AL IHWAN hausa

AL IHWAN hausa wannan shafin,an Samar da shine don isarwa alumma ingantattun labaru.

08/06/2023

WANI MAGIDANCI A KASAR GHANA YA HALLAKA MATARSA HAR LAHIRA.

Daga wakiliyarmu: Hadiza Iddi daga Ghana.

Wani magidanci a kasar Ghana ya hallaka matarsa mai suna Eunice dasuke zaune a garin Nungua Accra ta kasar ghana har lahira ta hanyar sassarata da adda.

Eunice yar shekara ashirin da biyar Inda ta bukaci mijin nata daya saketa, hakan ya hasalashi s**akama sa insa,akarshe ya rarimu adda ya dosa sararta kamar an aikoshi, itako mai zatayi sai tace ga garinku. Bayan ya kaita kasa yaga abin bai isheshiba yace dawa zaa hada sai ya rarumi sirikinsa mahaifin mamaciyar Inda bai sami saa ba.

Eunice tabar gidan mijin nata ne tun abaya saboda cin mutuncita da yakeyi ba dare barana .

Ebenezer Dwomoh mahaifine ga marigayiyar ya tabbatar mana da mutuwar diyar tasa alokacin da mane ma labaru suke hira dashi,yakara dacewa sunyi matukar gigicewa lokacin da labarin abun da yafaru ya ishe masu. Yacigaba da cewa,sirikin nasa yana yawan dukan yar tasa adalilin hakanne yasa tabar gidan Inda ta dawo gidana.

Ya kara dacewa Eunice ta bar gidan mijin natane sabida dauri hari har ila yau da sauran nau ika na azaba. Har yakan iya zuwa gidana yayi mata dukan tsiya bama nanba ko inama yakan iya binta ya doketa, hardai said a ya ga ya kasheta hankalinsa ya kwanta. Daga bisani yayi yunkurin guduwa amma mutan unguwa s**ai nasarar cafkeshi dayimasa dukan tsiya, harsaida hukumar yansanda s**a kwaceshi amma da anyi masa jinajina.

Mr. Dwomoh mahaifin mamaciyar ya kai rahoto ga jamiaan yansanda na Ghana tareda rokon cewa sutabbatar Wanda ya aikata kisan yafuskanci hukunci kamar yadda dokar kasa ta tanada, kuma sunaji suna gani akarshe yace sunason adalci ga Eunice.

An rantsarda sabon sakataren gwamnatin ta rayyaDaga  Faruq Muhammad Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Sanata Georg...
07/06/2023

An rantsarda sabon sakataren gwamnatin ta rayya

Daga Faruq Muhammad

Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Takaitaccen taron wanda ya tara manyan baki da s**a hada da wasu masu rike da mukamai da kuma tsofaffin Gwamnoni, ya ga Sanata Akume ya yi rantsuwar mubaya’a tare da rantsar da shi da misalin karfe 11:06 na safe a cikin harabar majalisar ta Villa Daga cikin wadanda s**a halarci bikin akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima; Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan; Gwamnan Kwara AbdulRahman AbdulRazaq; Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr FolasadeYemi-Esan da uwargidan sabon SGF, Misis Regina Akume.

22/04/2023
Yadda bikin sallah ya kasance kenan aksar zazzau inda sarkin na zazzau ambasada Ahmad Nuhu Bamalli yayi rangadi a garin ...
22/04/2023

Yadda bikin sallah ya kasance kenan aksar zazzau inda sarkin na zazzau ambasada Ahmad Nuhu Bamalli yayi rangadi a garin na zazzau.

Yadda sallar idi karama ta gudana a fudiyya babban dodo Zaria, inda shaik Abdullahi zango ya jagoranta.
22/04/2023

Yadda sallar idi karama ta gudana a fudiyya babban dodo Zaria, inda shaik Abdullahi zango ya jagoranta.

Sallar Idin Karamar a jihar Katsina Sallar Idin Karamar a Babban Masallacin Idin KATSINA, Sarkin Katsina Alh Abdulmumini...
22/04/2023

Sallar Idin Karamar a jihar Katsina

Sallar Idin Karamar a Babban Masallacin Idin KATSINA, Sarkin Katsina Alh Abdulmumini Kabir Usman Tare Da Tawagarsa Sun Sami Halartar Sallar Idin.

Zababben Gwamnan kano Engr Abba kabir Yusuf da jagoran kwankwasiya Engr Rabi'u Musa Kwankwaso sun gudanar da  sallah idi...
22/04/2023

Zababben Gwamnan kano Engr Abba kabir Yusuf da jagoran kwankwasiya Engr Rabi'u Musa Kwankwaso sun gudanar da sallah idi karama a masallacin margayi musa Saleh kwankwaso dake miller road a jihar kano .

Sallar Idi Karama A Masallacin An-Noor Jibwis Central Mosque Dake Kofar Galadima Birnin Zariya.
22/04/2023

Sallar Idi Karama A Masallacin An-Noor Jibwis Central Mosque Dake Kofar Galadima Birnin Zariya.

20/04/2023

SANARWA:

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد وال محمد وعجل فرجهم

Ya zuwa yanzu mun sami labarin tabbacin ganin jinjirin watan Shawwal 1444, a yau Alhamis 29 ga Ramadan, 20/04/2023

Wasu 'yan'uwa da mutane da yawa a cikin garin Sakkwato da Faru, Karamar Hukumar Talata Mafara, Ringim da Nguru ta Jihar Yobe, sun tabbatar da ganin jinjirin watan. Don haka gobe Juma'a ta zam 1 ga watan Shawwal 1444. In sha Allah.

Allah ya amshi ibadodinmu ya kuma maimaita mana.

تقبل الله منا ومنكم صالح الأعمال🙏



20/04/2023

RUFE TAFSIR NA YOUNG SHEIKH ZARIYA.Daga Abu Muslim:A yinin yau Laraba 28 ga watan Ramadan  , 19 ga watan Aprilu 2023 ,  ...
19/04/2023

RUFE TAFSIR NA YOUNG SHEIKH ZARIYA.

Daga Abu Muslim:

A yinin yau Laraba 28 ga watan Ramadan , 19 ga watan Aprilu 2023 , Muhammad Zakeer Shamsudeen Ali Mai Yasin , wanda akafi sani da young sheikh Zariya ya rufe Tafsirin al Qur'ani mai girma na wannan shekara.
Wannan rufe tafsir na yau shine karo na uku da sheikh din yagabatar.
Dunbin jama'a maza da mata yara da manya s**a halartar . Malamai na addini da malamai daga manyan makarantu da sarakuna iyayen al umma duk sun halarci rufewar.

Bayan kammala karatun ankarata tambayoyi shikuma sheikh din yabayar da amsa.

Young Sheikh dan shekara tara da haihuwa , karatuttukan sa yana cikin wanda yake daukan hankali dakuma tattaunawa akai.

07/04/2023

Humaid Umar daga birnin Zaria nayiwa iyaye barka da shan ruwa.

07/04/2023

AL- IHWAN HAUSA nayiwa daukacin alummar musulmin duniya barka da shan ruwa Allah ya amshi ibadunmu yasanyamu cikin 'yan tattun bayi na wannan wata.

Molewar Kan Jarirai | Laifin Ungozoma Ne?Ta wace hanya za a kauce wa matsalar?Sau da yawa, idan mutane s**a ga yaron da ...
06/04/2023

Molewar Kan Jarirai | Laifin Ungozoma Ne?

Ta wace hanya za a kauce wa matsalar?

Sau da yawa, idan mutane s**a ga yaron da kansa ya ɗan mole ko ya taɓe daga goshi ko ƙeya sai su ce wai laifin ungozomansa ce da ba ta daidaita kan yadda ya kamata ba. Sai dai, wannan magana ta yi hannun riga da binciken masana. Domin ƙoƙon kan jarirai an haɗa shi ne da ƙasusuwa masu faɗi guda bakwai, waɗannan ƙasusuwa suna haɗewa kuma su yi ƙarfi har su bayar da cikakkiyar siffar ƙoƙon kai a cikin watanni shida.

Saboda haka, kan jarirai na iya canja sifa idan aka samu ƙarancin lura yayin raino, musamman a watannin farko bayan haihuwa.

Me ke kawo kan jarirai ko yara ke molewa, taɓewa ko kusurwa daga goshi ko ƙeya?

Daga cikin matsalolin da ke haddasa wannan matsala akwai matsalar nan da a ke cewa "Positional Plagiocephaly" a turancin likita. Wannan matsalar sifar ƙoƙon kai tana faruwa ne sakamakon kwantar da jarirai a bayansu tsawon lokaci ba tare da ana jujjuya su ba. Sakamakon ƙoƙon kan jariarai bai gama yin ƙwari sosai ba, wannan ya sa ƙoƙon kansu ke da haɗarin yin kusurwa.

Daga cikin alamun sun haɗa da:

1] Molewa, taɓewa ko kusurwar ƙoƙon kai daga ƙeya.

2] Saɓawar kunnuwa; ta yadda idan aka kalli kan yaro ko jariri daga sama za a ga kunnen ɓarin da ke da matsalar ya zarce gaba zuwa fuska fiye da na ɗaya ɓarin.

Wannan matsala an kasa ta zuwa : Mafi ƙaranci, matsakaiciya da kuma mafi tsanani.

Amma wannan matsala ba ta shafar aiki ko lafiyar ƙwaƙwalwa, sai dai matsalar sifar ƙoƙon kan kawai.

Abubuwan da ke iya janyo wannan matsala:

Bayan kwantar da jarirai tsawon lokaci a bayansu ba tare da ana jujjuya su zuwa hagu, dama ko rib-da-ciki ba.

Akwai abubuwan da ke ƙara haɗarin samun molewar kan jarirai kamar haka:

1] Ƙarancin ruwan mahaifa yayin goyon ciki.

2] Ƙuncin ƙugu ko mahaifar uwa.

3] Ɗaukar cikin tagwaye, ko fiye da haka.

4] Ɗaurewar tsokokin gefen wuya da ke kawo noƙewar wuyan jariri zuwa gefe guda wato "muscular torticolis", da dai sauransu.

Yadda za a magance

FATIMA Sadeeq Aliyu yara manyan gobe nayi maku barka da shan ruwa.
05/04/2023

FATIMA Sadeeq Aliyu yara manyan gobe nayi maku barka da shan ruwa.

11/11/2022

Buhari zai bude asibitin fadar shugaban kasa da aka gina shi a Naira biliyan 21

By Kubra muhammd

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da asibitin bangaren shugaban kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Wanda aka gina tare da samar da kayan aiki a kan kudi naira biliyan 21, ya kasance wani gagarumin aiki abin koyi a gwamnatin Buhari.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha, ya kaddamar da sabbin ayyuka guda hudu a asibitin a jiya Alhamis.

Ayyukan sun haɗa da ɗakin gwaje-gwaje na Molecular Level 2, wanda Cibiyar Kula da Cututtuka ta Ƙasa, NCDC ta sahale, da kuma wani matsakaicin ɗakin ƙone cututtuka wanda ofishin kula da yanayin muhalli, ƙarƙashin ofishin SGF ya bayar.

Ginin faɗaɗa ɓangaren hakori da kuma ɗakunan ma’aikata me sashe biyu na asibitin da SGF ɗin shima ya kaddamar.

A jawabinsa a wajen taron, Mustapha ya bayyana ayyukan a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Buhari na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga ƴan Nijeriya.

Kotu ta aike da shugaban EFCC zuwa gidan yariMai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin ta...
09/11/2022

Kotu ta aike da shugaban EFCC zuwa gidan yari

Mai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin aike shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC zuwa gidan yari bisa laifin ƙin bin umarnin kotu.

Alkalin ya kuma umurci Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar da ya tabbatar da an aiwatar da hukuncin.

Oji ya ba da umarnin ne a ranar 28 ga Oktoba, in da a ka raba wa manema labarai a Abuja kwafin umarnin.

AVM Rufus Adeniyi Ojuawo ya gabatar da korafi a kan gwamnatin tarayya mai lamba FCT/HC/M/52/2021 a kara mai lamba FCT/HC/CR/184/2016.

AVM Ojuawo ta bakin lauyansa R.N. Ojabo, ya nemi umarnin daure Shugaban Hukumar EFCC a gidan yari.

Hakan ya bayu ne bisa rashin biyayyarsa ga kotu, ya kuma ci gaba da bijirewa umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018.

Kotun ce ta umarci EFCC, Abuja da ta mayar wa wanda ya shigar da korafi motsa kirar Range Rover (Supercharge) SUV da kudin ta ya kai Naira miliyan N40.

07/11/2022

The Coalition of Civil Society Organizations under Secure Nation-Builders have lauded the effort of the Islamic Movement in Nigeria for creating a political wing, which they call Political Forum and therefore call on Nigerians to adopt its objectives which was centered on national unity and the emancipation of the downtrodden citizens irrespective of their religious, ethnic and political affiliations.

The call was made at a press conference held at Kaduna Central Area Multi-Purpose Hall Kaduna on Monday November 7, 2022 and jointly signed by the Chairman Ameh Allen Christopher and the Secretary of the coalition, Halima Bukar.

The statement acknowledges the development coming from the Islamic Movement in Nigeria with Shia majority adherents for creating a Political Forum. With their solid structure, such a mass movement of millions of people have the capacity to change the equation of the Nigerian political activities as truthfulness, dedication, courage are among their characteristics.

Some of the objectives of the political Forum are made to bridge ethnic divide in Nigeria, Protecting the rights of all Nigerians, facilitating peaceful coexistence and harmony among Nigerians, and to also

ensure equal distribution of Nigerian resources, safeguarding lives and properties of the Nigerian Population, maintaining diplomatic ties and striving towards social justice, sensitization of the public on their rights and responsibilities are among the objectives of the Political Forum of the Islamic movement in Nigeria.

These objectives are what all political struggle should uphold in their quest to clinch to power, it is clear that the leader of the Islamic movement Sheikh Ibraheem Zakzaky has over the years stick to what he believes as true teachings of Islam, the Sheikh married a Yoruba lady Zeenat Ibraheem, he established an annual programme he named unity week, encourages his disciples to embark on selfless services to their immediate communities in a wide-spread recognition of the need for the unity of the Nigerian people and Africa at large.

In conclusion, the groups call on the Political Forum of the Islamic movement not to support any particular person or party with a bad human right record, bad economic record and bad security record.

Koriya Ta Arewa Ta Mayar Da Matani Ta Hanyar Harba Makamai Masu Linzami Yau Laraba.Daga Ahmad Isah AhmadKasar Koriya ta ...
03/11/2022

Koriya Ta Arewa Ta Mayar Da Matani Ta Hanyar Harba Makamai Masu Linzami Yau Laraba.

Daga Ahmad Isah Ahmad

Kasar Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami, makamin wanda ya ratsa sararain samaniyar
makwabciyarta wato Koriya ta Kudu.

Koriya ta Arewa ta harba wadannan makamai masu linzami ne domin mayar da martani bayan kasar ta gargadi kasar Amurka da kasar Koriya ta Kudu da su daina yin wani atisayen da sojojinsu ke yi a yankin.

An baiyana cewa wannan shi ne karo na farko da wani makami irin
wannan ya ratsa kan iyakar kasashen biyu tun bayan raba kasar gida biyu.

Makamin da ya kasance mai gajeren zango ne, ya fada cikin tekun da ke kusa da gabar tekun Koriya ta Kudu daf da wani tsibiri mai suna Ulleungdo.

Leadership ta rawaito cewa Koriya ta Kudu ta ce makamai 10 aka harba da safiyar yau Laraba.

Japan da Koriya ta Kudu sun soki matakin makwabciyar ta su na harba wadannan makaman.

24/10/2022

‘Yan Bindiga Sun mamaye Najeriya Saboda Gwamnati Ta Basu dama ne- TY Ɗanjuma.

Tare da rahotar alfijir Hausa

“Theophilus” Danjuma, tsohon ministan tsaro, ya ce rashin tsaro a ƙasar ya biyo bayane bayan gazawar gwamnati.”

Ɗanjuma ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Wukari, jihar Taraba, a lokacin naɗin sarauta, “inda wakiliyar ALFIJIR HAUSA ta tattaro mana kanun labaran."

Janar din mai ritaya ya ce manufar ‘yan bindigar ita ce sake mayar da Najeriya mulkin mallaka.”

Ɗanjuma dai, a shekarar 2018, ya zargi sojoji da sauran jami’an tsaro da hada baki da masu kashe mutane wajen kai wa ‘yan Najeriya hari.

“Ya zargi sojojin da "nuna son zuciya", yana mai cewa sun gaza a alhakin da suke da shi na kare kasar daga hare-hare.

“Rundunar soji ba sa tsaka-tsaki. Suna hada baki da 'yan fashi da makami. Suna kashe mutane, suna kashe ’yan Najeriya. Suna sauƙaƙe motsinsu, suna rufe su,” in ji Ɗanjuma.

"Idan kuka dogara ga sojoji don dakatar da kashe-kashen, duk za ku mutu ɗaya bayan ɗaya don haka ku tashi ku kare kanku.”

MASHA ALLAH: Shahararriyan 'yar fim ta ƙasan Ghana ta karbi addinin musulunci.Fitacciyan 'yar “film” ta kasan Ghana mai ...
24/10/2022

MASHA ALLAH: Shahararriyan 'yar fim ta ƙasan Ghana ta karbi addinin musulunci.

Fitacciyan 'yar “film” ta kasan Ghana mai suna Rosemond Alade Brown wadda akafi sani da (Akuapem Poloo), ta karbi addinin musulunci bayan tayi kalman shada tare da kadaita Allah.

Jaruman ta wallafa a shaginta na instagiram inda tayi hamdala da godiya ga ubangiji, akan wannan ni'ima da yayi mata sannan tayi godiya ga wasu limamai da sauran al'umman musulmi.

Allah ya kara daukaka musulunci da musulmi.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Sallami Shugaban Hukumar Kula Da Bunƙasa Yankunan Naija Dalta NDDC Na Riƙon Kwarya, Ef...
20/10/2022

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Sallami Shugaban Hukumar Kula Da Bunƙasa Yankunan Naija Dalta NDDC Na Riƙon Kwarya, Effiong Akwa Kuma Ya Umurci A Kafa Sabon Kwamitin Gudanarwar Hukumar....

Kabilun da s**a fi kowane arziki a Afrika Richest Tribes In Africa 1. Batswana 🇧🇼🇿🇦2. Igbo 🇳🇬3. Kikuyu 🇰🇪3. Yoruba 🇳🇬4. ...
19/10/2022

Kabilun da s**a fi kowane arziki a Afrika

Richest Tribes In Africa

1. Batswana 🇧🇼🇿🇦
2. Igbo 🇳🇬
3. Kikuyu 🇰🇪
3. Yoruba 🇳🇬
4. Tutsi 🇷🇼
5. Tigray 🇪🇹
6. Ashanti 🇬🇭
7. Banyankole 🇺🇬
8. Somali 🇰🇪🇸🇴🇪🇹
9. Oromo 🇪🇹
10. Zulu 🇿🇦

Souce -AfrikaChikana

18/10/2022

Aisha Jarumar 'Yan Matan Arewacin Najeriya, Mai Kiwon Zaki.
Wane fata zakuyi Mata?

Address

Kaduna

Telephone

+2347067821832

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AL IHWAN hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Media/News Companies in Kaduna

Show All