauyan gwamnati da kuma hukumar kasa da safiyo da ta tsarawa da raya birane ta Kano.

Mai shari’a Hafsat Yahaya Sani, ta bayar da umarnin na wucin-gadi na hana wadanda ake karar su ds kansu, ko wakilai ko ma’aikata shiga filin har sai an saurari karar da kuma yanke hukuncin a kan ƙorafin.

Misis Yahaya Sani ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 26 ga Oktoba.

Babban matsala ga Emefiele yayin da gwamnatin Tinubu ke tuhumar sa da laifin mallakar makami ba bisa dokaba.Gwamnatin Ta...
15/07/2023

Babban matsala ga Emefiele yayin da gwamnatin Tinubu ke tuhumar sa da laifin mallakar makami ba bisa dokaba.

Gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shigar da kara a cikin kasashe biyu na mallakar bindigogi da makami a kan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar ( CBN ) Gwamna, Godwin Emefiele, a gaban Babban Kotun Tarayya a Legas.

A cewar rahotannin talabijin na Channels a ranar Asabar, 15 ga Yuli, 2023, Gwamnatin Tarayya ta zargi Emefiele da mallakar bindiga mai shinge guda daya ( JOJEFF MAGNUM 8371 ) ba tare da lasisi ba. Gwamnati ta tabbatar da cewa laifin ya sabawa Sashe na 4 na Dokar bindigogi, Dokokin Cap F28 na Federationungiyar 2004, kuma ana iya yanke hukunci a ƙarƙashin Sashe na 27 ( 1b ) na wannan Dokar. A cikin ƙidaya na biyu, An zargi gwamnan CBN da ya dakatar da mallakarsa a cikin jerin gwanon 123 na ammonium ( Cartridges ) ba tare da lasisi ba, wanda ya sabawa Sashe na 8 na Dokar bindigogi Cap F28 Dokokin Tarayya 2004 kuma ana iya yanke hukunci a ƙarƙashin Sashe na 27 ( 1 ) ( b ) ( il ) na wannan Dokar.

Da dumi, dumi Dr. Mustapha Muhammad Inuwa tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Katsina yabar jam'iyyar Apc tare da dubban Ma...
16/10/2022

Da dumi, dumi Dr. Mustapha Muhammad Inuwa tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Katsina yabar jam'iyyar Apc tare da dubban Magoya bayansa, ya koma Jam'iyyar PDP.

DA DUMI-DUMINSA: Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o'i Da Su Bude Jami’o’i, Dalibai Su Koma KaratuDaga Comr ...
26/09/2022

DA DUMI-DUMINSA: Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o'i Da Su Bude Jami’o’i, Dalibai Su Koma Karatu

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da jami'o'i (NUC) ta umarci shugabannin jami'a da su gaggauta bude makarantu kana dalibai su koma karatu.

Wannan na fitowa ne daga wata wasikar da ke dauke da sa hannun daraktan kudi na NUC, Sam Onazi a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed.

Jairdar Punch ta ce ta samu wasikar ne kai tsaye daga hukumar, inda aka umarci shuganannin jami'o'i da masu gudanar dasu da su koma bakin aiki.

Mudai ba muda abun cewa kawai namu ido da kuma bin umurni, amma dai bani tunanin hakan zai kawo karshen rikicin ASUU da gwamnatin Tarayya.

"Ni mai arziki ne domin ba gidan matsiyata na tashi ba, don haka babu abin da zanyi da kuɗin Jihar Katsina nazo ne domin...
23/08/2022

"Ni mai arziki ne domin ba gidan matsiyata na tashi ba, don haka babu abin da zanyi da kuɗin Jihar Katsina nazo ne domin na taimaku ku Al'ummar Jihar"~ Inji Ɗan takarar Gwamna Yakubu Lado yayin da yake zantawa da manema labarai a katsina.

YANZU-YANZU: Ban zama mataimakin Tinubu ba don k@re martaban musulunci da Musulmai, sarkin musulmi shike da hakkin kare ...
22/07/2022

YANZU-YANZU: Ban zama mataimakin Tinubu ba don k@re martaban musulunci da Musulmai, sarkin musulmi shike da hakkin kare martaban musulunci da Musulmai,

Babban Burina shine yin aiki domen kare mutunci Najeriya da yan Najeriya baki daya, ba tare da nuna bambancin addinanci ba, Cewar Kashim Shattima, a hirar a ayi da shi da wakilin Channels TV

YANZU-YANZU: An Kara Farashin Litan Man Fetur A Fadin Najeriya Gaba DayaA jihohin Arewa maso yamma ana sa ran yanzu za a...
19/07/2022

YANZU-YANZU: An Kara Farashin Litan Man Fetur A Fadin Najeriya Gaba Daya

A jihohin Arewa maso yamma ana sa ran yanzu za a rika sayar da litar fetur kan kudi Naira 184, Naira 189 a yankin arewa maso gabas.

Jaridar Daily Trust wacce ta ce ta samu tabbacin karin a Talatar nan, ta ce za a rika sayar da litar fetur a Naira 169 a Lagos, Naira 174 kuma a Abuja.

17/07/2022
07/07/2022

GADAR DA MAIGIRMA GWAMNAN JAHAR KATSINA YAKE GINAWA KENAN A KATSINA KOFAR KAURA...

YANZU YANZU: Yan takarar Gwamnan Jihar Sokoto Akar kashin Jam iyar APC sunkoma Jam iyar PDPHakan Yabiyo bayan Faduwa Zab...
26/06/2022

YANZU YANZU:

Yan takarar Gwamnan Jihar Sokoto Akar kashin Jam iyar APC sunkoma Jam iyar PDP

Hakan Yabiyo bayan Faduwa Zaben Fidda Gwani wanda Jam iyar ta gudanar Acikin watan dayawuce

MAJIGIRI SAI TSAYA TAKARAR DAN MAJALISSAR TARAYYA MASHI DA DUTSIAkwai yiyuwar Alhaji Salisu Yusufu Majigiri shugaban jam...
25/06/2022

MAJIGIRI SAI TSAYA TAKARAR DAN MAJALISSAR TARAYYA MASHI DA DUTSI

Akwai yiyuwar Alhaji Salisu Yusufu Majigiri shugaban jam iyyar PDP a yanzu kuma Wanda ya sha kaye a zaben fitar da Dan takarar gwamna a PDP, ya koma yayi takarar Dan majalisar tarayya a kananan hukumomin Mashi da Dutsi.
Majiyarmu a cikin jam iyyar PDP ta tabbatar mana yanzu haka tattaunawa tayi nisa akan hakan.
A tsarin Wanda yaci zaben takarar a PDP Alhaji sule Yusuf shabeji daga karamar hukumar Dutsi zai janye ya rubuta ma hukumar jam iyyar sa da hukumar zabe.su kuma jam iyyar zasu maye sunan sa da majigiri.
Wata majiya ta tabbatar mana har anyi hakan a satin da muke ciki.majiyarmu tace tsakanin talata zuwa Alhamis hedkwatar jam iyyar PDP ta kasa ta aika ma suna INEC da sunan Majigiri a matsayin chajin sule Yusufu. Bisa kaidar da dokar zabe ta tanada.
Wani na kusa da Majigiri ya tabbatar mana da labarin, cewa ana wannan maganar amma ba a kammala ta ba.
Yace Majigiri Dan siyasa ne, mai son jama arsa da cigaban su amma ba girman Mukami ba.
Yace majigiri yana neman ya zai kawo cigaba ne ga al umma ba wai wane girman mukami ba,shi ya sa muka Sanya ya amince da wannan tsarin.
Ya kara da cewa shima Wanda yaci zaben takarar Alhaji sule Yusufu ba ya shigo siyasa bane don mukami ya shiga ne don taimakon al umma .
Idan wannan takarar ta tabbata, majigiri zai shiga kundin tarihi.na yayi rike shugaban jam iyya,yayi takarar mataimakin gwamna.yayi ta gwamna.yanzu zai yi ta Dan majalisar tarayya.
Majigiri zai kara da Babban yaron shi a siyasa,Alhaji Mansur Ali mashi a jam iyyar APC. Mansur Ali mashi ya koyi horon siyasa ne a wajen Majigiri.
Don haka akwai yiyuwar a zaben 2023 a yi karon battar karfe tsakanin yaro da ubangidansa a zaben Dan majalisar tarayya na mashi da Dutsi.

HUKUMAR DSS NANEMAN WANDA YAYI WAKAR BATANCI GA MATAN KANNY WOODBiyo bayan wani korafi da wasu matan Kannywood s**a aike...
25/06/2022

HUKUMAR DSS NANEMAN WANDA YAYI WAKAR BATANCI GA MATAN KANNY WOOD
Biyo bayan wani korafi da wasu matan Kannywood s**a aikewa Shugaban MOPPAN na Kasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, mai taken: “KORAFIN CIN ZARAFI DA WANI MAWAKI MAI SUNA ‘SUFIN ZAMANI,” a cikin takarda, wadda tsohuwar jarumar fim Wasila Isma’il ta sanya wa hannu, a madadin Matan Kannywood, MOPPAN, a cikin gaggawa ta tsunduma cikin binciken korafin, daga bisani, ta rubutawa Hukumar DSS, domin ta yi abin da ya dace.

Bayan da MOPPAN ta aikewa hukumar ta DSS ne, hukumar ta yi nata ayyuka din, kana ta nemo gami da cafke mawakin.

A ranar Larabar nan 22 Yuni ne, hukumar ta kamo Sufin Zamani, kana kuma ta bayar da belinsa a ranar Alhamis (23 ga Yuni), bisa wadannan sharudda:

1. Zai yi bidiyo da Audio na ban hakuri da kuma karyata kansa game da wakar batancin da ya yi.

2. Zai yi waka kishiyar wacce ya yi, wato ya bi matan kannywood, ya fadi alherinsu kuma ya nuna masu zaman aure ne.

3. Zai rubutawa MOPPAN takardar ban hakuri

4. Zai rubutawa hukuma undertaking cewar ba zai kuma yin batanci ga duk wani dan fim ba.

5. Bayan yayi wannan kuma hukumar DSS za ta yi masa hukunci da ya dace, domin yayi musu karya a farkon kamun da aka yi masa.

Duk wannan ya biyo bayan amincewa da ya yi cewa ya aikata laifin.

Sa hannun
Al-Amin Ciroma
Kakakin MOPPAN na Kasa

LABARAN SAFIYA: Anbaiwa Gwamna Nasir El-rufa'i Sarautar GARKUWAN TALAKAWAN KADUNA
24/06/2022

LABARAN SAFIYA:

Anbaiwa Gwamna Nasir El-rufa'i Sarautar GARKUWAN TALAKAWAN KADUNA

YANZU YANZU: Gwamnatin Najeriya Ta Amince da Dukkan Kudurorin Dake a Takardar Yarjejeniyar Ta Shekarar 2009 Tsakaninta D...
23/06/2022

YANZU YANZU:
Gwamnatin Najeriya Ta Amince da Dukkan Kudurorin Dake a Takardar Yarjejeniyar Ta Shekarar 2009 Tsakaninta Da Hukamr ASUU.

yaune Gwamnatin Zata Zanta da ita Wannan Hukuma ta ASUU domin Tabbatar Masu da Amincewar.

Ana Sa Ran dai ASUU zata janye yajin aikin Cikin Lokaci Kankani daga yanxu

Daga KGF

Farin Jinin mutane ya sanya APC ta tsane ni a Katsina - Babba KaitaSanata mai Wakiltar Shiyyar Daura a Jahar Katsina, Sa...
23/06/2022

Farin Jinin mutane ya sanya APC ta tsane ni a Katsina - Babba Kaita

Sanata mai Wakiltar Shiyyar Daura a Jahar Katsina, Sanata Ahmed Babba Kaita yace farin jinin sa da mutane, a dalilin samar da ɗumbin romon Dimokuraɗiyya a Shiyyoyi uku na Jahar, shine ya zama dalilin da ake ƙyarar shi da tsana a Jahar.

Ahmed Babba Kaita yace a dalilin rashin iya hana shi karɓuwa daya ke samu a tsakanin Al'ummar Jahar, abin baƙin ciki ya zama dalilin daya sanya, kasancewar shi zaɓin Al'umma, ana cigaba gargaɗin shi ta hanyar nuna son Kai daga wasu ƴan tsirari a Jahar.

Sanata Babba Kaita ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, daya sanya wa hannu, mai

kwanan wata 21 ga watan Yunin shekarar 2022, daya aikewa Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmed Lawan, akan Ficewar sa daga Jam'iyyar APC.

Sanatan a cikin sanarwar yace "a matsayina na Sanata mai Wakiltar Katsina ta Arewa, na rubuto takardar nan, domin in sanar da fice wa ta daga Jam'iyyar APC zuwa Jam'iyyar PDP.

A cewar sa ya fita daga Jam'iyyar APC a dalilin Son kai, da kuma nuna wariya da masu ruwa da tsakin Jam'iyyar daga Gwamnatin Jahar suke nuna mashi, da Shuwagabancin Jam'iyyar a Jahar Katsina.

Sanata Ahmed Babba Kaita yace tuni ya samu gagarumar tarba da karɓuwa a tutar jam'iyyar PDP ta Jahar Katsina.

Source: KatsinaPost

Za'a Fara Sabbin Kwasa-kwasai 9 A Makarantar HUKHukumar da ke kula da tsarin Karatu da Tantance Kwasa-kwasai ta Najeriya...
22/06/2022

Za'a Fara Sabbin Kwasa-kwasai 9 A Makarantar HUK

Hukumar da ke kula da tsarin Karatu da Tantance Kwasa-kwasai ta Najeriya NCCE ta Tantance ƙarin wasu kwasa-kwasai guda tara da za’a fara karantar dasu a Makarantar Kimiyya da fasaha ta Hassan Usman (Hassan Usman Katsina Polytechnic).

Biyo bayan Ziyara da Duba bangaren sabbin Kwasa-kwasan, d wakiliyar NCCE daga Babban Ofishin hukumar daga Abuja da ‘yan tawagar ta s**a yi, inda s**a duba sabbin gine-gine da kayi a makarantar gami da jinjinawa yanda ake

gudanar da karatu da bada wasu shawarwari d zasu taimaka domin cigaban Ilimi a jihar Katsina da ma ƙasa baki daya.

Da yake maida jawabi, a madadin Hukumar gudanarwar ta makarantar Hassan Usman Katsina Polytechnic, Dakta Mudi Kurfi, ya godewa hukumar, kwarai da gaskiya na irin yanda makarantar ta samu kyakkyawar kulawa da bada shawarwari da zasu amfani makarantar da ɗalibai, inda ya sha alwashin dauka da aiki da duk wata Shawara da hukumar ta bada, domin fara karatun sabbin Kwasa-kwasan a kan lokaci.

Source: Katsina Post

JUST IN: Kotu Ta Kwace Madallacin Juma a Na Shaik Mahmud Adam dake a Kano.Babbar kotun Jihar Kano mai lamba 5 a jiya Lit...
21/06/2022

JUST IN:

Kotu Ta Kwace Madallacin Juma a Na Shaik Mahmud Adam dake a Kano.
Babbar kotun Jihar Kano mai lamba 5 a jiya Litinin ta garkame gami da kwace masallacin Juma’ar Unguwar Sabuwar Gandu, inda marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ke limanci daga Hannun Kungiyar Izala ta mika wa kungiyar cigaban unguwar.

JUST IN: Shugaba Muhammad Buhari yanada sababbin MinistociBuhari ya nada sababbin ministociShugaban Najeriya Muhammadu B...
21/06/2022

JUST IN:

Shugaba Muhammad Buhari yanada sababbin Ministoci

Buhari ya nada sababbin ministoci
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sababbin ministoci bakwai domin maye gurbin wadanda s**a sauka da wadanda ya sauke daga kan mukamansu.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan ne ya karanto sunayen sababbin ministocin da Shugaba Buhari ya aike wa majalisar a zaman da ta yi ranar Talata.
Sabbin ministocin sun hada da Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano, Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Henry Ikechukwu Iko (Abia), Ademola Adegoroye (Ondo), Odum Odi (Rivers).
Sauran su ne Goodluck Nnana Opia (Imo) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi ).
Sanata Lawan ya ce nan gaba za su tantance ministocin da aka mika musu domin tabbatar da su ko kuma akasin haka.
A watan Satumbar 2021 ne Shugaba Buhari ya sauke Ministan harkokin Gona, Alhaji Sabo Nanono da Ministan Ma'aikatar Lantarki, Injiniya Saleh Mamman ba tare da bayyana wani dalili ba.
Kazalika a watan jiya ya umarci ministocinsa da ke son tsayawa takarar siyasa su sauka daga mukamansu.
Ya bayar da umarnin ne domin yin biyayya ga dokar kasar da ta bukaci masu rike da mukaman gwamnati su ajiye aiki kafin su tsaya takara.
Ministoci da dama sun sauka daga mukamansa, sai dai daga bisani wasu sun janye inda s**a koma bakin aiki.
Ministocin da ba su koma kan kujerunsu ba sun hada da Rotimi Amaechi, tsohon ministan Sufuri; Ogbonnaya Onu, tsohon ministan Kimiyya da Fasaha; Godswill Akpabio, tsohon ministan Neja Delta da kuma Emeka Nwajiuba, tsohon ministan, tsohon karamin ministan Ilimi.

20/06/2022

News

20/06/2022

News

19/06/2022

News

18/06/2022

News

18/06/2022

News

17/06/2022

News

17/06/2022

News

17/06/2022

News

16/06/2022

News

Address

Tudun Matawalle
Katsina
821012

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Media News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Media News:

Videos

Share



You may also like