Hadiza Gabon

Hadiza Gabon Film production

My grandma
25/07/2022

My grandma

31/10/2021
10/10/2021
Dafatan munsha Ruwa lfy
29/04/2021

Dafatan munsha Ruwa lfy

26/04/2021

*ZUMUNCI BA RA'AYI NE BA, WAJIBI NE... SHIN KANA KO KINA SADA ZUMUNTA❓*
GA *HUJJOJI 20* GAME DA ZUMUNCI.

1- Allah Ta'ala, Ya yi Umarni da sada zumunta.

*Suratul Bakara 36, Suratul Isra'i 26, Suratul Rum 38, Suratul Bakara 210, Suratul Nisa'i 2.*

2- Sada zumunta yana kara tsawon rai,
*Bukari 5986, Muslum 2557.*

3- Sada zumunta yana kara arziki,
*Bukari 5986*

4- Sada zumunta yana cikin abubuwan da aka yi Umarni da shi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, *Bukari 7*

5- Sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah,
*Bukari 5983*

6- Sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah Yake so.
*Sahihut-targib 2/667.*

7- Sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, *Abu Dauda 4902*
8- Sada zumunta wasiyyar da Annabi (S.A.W) ya yi wa Al'ummarsa ce. *Sahihut-targib 2/669*

9- Sadar da zumunta siffar muminai ce.

10 Sada zumunta yana sawa a karfi aikin mutum. Sahihut-targib 2/674

11- sada zumunta yana cikin siffofin masu hankali.

12- Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira, ya zamanto mai sada zumunta,. *Bukari da Muslum*.

13- Sada zumunta yana kare mutum daga la'antar Allah ,
*Tafsir Ibn kasir Suratul Ra'adi,25*

14- Yin Sadaka ga yan uwan zumunta, yana jawo lada biyu, na Sadaka da na zumunta. Sahihu, *Sunanil Tirmiziy. 1/202*

15, Sada zumunta yana kara soyayya tsakanin 'yan uwa (dangi).

16- Sada zumunta yana kara hadin kai tsakanin 'yan uwa.

17- Wanda ba ya sada zumunta ba zai shiga Aljannah ba.

18- Allah Ta'ala Ya yi wa zumuntaa alkawari zai sadar da wanda ya sadar da ita ga rahamarSa, zai yanke wanda ya yanke ta.

19 , Mai sada zumunta shi ne wanda ko ba a zo masa ba, shi zai je.

20, Ba ya cikin sada zumunta sai wanda ya zo maka kawai za ka je masa.

YA ALLAH KA BA MU IKON SADAR DA ZUMUNTA AMEEN... 🤲🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻

https://youtu.be/XgI2b8KhYqI
08/03/2021

https://youtu.be/XgI2b8KhYqI

kuyi subscribe sannan Ku danna kararrawa domin samun shirye shiryenmu sannan a danna like da kuma comments ayi sharing groups groups da kuma yan uwa mun gode

Assalamu Alaykum. "Truly, Allah is full of kindness and the most merciful towards mankind". (Q2:143). May you and your f...
26/02/2021

Assalamu Alaykum. "Truly, Allah is full of kindness and the most merciful towards mankind". (Q2:143). May you and your family enjoy His mercies and kindness Forever. Amin. Jumma'at Mubarak

Sirrinsu
09/02/2021

Sirrinsu

Lokacin aiki
09/02/2021

Lokacin aiki

04/02/2021

*DAN TSOKACI*

*Akwai matukar dadi da annashuwa idan soyayya ta kasance tsakanin masoya har karshen rayuwa.*

*Kauna da kular da ke zama a zukatan masoya ba gama-gari bace kuma ba abar dauka da wasa bace.*

*Soyayya na bukatar kulawa, raino, lokaci da kuma abubuwa da yawa dake iya saw ta dade na tsawon lokaci.*

*A wannan lokacin zamu tattauna akan abubuwan dake sa son namiji ya fita daga zuciyar mace ko son mace ya fita daga namiji kwata-kwata.*

*Ga kadan daga ciki:*

*1. Rashin Kula:*

*Masu iya magana sunce yawan lokacin daka bawa kowanne abu shi yake bayyana makomarsa.*

*Misali, yawan lokacin da kake bawa aikinka na bayyana yawan abinda zaka samu a karshe.*

*Haka zalika soyayya kuwa, yawan lokacin daka bata na nuna yadda zata girma tare da habaka.*

*Rashin kula*

*Rashin kula kuwa na tarwatsa soyayya daga zuciyar masoya dungurungum kowace irice kuwa soyayyar Kuma ko su waye suke yinta saboda haka kulawa a soyayya Babban jigo ce wadda kowane bangare mace da namiji suke bukatar kulawa daidai wa daidai, duk lokacin da wani bangare na masoya yaji cewa shine mafi cancantar abawa kulawa to daga lokacin soyayyar ta fara komawa koma baya Kuma bayan zatai tayi har a neme ta a rasa ko Kuma ga soyayyar a naji a zuciya amma angunduri juna*

*2. Rashin Yabo*

*Dukkanin bangarorin masoya mace da namiji suna San yabawa Amma Mata na son a nuna musu yabawa sosai idan har abu ya birge ko kuma sun yi dai-dai.*

*Misali*

*Mata na son a yaba kwalliyarsu, girkinsu, maganarsu da sauransu.*

*Maza ku sani Rashin yabo na sawa soyayyar namiji ta fita daga zuciyar mace.*

*3. Kunci:*

*Kunci na kawo rashin zaman lafiya a kowacce irin alaka.*

*Ba soyayya kadai ba, hatta kawance babu mai son yi da mutum mai matukar kunci.*

*Kunci na taka rawar gani wajen wargaza soyayya a tsakanin masoya*

*4. Kalubalanta*
*akai akai*

*Mata basa kaunar namiji mai yawan kalubalantar su haka ma mazan basa so*

*Kalubalanta na fara shiga tsakanin masoya ake samun babbar matsala*

*5. Yiwa

Address

Malali
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hadiza Gabon posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hadiza Gabon:

Share


Other Media/News Companies in Kaduna

Show All