Arewa cloud 5

Arewa cloud 5 Arewa cloud 5 computer software and Hardware solution
(4)

Koto ta kara tabbatar da Gawuna a matsayin gov
17/11/2023

Koto ta kara tabbatar da Gawuna a matsayin gov

Shaidu sun bayyana yadda jirgi ya yi hatsari a AbujaShaidun da s**a gane wa idonsu sun bayyana yadda wani jirgin sojoji ...
21/02/2021

Shaidu sun bayyana yadda jirgi ya yi hatsari a Abuja
Shaidun da s**a gane wa idonsu sun bayyana yadda wani jirgin sojoji ya yi hatsari a Abuja ranar Lahadi.

Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce dukkanin mutum bakwai da ke cikin jirgin ne s**a mutu a hatsarin.

Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya Air Vice Marshal Oladayo Amao ya kafa kwamitin bincike kan musabbabin hatsarin.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya ce jirgin mai suna King Air 350 ya yi hatsari ne bayan ya samu matsalar na'ura a lokacin da ya tashi sama, k**ar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Vice Marshal Daramola ya faɗa wa BBC cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa ceton mutum 42 ne da 'yan bindiga s**a yi garkuwa da su a Jihar Neja kafin ya juya zuwa Abuja saboda matsalar na'ura.

Jirgin wanda ba shi da girma ya faɗo ƙasa a kusa da garin Basa da ke babban birnin ƙasar, Abuja.

Waɗanda s**a gane wa idonsu sun faɗa wa BBC cewa sun ji ƙara mai ƙarfi kafin jirgin ya k**a da wuta.

Tazarar kilomita 100 ne tsakanin Minna, babban birnin Jihar Neja, da kuma Abuja.

Bayanai sun ce jirgin yana cikin wadanda Najeriya ta yi sayo domin ayyukan tsaro da leken asiri a ƙasar.

Sunayen sojojin da s**a rasu

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta bayyana sunayen mutum bakwai da s**a rasa rayukansu a hatsarin k**ar haka:

Flight Lieutenant Haruna Gadzama (Captain)

Flight Lieutenant Henry Piyo (Co-Pilot)

Flying Officer Micheal Okpara (Airborne Tactical Observation System (ATOS) Specialist).

Warrant Officer Bassey Etim (ATOS Specialist)

Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (ATOS Specialist)

Sergeant Ugochukwu Oluka (ATOS Specialist)

Aircraftman Adewale Johnson (Onboard Technician).

Fatima Isaacs: Matar da ta kwato wa mata Musulmai sojoji 'yancin sanya hijabi a Afirka ta KuduRundunar sojin Afirka ta K...
30/01/2021

Fatima Isaacs: Matar da ta kwato wa mata Musulmai sojoji 'yancin sanya hijabi a Afirka ta Kudu

Rundunar sojin Afirka ta Kudu ta sauya tsarin tufafin jami'anta ta yadda sojoji mata Musulmi za su samu damar sanya hijabi.

Hakan wata nasara ce ga Manjo Fatima Isaacs, wadda ta kwashe shekaru uku tana shari'a da rundunar sojin domin ganin an tabbatar mata da 'yancinta na addini ta hanyar sanya hijabi a karkashin hularta ta soja.

A makon jiya rundunar sojin ta janye shari'ar da take yi da Manjo Isaacs lamarin da ya tabbatar mata da sauran sojoji Musulmi da damarsu ta sanya hijabi.

Ta fuskanci kora daga aiki a kan "bijire wa doka da kuma umarni" ta hanyar kin cire hijabin da take sanyawa.

Manjo Isaacs, wadda ke aiki a matsayin jami'ar bincike kan masu mutuwar farat-daya a asibitin sojoji, ta shaida wa jaridar Cape Times cewa hakan wata nasara ce ba wai kawai gare ta ba, har ma da sauran mutanen da ke "nunawa wariya" saboda addininsu.

"Muna zaune a kasar da ke bin tafarkin dimokradiyya abin da ke nufin bai k**ata a rika nuna bambanci ga kowa ba bisa addinin da yake bi. Na yi amannar cewa addini shi ne ginshikin tarbiyya ga kasa. Wannan nasara ce mai cike da muhimmanci," a cewarta..

Ta kuma gode wa Cibiyar Legal Resource Centre (LRC), wato kungiyar da ta taya ta fafutukar ganin ta samun 'yancin sanya hijabi a 2019.

Bayan rundunar sojin ta janye karar da ta shigar a makon jiya, an amince cewa Manjo Isaacs za ta iya saka matsattsen dan-kwali, wanda bai rufe kunnuwanta ba, kuma fari - kodayake tsarin tufafin sojin ba zai sauya ba a hukumance.

Daga nan ne kungiyar ta LRC ta shigar da kara a kotu, inda ta ce tsarin tufafin rundunar sojin Afirka ta Kudu ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasar.

Daga bisani, rundunar tsaron kasar ta "gyara tsarin sanya tufafi na addininta domin bai wa Musulmai mata damar sanya hijabi a saman kakin sojinsu," a cewar sakon da LRC ta wallafa a Tuwita..

"Ba za mu ci gaba da bibiyar wannan batun ba saboda a halin yanzu tsarin rundunar tsaron k

20/01/2021

Gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Sokoto 'ta laƙume miliyoyin naira'
Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto da ke arewacin Najeriya, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira.

Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne da safiyar yau Talata kuma zuwa lokacin wannan rahoto, wutar na ci gaba da ci.

A hukumance, ba a san musababbin tashin gobarar ba, sai dai bayanai sun ce gobarar ta soma tashi ne daga Kofar Yan Roba.

Jami'an hukumar kashe gobara sun gargzaya kasuwar inda s**a yi ta kokarin kashe wutar.
Naru Bello, wani dan kasuwa ne da ke da shago a kasuwar, ya shaida wa BBC cewa gobarar ta tashi da misalin karfe bakwai na safe kuma ta cinye dukkan kayan da ke shagonsa da ma na wasu abokan sana'arsa.

Ya ce masu kashe gobarar sun fuskanci kalubale saboda yadda aka gina shaguna a kan hanya.

20/01/2021

Gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Sokoto 'ta laƙume miliyoyin naira'

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto da ke arewacin Najeriya, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira.

Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne da safiyar yau Talata kuma zuwa lokacin wannan rahoto, wutar na ci gaba da ci.

A hukumance, ba a san musababbin tashin gobarar ba, sai dai bayanai sun ce gobarar ta soma tashi ne daga Kofar Yan Roba.

Jami'an hukumar kashe gobara sun gargzaya kasuwar inda s**a yi ta kokarin kashe wutar.
Naru Bello, wani dan kasuwa ne da ke da shago a kasuwar, ya shaida wa BBC cewa gobarar ta tashi da misalin karfe bakwai na safe kuma ta cinye dukkan kayan da ke shagonsa da ma na wasu abokan sana'arsa.

Ya ce masu kashe gobarar sun fuskanci kalubale saboda yadda aka gina shaguna a kan hanya.
Shi ma Zaiyanu Yahaya Assada, wanda daya ne daga cikin 'yan kasuwar, ya ce gobarar ta kona kusan daukacin kayansa yana mai cewa barayi suna shiga suna sata.

Shugaban gudanarwa a babbar kasuwar ta birnin Sokoto, Alhaji Ibrahim mil Goma, ya ce 'yan kasuwar ne da kansu s**a lalata hanyoyin da ke ciki kasuwar shi ya sa masu aikin kashe gobara suke shan wahala wurin kashe ta.

A cewarsa, gwamnati ta yi bakin kokarinta wajen gyara kasuwar.

Gwamnan jihar ta Sokoto, Aminu Waziri tambuwal, wanda ya ziyarci kasuwar, ya kuma jajanta wa 'yan kasuwar ta Sokoto Central Market bisa wannan ibtila'i.

Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya ya gargadi gwamna Rotimi Akeredelu na Ondo kan korar makiyayaA karon farko, Shugaban...
20/01/2021

Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya ya gargadi gwamna Rotimi Akeredelu na Ondo kan korar makiyaya
A karon farko, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan matakin da gwamnan Ondo da ke kudancin kasar, Rotimi Akeredolu ya ɗauka na korar makiyaya daga dazukan jihar.

A wani saƙo da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ya aika wa manema labarai, ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasar na sane sannan tana bibiyar abubuwan da ke faruwa musamman kan batun matakin da gwamnan na Ondo ya ɗauka.

A cewarsa, rashin daidaito a irin yadda ake aika saƙo ne yake jawo ce-ce-ku-ce game da ainihin saƙon da ake so a aika wa jama'a.

"Babu wani abin cewa illa kira ga ɓangarorin su yi sulhu da kuma neman gwamnatin jihar da kuma shugabancin Fulani su ci gaba da tattaunawa domin fahimtar juna domin kawo ƙarshen rashin tsaron da ake fama da shi a jihar cikin sauri," in ji shugaban.

Shugaban ya yaba wa gwamna Akeredolu inda ya ce a matsayinsa na babban lauya kuma tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya ba sa tsammanin zai kori dubban makiyaya waɗanda s**a shafe rayuwarsu a cikin jihar sak**akon ayyukan wasu ɓata-gari da ke aikata laifuka a daji.

Shugaba Buhari ya kuma ce idan da gaske ne, lallai ƙungiyoyin kare haƙƙi na kan gaskiyarsu ta nuna damuwa kan cewa wannan matakin zai iya tayar da zaune tsaye.

Sai dai Garba Shehu ya shaida wa BBC Hausa cewa suna jira su gani ko gwamnan zai yi biyayya ga umarnin Shugaba Buhari idan ba haka ba za su ɗauki mataki na gaba.

Ya kuma ƙara jaddada cewa garkuwa da mutane da fashi da makami da satar dabbobi laifi ne kuma ko su wa ke aikata irin laifukan bai k**ata ana yi wa wata ƙabila kuɗin goro ba ana siffanta ta da wani laifi na musamman.

FG Unveils Car Made By 30-Year-Old NigerianThe Minister of Science and Technology, Dr. Ogbonnaya Onu, has unveiled a car...
20/01/2021

FG Unveils Car Made By 30-Year-Old Nigerian
The Minister of Science and Technology, Dr. Ogbonnaya Onu, has unveiled a car built by Mr Auwal Hassan, a 30-year-old Nigerian inventor.

Speaking in his office in Abuja on Monday, the minister called on youths to be innovative in producing goods and services that are usually imported, saying that would improve the Gross Domestic Product (GDP), create employment and reduce imports.

Dr. Onu reiterated the commitment of the ministry in partnering and supporting young innovators.

In his remarks, Mr Hassan solicited for the cooperation of the ministry in developing more automobiles and other engineering feats such as the production of helicopters.

He said the vehicle has a speed capacity of 50 kilometres per hour, a five gear transmission and six horsepower engine speed.

Director General of the National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI), Prof. Mohammed Haruna, said the locally produced car was assessed by his agency, adding that they will work closely with the innovator in improving the standard and quality of the car.

DSS ta bankado wani shirin tayar da rikicin addini a sassan NajeriyaHukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta ce ta ...
12/01/2021

DSS ta bankado wani shirin tayar da rikicin addini a sassan Najeriya
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta ce ta bankaɗo wani shiri na ƙoƙarin tayar da rikicin addini a wasu jihohin ƙasar.

Sanarwar da kakakin hukumar DSS Peter Afunanya ya fitar ranar Litinin ta yi gargadi ga al'ummar ƙasar kan abin da ta ce wasu na ƙoƙarin tayar da rikicin addini a sassan ƙasar.

Kuma sanarwar ta ambaci jihohi da s**a ƙunshi Sokoto da Kano da Kaduna da Filato da Rivers da Oyo da Legas da ta ce ana shirin tayar da rikicin addini. "Wani ɓangare na shirin shi ne haifar da rikice-rikice tsakanin addinai tare da kai hari wasu wuraren ibada da shugabannin addinai da wasu manyan mutane kuma wasu muhimman wurare," in ji sanarwar.

Sanarwar ta yi gargaɗi ga ƴan Najeriya su yi hankali kuma su guje wa duk wasu daɓiu da nufin tunzura su ko tayar da rikici tsakanin junansu.
Hukumar ta ce za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umma.

Ta kuma yi gargaɗi ga waɗanda ta ce suna ƙoƙarin kitsa makircin da su ƙauracewa wa aikawa hakan domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaban ƙasa.

10/01/2021
Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin rage kuɗin wutar lantarkiA dai makon da ya gabata ne ma'aikatar da ke kula da harkok...
10/01/2021

Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin rage kuɗin wutar lantarki
A dai makon da ya gabata ne ma'aikatar da ke kula da harkokin wutar lantarki ta Najeriya ta dakatar da wani ƙarin kuɗin wuta da aka yi, bayan barazarar da kungiyoyin ƙwadago s**a yi na sa-kafar-wando-guda da gwamnati.

Hakan ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da aka sanar da ƙarin farashin, wanda mahukunta s**a danganta da hauhawar farashi, inda kilowatt ɗaya ya tashi daga naira biyu ya koma naira huɗu.

Ma'aikatar wutar ta hanzarta sanar da janye karin kuɗin wutar da aka yi ne, k**ar yadda ta ce domin ta fahinci cewa an jahilci ƙarin, saboda wasu na cewa ya kai kashi hamsin cikin ɗari, alhali, ƙarin yana da nasaba ne da hauhawar farashi, kuma doka ce duk bayan wata shida, hukumar da ke kula da harkokin wutar lantarki da sauran ɓangarorin da abin ya shafa, kan yi nazarin halin da ake ciki domin daidaita ƙarin da ya dace.

Zaizayewar ƙasa ta kashe mutum 11 a Indonesia
10/01/2021

Zaizayewar ƙasa ta kashe mutum 11 a Indonesia

Gobara ta ƙone ofisoshin hukumar Immigration ta NajeriyaGobara ta ƙone ofisoshi a ginin hedikwatar hukumar shige da fice...
10/01/2021

Gobara ta ƙone ofisoshin hukumar Immigration ta Najeriya
Gobara ta ƙone ofisoshi a ginin hedikwatar hukumar shige da fice ta Najeriya wato Nigeria Immigration Service da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ya ce gobarar ta shafi wasu ne daga ofisoshin nata.

"Gobara ta tashi a hedikwatarmu a safiyar yau (Lahadi)," a cewar saƙon.

"Hukumar kashe gobara ta ƙasa da taimakon sauran hukumomi a kusa da filin jirgin sama sun kashe wutar."

Hukumar ta ce zuwa yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba amma ana ci gaba da bincike.

View more on TwitterView more on twitter

Prof
10/01/2021

Prof

Rikicin Tigray: Habasha za ta gyara Masallacin Najashi da 'Sahabban Annabi' s**a ginaGwamnatin Habasha ta yi alkawarin g...
06/01/2021

Rikicin Tigray: Habasha za ta gyara Masallacin Najashi da 'Sahabban Annabi' s**a gina
Gwamnatin Habasha ta yi alkawarin gyara wani masallaci da ya shafe daruruwan shekaru, wanda aka rusa a rikicin watan jiya a yankin Tigray.

Rahotanni sun ce an harba wa Masallacin Najashi bom. An lalata hasumiyar masallacin da kuma kaburburan wasu jagororin Musulunci.

Gwamnati ta ce za ta kuma ta gyara wata coci mai makwaftaka da masallacin, wacce ita ma aka lalata.

Mazauna yankin sun yi amanna cewa sahabban Manzon Allah SAW da s**a yi hijira zuwa Habasha su ne s**a gina masallacin.

Sun gujewa cuzgunawa ne da cin zarafin da mutanen Makka suke yi musu a lokacin, kuma Najashi ya ba su mafaka a masarautar Aksum a lokacin.

Mazauna yankin sun yi amanna cewa awai kaburburan sahabbai 15 a wurin da aka lalata.

Sun kuma yi imani da cewa masallacin ne mafi tsufa a Afirka, sai dai wasu sun ce wani masallaci a Masar ya fi shi daɗewa.

Masallacin yana kusa da garin Wukro, mai nisan kilo mita 800 daga babban birnin kasar, Addis Ababa.

An kuma rusa wata Cocin Kiristocin gargajiya masu bin ra'ayin 'yan mazan jiya, sai dai babu karin bayani.

Wata hukuma a Turkiya ta kaddamar da wani aiki a 2015 na gyaran masallacin, tana cewa tana so ta adana tarihin masallacin sannan tana so ya zama wajen da masu yawon bude ido na addini za su ringa ziyarta.

Masallacin da kuma wata coci da ke kusa da shi an lalata su ne yayin rikicin da aka shafe wata guda ana yi wanda ya janyo aka tumbuke jami'iyyar Tigray People's Liberation Front (TPLF) daga mulki a yankin ranar 28 ga watan Nuwamba.

Burtaniya ta kammala ficewa daga Tarayyar TuraiFafutukar da 'yan Burtaniya s**a fara shekaru da rabi da s**a gabata ta z...
31/12/2020

Burtaniya ta kammala ficewa daga Tarayyar Turai
Fafutukar da 'yan Burtaniya s**a fara shekaru da rabi da s**a gabata ta zamo gaske a daren Laraba, bayan da aka rattaba hannu a yarjejeniyar yanke alakar kasuwanci tsakanin Burtaniyar da EU.

Firai ministan Burtaniya, Boris Johnson ne ya sa hannu a kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu bayan ficewar Burtaniyar daga Tarayyar watanni 11 da s**a gabata.

Majalisar wakilan kasar ce dai ta ta fara amincewa da yarjejeniyar ba tare da hamayya ba.

Sojojin yakin Burtaniya ne s**a dauko kundin yarjejeniyar daga Brussels zuwa Burtaniyar inda firai minista Boris Johnson ya sanyawa hannu.

A makon da ya gabata ne dai Burtaniya da Tayyara Turai s**a rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta fayyace alakar bangarorin biyu bayan ficewar Burtaniya daga EU.

Bisa wannan yarjejeniya, yanzu Burtaniya ta kammala ficewa daga kasuwar bai daya da shigi da fici na Tarayyar ta Turai.

Firai ministan kasar, Boris Johnson ya shaida wa BBC cewa yarjejeniyar na da matukar alfanu ga 'yan Burtaniya.

"Ina son kowa ya fahimci cewa wannan yarjejeniya da na sanya wa hannun yanzu ba it ace karshen al'amari ba.

Danba ne na kulla sabuwar alaka tsakanin Burtaniya da 'yan uwanmu da abokanmu da ke Turai. Jama'a al'amarin ya tabbata. Ga shi fa.

Na san tambayar da za ku yi it ace shin ko na karanta kundin. Amsar ita ce e na karanta. Kundi ne mai alherin gaske ga kasar nan har ma ga abokanmu da abokan huldarmu."

To sai dai abokan hamayya sun ce al'amarin ya yi k**a da an gudu ba a tsira ba.

A watan Janairun shekarar nan ne Burtaniya ta fice daga tarayyar amma batun alakarta ta kasuwanci da EU ya hana ta sakat.

Tun dai tsakiyar shekarar 2015 Burtaniya ta fara fafutukar ficewa daga tarayyar ta turai amma sai a daren jiya Laraba ne mafarkinta ya tabbata na yanke alakar shekara 47.

Sanata Saidu Umar Kumo ya rasuAllah Ya yi wa Sanata Saidu Umar Kumo rasuwa da safiyar yau Lahadi, 27 ga watan Disamban 2...
28/12/2020

Sanata Saidu Umar Kumo ya rasu
Allah Ya yi wa Sanata Saidu Umar Kumo rasuwa da safiyar yau Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020.

Tsohon sanatan wanda ya wakilci mazabar Jihar Gombe ta Tsakiya, ya rasu ne a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Kafin rasuwarsa, shi ne Garkuwan Gombe. Ya riƙe shugaban kamfe ɗin Alhaji Atiku Abubakar a shiyyar arewa maso gabas a zaɓen shugaban ƙasa na 2019.

Sai dai Sanata Kumo ya koma jam'iyyar APC mai mulki a watan Janairun 2019 kafin a shiga zaɓen da Muhammadu Buhari ya lashe a watan Fabarairu.

An zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa a shekarar 1999 zuwa 2003 kafin daga baya ya yi takarar gwamnan Gombe a 2011, inda ya sha kaye a hannun Ibrahim Hassan Dankwambo.

Za a yi jana'izarsa a Masallacin Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Ƙungiyar ƴan Naija Delta ta bawa Buhari wa'adiWata ƙungiyar masu ɗauke da mak**ai a yankin Naija Delta, ta buƙaci shugab...
28/12/2020

Ƙungiyar ƴan Naija Delta ta bawa Buhari wa'adi
Wata ƙungiyar masu ɗauke da mak**ai a yankin Naija Delta, ta buƙaci shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta umartar jami'an hukumar EFCC su janye daga harabar gidan jagoransu Tompolo, sannan a bude masa asusunsa na banki.

Kungiyar mai suna 21st Century Youths of the Niger Delta and Agitators ta bayyana damuwa dangane da yadda aka ki mutunta umarnin wata kotu na wanke jagoran nata.

Cikin wata sanarwar Email da kungiyar ta fitar k**ar yadda jaridar The Natiins ta rawaito, ta ce jan hankalin ya zama dole domin gudun haddasa danyar fitina a yankin na Naija Delta.

"A bawa Tompolo kadarorinsa da aka karbe, matasan kabilar Ijaw da kuma na Naija Delta ba za su sake naɗe kafa su tsaya suna kallon irin wannan cin fuska ba" " ini sanarwar.

Kungiyar ta kara da cewa idan har aka gaza yin abinda ta nema, to kuwa za ta tura mutanenta su mamaye gidan da har ywnzu jami'an EFCC ke ci gaba da mamaya a cikinsa.

Ministar al'amuran mata ta Najeriya ta kamu da koronaMinistar al'amuran mata ta Najeriya Paulinee Tallen ta kamu da cuta...
28/12/2020

Ministar al'amuran mata ta Najeriya ta kamu da korona
Ministar al'amuran mata ta Najeriya Paulinee Tallen ta kamu da cutar korona.

Ministar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta aikawa manema labarai mai dauke da sa hannunta.inda tace cutar bata ci karfinta tukuna.

Adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona a Najeriya dai na ci gaba da karuwa a dai dai wannan lokaci.

A makon da ya gabata ne hukumomi s**a sake rufe makarantu da wuraren shakatawa domin dakike yaduwar cutar.

Boko Haram ta kashe masu faskare uku, ta k**a 40 a BornoWasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe masu saran itace...
28/12/2020

Boko Haram ta kashe masu faskare uku, ta k**a 40 a Borno
Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe masu saran itace uku, sun kuma sace wasu kimanin 40 a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Jami'an sa-kai a yankin sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an yi wa masu saran itacen tsinke ne a dajin Wulgo da ke kusa da kan iyakar Kamaru.

Da ma dai yankin sananne ne wajen ayyukan 'yan ta-da-ƙayar-bayan, inda suke da sansanoni da yawa.

Masu faskaren sun je dajin Wulgo ne don neman itace amma ba su dawo ba har maraiace, abin da ya sa 'yan gora s**a bi bayansu, sai dai ba su ga kowa ba sai gawa uku da aka harba a baya
Ga dukkan alamu, duka mutum ukun an harbe su ne bayan sun yi yunƙurin tserewa saboda dakkansu an harbe su a baya," a cewar wani shugaban ƙungiyar 'yan gora a yankin.

An shafe tsawon lokaci babu layin salula a yankin sak**akon hare-haren da Boko Haram ta riƙa kaiwa tare da karya turakun layukan. Hakan ya tilasta wa mazauna yankin amfani da layukan Kamaru.

Mayaƙan Boko Haram na ƙara far wa masu saran itace da manoma, bisa zargin suna bai wa sojoji da 'yan gora bayanai.

Hukumomi na gargaɗin masu faskare su guji shiga daji, sai dai rahotanni na cewa tilas ce ke sanya su yin hakan saboda an sare tsirrai a yankunan da ke da zaman lafiya.

An sace wani malamin addinin kirista da matarsa a KadunaYan bindiga a Kaduna, sun sace wani malamin addinin kirista Apos...
26/12/2020

An sace wani malamin addinin kirista da matarsa a Kaduna
Yan bindiga a Kaduna, sun sace wani malamin addinin kirista Apostle Emmanuel Egoh Bako tare da matarsa Cindy Bako.

Rahotannin hukumomin tsaro a Najeriya sun ce maharan sun bude wuta kan wani majalisi yayin da ake gudanar da harkokin ibada, a kusa da hanyar Afana zuwa Fadan a karamar hukumar Jema'a, inda daga bisani s**a yi nasarar yin awon gaba da malamin da matarsa, da kuma wani mutum guda.

Sanarwar kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ta ce sojoji sun yi yunkurin bin sahun maharan, sai dai basu yi nasarar samunsu ba.

Ga hotunan daya daga cikin motocin da harsashi ya huda yayin harin.

Covid-19: An shiga kullen Korona mai tsanani a BurtaniyaShirin sassaucin dokar kullen annobar Korona a lokacin bikin kir...
21/12/2020

Covid-19: An shiga kullen Korona mai tsanani a Burtaniya

Shirin sassaucin dokar kullen annobar Korona a lokacin bikin kirsimeti a Burtaniya ya gamu da cikas, bayan da hukumomi s**a janye batun ɗaga ƙafa kwata-kwata.

Matakin wanda ya fara aiki daren Asabar ya biyo bayan gargadin da masana s**a yi cewa yanzu haka nau'in annobar wanda yafi na baya haɗari na ci gaba da ɓarna musamman a London.

Baya ga London, sun ce za a dauki matakan kullen masu tsanani a yankunan Kent da Essex da Bedfordshire.

Akan haka ma Firanminista Boris Johnson ya sanar cewa yankunan da ke mataki na hudu na kullen kada su kuskura su yi cuɗanya da makwabtansu ko kuma duk wani da ba a zaune yake a cikin gidansu ba.

Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya ta tabbatar da ceto 'yan makarantar Islamiyya 80 da ɓarayin m...
21/12/2020

Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya ta tabbatar da ceto 'yan makarantar Islamiyya 80 da ɓarayin mutane s**a yi yunƙurin sacewa ranar Asabar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Gambo Isa, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Funtua.

A cewarsa ɓarayin, sun sato mata huɗu a ƙauyen Dan Baure da ke yankin, inda a hanyarsu s**a haɗu da 'yan Islamiyyar da a kan hanyar komawa gida daga wurin Maulidi.

"Ɗaliban na Hizburrahim Islamiyya da ke Mahuta guda 80, sun fito ne daga wurin Maulidi da aka yi a Unguwan Alkasim da ke Dandume sai barayin s**a hada su da mutum hudu da s**a sato da shanu 12," in ji ASP Isa.

"Daga nan wasu s**a rugo s**a ba mu labarin abin da yake faruwa sai muka tura jami'anmu da haɗin gwiwar sojoji da 'yan ƙato-da-gora s**a yi ba-ta-kashi da ɓarayin."
A cewar kakakin 'yan sandan, lamarin ya yi sanadin mutuwa da kuma jikkatar ɓarayin "kodayake har yanzu ba mu san adadinsu ba".

"Amma kwamishinan 'yan sanda ya tura ƙarin jami'ai yanzu da safen nan domin kirga waɗanda s**a mutu. Mu dai a ɓangarenmu babu wanda ya mutu."

Lamarin na faruwa kwana biyu bayan sakin 'yan makarantar sakadaren maza ta Kankara guda 344 da aka sace a jihar ta Katsina a makon jiya.

Sace su ya ja hankalin duniya a kan matsalar rashin tsaro da ke ta'azzara a arewa maso yammacin Najeriya.

Kasashen Turai da dama sun haramta, ko kuma suna shirin hana jiragen da s**a taso daga Birtaniya shiga cikinsu da zummar...
21/12/2020

Kasashen Turai da dama sun haramta, ko kuma suna shirin hana jiragen da s**a taso daga Birtaniya shiga cikinsu da zummar hana yaduwar wani sabon nau'i na cutar korona.

Netherlands da Belgium sun dakatar da jiragen Birtaniya sauka, yayin da Italiya za ta bi sahu. Kazalika an dakatar da jiragen kasa daga Birtaniya zuwa Belgium.

Ana sa rai Ireland za ta takaita tashin jiragen sama da kuma jigilar jiragen ruwa daga karfe 12 na daren Lahadi. Faransa da Jamus na cikin kasashen da ke duba yiwuwar daukar irin wannan mataki.

Sabon nau'in cutar ta korona ya yaɗu cikin sauri a Landan da kuma Kudu maso Gabashin Ingila.
Firaminista Boris Johnson ya saka sabbin dokokin kulle na mataki na huɗu masu tsauri, har ma aka fasa yin sassauci kan shirin bikin Kirsimeti, wanda gwamnati ta yi alƙawari a baya.Manyan jami'an lafiya sun ce babu wata shaida da ke nuna cewa sabon nau'in ya fi barazana, ko kuma ba ya jin riga-kafi, sai dai kashi 70 cikin dari ya fi yaduwa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin buɗe iyakokin Najeriya huɗu na kan tudu da s**a haɗa da Seme da Illela da M...
17/12/2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin buɗe iyakokin Najeriya huɗu na kan tudu da s**a haɗa da Seme da Illela da Maigatari da kuma Mfun.
Mai taimaka wa Shugaba Buharin kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a Tuwita a ranar Laraba da yamma.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilan da s**a sa aka buɗe iyakokin ba, duk da cewa ƴan ƙasar sun daɗe suna fata ganin hakan.
Amma mai bai wa Shugaba Buharin shawara kan yada labarai Garba Shehu ya cewa BBC dalilin buɗe iyakar shi ne sak**akon shawarar da wani kwamiti na musamman da shugaban ƙasar ya kafa kan matsalar rufe iyakar.
Amma kafin nan sai da aka samu hadin kai daga makwabtan kasashe kan matsalolin da s**a sa aka rufe iyakokin.
A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Shugaba Buharin ta rufe dukkan iyakokin ƙasar na kan tudu sak**akon abin da ta kira barin su a buɗe na jawo fasa ƙwaurin miyagun ƙwayoyi da maamai waɗanda suke barazana ga tsaro.
Sannan gwamnatin ta ce cikin dalilan har da ƙoƙarinta na hana shiga da shinkafa ƴar waje cikin ƙasar a ƙoƙarinta na bunƙasa noman shinkafar a cikin gida.Shugabannin ƙasashe maƙwabtan Najeriya sun daɗe suna roƙonsa da ya buɗe iyakokin.
Dukkan iyakokin da aka bayar da izinin buɗewa ɗin waɗanda suke kan iyakar ƙasar ne da jamhuriyyar Nijar da ta Benin.

Ƴan Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan umarnin sake buɗe kan iyakokin tudu guda huɗu da shugaba Muhammadu Buhar...
17/12/2020

Ƴan Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan umarnin sake buɗe kan iyakokin tudu guda huɗu da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da yammacin jiya Laraba.
A cikin watan Agustan bara ne, gwamnatin ƙasar ta sanar da rufe kan iyakokin da nufin daƙile fasa-ƙwaurin shinkafa da mak**ai.
Gwamnatin dai ta sha cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu wajen rufe iyakokin.
Sake buɗe iyakokin a wannan lokaci yazo da bazata kuma babu wani dalilai da gwamnati ta bayar da s**a sa aka sake buɗe su, duk da cewa ƴan ƙasar sun daɗe suna fatan ganin hakan.
Amma mai ba wa shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa an buɗe iyakokinne sak**akon shawarar da wani kwamiti na musamman da shugaban ƙasar ya kafa kan matsalar rufe iyakar.
Sai dai Dr Abdurrazak Ibrahim Fagge, shugaban sashen nazarin tattalin arziki a jami`ar Yusuf Maitama Sule a Kano ya shaida wa BBC cewa buɗe iyakokin, shi ne mafi alheri.

Juventus ta soma tattaunawa da wakilin Paul Pogba Mino Raiola a yayin da take yunkurin sake daukar dan wasan na Manchest...
17/12/2020

Juventus ta soma tattaunawa da wakilin Paul Pogba Mino Raiola a yayin da take yunkurin sake daukar dan wasan na Manchester United mai shekara 27. (Express)
Dan wasan Chelsea da Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 22, wanda ake rade radin zai tafi Leeds, na shirin tafiya kungiyar kwallon kafar Rennes da ke Faransa domin yin zaman aro zuwa karshen kakar wasa ta bana. (Talksport)
Liverpool na sanya ido kan dan wasanLille dan kasar Portugal Renato Sanches, mai shekara 23.
(Le10 Sport - in French)
Liverpool ta mayar da hankali kan Sanches ne domin ya maye gurbin Georginio Wijnaldum, wandatake son rikewa, ko da yake ba ta son amincewa da bukatar dan wasan mai shekara 30 dan kasar Netherlands ta ba shi kwangilar shekara hudu. (Express)
Manchester United za ta jira zuwa watan Janairu domin yanke hukunci kan ko za ta bar dan wasan Ingila mai shekara 20 Brandon Williams - wanda ake rade radin zai tafi Southampton ko Newcastle - ya tafi zaman aro. (Manchester Evening News)

Daliban Kankara: Shin rufe makarantun boko a arewa nasara ce ga Boko Haram?Rufe makarantu a arewacin Najeriya ya haifar ...
17/12/2020

Daliban Kankara: Shin rufe makarantun boko a arewa nasara ce ga Boko Haram?
Rufe makarantu a arewacin Najeriya ya haifar da saɓanin ra'ayi tsakanin masana inda wasu ke ganin matakin "fargar jaji ne" wasu kuma suna ganin babu wani zaɓi.
Sace ɗaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina da ƴan bindiga s**a yi ya tayar da hankalin Najeriya da duniya, dalilin da ya sa wasu jihohin arewa da ke fama da matsalar tsaro s**a sanar da rufe ƙanana da manyan makarantunsu.
Gwamnatocin Katsina da Zamfara da Kano sun rufe makarantun ne saboda dalilin tsaro, yayin da kuma Kaduna da Jigawa s**a ce saboda dalilai na annobar korona.
Sai dai masana sha'anin tsaro, da masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin cewa gwamnatocin jihohin na arewa maso yammacin Najeriya sun yi gaggawa wajen rufe makarantun.
Ta wata fuskar kuma, masana na ganin gwamnonin ba su da zaɓi domin sace ɗaliban wani babban tashin hankali ne kuma rufe makarantun mataki ne da ya dace saboda rashin tabbas kan abin da zai iya biyo wa baya bayan abin da ya faru a Kanƙara.
Boko Haram ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin sace daliban, a wani saƙon bidiyo da shugaban ƙungiyar ya fitar, ko da yake gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya musanta iƙirarin na Boko Haram.

Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya Aminu Bello Masari ya ce sun san inda aka ɓoye ɗaliban makarant...
17/12/2020

Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya Aminu Bello Masari ya ce sun san inda aka ɓoye ɗaliban makarantar sakandaren kimiyya ta maza ta Ƙanƙara da aka sace ranar Juma'ar da ta gabata.
Ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa ranar Laraba inda ya ce a halin yanzu suna da kyakkyawan yakini da bayanin inda yaran suke.
Gwamnan ya ce a yanzu haka bayanai sun nuna cewa yaran suna cikin dajin jihar Zamfara, "kuma ko ba dukkansu ba to mafi rinjayensu dai suna can wajen."
Ya ƙara da cewa a yanzu ƙoƙarin da gwamnati ke yi shi ne na a karɓo yaran ba tare da an yi amfani da bakin bindiga ba saboda kar a ji wa wsu rauni ko a kashe wasu bisa tsautsayi.
"A yanzu haka jami'an tsaro sun zagaye dukkan waɗannan wurare da ake zaton yaran suna can," in ji Masari.
Tun da farko dai gwamnatin jihar Katsinan ta ce yara 333 ne suke hannun ƴan bindigar da s**a sace su ranar Juma'a da daddaren, a garin Ƙanƙaran da ke kusa da dajin Rugu da ya yi ƙaurin suna wajen zama maɓoyar ƴan fashin da s**a addabi jihar Katsina da maƙwabtanta.
Amma wasu kafofin suna cewa yawan yaran da aka sace ɗin ya haura 600, duk da cewa wasu sun samu kuɓuta a ranar da abin ya faru.
Sai dai bayan da BBC ta tambayi gwamnan iya adadin da a yanzu s**a san cewa suna hannun maharan, sai ya ce suna ci gaba da tattara bayanai daga iyayen da suke lunguna da saƙo da ake wahalar samunsu, "yanzu dai yaran za su kai daga 333 zuwa 400.
"Saboda akwai yaran da aka tabbatar da cewa suna makarantar k**ar 867 a lokacin inda a yanzu 465 suke tare da iyayensu, wasu kuma suna hannun hukumar makaranta.
"Sannan ga sauran iyaye da ba za su iya zuwa Ƙanƙara ba an buɗe ofisoshi a kowace karamar hukuma ta jihar da za su iya zuwa su bayar da lambarsu da sunan ƴaƴansu, ta haka ne za mu iya tantance yawan yaran da suke hannun ƴan ta'addan."

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa manyan jami'anta 26 sun kamu da cutar korona.Sanarwar da daraktan watsa laba...
15/12/2020

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa manyan jami'anta 26 sun kamu da cutar korona.

Sanarwar da daraktan watsa labaran rundunar Kanar Sagir Musa ya fitar ta ce gwajin da aka yi musu ne ya nuna cewa sun kamu da cutar.

Amma wasu rahotanni sun nuna cewa a cikinsu har da janar-janar 18.

Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaya daga cikinsu, Manjo Janar JO Irefin wanda shi ne kwamandan bataliya ta 6 da ke birnin Fatalwal, ya sanar da cewa yana fama da zazzabi da tari a ranar da aka yi taron ƙaddamar da sashen yaƙi da laifukan intanet na rundunar, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya halarta ta bidiyo a ranar 7 ga watan Disamban 2020.a lokacin ne aka ɗauke shi zuwa asibitin soji rundunar sojin Najeriya da ke Fatakwal, daga bisani kuma a ranar Laraba 8 ga watan Disamba aka ɗauki samfurinsa domin yin gwajin cutar korona.

A dai wannan rana ce kuma sak**akon gwajin ya nuna cewa yana ɗauke da cutar ta korona, domin haka ne aka kai shi cibiyar killace wadanda s**a kamu da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin ƙasar.

Sanarwar rundunar ta ƙara da cewa bayan da sak**akon Janar din ya nuna cewa yana dauke da cutar korona, babban hafsan sojin kasa na Najeriya ya bayar da umarnin dakatar da taron, sannan dukkanin waɗanda ke halartar shi su kebe kansu, bisa ka'idar dokokin Najeriya na yaki da cutar korona.

Ta ƙara da cewa an yi wa manyan jami'an rundunar soji 417 daga cikin mahalarta taron gwaji zuwa yanzu, sannan sak**akon 26 daga cikinsu ya nuna cewa sun kamu da cutar korona cikinsu har da janar 18.

Boko Haram ta ƙone gari ta kashe mutum 27 a NijarƘungiyar Boko Haram ta kai wani mummunan hari a yankin Diffa kudu maso ...
15/12/2020

Boko Haram ta ƙone gari ta kashe mutum 27 a Nijar
Ƙungiyar Boko Haram ta kai wani mummunan hari a yankin Diffa kudu maso gabashin Nijar inda ta kashe aƙalla mutum 27.

Ƙungiyar ta kuma ƙone ɗaruruwan gidaje da kasuwa da motoci a harin da ta kai da ta shafe sa'a uku a a ƙauyen Toumour a tsakanin daren Asabar zuwa Lahadi.

Mutane da dama ne aka ƙone bayan cinna wa gidajensu wuta, kuma da dama sun ɓata sun shiga daji.

An kai harin ne yayin da ƙasar ke shirin zaɓen ƙananan hukumomi a ranar Lahadi.Bayanai sun ce tsakanin gida 800 zuwa 1,000 aka ƙone. Mayakan sun kuma kashe mutane bayan buɗe masu wuta.
Wani jami'i a yankin ya ce mayaƙan kimanin 70 ne s**a abka wa garin na Toumour da yamma.

Kuma sun fara kai hari ne a gidan mai gari, wanda Allah ya ba shi sa'ar tserewa.

Jami'in ya ce kusan kashi 60 na gidajen garin aka ƙone.

Yankin Diffa na Nijar da ke makwabtaka da jihar Borno ta Najeriya ya sha fama da hare-haren Boko Haram, kuma bayanai sun ce mayakan sun ƙetara tafkin Chadi ne s**a kai harin na ranar Asabar.

Address

Gida Dubu YA
Dutse

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa cloud 5 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa cloud 5:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Dutse

Show All