10/06/2022
*Takaitaccen Tarihin Imam Aliyu Bn Musa (A.S)*
*🌲UMMU ABEEHA GROU ام ابيها🌳*
*SUNA DA NASABARSA (A.S):*
Sunansa shi ne Aliyu bn Musa bn Ja’afar bn
Muhammad bn Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi
Talib (a.s).
*MAHAIFIYARSA (A.S):*
Wata kuyanga ce da ake kiranta Najma,
wasu kuma suna kiranta da wani sunan.
*ALKUNYARSA (A.S):*
Abul Hasan, Abu Ali da sauransu.
*LAKABINSA (A.S):*
Al-Ridha, Al-Sabir, Al-Radhi, Al-Wafi, Al-
Fadhil da sauransu.
*TARIHIN HAIHUWARSA (A.S):*
An haife shi ne a ranar 11 ga watan
Zil’Ka’ada shekara ta 148 bayan hijira, akwai
kuma wasu maganganu na daban kan
lokacin haihuwar nasa (a.s).
*WAJEN HAIHUWARSA (A.S):*
Birnin Madina.
*MATANSA (A.S):*
1. Kuyangar da ake kiranta da Sukaina al-
Marsiyya, wasu kuma suna kiranta da Al-
Khaizaran.
2. Umm Habib bint Ma’amun.
*‘YA’YANSA (A.S):*
1. Imam Muhammad al-Jawad (a.s).
2. Al-Qani'i
3. Ja’afar.
4. Ibrahim.
5. Al-Hasan.
*RUBUTUN HATIMINSA (A.S):*
Ma Sha’Allah La Quwata illa billah.
*SHEKARUNSA (A.S):*
Shekaru 55.
*SHEKARUN IMAMANCINSA (A.S):*
Shekaru 20, wasu kuma suna ganin sabanin
hakan.
*SARAKUNAN ZAMANINSA (A.S):*
1. Harun al-Rashid.
2. Al-Amin.
3. Al-Ma’amun.
*LOKACIN SHAHADARSA (A.S):*
Karshen watan Safar, shekara ta 203, wasu
kuma suna ganin sabanin hakan.
*WAJEN SHAHADARSA (A.S):*
Tus, a Khorasan - Iran.
*DALILIN SHAHADARSA (A.S):*
Ya yi shahada ne sakamakon guban da aka
sanya masa lokacin mulkin halifan
Abbasiyawa Ma’amun.
*KABARINSA (A.S):*
Khorasan (Masshad) – Iran.