Public reporters hausa

Public reporters hausa Public reporter's jarida ce cikin harshen Hausa wacce ke kawomuku ingantattun labarai na duniya da g

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Yana neman Majalisa ta sahalemasa ya rabawa Yan Najeriya  naira biliyan 500. (Dari biyar...
13/07/2023

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Yana neman Majalisa ta sahalemasa ya rabawa Yan Najeriya naira biliyan 500. (Dari biyar) a matsayin tallafin rage radadin cire tallafin Manfetur.
Menene ra'ayin ku?

Shugaba Buhari na jagorancin taron majalisar tsaro kan zaben Najeriya.
22/02/2023

Shugaba Buhari na jagorancin taron majalisar tsaro kan zaben Najeriya.

Zaɓe: A kasa, a tsare, a raka ba zai yi aiki ba wannan karon, in ji INECHukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ce...
22/02/2023

Zaɓe: A kasa, a tsare, a raka ba zai yi aiki ba wannan karon, in ji INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ce tsarin a kasa a tsare, a raka ba zai yi aiki ba a zaɓen bana.

INEC ta shaida hakan ne a wata tattaunawa da BBC ta yi da jami'arta, a ci gaba da kawo bayanai kan muhimmancin abubuwa da ya k**ata a sani ko tunatarwa kafin ranar zaɓe.

Hukumar INEC ta ce a yanzu sai dai a ce a kasa a tsare a rumfar zaɓe, saboda komai zai kasance cikin na'ura wanda za a riƙa aikewa kai-tsaye zuwa cibiyar tattara sak**ako.

Hajiya Zainab Aminu Abubakar da ke magana da yawun hukumar ta ce ta yanar gizo za a rinƙa aike sak**akon zaɓen.

16/02/2023

Shugaba Muhammadu Buhari ya qara wa’adin naira dari biyu da taci gaba the anfani har zuwa kwana sittin daga jiya. Saboda haka jamaa Sai muyi hakuri, mubi doka, mucigaba da al’amuran mu cikin lumana. Allah Ya taimake mu. Ameen.

05/02/2023

ZAƁEN 2023: Arewa Decide Ta Gudanar Da Gagarumin Taro A Jihar Jigawa A ranar asabar 4 ga watan Fabrairu Arewa Decide mai taken "Naka Sai Na...

05/02/2023

He was a very strict servant of God, living in a rented house with his wife, and one day his wife went to his neighborhood and he went into...

31/12/2022

Mutum 1, sai ya haifi yara sama da 10, a ciki a samu mata wajen 6. Baisan ya ba su kudin auduga (pad), sabulun wanka da wanki, kayan kwalliya, kwalam da makulashe, anko da sauran su. Sai dai yarinya ta dinga bani in baka da gayu a waje domin ta samu kudin da mahaifinta ne ya k**ata ace ya na ba ta.

Nasan za'a ce nauyi yai masa yawa amma duk wanda yasai rariya, yasan zata zubda ruwa. Babu yadda za'ayi ka tara bataliya kace baza su ci kudi ba sosai. Mu 4 ne a gida na, babu yadda za'ayi mu ci shinkafa buhu (50 kg) biyu ko taliya sama da katan 2 a shekara. Wanda su ke su 10 fa? Shima yasan za'a ci da yawa.

Hakan yasa galibin kasashen musulmai a duniya basa tara yara k**ar na yan Nigeria da Niger. Kila ko mu mu ka fi kowacce kasar musulmai a duniya fahimtar addini a duniya. A tara yara, a ki kula da su yadda ya k**ata.

28/12/2022

Na Daina Jin Daɗin Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai, Cewar Alhaji Aminu Dantata

Hamshakin attajirin nan na Jihar Kano, Aminu Alhassan Dantata, ya ce daina jin dadin rayuwa, kuma ba shi da wani buri sama da cikawa da imani.

Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima.

Ya ce ton tasowarsa, ya samu damar haduwa da mutane da dama, kuma ya kulla abota da jama’a a duka jihohin kasar nan.

Sai dai, ya ce a halin yanzu da walan gaske ya samu mutum 10 daga cikin abokan nasa da ke raye.

“Na karade jihohin Nijeriya, kuma na yi harkoki da jama’a a daukacin jihohin, na yi abokai da dama sai dai abin bakin cikin shi ne, da wuya in ambato 10 daga ciki wadanda ke raye.

“Gaskiya a yadda nake yanzu, lokaci kawai nake jira. Ina fata in bar wannan duniya da imani.

“Ina fata ban saba wa kowa ba a rayuwa, idan kuwa hakan ta faru, ina fata za a yi mini ahuwa, ni ma na yafe wa duk wani da ya saba mini.

“A zuri’armu ni kadai na rage, inda nake rayuwa a tsakanin jikoki,” in ji Dantata.

Daga nan, ya yaba da ziyarar da aka kai masa, kana ya yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya ga Nijeriya da al’ummarta.

Sojoji uku ne s**a rasu yau da safe bayan faduwar wani jirgi da yayi mugun tashi a babban filin jirgin sama na Niamey, N...
26/12/2022

Sojoji uku ne s**a rasu yau da safe bayan faduwar wani jirgi da yayi mugun tashi a babban filin jirgin sama na Niamey, Niger.

NDLEA ta rufe gidan abinci bisa zargin sayar da kayan maye a KanoHukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya...
01/08/2022

NDLEA ta rufe gidan abinci bisa zargin sayar da kayan maye a Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta rufe wani gidan abinci da take zargin ana sayar da kayan maye tare da k**a kusan mutum 51 a Kano.

BBC Hausa ta rawaito cewa hukumar ta NDLEA ta ce ta k**a mutanen ne bayan samun korafi daga mazauna unguwar da gidan abincin yake a titin Lamido Crescent da ke cikin birnin na Kano, saboda yadda matsalar ke neman gurbata tarbiyar ya'yansu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta aike da wani mai sayar da magungunan jabu zuwa gidan yari na tsawoin shekaru uku, tare da biyan tarar naira 200,000.

Can ma a birnin Legas da ke Kudancin kasar NDLEA ta k**a ƙwayar Tramadol sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai, da aka yi yunkurin fita da ita kasashen waje daga tashar ruwan Apapa.

NDLEA ta ce kwayar na dauke ne a cikin katan-katan 55, da s**a hada da nau'ukan Tapentadol da kuma Carisoprodol na Tramadol, da kudinsu ya kai naira miliyan daya da dubu dari uku da saba'in da biyar.

barkanmu da wannan lokaci
15/06/2022

barkanmu da wannan lokaci

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Public reporters hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Public reporters hausa:

Share