Labaran Duniya

Labaran Duniya labarai da rahotanni na gaskiya daga sassan Duniya

ALBISHIRIN KUAKWAI GIVEAWAY MAI ZAFI DA ZAN GABATAR DAGA NAN ZUWA LARABA IN SHA ALLAHZANBA REFERRALS DINA WANI ABU DAGA ...
15/03/2024

ALBISHIRIN KU

AKWAI GIVEAWAY MAI ZAFI DA ZAN GABATAR DAGA NAN ZUWA LARABA IN SHA ALLAH

ZANBA REFERRALS DINA WANI ABU DAGA ABUN DA NA SAMU NA AVACOIN

KA'IDAR GIVEAWAY DIN SHINE

1. wanda zai samu dole sai ya kasance da referral link dina yayi register na avacoin

2. Kuma dole sai yana daily clicks na avacoin din
3. Ina da sunayen referrals dina wadanda suke dannawa kullum zan sanar da sunayen su anan.
4. Idan kaga sunan ka zakamun screenshot na profile dinka na telegram da account number da zan sa maka kudin.
5. Idan baka fara ba kaima kada abarka abaya ga link dina kayi register👇👇👇 https://t.me/avagoldcoin_bot?start=0d3d5c946f74338836c0
in sha Allah kaima Zaka sha jar miya

Kada amanta ko da kayi register da link dina indai baka yin clicking bazaka ga sunan Ka ba

Tinubu ya nuna girgizuwarsa a kan jefa wa yan mauludi bom a Kaduna, ya bayar da umurnin a gaggauta bincikeShugaban kasa ...
05/12/2023

Tinubu ya nuna girgizuwarsa a kan jefa wa yan mauludi bom a Kaduna, ya bayar da umurnin a gaggauta bincike

Shugaban kasa Tinubu ya bayyana abin da ya afku a kauyen Tudun Biri karamar hukumar Igabi jihar Kaduna ga masu bikin mauludi, a matsayin babban abin bakin ciki da takaici

Shugaban ya kuma umurci da a gaggauta binciko masu alhakin sakar wa mutanen bam, a lokacin da suke tsaka da bikin addininsu

Kamar yadda mai magana da yayun Shugaban kasa ya fitar a yau Talata Chief Ajuri Ngelale, ya ce Shugaban kasar ya kuma bayar da umurnin a gaggauta kai waɗanda s**a jikkata sak**akon harin zuwa asibiti, waɗanda s**a rasu kuma Ya yi masu adduar Allah Ya gafarta masu

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un A jiya lahadi 3/12/2023 jirgin sama ya jefowa 'yan uwa musulmai BOM a filin mauludi ...
04/12/2023

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un

A jiya lahadi 3/12/2023 jirgin sama ya jefowa 'yan uwa musulmai BOM a filin mauludi da yake gudana a garin TUDUN/BIRI dake yankin airport Kaduna a cikin dare wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayuka sama da mutum 80

muna rokon Allah ya gafarta masu ya hadasu da wanda su ka taru domin sa Sallallahu Ta'ala AlaiHi Wa Sallam ya kuma karbi shahadarsu.

Abdulrazak A Zazzau II ✍️

Magidanci ya aje aikin kamfani don ya samu damar saduwa da matarsa.Mutumin yace matarsa ce ta nemi ya aje aikin ya dawo ...
03/12/2023

Magidanci ya aje aikin kamfani don ya samu damar saduwa da matarsa.

Mutumin yace matarsa ce ta nemi ya aje aikin ya dawo su zauna a gida tare don su samu damar yin Jima'i a duk lokacin da suke buƙata kasancewar idan ya fita wajen aiki tun karfe 7 na safe baya dawowa gida sai ƙarfe 6 na yamma kuma zai dawo da gajiya, ita kuma tana da bukatar yin jam'in a ko wane lokaci, wannan shine dalilin da yasa ya ajiye aikin k**ar yadda ya rubuta a cikin takardar aje aikin daya aikewa kamfanin.

An hana sallatar gawar duk wanda baya zuwa masallaci a unguwar Bajabure da ke karamar hukumar Girei a Jihar Adamawa. Yay...
02/12/2023

An hana sallatar gawar duk wanda baya zuwa masallaci a unguwar Bajabure da ke karamar hukumar Girei a Jihar Adamawa.

Yaya kuke ganin matakin a addinance?

Jaruma Maryam KK ta ce ta yi matukar kaduwa da ta ji cewa marigayi Darakta Aminu S. Bono a gidan haya yake har ya rasu.
28/11/2023

Jaruma Maryam KK ta ce ta yi matukar kaduwa da ta ji cewa marigayi Darakta Aminu S. Bono a gidan haya yake har ya rasu.

Budurwa ta ɓarke da kuka harda Zawo bayan an ɗaura aurenta a TikTok daga wasa abu ya zama gaske. A cikin hoton Bidiyon d...
27/11/2023

Budurwa ta ɓarke da kuka harda Zawo bayan an ɗaura aurenta a TikTok daga wasa abu ya zama gaske.

A cikin hoton Bidiyon data saki wannan budurwa ta nemi jama'a masana da sauran malaman addinin Musulunci da su shigo cikin wannan lamari daya faru da ita don samun mafita, ta bayyana cewar "Daga ina yin live Bidiyo sai ɗaya daga cikin abokaina na TikTok yace yana son aurena, ni kuma sai nace masa ba damuwa idan wane ya bada ni to na badu, sai na faɗi sunan ɗaya daga cikin masu bibiya ta a Live Bidiyon, kuma shi wanda nace idan ya bada ni na badu ɗan uwana ne muna da alaƙa ta jini da shi

Ma'ana zai iya aurar dani, shikenan sai aka ce shi wanda yace yana sona idan ya shirya aure na ya turo sadaki, kuma na sa Account Number, sai ga sadakin Naira dubu 100 ya turo nan take aka ɗaura aure kuma ga wasu daga cikin mabiya shafina sun zama shaidu, wallahi tun shekaran jiya nake zawo har yanzu na rasa me ke damu na, menene dalilin da yasa zasu yi min haka k**ar wacce bata da iyaye, nifa da iyaye na kuma sune zasu aurar dani

Sannan nace su turo Account Number in mayar musu da sadakin dubu ɗarinsu sun ƙiya sunce aure ya ɗauru don Allah jama'a ku bani shawara menene matsayin auren nan a shara'ance,? Ku taimaka min wajen turawa zuwa sauran groups ko Allah zai sa wani malamin addinin ya gani don ya warware min gaskiyar zance" In ji ta k**ar yadda ta bayyana a cikin Bidiyon

Kunji fa menene ra'ayoyinku shin kun gamsu da sahihancin wannan aure ko kuwa bai ɗauru ba?

TIRƘASHI: Mafi yawan Hausawa munafukai ne, Cewar Nafisa Abdullahi.Me Zaku Ce?
26/11/2023

TIRƘASHI: Mafi yawan Hausawa munafukai ne, Cewar Nafisa Abdullahi.

Me Zaku Ce?

YANZU YANZU: Garin gudun ceton rai wani ɓarawon babur ya faɗa cikin kaskon mai ƙosai a gwargwaje Zariya.
23/11/2023

YANZU YANZU: Garin gudun ceton rai wani ɓarawon babur ya faɗa cikin kaskon mai ƙosai a gwargwaje Zariya.

BREAKING NEWS 📰Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano na cewar yanzu haka zanga-zanga na can ta barke har da kone-konen...
22/11/2023

BREAKING NEWS 📰
Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano na cewar yanzu haka zanga-zanga na can ta barke har da kone-konen tayoyi.

Allah ya mana maganin masifa

ANGO DA AMARYAWane fata za ku musu?
22/11/2023

ANGO DA AMARYA

Wane fata za ku musu?

Mawaki Abdul Kamal Ya Maka BBC Hausa A Kotu, Yana Menan Diyyar Miliyan 120Mawaki Abdul Kamal na neman diyyar miliyan 120...
16/11/2023

Mawaki Abdul Kamal Ya Maka BBC Hausa A Kotu, Yana Menan Diyyar Miliyan 120

Mawaki Abdul Kamal na neman diyyar miliyan 120 daga Sashen Hausa na BBC kan amfani da kidan wakarsa ba da izininsa ba

Wani mawakin Hausa mai suna Abdul Kamal ya maka Sashen Hausa na BBC a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano bisa zargin amfani da kidan wakarsa ta ‘Maryamu’ ba da izininsa ba.

Lauyan mawakin, Barista Bashir Ibrahim Umar ya shaida wa kotun cewa BBC suna amfani da kidan wakar Abdul a shirin su mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’ ba tare da izininsa ba, wanda hakan ke iya janyo masa matsala a harkar sana’arsa.

“Kasancewarsa mawaki mai tasowa, hakan na iya zama matsala gare shi domin wasu za su yi zaton shi ne ya dauki kidan daga BBC don neman shuhura ko wani abu mak**ancin hakan,” in ji lauyan nasa.

Don haka lauyan ya nemi kotun da ta dakatar da kafar BBC daga ci gaba da amfani da sautin kidan, ya kuma nemi kotun da ta tilasta BBC biyan Abdul Kamal diyyar Naira miliyan 120.

Sai dai lauyan BBC, Barista Shakirudden Mosobalage ya mayar da martani cewa BBC ta sayi sautin kidan ne daga hannun wani kamfani da ke zaune a Abuja.

Barista Shakirudden Mosobalage ya kuma roki kotun da ta ba su dama su gabatar mata da wasu takardu, rokon da kotun ta amince da shi.

Alkalin kotun, Mai sharia. N. M. Inusa ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba

📸 Labaran Duniya

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUNWaɗannan wasu daga cikin amfanin gonakin Al'umma ne da barayin daji s**a kona a karamar...
16/11/2023

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN

Waɗannan wasu daga cikin amfanin gonakin Al'umma ne da barayin daji s**a kona a karamar hukumar Kontagora dake jihar Neja.

Allah ka kawo mana ƙarshen wannan bala'i badon halin mu ba.

Daga: nuraddeen kwantagora

MUHIMMAN ABUBUWA 9 GAME DA SABUWAR FASAHAR 'HUMANE AI PIN' WADDA KA IYA MAYAR DA RIƘE WAYAR SALULA ƘAUYANCIDaga Sadiq Tu...
14/11/2023

MUHIMMAN ABUBUWA 9 GAME DA SABUWAR FASAHAR 'HUMANE AI PIN' WADDA KA IYA MAYAR DA RIƘE WAYAR SALULA ƘAUYANCI

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

1. Humane AI Pin ƙaramin sunduƙi ne mai k**a da agogon hannu samfurin 'Smartwatch'. An samar dashi ne a matsayin naurar komai da ruwanka wadda zata iya abokantakar ɗan Adam wajen samar masa da bayanai cikin hanzari da kuma biya masa waɗansu buƙatu na rayuwa.

2. Kamfanin 'Humane' wanda Imran Chaudri da Bethany Bengiorno s**a kafa a shekarar 2019 ne ya samar da wannan gagarumar fasaha tare da haɗin guiwar kamfanonin Microsoft, da OpenAI, da Qualcomm da kuma T-Mobile.

3. Humane AI na iya tattaro duk bayanan da ake so daga yanar gizo sannan ya tantance wanda ake da muradi tare da bayar dashi cikin mafi sauƙin harshe, a mafi ƙanƙantar lokaci sama da yadda fasahar Chatgpt-4 zata yi.

4. Babu buƙatar danna madannin kira ga wanda ya maƙale fasahar Humane AI Pin a rigar sa idan har yana son yin magana da wani. Abinda kaɗai zai yi shine; ya danna na'urar, sannan yace mata "kira mini wane".
Idan kuwa saƙo zai tura, da zarar ya danna masarrafar, sai ya bayar da umarnin abinda za a aikewa wanda yake son turawa saƙon.

5. Fasahar tana da ƙarfin ikon fassara abinda taji daga mabanbantan harsuna. Don haka, anan gaba babu buƙatar kowa da kowa ya iya yaruka da yawa. Da zarar ka haɗu da wani mutum wanda baka iya gane abinda yake faɗa, sai ka danna madannin naurar ka umarce ta da fassara maka abinda ake magana akai, ai kuwa nan take zata fassara shi daki-da-daki cikin nutsuwa.

6. Fasahar na iya gane mabanbantan abubuwa. Don haka da zarar ka ga wani abu wanda baka gane masa ba, kai tsaye kana iya danna madannar na'urar tare da tambayar ba'asin wannan abu. Ita kuwa cikin ƙanƙanin lokaci zata ɗauki hoton abin, ta nazarce shi sannan ta fara kawo maka zantuka game dashi a sauƙaƙe.

7. Fasahar na da ikon taimakon mutum game da lafiyar sa. Tana iya bayar da shawarwari game da abinda ya k**ata aci ko asha. Tana iya sanar da kai adadin sinadaran ƙara l

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Imo na LP Ya Bayyana Cewa Shine Ya lashe Zaɓen Jihar Amma aka juya Sak**akon Zuwa APCA wani ka...
12/11/2023

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Imo na LP Ya Bayyana Cewa Shine Ya lashe Zaɓen Jihar Amma aka juya Sak**akon Zuwa APC

A wani kakkausar s**a kan yadda zaben Gwamnan jihar Imo ya Gudana, Ɗan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) Athan Achonu ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da hannu a wani shiri na karkatar da ra’ayin jama’a. Achonu, Wanda ke ikirarin shi ne ya lashe zaben, yayi kira da a sake Zaɓen a wasu yankunan da ake zargin an tabka magudi.

Hukumar zaɓe Mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) dake da alhakin sa ido kan Yadda za'a Gudanar da sahihin zabe, ta samu kanta a tsakiyar wannan cece-ku-ce. Hukumar na da alhakin magance zarge-zargen na Achonu Cikin Gaggawa da kuma bayyana Gaskiya.

LABARAN DUNIYA

Allah Ya yi wa tsohon dan wasan kwaikwaiyon nan na arewacin Najeria, Alhaji Usman Baba Patigi wanda da aka fi sani da Sa...
12/11/2023

Allah Ya yi wa tsohon dan wasan kwaikwaiyon nan na arewacin Najeria, Alhaji Usman Baba Patigi wanda da aka fi sani da Samanja Mazan Fama, rasuwa.

Samanja ya rasu cikin daren da ya gabata bayan jiyya da ya yi fama da ita; yana da shekaru 81.

Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 10 na wannan safiya ta Lahadi a gidansa da ke Kabala Costain a Kaduna.

Allahu Ya gafarta wa Samanja.

- DW Hausa

TA LEKO TA KOMA: Kowa Ya Ci Fa Sai Ya Biya, MTN Sun Ce Matsalar Injin Na'ura Ne Ya Sa S**a Turo Da Sakon Yafe Bashi
11/11/2023

TA LEKO TA KOMA: Kowa Ya Ci Fa Sai Ya Biya, MTN Sun Ce Matsalar Injin Na'ura Ne Ya Sa S**a Turo Da Sakon Yafe Bashi

HOTO: An fara jefa kuri'u a zaben Gwamna Dake gudana a jihohin Kogi Imo da Bayelsa yanzu haka.
11/11/2023

HOTO: An fara jefa kuri'u a zaben Gwamna Dake gudana a jihohin Kogi Imo da Bayelsa yanzu haka.

INA MURJA YAU GA RANARKI: An Ce Wannan 'Yar Kadunan Ta Yi Wa Kanawa Cin Mutuncin Kare-Dangi! Don Haka Mun Bar Ki Da Ita,
11/11/2023

INA MURJA YAU GA RANARKI: An Ce Wannan 'Yar Kadunan Ta Yi Wa Kanawa Cin Mutuncin Kare-Dangi! Don Haka Mun Bar Ki Da Ita,

Mun wayi gari da labarin kamfanin MTN sun yafewa kwastomomin su da yawa bashukan da suke binsu. Kuyi Checking Balance di...
11/11/2023

Mun wayi gari da labarin kamfanin MTN sun yafewa kwastomomin su da yawa bashukan da suke binsu.

Kuyi Checking Balance dinku, ku gani shin labarin da gaske ne, ko kuma labarin teburin me shayi ne?

Code din checking Balance *310 #

Daga Abdulrazak A Zazzau II

NEMAN TAIMAKON Al'ummaWani mawakin masarauta da yake a zaria watoABBA DON ZARIA Yayi kira ga 'yan jaridu da su isar da s...
04/05/2023

NEMAN TAIMAKON Al'umma

Wani mawakin masarauta da yake a zaria wato
ABBA DON ZARIA

Yayi kira ga 'yan jaridu da su isar da sakonsa k**ar haka

Kiran Gaggawa
Ina Kira ga Manyan Jaridun Hausa da Turanci Dan Allah A Wallafa Wannan Ko Allah Zaisa a Dace Wannan Shine Nasir Aliyu Babanyaya fitaccen Dan Gwagwar Mayar Siyasane Kuma Yayi Fice A Kafar Sadarwa Ta Facebook Saidai Har Yanzu Aure ya gagareshi A Iyakar Bincike da Mukayi mun gano cewa Hannu akasa Masa Kuma Wata Tsohuwar budurwarsa Daya yaudara ita tasa Masa Hannu

Muna Kira ga Manyan Malamai Dan Allah Asashi a Addu'a Ko Zaa Dace Ku Kuma Yan Mata Duk wacce taga yayi Mata ta ajiye comment da yayi insha Allah Zai duba Domin kuwa ayanzu harya Fara funfuna jiya da muka hadu na Kare Masa kallo Saina kula harya Fara kodewa Saboda tsabar Zama gwauraki 🤣🤣🤣

Kasar China sun samar da Macen Robot ta Farko Mai Jiki irin na mutane tare da magana irinta mutane.Wannan Robot din tana...
01/05/2023

Kasar China sun samar da Macen Robot ta Farko Mai Jiki irin na mutane tare da magana irinta mutane.

Wannan Robot din tana yin duk wani abu da mace Yar Adam take yi, misali aure, dafa abinci, wanke-wanke, wanki, guga tare da haihuwa ta hanyar "Artificial Insemination"

Haka zalika idan kana so za ka iya sakata aiki wajen tayaka yin kasuwanci tare da nema maka kudi ta hanyoyi da dama, dadin dadawa, ita dai wannan zankadediyar budurwar ba za ta taba bata maka rai ba, kuma idan ta fahimci ranka a bace yake za tayi duk mai yiwuwa wajen kwantar maka da hankali.

Lokaci yayi daya k**ata Yan Mata su rage jan aji da jiji dakai.

Daga MIKIYA NEWS

Hukumomi a Saudiyya sun ce ranar Juma'a ce Idin Ƙaramar Sallah, wadda ta yi daidai da 21 ga watan Afrilu.Ƙarin bayani: h...
20/04/2023

Hukumomi a Saudiyya sun ce ranar Juma'a ce Idin Ƙaramar Sallah, wadda ta yi daidai da 21 ga watan Afrilu.

Ƙarin bayani: https://bbc.in/3mThy5y

18/04/2023

Mutum Mai Hankali Shine Yake Tuna Mutuwa Kuma Yake Yi Mata Tanadi. Ubangiji Allah Yasa Mucika da Kyau da Imani Ameeeen 🤲🏻🙏🏻

KUTURU DA KUDINSA...Wani Dan Nijeriya Ya Siyo Bulo Daga Saudiyya Zai Yo Jigilarsu A Jirgi Zuwa Gida Nijeriya Saboda Inga...
16/04/2023

KUTURU DA KUDINSA...

Wani Dan Nijeriya Ya Siyo Bulo Daga Saudiyya Zai Yo Jigilarsu A Jirgi Zuwa Gida Nijeriya Saboda Ingancinsu

Duk wanda ya Kawo hotan Zakzaky Yana aiki umarah Za'a Bashi Miliyan Daya.MEYASA ZAKZAKY YAKE BOYEWA MABIYANSA HALAYANSA ...
15/04/2023

Duk wanda ya Kawo hotan Zakzaky Yana aiki umarah Za'a Bashi Miliyan Daya.

MEYASA ZAKZAKY YAKE BOYEWA MABIYANSA HALAYANSA NE❓❓❓❓

DA YAWAN YAN SHI'A BASUTABA SANIN CHEWA JAGORANSU ZAKZAKY BAITABAYIN AIKIN HAJJI KO UMMARA BA, SABODA ZAKZAKY YANA BOYEMUSU ‼️

DAN HAKA MUNSA NAIRA MILLION 1 GA DUK WANDA YAKAWO HOTON ZAKZAKY SANYE DA HARAMI A KA'ABA YANAYIN DAWAFIN UMMARA KONA AIKIN HAJJI WLH WLH DUK WANDA YAKAWO ZA'ABASHI 1M.

INDA RANKA...Dubun Wani Namiji Mai Shigar Mata Yana Damfarar Maza Ta Cika
14/04/2023

INDA RANKA...

Dubun Wani Namiji Mai Shigar Mata Yana Damfarar Maza Ta Cika

13/04/2023

Mun dauki azumi na 22 masu Albarka. Allah yasa ya zama silar samun tsirar mu duniya da lahira.

Address

Zaria
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labaran Duniya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Labaran Duniya:

Videos

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Kaduna

Show All