25/07/2024
DA ƊUMI ƊUMI: An Fitar Da Jadawalin Yadda Zanga-zanga Zai Kasance A Birnin Dutse
Al'Ummar dake yanki k**ar Haka:
(1)Al,ummar garin shuwarin zasu rufe hanyar kano-maidugiri 6:00am na safe
(2)Al,ummar kudai - laraba zasu rufe hanyar kwanar huguma - Birnin kudu
(3)Al ummar cikin Birnin Dutse zasu rufe hanyar bayan FUD - sundimina dakuma hanyar Limawa zuwa fanisau
(4)Al ummar warwade zasu rufe hanyar baya
Duka a karfe 6:00am na safe
DOKA! DOKA!! DOKA!!!
(1)- Babu mākāmî. ⚠️
(2)- Babu taba kayan kowa ⚠️
(3)- Babu fada ku cin zarafin wani. ⚠️
(4)- kowa ya fito da rubutu na kokensa a jikin kwali ✅
(5)- idan da hali kowa yayi shigar farar riga da bakin wando, ko kuma duk shigar da kaga dama amma shiga mai ma'ana. ✅
TAIMAKO! TAIMAKO!! TAIMAKO!!!
(1)- masu halin cikinmu su dafo abinci. ✅
(2)- wasu su taimako da ruwan sha da kuma magani. ✅
(3)- mu taimaki duk wanda yake bukatar taimako ko wannne iri" uwa daya uba daya. ✅
Bamu daukewa kowa ba" daga kan Dan shekara 18 zuwa sama" matasa maza da mata" Dattijai da tsofaffi" kowa ya fito domin ceto kasar mu daga halin da shugabanni s**a jefata na tsananin yinwa da tsaradar rayuwa da kuma rashin tsaro.
ABINDA AKE BUƘATA GWAMNATI TA YI SHINE
(1)- A bude bodojin Arewa baki daya domin ashigo da abinci k**ar yadda yake a baya da kuma kaiyade masa farashi.
(2)- A dawo da tallafin man Fetir ya dawo 200 duk lita.
(3)- Duk yan kunan dake fama da rashin tsaro a Arewa a dawo da zaman lafiyar yankin domin cigaba da noma da kiyo.
(4)- A dawo da tallafin karatu domin Dan Talaka ya yaki Jahilci.
(5)- A samarwa matasa maza da mata aiyukan dogaro dakai domin gujewar aikata munanan laifuka.
(6)- A dawo da tallafin wutar lantarki, domin karfafar masana'antu manya da kanana
Lokacin fitowa karfe 60:00Am na safe zuwa 60:00Pm na yamma.
Kafin afito kowa ya karanta duk wata addu'a wanda ya iya domin neman taimakon Ubangiji
By Aliyu Abdullahi Limawa (target)
Shafine dazaike kawo muku labaran Nishadi, Barkwanci, wasanni, siyasa, da sauran su.