Zirnaniya

Zirnaniya Zirnaniya is an online News,Broadcasting, religious and entertainment channel.
(1)

A YAU Talata ne, za a rantsar da sabon zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, inda zai fara mulki.Mista...
02/04/2024

A YAU Talata ne, za a rantsar da sabon zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, inda zai fara mulki.
Mista Faye ya yi nasara da kashi 54 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben da aka jinkirta a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam'iyyu masu mulki.
A ranar Juma'a ne Kotun Kolin kasar ta yammacin Afirka, ta tabbatar da Mista Faye a matsayin wanda ya ci zaben na ranar 24 ga watan Maris 2024.
Ana sa ran gudanar da bikin ne a cikin wani zauren taro da ke wajen babban birnin kasar ta Senegal, Dakar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO zai kasance cikin shugabanni kusan 15 da za su halarci bikin a yau Talata.

Sauyin shugabancin bai kasance na kai tsaye salin-alin ba, daga Shugaba Macky Sall mai barin-gado zuwa ga Shugaba mai jiran-gado ba, Diomaye Faye.
Kafin a kai ga zaben, kasar ta yi fama da tarzoma mummuna bayan da Shugaba Sall ya yi yunkurin jinkirta zaben.
A da ya kamata a yi shi ranar 25 ga watan Fabarairu amma ya dage shi zuwa watan Disamba, abin da Kotun Kolin kasar ta haramta.
Bugu da kari shugaban mai jiran-gado, ya shaki iskar ‘yanci ne daga kurkuku ‘yan kwana 10 kafin zaben, albarkacin afuwar gwamnati.
A jawabin da ya gabatar na nasarar da ya samu a cikin harshen Faransanci da kuma Wolof, Faye ya ce abin da zai ba fifiko a mulkin nasa shi ne, sasanta al’ummar kasa, da kokarin samar da saukin tsadar rayuwa da yaki da rashawa.
Ya kuma yi alkawarin wanzar da salon mulki na ‘yan gaba-da-gaba-dai, wato ra’ayin sauyi na dunkulalliyar Afirka, domin mayar da kasar kan turbar ‘yancin kasar da ya ce an cefanar a rahusa.
Haka kuma ana ganin zai nemi sauya kudin kasar daga CFA da kasar ke amfani da shi a yanzu.
Zai kuma yi kokarin mayar da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar, cikin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO.
Mutane da dama a kasar ta Senegal na daukar, Mista Faye, wanda zai kasance shugaba mafi karancin shekaru a Afirka, inda yake da shekara 44, a matsayin wata alama ta kyakkyawan fata.

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu ya musanta bayanan dake kunshe a cikin rahoton hukumar kula da basuss**a ta Naj...
02/04/2024

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu ya musanta bayanan dake kunshe a cikin rahoton hukumar kula da basuss**a ta Najeriya cewa gwamnatinsa ta ƙarɓi bashin kimanin naira biliyan 89 a cikin gida da kuma kusan dala miliyan talatin da bakwai daga waje.
Gwamnan ya ce bai ci bashin ko sisin kwabo ba a cikin wata goman da ya yi yana gwamna, "Ko tsakanin mutum da mutum za a ƙarbi bashi akwai yarjejeniya b***e bashin da ya shafi gwamnati, kuma ana bin dokar zuwa majalisa kafin a anso bashin amman mu ba mu yi ko wanne ba."
Alhaji Ahmed Aliyu ya ce rahoton ƙarya ne bai da asali bai da tasiri, kuma yana kira ga dukkan wanda ya ce ya ci bashi ya zo ya bada shaidar hakan," Idan ma an yi domin a ɓata mani suna ne, hakan bai shiga ba saboda a matsayina na gwamnan jihar Sokoto tun lokacin da na anshi mulki ina biyan albashi 18 ko 19 ko 20 ga wata."
Gwamnan ya bayyana cewa ba wai yana nufin ba zai ci bashi a nan gaba ba, amman dai a halin da ake ciki bai ci bashi ba, kuma babu wani dan kwangila da ke binsu bashi.

Ramadan day 23, Allah ya karbi idadun mu.
02/04/2024

Ramadan day 23, Allah ya karbi idadun mu.

Allah ka sa muna Cikin yantattun bayinka. Allaahumma innaka 'afuwwun, tuhibb al-'afwa, fa'fu 'anni'.
31/03/2024

Allah ka sa muna Cikin yantattun bayinka.
Allaahumma innaka 'afuwwun, tuhibb al-'afwa, fa'fu 'anni'.

Ramadan day (20) Allah ya karba mana ibadun mu , Allah ka sa muga karshen sa lafiya. Amin.
30/03/2024

Ramadan day (20) Allah ya karba mana ibadun mu , Allah ka sa muga karshen sa lafiya. Amin.

27/03/2024

60 seconds · Clipped by ZirnaniyaTV+AFRICA · Original video "LABAREN MU NA YAU 25 MARIS 2024 ||Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji"...

Ramadan Day 17. Allah ya harbi ibadun mu
27/03/2024

Ramadan Day 17. Allah ya harbi ibadun mu

25/03/2024

Zaku iya bibiyar mu a safin mi na what'sapp

Follow the Zirnaniyatvplus channel on WhatsApp:

25/03/2024

https://youtu.be/YvSGWOqu9M0?si=zmVZXlUniJSV9Wm6

- Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin s**a koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya.

Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.

Ramadan day 15, Allah ya karbi ibadun mu
25/03/2024

Ramadan day 15, Allah ya karbi ibadun mu

Wannan shine Mutumin da ake kira "Mai Makara" Wanda Yake Bi Garuruwan Arewa Wanda  Ta'addanci ke addaban su.idan ya je g...
24/03/2024

Wannan shine Mutumin da ake kira "Mai Makara" Wanda Yake Bi Garuruwan Arewa Wanda Ta'addanci ke addaban su.idan ya je garin sai ya sa a Haka Kabari bayan an haka sai ya saka Sai Alqur'ani Da Likafani A Ciki kabarin Ya Kona.

Dalilin sa na yin hakan shine wai "duk garin da ya yi wa haka to wannan garin ya fi karfin 'yan ta'adda, ko sun zo garin ba za su iya cutar da kowa ba kuma ba za su iya daukar kowa ba.

Menene ra'ayin ku akan hakan?
shin ya dace a dinga kona Alqur'ani ancikin kabari tare da lakafani domin kauda ta'addanci?
Ko Kuna ganin wannan hanya ita ce mafi dacewa da kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa?

22/03/2024

AL'UMMA NA GUDUN HIJIRA A JIHAR ZAMFARA. SHIN MENE DALILIN HAKAN?

A Najeriya, 'yan bindiga na kara matsa kaimi a har-haren da suke kaiwa wasu garuruwan JANGEBE da MAGAZU na jihar Zamfara, inda suke sace mutane don neman kudin fansa, bayan sun aikata kisan gilla da barnata dukiyoyin jama'a.

Matsalar hare-haren 'yan bindiga da ta addabi al'ummar garin Jangebe da wasu kauyukansa akalla biyar, a yankin karamar hukumar TALATAR MAFARA Da ke jihar Zamfara, Wanda ya ke kara ta’azzara.

A cewar wani mutumin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun daga ranar talata har zuwa laraba, kauyukan JANGEBE biyar zuwa shida suna cikin iftila’in kashe-kashe.

RAMADAN DAY 12
22/03/2024

RAMADAN DAY 12

21/03/2024

A daren ranar Asabar sojojin Najeriya su ka sanar da nasarar dakile yunkurin sace mutane 16 daga yankin KAJURU mai fama da matsalar tsaro a jihar Kadunan arewa maso yammacin kasar.

Sai dai a wannan daren, 'yan ta'addar sun kai hari a dai yankin na Kajuru tare da sace gwamman mutane.
Makwanni biyu da s**a gabata, arewacin Najeriya ya fuskanci sace-sacen mutane akalla sau shida .

21/03/2024

TAMBAYOYI DA AMSOSHIN SU TARE DA| Prof. Isa Ali Pantami, CON

21/03/2024

MU KYAKYATA TARE DA

21/03/2024

https://youtu.be/F8JCN5NWOJw

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta gurfanar da tauraruwar finafinan Kannywood Amal Umar a gaban kotu bayan ta yi yunƙurin bai wa wani jami'inta cin-hanci.

Rundunar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Nijeriya Shiyya ta Ɗaya da ke Kano Bashir Muhammad da ya gabatar ranar Labara a birnin na Kano.

Majalisar dattijai ta amince da wani kudirin doka da ke neman a kafa asusun tallafawa masu yi wa kasa hidima (NYSC).Ƙudu...
21/03/2024

Majalisar dattijai ta amince da wani kudirin doka da ke neman a kafa asusun tallafawa masu yi wa kasa hidima (NYSC).

Ƙudurin dokar wanda Sanata Yemi Adaramodu ne ya dauki nauyinsa na neman samar da dorewar samun kuɗi ga hukumar ta NYSC da koyon sana’o’i da horarwa da karfafawa ‘yan kungiyar kwarin gwiwa da sake horar da ma’aikatan hukumar da kuma bunƙasa sansani mai inganci.

Adaramodu yayin da yake zantawa da manema labarai bayan zartar da ƙudurin dokar ya tabbatar da cewa idan aka sanya hannu kan dokar, ba za a ci zarafin hukumar ta NYSC ba kamar sauran shirye-shiryen shiga tsakani da ake yi.

An bude shagon shan barasa a kasar Saudiyya, irinsa na farko a tsawon shekarau 70.An dai takaice shagunan ne ga jami'an ...
21/03/2024

An bude shagon shan barasa a kasar Saudiyya, irinsa na farko a tsawon shekarau 70.

An dai takaice shagunan ne ga jami'an huldar jakadancin kasashe da ke Saudiyyar.

Ana dai yi wa wannan mataki kallon wani kokari a kasar da ta haramta sayar da shan barasa tun shekarar 1952.

Tun dai a watan Janairu ne kasar ta sanar da cewa za ta bude shagunan sayar da barasa ga wasu kayyadaddun mutanen da ba Musulmi ba a birnin Riyadh.

Yanzu dai jama'a na dasa ayar tambaya ga yunkurin kasar ta Saudiyya, inda suke neman sanin ko dai akwai yiwuwar kara fadada damar shan barasa a kasar fiye da takaice shi ga jami'an huldar jakadanci?

Menene ra'ayin ku?

21/03/2024

KA TUNA DA YARANTAR KA.

Jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu jihohi hudu na arewa sun kashe naira biliyan 28 kan ciyar da talakawa abinci a w...
20/03/2024

Jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu jihohi hudu na arewa sun kashe naira biliyan 28 kan ciyar da talakawa abinci a watan azumin Ramadana.

Shin wadannan kudade na kaiwa ga mutanen da s**a dace kuwa?

Muna jiran amsoshin ku.

20/03/2024

Gwamnatin Najeriya ta sa hannu kan wata yarjejeniyar gina cibiyar samar da wutar lantarki mai amfani da ruwa da hasken rana da za ta samar da wuta mai ƙarfin megawatt 20.

Shirin samar da lantarki mai ƙarfin megawatt 300 wani ɓangare ne na ƙudurin Najeriya na komawa ga amfani da makamashi mara gurɓata muhalli.

Za a gina cibiyar a Shiroro da ke jihar Neja a tsakiyar Najeriya kuma zai zama shirin haɗin gwiwa tsakanin kamfanin NSP mai zaman kansa da hukumar NSIA mai bibiyar harkokin gwamnatin a Najeriya.

"Wannan wani shiri ne na farko na samar da lantarki mai amfani da hasken rana da ruwa," in ji mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Ya ƙara da cewa shirin zai taimaka wa Najeriya ta faɗaɗa hanyoyin da take amfani da makamashi.

Najeriya dai na fama da matsalar rashin tsayayyiyar wutar lantarki tsawon shekaru duk da kasancewarta babbar mai samar da iskar gas da man fetur.

Lamarin yana yawan janyo matsala a babban layin da ke samar wa ƙasar wuta tare da jefa jama'a cikin duhu.

Galibin mutane a yanzu suna komawa amfani da injin janareto da wutar sola mai amfani da hasken rana domin kaucewa yawan dogaro ga babban layin wutar da ke yawan fuskantar matsala.

20/03/2024

BARKAN MU DA SHAN RUWA. MUSHAKATA DA KANO PILLARS

20/03/2024

Tambaya da Amsa| Hausa| Prof. Isa Ali Pantami, CON

YAU RANAR FARIN CIKI TA DUNYA. ME TINUBU YA KAMATA YA YI DON YA SAKA KU FARIN CIKI?
20/03/2024

YAU RANAR FARIN CIKI TA DUNYA. ME TINUBU YA KAMATA YA YI DON YA SAKA KU FARIN CIKI?

20/03/2024

Idan ka cire kisan da kungiyoyin 'ta'addanci' kamar Boko Haram da ƴan awaren Biafra da ƴan bindiga masu satar jama'a ke yi, wani kisan da ke ci wa jami'an tsaron Najeriya tuwo a ƙwarya shi ne wanda al'umma kan yi wa jami'an

https://youtu.be/ewGjAUnTBgA?si=G35gypSIDcXEHb1t

Hukumar kare haƙƙin dan Adam ta Najeriya ta kammala bincike kan zargin da ake yi wa sojojin kasar na gudanar da wani shi...
20/03/2024

Hukumar kare haƙƙin dan Adam ta Najeriya ta kammala bincike kan zargin da ake yi wa sojojin kasar na gudanar da wani shirin zubar da ciki a asirce.

Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa a watan Disambar 2022 ya yi zargin cewa sojojin Najeriya sun zuɓar da cikin mata masu juna biyu 10,000 a yankin arewa maso gabashin kasar, tun daga shekarar 2013.

Rahoton ya ce dayawa daga cikin waɗannan matan an kuɓutar da su ne daga hannun masu iƙirarin jihadi da s**a yi garkuwa da su tare da yi musu fyaɗe.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya tattauna da 33 daga cikin matan, inda ɗaya daga cikinsu ta zargi cewa sojojin ne s**a zubar musu da ciki ba tare da izininsu ko saninsu ba.

Hukumar kare haƙƙin bil adama ta kasa NHRC ta kafa wani kwamitin da ya fara gudanar da bincike a cikin watan Fabrairun bara.

"Sojoji sun bukaci kwamitin da ya wanke su daga dukkan zarge-zargen da ke ƙunshe a cikin rahoton na Reuters," in ji NHRC a wani sakon da ta wallafa a shafin X a ranar Talata, yayin da ta sanar da kammala binciken na ta.

Hukumar dai ba ta bayyana sakamakon binciken ba kuma ta ce ba laile ta bayyana sakamakon ga bainar jama'a ba.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce ya nazarci takardun soji da na asibiti tare da yin hira da shaidu da dama, da s**a haɗa da ma'aikatan kiwon lafiya na farar hula da sojoji da jami'an gwamnati da aka ruwaito suna da hannu a shirin zubar da cikin.

Sojojin dai sun musanta rahoton lokacin da ya fara fitowa.

19/03/2024

Barkan Mu da Shan Ruwa. Allah ya karbi ibadun mu.

Ku latsa Dan kasanncewa da mu a

Shugaban Majalisar Malamai ta Kano ya roki gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba wa Murja Kunya mukamin SA ko SSA domin za ta iy...
19/03/2024

Shugaban Majalisar Malamai ta Kano ya roki gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba wa Murja Kunya mukamin SA ko SSA domin za ta iya gyara tarbiyar matasa.

Shin wanna mukami ya kamace ta?
Muna jiran amsoshin ku.

Source:

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zirnaniya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zirnaniya:

Videos

Share


Other News & Media Websites in Kano

Show All

You may also like