17/08/2024
Coordinator Arewa APC Merger Group Musa Mujahid Zaitawa Ya Zargi Gwammatin Jihar Kano Da Kin Rabawa Al'ummar Jihar Tallafin Gwamnatin Tarayya
Daga Khadija Nasara
Musa Mujahid Zaitawa Coordinator Arewa APC Merger Group ya nemi Hukumar yaki da chin hanchi da rashawa ta kasa (ICPC) Data binciki gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna mai ci akan karkatar da tallafin da gwamnatin tarayya ke ba al'ummar jihar kano.
Musa Mujahid Zaitawa ya shigar da korafin ne gaban hukumar yaki da chin hanchi da rashawa (ICPC) Inda hukumar ta karbi korafin kuma ta aminci zatayi bincike akai.
Kamar yadda muka samu labari akai Musa Mujahid Zaitawa ya rubutawa hukumar ta (ICPC) Wasikar cewa muna neman wannan hukuma ta ICPC mai tarin albarka data binciki gwamnatin jihar Kano kan zarge-zargen rashin gudanar da rarrabe rarraben kayan masarufi a karkashin kulawar sakataren gwamnatin Jiha da Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Jihar Kano.
Musa Mujahid Zaitawa yace a ranar 3 ga watan Disamba, 2023, Gwamnan jihar Kanon Abba Kabir Yusuf ya bankado wani dakin ajiyar kaya a rukunin masana’antu na Sharada inda ake karkatar da kayayyakin abinci da aka tanada na kayan abinci, musamman masara da shinkafa.
Rahotanni sun ce an sake dawowa da wadannan kayayyaki aka sake sayar da su a kasuwa, maimakon a raba wa wadanda aka tanada, wadanda s**a hada da masu fama da matsalar jiki da matan da s**a mutu na sojoji da sauran jami’an tsaro a Kano.
Duk da umarnin gaggawa da Gwamna ya bayar na kwamishinan ‘yan sandan ya karbe rumbun ajiyar tare da gudanar da bincike cikin gaggawa, ga dukkan alamu babu wani ci gaba da aka samu wajen gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kuliya.
A wannan lokacin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta k**a wasu mutane biyu, Tasiu Al’amin Roba, babban mataimaki na musamman ga gwamna (SSA) na ofishin sakataren gwamnatin jihar da kuma Abdulkadir Muhammad.
Sai dai da alama binciken ya tsaya cak, kuma babu wani mataki da aka dauka kan wadanda ake zargi ko wasu masu hann