21/09/2024
MANZON ALLAH NE SAMFURI ABIN KOYI DON SAMUN MAFITA
- Inji Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin jawabin ranar Mauludin bana a Abuja
Daga Ofishin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
“Manzon Rahma (S) shi ne mafi kyawun alami da aka ajiye domin a kwafa. Shi ne samfur wanda kowane zai kwafa. Allah Ta’ala yana cewa: “Kuna da kyakkyawan misali ga Manzon Allah, ga mai kaunar Allah da ranar Lahira.” Wato wanda yake tunanin gamuwarsa da Allah a gobe kiyama, to ya san cewa wannan Manzo shi ne kyakkyawan misali (abin koyi).”
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabin Mauludin Manzon Allah (S) a gaban dimbin al’umma a ranar Juma’a 17 ga Rabi’ul Auwal 1446 (20/9/2024) a garin Abuja.
Shaikh Zakzaky ya kara da bayyana cewa: “Canjin dabi’a shi ne muhimmin abu, kuma shi ke gabanmu, wanda kuma shi ke da wahala. Ka zama mutumin kirki, kana da kyakkyawan misali ga Manzon Allah, shi ne abin koyi. Duk cikanmu ba wanda zai zama kamar shi, ballantana ya fi shi, amma za a dauke shi amatsayin abin koyi kuma abin kwafa.”
Ya kara da cewa: “Lokacin da muke batun hadin kai, batun kawo Annabi (S) a matsayin ‘ramzi’ shi ne babba, saboda shi (Annabi) ne kyakkyawan ‘ramzin’ da za a yi koyi da shi domin haduwa akan abu guda. Duk mu hadu muce waye shugabanmu, jagoranmu; Manzon Rahma (S).”
Yace: “Daidai wannan lokaci, abin da muke karfafa junanmu gabadaya shi ne, mu hadu akan abu guda, sunanmu Musulmi, sunan addininmu Islam, sunan Manzonmu Muhammad (S), abin da ya zo da shi shi ne addini, yarda da abin da ya zo da shi shi ne Musulunci, shi ne kuma za mu tsaya a kai kyam, kuma insha Allahul Azeem tabbas abin nan da suke gudu na tabbatan addini, addinin nan fa zai tabbata! Saboda mene? alkawari ne na Allah, Allah kuma baya saba alkawari.”
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa, mutane su gama duk kewaye-kewayen neman mafitansu a wurare, a karshe za su dawo ga inda mafitan na hakika yake. “Karshe za ku zo kuce ina mafita? Sai mu ce, to dama mun fada muku, mafita shi ne sakon da Allah ya aiko Manzonsa da shi.” Ya jaddada.
A wani bangaren jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya yi tsokaci akan wautan ‘yan sanda bayan budewa taron Arba’in din Imam Husaini (AS) na bana wuta da s**a yi a Abuja. Yace: “wanda s**a yi na kwanan nan, wanda yake dariya zai baka ko mamaki ne ma, don wautan ta cika yawa, shi ne, yadda aka ce, wai folisawa sun ce, wai su wadannan masu jajen sun far musu, wai har sun kashe mutanensu.”
Shaikh Zakzaky yace: “To na san an yi rubuce-rubuce da bayanai (akan hakan a baya), amma abin da nake cewa shi ne, ni abin da na sani, wannan Harkar (ta Musulunci) mun fara ta tun karshen saba’inoni, na tabbatar kuma wanda yake yin I.G yanzu haka a lokacin (da muka fara Harkar) kila yana Firamare ne ma. Kuma wanda yake Kwamishinan ‘Yansanda shi ma kila bai shiga ko Firamare ba. Kuma da yawan ‘yan sanda ko haihuwarsu ma ba a yi ba, don da yawansu ‘yan kasa da shekara 40 ne, kowannensu ya bude ido ne ya gammu muna wannan abin. To yaushe rana tsaka za su canza mana, su ce wani abu muke yi?”
Yace: “Illa iyaka in kwangila aka baka, sai ka yi ka karbi abinka, amma ba yadda za a yi ka iya canza wai duban da ake yi mana, hatta a Abuja, ballantana a duniya, wanda Harkar da muke yi tun kafin a gina Abuja.”
Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda ‘yan sandan bayan sun dirarwa ‘yan uwa, s**a kuma bayyana a fili suna fada da addinin Musulunci ne. Yace: “Sun yi wani abu wanda ya nuna baro-baro suna adawa ne da addinin Musulunci; shi ne cire wa mata hijabi. Don shi Hijabi umuni ne na Allah Ta’ala a ayoyin Alkur’ani daban-daban, kuma Sunnah ta tabbatar da shi, kuma ba wani wanda ke musu dangane da matsayin shi a tsakanin Musulmi. Kuma akan cire wa mace Hijabi aka yi rigimar farko (tsakanin Musulmi) da Yahudawan Banu Qainuka (a Madina).”
Ya kara da cewa: “In kuka yi fada da Hijabi, kun yi fada da addinin Muslunci ne, ba da wadansu mutane ba. Da addinin Musulunci ne gabadayansa kuke fada, da Alkur’ani kuke fada, kuma duk Musulmin duniya ya san cewa kuna fada da addini ne.”
Jagora, ya yaddada cewa: “Wannan lokaci namu, lokaci ne da ya kamata ba al’ummar Musulmi kawai ba, dukkanin mutane ya zama sun shiga hankalinsu, su gane meye mafita gare su. Ya zama sun fahimci cewa, in ma za ka rayu ne a doron kasa, baka dauka ma gwadaka ake ba, ka dauka ma nan ne wajen zama, to zaman ma da wahala, kuma wadansu mutane sun dauka ma kansu su saka ku a cikin wahaloli domin su su ji dadi. Kuma lallai dole ka yi tunanin to ina mafita? To ballantana mu da muka san cewa mun zo gidan gwaji ne, ana gwada mu ne, ana kuma gwada mu da juna ne. Mun san cewa lazim ne muna da mafita, mafitan nan kuma shi ne wannan sakon na Allah Ta’ala, wanda ya aiko wannan Manzo. Sakon karshe, dauke da addini cikakke, da shari’a cikakkiya, wanda ba za a yi wata shari’a ta zo ta wuce ta ko ta yi daidai da ita ba, ballantana ace ta fi ta. Ita ce kawai mafita.”
Ya karkare da fata Allah Ya hada kan al’ummar nan a karkashin La’ilaha ilallah. Tare da addu’ar “Allah Ya nuna mana lokacin da tutar La’ilaha illallah za ta filfila a kasar nan, har ya zama komai za a yi sai an ce Allah Ya ce, Manzonsa Ya ce.”
18/RabiuAwwal/1446
20/09/2024