29/10/2022
Immortal JellyFish, halittar da ba ta mutuwa, sai dai idan an kashe ta.
Kamar yanda na karanta bayanan wannan halitta mai suna Jellyfish, halitta ce a cikin jinsin Turritopsis, sannan nau'in stingray ne. Ana samun wannan halitta ne a cikin Kogin Rum, da Japan. An gano ta ne tun a shekarar 1883, tun daga wancan lokaci bayanan wannan halitta sun ja hankali, musamman da aka gano ta a matsayin ɗaya daga cikin halittu masu juriya a kowane irin mawuyacin yanayi.
Wannan nau'in halitta, ba sa mutuwa sai dai idan kashe su aka yi, wato idan ba kashe su aka yi ba, to zasu rayu ne har abada. Ana ƙyanƙyashe nau'in wannan halittu ne har su girma su kai matakin balaga k**ar sauran halittu, amma maimakon su mutu a matakin samartaka ko tsufa, sai dai su sake komawa tamkar jariri, su fara sabuwar rayuwa. Sai dai kuma bincike ya tabbatar da cewa basu da kariya daga kowace irin barazana musamman daga manyan halittun cikin ruwa.
Matakin rayuwar wannan halitta yana farawa ne daga ƙwai, idan aka ƙyanƙyashe su sai su zama ƙaramar tsutsa me ninƙaya da aka fi sani a ilimin halitta da Planula, sai suyi iyo har sai sun kai ga can ƙasan teku, anan suke girma har su zama balagaggu cikin makwanni, saboda canjin ƙwayoyin halitta da suke samu daga Polyp. Waɗannan halittu suna cin ƙananan halittu irin su Tsutsa da ƙwan kifi. Jikinsu yana da laushi, girmansu baya wuce 4.5mm (inci 0.18), suna kuma da ƙwarewar rayuwa ta ban mamaki, musamman idan aka yi la'akari da ƙanƙantar su, da kuma inda suke rayuwa.
Allahu Akbar! Haƙiƙa Allah maɗaukakin Sarki shi ne gwanin halitta, hikimar sa da buwayar sa sun wuce duk tunanin mu. To muna roƙon Sa da ya ci gaba da tabbatar da mu akan tafarki madaidaici, Amin.
Imran Abubakar Adam Yalo