Majingina

Majingina Ku kasance da jaridar majingina domin kawo muku sahihan labarai don sanin halin da duniya take ciki.

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Fulani Ta Cikin Shirin 'Labarina' Ta Raau
25/12/2025

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Fulani Ta Cikin Shirin 'Labarina' Ta Raau

Waɗannan su ne fuskokin wasu daga cikin ’yan’uwa da s**a rasa ransu a harin masallaci a Jihar Maiduguri. Sun je Sallah d...
25/12/2025

Waɗannan su ne fuskokin wasu daga cikin ’yan’uwa da s**a rasa ransu a harin masallaci a Jihar Maiduguri. Sun je Sallah domin bautar Ubangijinsu, wasu kuma sun kashe su ba laifin fari b***e na baki.

Muna addu’ar Allah Ya jikansu da rahama, Allah Ya karɓi shahadarsu. Wadanda s**a samu raunuka Allah ya ba su lafiya. Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan musiba ta kashe-kashe ba gaira ba dalili. Ameen.

Da Karatun Diwani Shehu Ya Cika - Sayyada Aisha Matar Ɗahiru Bauchi Lokacin da naga ciwo ya tsananta ga Shehu Sai na k**...
30/11/2025

Da Karatun Diwani Shehu Ya Cika - Sayyada Aisha Matar Ɗahiru Bauchi

Lokacin da naga ciwo ya tsananta ga Shehu Sai na k**a karanta mishi Diwani k**ar yadda na saba a tsawon lokaci, ina karanta baitocin ina tofa mishi yana bisa cinya ta har ya cika!

Sayyada Aisha ta bayyana hakan ne a yayin tattaunawar da gidan rediyon BBC Hausa ya yi da ita

TIRKASHI: Rundunar Hisbah ta k**a saurayi da budurwa suna goge raini har ya ɗirka mata ciki a DandumeHukumar Hisbah ta g...
21/11/2025

TIRKASHI: Rundunar Hisbah ta k**a saurayi da budurwa suna goge raini har ya ɗirka mata ciki a Dandume

Hukumar Hisbah ta garin Dandume tayi nasarar k**a saurayi da budurwa suna sharholiyya har ta kai ga an samu juna biyu a jikin ta daga hira.

A ranar alhamis din ds ta gabata hukumar hisbah ta karamar hukumar Dandume ta gudanar da wani oppression cikin sirri karkashin jagorancin Malam Aliyu Ahameda, Inda tasamu nasarar cafke wani matashi Dan asalin Jihar Kaduna da ya ke zuwa wajen wata budurwa hira yana yin lalata da ita Wanda a karshe dai har yayi mata ciki yanzu haka Yana hannun jami an hukumar ta hisbah Domin cigaba da bincike

Fuskokin Wasu Daga Cikin Dalibai Mata Da Aka Sace A Garin Maga Dake Jihar Kebbi, Ciki Har Da Guda Hudu Yaran Mutum DayaA...
19/11/2025

Fuskokin Wasu Daga Cikin Dalibai Mata Da Aka Sace A Garin Maga Dake Jihar Kebbi, Ciki Har Da Guda Hudu Yaran Mutum Daya

Allah Ya kubutar da su.

Allah ya yi wa Malam Tanimu  na shirin Dadin Kowa rasuwa yau.Marubuta shirin Zuwairiyya Admu Girei da Fauziyya D. Sulaim...
17/11/2025

Allah ya yi wa Malam Tanimu na shirin Dadin Kowa rasuwa yau.

Marubuta shirin Zuwairiyya Admu Girei da Fauziyya D. Sulaiman sun tabbatar da rasuwar.

Allah yaji kansa ya gafarta masa amin

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun kakakinta, SP Josephine Adeh, an bayyana cewa babu wani tushe ko sha...
17/11/2025

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun kakakinta, SP Josephine Adeh, an bayyana cewa babu wani tushe ko shaida da ke tabbatar da wannan iƙirari. Rundunar ta kara da cewa, duk wasu labarai da ke yawo a yanar gizo game da harin ba gaskiya ba ne kuma jama’a su daina yada labarai marasa tushe.

Rundunar ƴansandan ta kuma jaddada cewa tana ci gaba da tabbatar da tsaro a birnin Abuja, tare da saka idanu kan duk wani abu da ka iya kawo rikici ko barazana ga rayuwar jama’a.

Da dumi-dumi: Rahotanni sun tabbatar da majiyar soji sun tabbatar mata cewar wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya a cikin w...
16/11/2025

Da dumi-dumi: Rahotanni sun tabbatar da majiyar soji sun tabbatar mata cewar wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya a cikin wasu motoci ƙirar Hilux da basu da lamba sun yi ta bibiyar Yarima daga gidan man NIPCO zuwa babbar hanyar Gado Nasco dake Abuja a yammacin yau!

YANZU-YANZU; Wata babbar mota ɗauke da dabbobi ta faɗo daga saman gadar Hotoro da ke Kano, dabbobin da suke cikinta ragu...
16/11/2025

YANZU-YANZU; Wata babbar mota ɗauke da dabbobi ta faɗo daga saman gadar Hotoro da ke Kano, dabbobin da suke cikinta raguna da akuyoyi sun tarwatse a ƙasan gadar.

Kawo yanzu dai babu labarin asarar rai a hatsarin. Allah ya kiyaye gaba.

Ku yi following ɗin jaridar Majingina domin samun ingantattun labarai masu ƙayatarwa.

ABIN MAMAKI: Yadda Aka K**a Fasto da Zargin Kai wa 'Yan Bindiga Mak**ai a Jihar Filato.Najeriya ta shiga wani sabon babi...
16/11/2025

ABIN MAMAKI: Yadda Aka K**a Fasto da Zargin Kai wa 'Yan Bindiga Mak**ai a Jihar Filato.

Najeriya ta shiga wani sabon babi mai ban al’ajabi — Inda aka k**a wani malamin addinin kirista (Reverend Father) da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga muggan mak**ai a Jihar Filato da kewaye.

Eh, ka karanta daidai.
Wani limamin coci — wanda aka yarda da shi a matsayin mai addu’a, zaman lafiya da kare rayuka — yanzu ana zarginsa da taimakawa waɗanda ke hallaka al’umma marasa laifi.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun gano yana *tsara safarar mak**ai iri-iri*, wanda ake zargi da taimakawa 'yan ta'adda wajen sace mutane, kai hari da kashe-kashe.

Yanzu sai na sake tambaya...

Lokacin da wasu daga cikinmu s**a ce *matsalar tsaro a Najeriya ba ta addini bace*, mutane s**a ci mutunci, suna cewa muna goyon bayan mugunta.

Amma yanzu, me za su ce?

Shin waɗanda s**a yi gaggawar garzayawa Amurka suna kiran abun “kisan kiyashi ga Kiristoci” za su kai wannan labari wajen Donald Trump domin daidaita labarin?

Domin gaskiya ita ce:

Tsaro a Najeriya ba ya da addini.
(1) Ba ya sanye da zobon saliba ko tesbihu.
(2) Ba ya rike Alƙur’ani ko Littafi Mai Tsarki.
(3) Yana buya a daji, yana sayen mak**ai, yana halaka rayuka — Musulmi, Kirista, kowa.

Amma duk lokacin da aka fadi gaskiya, mutane kan mayar da martani da ji ba da hankali ba.

Wannan k**a ta bayyana gaskiya mai zurfi:

(1) Matsala laifi ce, ba addini ba.
(2) Mugaye suna ko’ina — a coci, a masallaci.
(3) Kuma yaƙi yana da su ne, ba da addininsu gabaɗaya ba.

Idan har Reverend Father za a k**a da kai wa 'yan bindiga mak**ai, to watakila... matsalar Najeriya ta fi “kisan kiyashi a ɓangare guda” girma da rikitarwa.

Mu kira gara gari.
Mu gyara matsalar tsaro — ba mu juya ta ta zama siyasa ko neman tausayi daga ƙasashen waje ba.

Daga: Abdul Mdk

ABIN MAMAKI: Baŕawo Ya Shiga Har Cikin Fadar Gwamnatin Kano Ya Saci MotaMajiyarmu ta bayayyna cewa motar da aka sace, ta...
11/11/2025

ABIN MAMAKI: Baŕawo Ya Shiga Har Cikin Fadar Gwamnatin Kano Ya Saci Mota

Majiyarmu ta bayayyna cewa motar da aka sace, tana daya daga cikin ayarin motocin mataimakin Gwamnan Kano.

TIRƘASHI: Akwai Bukatar Wike Ya Baiwa Shugaban Kasa Da Rundunar Sojoji Hakuri Kan Abinda Ya Hada Shi Da Jami'in Sojan Na...
11/11/2025

TIRƘASHI: Akwai Bukatar Wike Ya Baiwa Shugaban Kasa Da Rundunar Sojoji Hakuri Kan Abinda Ya Hada Shi Da Jami'in Sojan Nan A Abuja, Cewar Janar Buratai

Me zaku ce?

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Majingina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share