14/05/2020
SHUGABANNIN DA BA SA SANYA TAKUNKUMI.
Abin rufe baki da hanci ko takunkumi, yanzu ya kusan zama wani abin da mutane s**a saba da shi musamman a ƙasashen da aka tilasta amfani da shi, ɗaya daga cikin matakan kariya daga kamuwa da cutar korona, annoba a duniya.
Sai dai duk da tilasta amfani da takunkumin da wasu gwamnatocin ƙasashe s**a yi, amma akwai shugabannin da ba a gani sanye da takunkumin a duk lokacin da s**a fito bainar jama'a.
Kuma shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari da Firaministan Birtaniya Boris Johnson suna cikin shugabannin da ba a taba ganinsu sanye da takunkumi ba.
Ko da yake Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce takunkumin yana hana yaɗuwar cutar korona amma kuma ba wata babbar kariya ba ce ga hana kamuwa da cutar.
Watakila shi ne dalilin da ya sa shugabannin ba su damu da saka takunkumin ba, duk da sun umurci al'ummar kasarsu su dinga sakawa.
A jawabinsa na uku ga 'yan Najeriya kan cutar korona, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da ganin ana amfani da takunkumi ko abin rufe fuska a bainar jama'a da kuma ci gaba da ba da tazara da tsaftar jiki.
Shugaban na Najeriya ya kuma buƙaci gwamnatocin jihohi da kamfanoni da masu zuciyar taimakawa jama'a su tallafa wajen samar da takunkuman ga al'ummar ƙasa. Amma ba a taba nuna shugaba Buhari sanye da takunkumin ba domin koyi da shi.
Akwai hoto da na bidiyo da aka nuna shugaban yana wanke hannayensa - ɗaya daga cikin matakan kariya daga kamuwa da cutar korona da ake son a dinga yi a ko da yaushe.
Amma batun saka takunkumin ya janyo mahawara a shafin Facebook na BBC Hausa inda wasu ƴan ƙasar ke yaba wa da umurnin saka takunkumin, wasu kuma ke ganin ya kamata ace an yi koyi da shugaban.