Daily Trust Hausa

Daily Trust Hausa Jaridar Mikiya Hausa
(1)

Duk lalacewar PDP gwara ita da APC, in ji KwankwasoTsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar APC...
22/11/2022

Duk lalacewar PDP gwara ita da APC, in ji Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar APC ce mafi lalacewa cikin jam’iyyun siyasa a wannan lokaci.

Tsohon Sanatan ya kuma ce dukda dai itama PDP ɗin ba kanwar lasa bace wajen kama-karya a yanzu, amma dai za a iya cewa gwara-gwara idan a ka kwatanta ta da APC.

Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a jiya Lahadi, yayin taron masu ruwa da tsaki na ɗarikar Kwankwasiyya a gidansa dake Kano.

Ya ce wasu "sojojin gona" ne su ke yin kama-karya a PDP, inda ya koka da cewa duk cancantar mutum da haƙƙin sa, zai iya rasa shi ta dalilin waɗannan sojojin gonar.

Kwankwaso ya jadda cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, amma shirye-shirye sunyi nisa a tsakaninsa da jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso yace fita daga jam’iyya da komawa ba illa bane, kuma hakan ma shi ne kwarewa a siyasa.

Ya tuna cewa a shekarar 2018 da su ka yi zaben fidda gwani a Fatakwal, wadanda su ka zo na farko, na biyu, na uku da na hudu, duk sunbar PDP sun dawo, "sai kuma wasu tarkace da s**a biyo baya, a cewar Kwankwaso."

Rana mai Tarihi:A Yau Talata za a fara Tonon Arzikin Man Fetur Na Farko A Arewa .Jihohin Arewa biyu zasu shiga jerin jih...
22/11/2022

Rana mai Tarihi:

A Yau Talata za a fara Tonon Arzikin Man Fetur Na Farko A Arewa .

Jihohin Arewa biyu zasu shiga jerin jihohin Najeriya masu arzikin man fetur mai dinbin albarka

An yi kiyasin cewa arzikin danyen man da aka gano a Bauchi da Gombe ya kai ganga bilyan daya

An fara neman azikin man a jihar Borno amma matsalar rashin cewa ya tilasta dakatar da aikin

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a Yau Talata zai jagoranci kaddamar da hakan arzikin man fetur na farko a tarihin Arewacin Najeriya. Za'a fara hakan arzikin mai a jihar Bauchi da Gombe. Wannan hakar arzikin mai da zai kasance a Kolmani (OPL) 809 da 810.

Shekaru biyu da s**a gabata aka gani arzikin man fetur a Arewa. Gabanin gano arzikin, yankin Neja Delta kadai ke da arzikin man fetur a Najeriya.

Tun 2016, NNPC ta fara neman arzikin mai a wasu jihohin Najeriya kuma aka samu nasara a Bauchi, Gombe, Borno da Neja.

A cewar hukumomi a NNPC, kamfaonin da aka baiwa kwangilan hakan mai sun hada da Sterling Global Oil, New Nigeria Development Commission (NNDC) and NNPC Limited.

Daily Trust ta ruwaito wani jami'in gwamnati da cewa: "Bikin fara tonon zai gudana ne ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba kuma shugaban kasa da kansa zai halarta tare da yawancin ministocinsa fari da karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva."

Rahotanni sun nuna cewa arzikin man dake yankin Kolami ya kai gangan bilyan daya kuma wannan zai taimakawa Najeriya matuka wajen samun kudi.

Wannan sabon arziki na zuwa ne lokacin da Najeriya ke fama da karancin danyen mai sakamakon barayin mai da s**a addabi bututu a Neja Delta

Matukar aka zabe ni kamar an zabi Tafawa Balewa ne - Atiku ya ayyana kansa a matsayin "Abubakar Tafawa Balewa" a Jihar G...
21/11/2022

Matukar aka zabe ni kamar an zabi Tafawa Balewa ne - Atiku ya ayyana kansa a matsayin "Abubakar Tafawa Balewa" a Jihar Gombe

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya ce magoya bayan jam'iyyar a yankin arewa maso gabas suna da damar sake fitar da wani Tafawa Balewa ta hanyar zabe shi a 2023.

Atiku bubakar ya bayyana haka ne a filin wasa na Pantami dake Gombe a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a lokacin kaddamar da yakin neman zabensa a jihar.

Ya ce an dade da zama shugaban kasa a yankin kuma takararsa wata dama ce ta samar da wani shugaban kasa ta hanyar jefa kuri’a ga PDP.

“Yawancin ku ba a haife ku ba a lokacin da Marigayi Firimiyan Najeriya, Sir Tafawa Balewa yake mulki; yanzu kun sake samun damar fito da Abubakar Tafawa Balewa a cikina,’’ inji shi.

Malam Abubakar ya ce zuwansa jihar Gombe gida ne, kuma zai tabbatar da cewa jama’ar jihar sun samu karfin gwiwa tare da tallafa wa ‘yan kasuwa don samar da ayyukan yi idan aka zabe shi a 2023.

“Mun yi alkawarin fadada sana’o’inku ta yadda za mu samar da ayyukan yi ga matasan mu maza da mata; mun kuma yi alkawarin sake farfado da madatsar ruwan Dadin Kowa domin samar da wutar lantarki da noman ban ruwa,” inji shi.

Dan takarar shugaban kasa na PDP ya ce za a ba da fifiko kan tattalin arziki da noma tare da sake gina tituna a yankin Arewa maso Gabas domin bunkasa kasuwanci.

Mista Abubakar ya kuma yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas tare da tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya domin samun ci gaba cikin sauri.

Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom wanda shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP ya ce Abubakar ya kasance mafi cancanta a cikin ‘yan takara.

Mista Emmanuel ya bayyana cewa zaben Abubakar zai mayar da kasar kan turbar ci gaba da inganta rayuwar talaka

DA DUMI DUMINSA: Kai Mutum Ne Mai Gaskiya – Wike Ya Yi Alkawarin Goyon Bayan KwankwasoGwamna Nyesom Wike na jihar Rivers...
21/11/2022

DA DUMI DUMINSA: Kai Mutum Ne Mai Gaskiya – Wike Ya Yi Alkawarin Goyon Bayan Kwankwaso

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers a ranar Litinin ya yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso alkawarin samun goyon bayan yakin neman zabensa a jihar.

Wike ya yi wannan alkawarin ne a lokacin kaddamar da titunan a Mgbutanwo na karamar hukumar Emohua dake jihar.

A cewar Wike, tsohon gwamnan jihar Kano yana da abin da ake bukata kafin a zama shugaban kasar.

Ya ce: “Kai mutum ne mai gaskiya, abin takaici ba jam’iyya daya muke ba amma Allah zai taimakeka a lokacin da ya dace. Irin wadannan mutane ne da ya kamata su shugabanci kasar nan. Ina so in gaya muku idan za ku zo yakin neman zabe a nan, zan ba ku tallafin tsare tsare”.

Shin ko hakan na nufin Nyeson Wike zai yi anty-party ne ko kuma zai taimakawa dan takarar ne wajen cimma burikansa a nan gaba, wannan kuma lokacine alƙali.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daily Trust Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share