13/08/2022
Tarihin Janaral Muhammadu Buhari, GCFR
A Daure A Karanta
Shimfida
Manjo Janar Muhammadu Buhari, sojan Najeriya mai ritaya, sannan kuma ɗan siyasa. Jajirtaccen mutum wanda ‘yan Najeriya suke yiwa laƙabi da “Mai Gaskiya”. Wannan kalma ta ‘yan Najeriya ta tabbata a kansa saboda kasantuwarsa maras hannu a cikin badaƙalolin maƙudan kuɗaɗen da mafiya yawa daga tsoffi da sabbin shugabannin Najeriya s**a tsunduma kawukansu a ciki.
Janaral Muhammadu Buhari mutum ne da ke da gogayya a fannin mulki saboda aikin da ya yi a gidan soja, wanda ya fara tun daga sakan laftanar har sai da ya zamo shugaban ƙasa bayan tarin muƙaman da ya riƙe kafin hakan, sannan kuma bayan ritayar sa ya shiga siyasa wacce ta sake bashi damar sake ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu kuma a matsayin farar hula.
Ya samu kafa tarihin cewa shi ne farkon Ɗan’najeriya da ya taɓa tsayawa takarar zaɓe a jama’iyyar hamayya sannan kuma ya kayar da shugaban da ke kan karagar mulki.
Haihuwarsa
Janaral Muhammadu Buhari, haifaffen garin Daura ne ta cikin Jahar Katsina. An haife shi a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 1942. Sunan mahaifinsa Adamu, mahaifiyarsa kuma Zulaihatu. Mahaifinsa ya rasu a lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya ke da shekara huɗu kacal a duniya.
Karatunsa
Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya yi karatunsa na firamare a garin Daura da kuma Mai’adua daga shekarar 1948 zuwa 1952. Daga nan sai ya shige makarantar Middle ta Katsina a shekarar 1953. Sannan kuma sai ‘Katsina Provincial School’ wacce daga baya ta koma Kwalejin Gwamnati ta Katsina, daga shekarar 1956 har zuwa 1961.
A shekarar 1961, Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya samu shiga makarantar sojojin Najeriya da ke Kaduna (Nigerian Military Training School, Kaduna), inda ya gama a shekarar 1963.
Bayan kammala wancan horo da ya samu na soja a Kaduna, a cikin wannan shekara ta 1963 aka tura shi ƙaro karatu a ƙasar Ingila inda ya samu horo a makarantar ‘Cadet School’ da ke garin Aldershot ta ƙasar Ingila. Da Kammalawarsa.