
23/01/2025
NEMAN NA TUWO: An K**a Tsohon Inspector Na ’Yan Sanda Yana Aiki Duk Da Ya Yi Ritaya
An k**a Linus Monday, tsohon ɗan sanda mai mukamin Inspector kuma ɗan Najeriya, bisa laifin gudanar da bincike kan ababen hawa duk da cewa ya riga ya yi ritaya daga aikin ɗan sanda.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon jami’in ya ci gaba da gudanar da aikin bincike na tsayawa da duba mutane ba tare da izini ba, lamarin da ya jawo hankalin hukumomi har ya kai ga nasarar samun cafke shi.
Hukumar ’yan sanda tana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin don gano ainihin dalilan da s**a sa tsohon ɗan sandan ya ci gaba da wannan aiki bayan ritayarsa.
📷 ATP Hausa